Sashe 76
Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wattani biyu sun zo sun shafe kamar ƙiftawan ido, rayuwar dai ta cigaba da tafiya cikin godiyar Ubangiji, haka yake a bangaren Ummu Salma sai godiyar Allah an samu canji sosai daga yanayinta yanzu Ummu za ta zauna ta yi hira har da dariya, ta saki jikinta tana ƙokarin yaƙi da kaddaranta.
Duk da ba ta manta ba amma ta aro jarumta ta yafa ma rayuwarta saboda iyayenta da ƴan'uwanta, tana so ta ga farinciki a fuskokinsu kuma in dai tana son ganin haka sai ta aro ma rayuwarta farinciki, kuma da ta yi hakan ta ga canji Baffa da Ammah sun rage damuwa ganinta cikin farinciki ba abin da ke damunta ko ma yana damunta tana yaƙi da shi. Za ta fito ta yi ta nuna farinciki a fuskarta amma a zuciyarta Ubangiji ne kaɗai ya san irin ciwon da take ciki, sai dai in abin ya taso mata sai dai ta shige ɗaki ta yi ta kuka ba ta yadda ta fito sai ta wanke fuskarta.
Za ta manta amma ba da wuri haka ba domin taɓon da Habib ya yi silan saka mata a cikin zuciyarta ba mai warkewa ba ne da wuri tana tunanin nan da shekara goma wataƙila har abada ma.
A yanzu a ƙalla cikin ta ya kai kimanin wattani bakwai ne, kuma da ita da cikin jikinta duk suna cikin ƙoshin lafiya. Ba abin da za ta ce ma Iyayenta da yan'uwanta sai godiya, domin sun tsaya mata sun kula da lafiyanta da cikin da Habib ya ce ba ya so. Tana zuwa asibiti awo kuma Ummin ikki ke rakata duk lokacin da za ta je, sannan Hamma Abdullahi ke kai su sai dai in baya nan sai su hau kekenapep, su je su dawo kuma komai za a yi na laluranta kafin ma Baffa ya ba da yayyenta sun ba da ta yi komai da shi, cikin ya yi girma tsini gare shi ya yi wani ƙasa, Ummu Salma ta yi baƙi sosai ga kuraje duk sun lalata mata fuska kafafunta sun kumbura gabaɗaya dai hallitan ta ya sauya, jiki duk ya yi wani iri alamun rai na rayuwa tare da kai, Har kuma yau Habib ko wani ahalinsa ba su nemi Ummu ko iyayenta ba, su ma kuma kamar yadda Baffa ya ce ba wanda ya sake neman su, da farko Baffa Umaru ya so ya sake neman su Baffa ya ce har abada kuma shima baya fatan su neme shi nan gaba.
Ammh ba ta barinta ta yi aiki sai dai ita ce ke matsawa sai ta yi aikin tunda a asibiti an ce ta riƙa yawan motsa jikinta girman cikin ya sa kowa ke tunanin namiji za ta haifa, kuma ko a scanning ɗin da ta yi namiji ya nuna amma ita ba ta damu ba ita dai a koda yaushe fatan ta ta sauka lafiya namiji ko mace duk wanda Allah ya bata tana so, domin bayan cikin ba ta da wani abu na rayuwarta da ya yi mata saura, sannan ba ta zuwa ko'ina daga asibiti sai gida ko kwanaki Umma Salamatu ta aurar da Autarta Ammah ta so sai ta je bikin nan wai in ta ga y'anuwa za ta sake sosai ita ko ba ta son zuwa ko'ina ba, ba ta so ta je ana kallonta ana nuna ta cikin tausayi ana cewa Allah Sarki shi ya sa ta ce ba za ta je ba Baffa kuma ya goya mata baya sai dai Ammah ce ta je aka yi biki ta dawo.
Ko a anguwa an gama yawo da maganar an hakura tunda da dawowar Ummu yanzu wajen wata biyar kenan tuni zukata sun haƙura.
Komai na bukatar haihuwa Mami ta siya mata kaya masu kyau da yarari, domin ta ce duk abin da Ummu za ta haifa ita ce uwarsa da ubansa. Wasu kayan ma duk yan waje ne Mami ta siya mata kwanaki ma da suka je London ta siyo mata wasu kayan yara masu kyau sannan itama ta zo mata da dogayen riguna masu kyau sama da kala biyar tunda yanzu su take sawa kayanta duk sun yi mata kaÉ—an, balle ma tunda ta dawo gida ta daina amfani da kayan lefen Habibu kayanta tun na gida take sawa kuma yanzu ba sa shiganta sai dogayen rigunan da Mami ta siya mata take bumjumawa a cikin gida sannan atamfan wajen Hamma LamiÉ—o da Ammah ta ba ta ta raba shi uku duk ta yi zannuwa faya tana É—aurawa a gida biyun kuma suna cikin É—an kit É—in kayan haihuwan da Mami ta yo mata.
Ba mai zuwa wajenta sai Baɗɗo Shamsiya ma ta ja baya da ita ba ta san dalili ba. Sun daina waya kamar yadda suke a baya sannan tun bayan dawowanta gida sau uku ta zo, na ukun ma cingham da minti ta kawo mata wai an saka ranar aurenta ta daɗe tana faman mamaki, ita dai kamar yadda Shamsiyan ta faɗa mata gidan su ba ka yin aure sai ka yi Degree ka yi bautar ƙasa kuma haka ne tunda duk yayyen Shamsiyan ba wacce ta yi aure tana cikin karatu sai da suka gama, amma za ki iya ɗora karatunki na gaba a gidan mijin ki, amma sai ga shi ita tana aji uku ne ma a lokacin amma za ta yi aure sannan ƙarin mamakinta ba ta san Bestie na da wani saurayi ba, saboda dokar gidan su amma sai ga shi ta kawo mata mintin saka rana, sannan ita ko a labari ba ta taba faɗa mata ta samu miji ba, da Ummun Salma ta yi mata ƙorafin ta samu miji amma tana ƙawarta na kusa da ita ba ta sani ba?
Sai ta ce ta yi hakuri ganin tana cikin damuwa shi ya sa ba ta faÉ—a mata ba, kuma ba su daÉ—e da haÉ—uwa da mutumin ba.
Har tambayanta ta yi ya aka yi mahaifinta ya amince ta yi aure ba ta gama makaranta ba.? Sai da Shamsiyar ta yi wata bazawaarar dariya kafin ta ce dangin mahaifiyarta ne suka shige mata gaba, sannan shima mahaifin na su yana sonta saboda maraicinta shi ya sa ya yi mata abin da take so. Ummu ta yi mata fatan alheri da cewa ta bi dai a hankali domin yanzu maza ba a gane musu sai ka shiga kuma zence ya sha bambam.
"Bestie ki kwantar da hankalinki. Sweety yana sona, ni ce kusan rayuwarsa nima kuma shi ne rayuwata. Kuma ki cire ma kanki tunanin wai don ke ba ki yi sa'ar aure ba ki yi tunanin koma ba zai yi sa'a ba. Ke dai kawai ba ki yi dace ba ki bar shi a haka amma ni na san abin da na zaɓa ina mai bakin tabbacin na yi kyakyawan zaɓi kuma na yi dace.".
Kalamanta su ɗan yi ma Ummu tsauri amma ba ta nuna mata ba, ta yi mata fatan alheri da ta tambayan ta yaushe ne lokacin bikin! Sai ta ce ba a saka date ba amma in an sanya za ta faɗa mata har Ummu ta yi fatan cewa Allah ya sa lokacin ta haihu yadda za ta samu zuwa, domin ko ta daina fita ba za ta ƙi zuwa bikin Shamsiya da Baɗɗo ba su ne suka yi mata komai a nata bikin da Habib.
Ko BaÉ—É—o da ta zo Ummu ta faÉ—a mata an sanya ma Shamsiya ranar aure sai da itama mamaki ya kamata har sai da ta maganta da cewa ita da ta ce a dokar gidansu sai ka gama Jami'a za ka yi aure, nan fa Ummu ta karanta mata abin da ta ce mata bayan itama ta yi mata wannan tambayar.
"Tab. Ni ko ta ba ni mamaki duk yadda kuke bai kamata a ce sai dai ta zo kawo miki minti ba."
A lokacin Ummu shuru ta yi ba ta yi magana ba, BaÉ—É—o ta yi ta faÉ—a tana cewa Shamsiyar ta sauya tunda Ummun ta dawo gida.
"Ko saboda yanzu kin yi aure kin fito shi ya sa ta ja baya dake?
"Kin san tana makaranta, ba ta samun lokaci."
Daƙyar Ummu ta samu Baɗɗo ta bar maganar saboda kar Ammah ta ji daman da ta ce mata an sanya ma Shamsiyar ranar aure ga ma mintin da ta kawo mata nan ta nuna mata taɓe baki ta yi ta ce shi ya kawo ta kenan? Domin ita Ammah ta ce tun maganganun da ta ji tana yi yarinyar ta fita zuciyarta.
Ita kanta Ummun ta san alaqar su da Shamsiya ta ja baya kuma kamar Shamsiyan ne ke gudunta tunda ita tana kiranta amna ba ta ɗauka, sai a yi kwana huɗu sama da sati sannan za ta kirata da cewa karatu ya yi zafi shi ya sa ba ta samun lokaci itama daga baya da ta ga haka sai ta kama kanta amma ranar ta yi kuka, yau ace mutane sun fara gudunka saboda kaddara ta faɗa maka, tana tuna a baya yadda kowa ke haba haba da ita saboda tana gidan mijinta yanzu kuma duk abin da take tunanin ta samu sai da Habib ya dawo da ita baya ba ta da komai a rayuwarta in ta tuna yadda rayuwarta ta sauya lokaci ɗaya sai ta yi kuka sosai, har kuma yau yana nan a cikin zuciyarta duk da tana ta addu'an Allah ya cire mata tunanin shi da soyayyarsa a cikin zuciyanta. Tana ta samun sauƙi amma kuma bai fita duka ba, ta dai dangana ta kuma aminta da cewa wataƙila Habib ya yi nisan da ba zai taɓa dawo gare ta ba.