← Book details Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 92

Sashe 34

Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko da yaushe Ammah za ta kirata tana tambayanta yadda take sai ta ce suna lafiya haka ma Baffa, har Hamma Abdulrrahman sai da ya kirata yana mata jan ido da cewa Baffa ya faɗa masa an samu masalaha yana ta jan ta mganar cewa in Habib bai daina maganar zubar da ciki ba kar ta ɓoye masa ta faɗa masa shi zai tsaya mata, amma ta ce komai lafiya bayan sum gama waya ta yi ta kuka, da ma a ce za ta iya da ta faɗa masa komai amma ba za ta iya ba suna zaman su lafiya ba za ta zama silan matsala da damuwa ga iyayenta da ƴanuwanta ba. Tun tana jin Habib a ranta har ta daina jin sa kwata-kwata ya tozarta ta ya ci mutumcin ta, ta koma sai ta fita ta siyo dan abin da za ta ci kuɗaɗe ne a hannunta sama da dubu ɗari amma sai da suka ƙare a wajen ciyar da kanta da zuwa asibiti, tunda ta sake komawa cikin ta har ya shiga wattani uku sannan ga shi likita ya ce jininta ya yi ƙasa tana ɓukatar cin ganyayyaki saboda inganta lafiyanta da abin da ke cikin ta, ba saboda kanta ba saboda gudun jinin dake tare da ita, shi take so domin duk halin da ta faɗa saboda kare shi da ta yi ne shi ya sa nan duniya babu abin da take so da ƙoƙarin karewa sai cikin jikinta. Kuma a haka dare na yi Habib zai zo ya biya buƙatar shi da ita ko a jikinsa. Tabbas saboda jikinta ya aure ta, kuma yana moran abin shi son ran shi, Ummu ta gama sakawa a ranta jikin ta ne kuma da man Habib ya kusa kai sa zuwa ga expearing date ɗin shi, gwara ta bar masa komai ya ƙarisa shi tundaa shi ya fara.

Baɗɗo ba ta nan ta tafi gidan kakanin ta a Mubi, Shamsiya kuma ta kwana biyu ba ta ji ta ba, ba ta kiran kowa wanda ya kira ta kuma ta yi masa ƙaryan tana lafiya. Mami ma ta kirata tana ba ta haƙurin cewa ba za su samu zuwa jimeta ba za su je Paris ita da megidanta da yara sai dai in sun dawo ko ita kaɗai za ta zo ta duba su. Sai ta ji daɗin haka domin ba za ta so wani na ta ya zo ya ganta a cikin wannan halin ba, kuma ta tabbata in Mami da diro Jimeta sai ta zo gidan ta kamar yadda ta saba abu ɗaya take yi da ke saka ta farinciki kallon girke-girke a wayanta sai ko salla da karatun Qur'ani amma Allah kaɗai ya san girman nauyin da ke cikin zuciyarta ita kaɗai ta san abin da ke muƙurƙusanta a cikin zuciyarta ƙarfin imani ne kawai ke riƙe da ita.

****

Shafewar sama da kwanaki arba'in Ummu Salma na cikin wannan halin rayuwan Ammah ta kira ta a waya ta shaida mata zuwan Hamma Jibo tare da matarsa da yara. Sai ta yi saurin ce ma Amma za ta zo ta gaishe su, a lokacin ma ba ta da ko sisi ballanta ta yi kuÉ—in abin hawa, duk kuÉ—aÉ—en dake cikin acct É—in ta ta gama kashe su a hidimar kanta.
jiya ma waken da take dafawa ta haɗa da allaiyahu ya ƙare, kuma tun jiyan ba ta ci komai ba sai ruwan zafi kawai take sha cikinta na ɗagowa. Farkon cikin ne take laulayi ba ta iya cin abinci yanzu kuma da ta ɗan samu sauƙi tana ci ko da za ta yi amai haka likita ya ce saboda abin da ke cikin ta. Ba ta da kuɗi ta kuma rasa yadda za ta yi Allah ya dube ta a washegari Hamma Mustapha ya tura mata 10k kamar ya saka ta a aljannah haka ta ji ta kira shi tana yi masa godiya kamar za ta yi masa sujjuda.

Kuɗin sun zo mata a lokacin da take cikin matukar buƙatar su shi ya sa gari na wayewa ta shirya ta tafi kasuwa. Sai ta kwana uku ba ta sa Habib a idanuwanta ba wata rana ma ba ya kwana a gidan sai ranar da yake da buƙarar ta to tana ganin shi, shi ya sa game da fita neman abin da za ta ci da lafiyanta, in za ta fita za ta ce Allah kana gani na fita da izinin ka domin lafiyata da abin da ke cikina, sai ta saka kafarta ta fita to haka ta yi ranar ta je kasuwa ta kaso dubu takwas sauran ta dawo dasu domin ta yi na abun hawa zuwa gida gobe. Abin da ba ta sani ba tana fita ba daɗewa motar Hamma Jibo ɗauke da Matarsa Nauwara da yara suka shiga haraban gidan su, suka iske ƙofar bangarenta a rufe kuma Hamman na ta kiran wayan ta, tana ringing amma ba ta ɗagawa.

Megadi ya tambaya shi ya ba su tabbacin ta fita amma yana tunanin ba za ta daÉ—e ba sai Nauwara ta ce su zauna a mota su jira ta. Haka ko aka yi suna cikin mota suna hira Ummu Salma ta shigo gidan tana tafiya kamar za ta faÉ—i hijabi ne a jikinta amma duk wanda ya santa in dai ya ganta sai ya firgita da raman da ta yi sannan ta É—an yi duhu hasken ta ya ragu, hannunta É—auke da ledojin da ta auno shinkafa da fulawa sai wake da manja sai kayan ganye tun da yanzu ta daina cin mangyaÉ—a saboda ta fahimci in dai ta ci abincin mangyaÉ—a to ba za ta kwana lafiya ba bayan amai ta yi ta fama da tashin zuciya.

Ko kaɗan ba ta ma lura da motar dake bakin bangarenta ba, har ta nufi ƙofarta ta sauke kayan hannunta tana neman maƙulli a cikin jakar ta sai ji ta yi an kira ta kuma da sunan da aka kirata yan gidan su ne kawai ke kiranta da sunan sannan kuma ta jiyo murya kamar ta Hamma Mustapha.

"Auta."

Da sauri ta juya ba Hamma Mustapha ba ne, Hamma Jibo ne mamaki ya kamata sai da daburce.

"Hamma."

Ta faɗa cikin sauri nan da nan idanuwanta suka kawo ruwa da ta gan shi sai ta ji kamar ta warke da duka matsalolinta. Hamma Jibo ya kalli Nauwara itama ta kalle shi amma ba su yi mgana ba ya fara takawa zuwa ga Ummu sai ya ga ta kwaso gudu zuwa gare shi, ko da take gida in ya zo tana murna da ganinsa har ta zo ta riƙe mishi hannu amma ba ta taɓa faɗawa jikinsa irin na yau ba sannan lokaci ɗaya ta kece masa da kukan da ya ɗaga masa hankali.

"Hamma."

Ummu-Salma take faÉ—a cikin muryan kuka rike ta ya yi a zuciyarsa yana jin wani iri, me ya samu Ummu ne duk ta rame ta lalace haka?

ÆŠago kanta ya yi lokaci É—aya yana share mata hawaye da tafukan hannayen sa

"Ya isa haka Auta. Ya isa haka."

Ya ke faÉ—a yana sake share mata wasu hawayen da suka kwaranyo.
Nauwara na gefe ita da su Saudat duk jikinta ya yi sanyi yaran ma sun raɓe a jikinta suna kallon Babansu da Annin su, duk da yara ne amma suma sun ji wani iri fuskar su ta yi ɗif alamun damuwa.

"Me ya same ki Auta? Ko kin yi ciwo ne?

Ya faÉ—a yana kallon ta, sai ta basar da tambayan tana sakin shi wajen Nauwara ta nufa tana gaishe ta.
"Adda Nauwara ina shirin zuwa na gaishe ku ne fa."
"To ai duk ɗaya ne mu ba ga shi mun zo ba." 
Ta ba ta amsa suna gaisawa ta jawo Saudat jikinta tana yi mata fillaanci sai ta ba ta amsa itama da fillancin amma ta haÉ—a da turanci. Ummu ta yi dariya ta ba ta hannu suka tafa lokaci É—aya tana faÉ—in.
"Lalle za ku shirya da Amma yanzu."
Suka yi dariya gabaÉ—ayan su Ammi na gefe ta yi karaf ta ce itama ta yi iya fillanci Ummu ta ce ta yi mata ta ji, bayan ta tambaye ta ina su Isma'il? ganin ba ta gansu ba da yaren fillanci sai kawai Ammi ta ma yar mata da amsar tambayanta da turanci.
Da cewa suna gidan wajen Ammah.

"Ke kam Ammi za ki ko shirya da takwaran na ki kuwa ?

Ammi ta tura baki tana rantsuwan ta iya, Saudat na cewa ba ta iya ba sai kawai Ammi ta fara kuka sai da Ummu ta rumgumeta tana lallashinta. Hamma Jibo ne ya ce a waje za su cigaba da tsayuwa sannan Ummu ta tuna da suna waje ne  da sauri ta wuce gaba suka bi bayan ta, tana can ƙokarin neman maƙulli Hamma Jibo ya duƙa ya kwaso mata ledojin da ta ajiye a ƙasa.

"Auta Kasuwa kika je ne?

Ya faÉ—a lokaci É—aya yana duba ledojin hannunsa

"E Hamma."

Ta faɗa lokacin da ta ɗauko key din tana ƙoƙarin buɗe ɗakin, shi ko jikinsa ne ya yi sanyi har sake leƙa ledojin ya yi ganin abubuwan dake ciki, sai ya sake ɗagowa yana kallon Ummu lokacin da ta buɗe ɗakin tana cewa su shigo,  kallon matarsa ya yi itama ta kalle shi domin tana kusa da shi ne ta ga ƙulle ƙullen su manjan da ke ciki da shinkafa da wake da in an haɗa duka ba su wuce tiya ba.

  Sai da suka shiga falon suka zauna ita kuma ta kwashi kayanta zuwa kitchen sannan ta kawo musu ruwan a jug na famfo ne da ta siya, Hamma Jibo ya sake shan mamaki a ran shi sai yana tunanin ko dai mijin Ummu ya samu matsala ne a wajen aiki?
Nauwara ma tunanin da take yi a cikin ranta kenan amma ba ta furta ba.

"Anni ni swanwater na ke so na sha ba wannan ba"

Cewar Saudat. Da ya ke da Annni ƴa'ƴan yayyenta suke kiranta a matsayinta na ƙaramar uwa a gare su.

Ammi na jin haka itama ta ce" Anni ni kuma hollandian zan sha."
Ta faɗa da harshen turanci, Ummu ta kasa mgana ta yi wani wiƙi-wiƙi  da idanuwana duk Hamma  na lura da ita.
Chapter 34 · 0% Book details