Sashe 59
Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Allah ya kyauta na gaba. Allah ya saka mata."
Baffa ya amsa da Amin yana faÉ—in" Ya za a yi da lamarin da Ubangiji ya hukunta kenan. Zai wuce in sha Allahu."
Da za ta tafi ya yi ta mata addu'an Allah ya kawo mata miji na gari mai albarka nagartattace. Domin duk wanda ya san Ummu Salma a dangi ya san ta da ƙawarta Shamsiya tun suna yara. Kamar yadda aka san Shamsiya a gidan su Ummu haka aka san Ummu Salma a gidan su Shamsiya duk da mahaifiyarta ta rasu tun tana ƙarama matar mahaifinta da suke kira Anty ke riƙonta.
Da za ta tafi bayan ta yi ma Ammah sallama ta ce ta gaida mutanen gidan.
"Ammah don Allah ki yi haƙuri da maganganun da na yi ɗazu ba ki fahimce ni ba ne ba da wata manufa na yi maganar ba na damu da abin da ya faru da Ummu Salma sosai Ammah."
Shamsiya ta faɗa bayan ta duƙa har kasa a gaban Ammah.
Ammah ta yi mirmishin su manya kafin ta ce" Kar ki damu na fahimce ki. Ki gaida gida mun gode."
Har haraba Ummu Salma ta raka ta. Direban gidan su da ya saba kawo ta shi ne ya zo É—aukan ta.
Sai da suka tafi sannan Ummu dawo cikin gida ta iske Ammah na zaune a falonta kamar yadda suka bar ta.
"Har ta tafi?
Ammah ta tambaya tana kallon Autar na ta
"E ta tafi Ammah."
Ta faÉ—a a sanyaye cikin dashewar murya kamar ba ta son magana. Sai Ammah ta É—an gyaÉ—a kanta amma ba ta yi magana ba.
Shuru na wani lokaci Ummu na tsaye ita ba ta koma ɗaki ba sannan ita ba ta zauna ba Ammah na lura da ita amma ba ta nuna alamun ta fahimci tsayuwarta a wajen ba sai ma ta yi kamar hankalinta na wajen tibin da yake ta ɓaɓatu. Nan ko tana lura da duk motsin Ummun, tana kare mata kallo daga tsaye har cikinta ga shi nan ya fara turowa ta cikin doguwar rigar dake jikinta amma fa Ummu ta zube ta rame duk ta lalace kullum sai jan fuska da kumburarrun idanuwana saboda kuka, tausayinta take ji in ta kalleta sai ta tsine ma Habibu tsinuwar da ba ta so ya koma ga Allah bai ga sakayya tun a duniya ba.
"Ammah."
Ummu Salma ta kira sunan Ammah, ba ta amsa ba amma ta É—ago tana kallon ta.
Sai kuma ta yi shuru ta kasa magana.
"Me ya faru?
Ammah ta tambaya tana mai tsare ta da idanuwanta lura da cewa kamar akwai magana a bakin ta.
"Da ma Ammah.."
Sai ta yi shuru ta kasa mgana.
"Dama mene ne? Wani abu kike so?
Ammah ta tambayeta cikin kulawa.
"Aa dama mganar da kika ji Shamsiya na yi ne."
"Uhm sai aka yi ya ya?
Ammah ta faÉ—a har lokacin ba ta daina kallon ta ba.
Sai Ummu ta daburce kafin ta fara mgana tana in da in da.
"Da ma, zan ce ne kar ki ji haushin ta, ba da wata manufa ta faÉ—i haka ba."
"Madallah."
Ammah ta yi saurin katse Ummu Salma saboda ba ta son ma tana tuna mganganun yarinyar suna kona mata rai, suna sakawa tana jin kamar yarinyar za ta fita daga zuciyarta. Ta so ma ta ce mata in saboda su ko Ummu take kiran Habibu to kar ta sake sai kuma ta ga kamar ta yi tsauri da yawa shi ya sa ba ta yi maganar ba, amma sam maganganun yarinyar ba tausayawa ga halin Ummu ke ciki sam.
Ummu Salma ta gaji da tsayuwa, ganin Ammah ta yi mata banza daga ƙarshe ma cikin ɗakinta ta shiga ta ce za ta yi salla dole itama ta koma ciki ta shiga tiolet ta ɗauro alwala ta zo ta tayar da salla. Bayan ta idar sai ga Baffa da Hamma Saddam sun shigo falon Ammah, sai ta fita falon ta duƙa ta gaishe da Baffan tun da tun safe sai yanzu suka sake samun zama
"Auta ya karfin jikin?
Kanta na ƙasa tana sanye da hijabinta dogo da ta yi salla da shi ta amsa cikin sanyin murya.
"Na ji sauƙi Baffa."
"Kin tabbata ba in da ke yi miki ciwo?
Sai ta gyaÉ—a kanta sannan ta amsa da cewa ba in da ke yi mata ciwo.
"To Baffa ka tambayeta tana cin abinci?
Hamma Saddam ya faÉ—a yana yar dariya, da a baya ne harara zai sha a wajen Ummun amma yau kallon shi kawai ta yi ba tare da ta yi magana ba.
"Tana ci mana ko Auta?
Ya tambaya yana kallon ta.
"Ina ci Baffa, yau ma ba ka ga taliyan da na ci ba."
Ta faÉ—a da É—an mirmishi. Sai ta ga Baffa na dariyan jin daÉ—i da man abin da take son gani kenan.
"Madalla da Auta. Sannun kin ji? Allah ya raba ki da cikin jikin ki lafiya."
Kanta na ƙasa ta amsa da Amin a cikin zuciyarta, sai dai idanuwanta sun cika da kwallar tausayin kanta da na iyayenta.
"To gwara dai ki riƙa ci Ummu ko za ki yi kumari, kin gan ki kuwa? Kin ga ƙasusuwan da ke wuyan ki kuwa?
Ya faɗa yana yar dariya cikin zolaya sai a lokacin ta ɗan murmusa kanta na ƙasa.
"Kyale shi Auta. Za ki yi kiba har sai ya ce ki bar ta yi yawa."
Ita dai kanta na ƙasa tana wasa da gefen hijabinta. Baffa da Hamma Saddam suna ta hiran su, lokaci bayan lokaci suna ɗan sako ta a ciki koda ba za ta yi magana ba har Ammah ta idar da salla ta fito suka cigaba da hiran tare.
"Yaushe hutun na ku zai ƙare ne Saddam?
Baffa ya tambaye shi, kai tsaye ya ce sati na sama za su koma zai bari sai upper week sannan zai koma makaranta. Baffa da Ammah suka yi masa fatan alherin da suka saba a koda yaushe suna nan zaune suna hira har aka kira sallar isha'i Baffa da Saddam suka tafi masallaci itama Ammah ta shiga ciki domin ta gabatar da na ta, sai ita ma Ummu Salma ta tashi ta koma ciki tana da alwalanta ta tayar da salla.
Bayan ta idar ta fita tsakar gida zuwa kitchen ta zubo taliya ta ciko miya saboda cikinta kamar an yi yasa yanzu tana yawan jin yunwa sosai ba kamar baya ba.
Tas kuma ta cinye tana suɗan kwano, har Hamma Saddam na yi mata dariya Baffa ya ce in bai isheta ba ta je ta ƙaro ta ce ta koshi da yake a falon Ammah ta zauna tana cin taliya su kuma suna dawowa masallaci nan suka sake yada zango.
 Har wajen goma na dare tana falon tare da su Baffa suna ta hira, ita dai ba ta magana amma kuma zama cikin su yana rage mata damuwa da shiga tunani da ɗaki take shigewa zuwan Mami ne yasa dolenta ta fara fitowa falo. Sai da ta fara hamma wajen sha ɗaya saura na dare sannan Baffa ya ce ta je ta kwanta Hamma Saddam ma ya yi musu sai da safe ya wuce ɗakin sa. Ummu kuma bakin ta kawai ta wanke ta sha magungunanta ta kwanta ba daɗewa sai barci.
Haka dai rayuwar ta cigaba da tafiya da daɗi ba daɗi. A bangaren Ummu Salma rayuwa ba daɗi amma tunda ita musulma ce ta yarda da kaddara kuma tunda tana da rai da lafiya dole za ta cigaba da rayuwa a hakan nan, ta ɗan rage kuka yanzu amma duk lokacin da ta tuna sai ta koka ita kaɗai a ɗaki ta yi kukanta har sai ta ƙoshi sannan ta share hawayenta ta dangana tunda ba ita isa ta mayar da hannun agogo baya ba. Mai afkuwa ta afku ba ta kuma da yadda za ta yi ta gyara abubuwan da suka riga suka lalace tun daga farko.
Har yau kuma Ummu ba ta bi ta kan wayarta ba, tana nan a kashe a cikin kayanta. Duk wanda zai yi magana da ita sai dai ta wayar Ammah. Baɗɗo ce ta ce ta ɗauko wayar ta dawo amfani da ita wataƙila za ta deɓe mata kewa, amma ina ba za ta iya sake amfani da wannan wayar ba matuƙar akwai abubuwa da dama da za su iya tuna mata da Habib da irin rayuwar da suka yi mai daɗi a baya shi ya sa ba ta jin za ta iya amfani da wayar a yanzu in ma za ta yi amfani da waya sai dai sabuwar waya da sabon layin da ba zai tuna mata da komai ba.
In ta zauna tana tunanin farkon rayuwarta da Habib har zuwa ranar ƙarshe da komai ya ƙare. Sai ta ji da man ace ba ta san shi ba, domin sanin shi bai ƙare rayuwarta da komai ba sai ci baya. Ya shigo rayuwarta domin ya lalata mata gobenta kuma ya yi nasara. me take yi haka? me ya sa ta kasa tsanar Habib? me ya sa ta kasa mantawa da shi? me ya rage mata, ba ta da komai domin bai bar ta ba sai da ya ƙwace duka martabanta ya lalata mata rayuwarta ya juya baya ga gudan jinin su? me ya sa ba za ta yanke tsammani ba, ba ta da wani abu da zai sake jan hankalin wani namiji a kanta HABIB ya riga da ya lalata duk wani ƙwanjinta akan ko wani namiji a duniyar nan.
****
* SATURDAY:MURIVILL HOTEL YOLA, ADAMAWA OFF GIREI ROAD.
ROOM:226.
*8:21Pm*
Habib ne tsaye a gaban madubin dake É—akin Hotel É—in da ya zama gidan shi a halin yanzu tun bayan rabuwar su da Ummu Salma.
Turare yake fesawa bayan ya gama ya ɗauko wata hula baƙar dara ya ɗora saman sumar kansa da ta sha gyara tunda ya ɗan tara suma. Jikinsa kuma wata farar shadda ce tana maiƙo da yarari daga ganin ta ma sabuwa ce yau ya taɓa sakata saboda yadda take maiƙon sabunta.