Sashe 61
Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya faÉ—a yana mirmishi.
Daga can bangaren aka ce.
"Na ga zuwan ka, ina sama ina hangen ka a cikin mota."
Jin abin da ta ce ne ya sa ya É—aga kai yana kallon saman, dai dai lokacin da aka saki labule aka juya. Mirmishi ya yi zuciyarsa har wani rawa rawa take yi saboda yadda yake daraja wannan ranar.
*Janafty*
*FARGAR JAJI.*
*Wattpad:JamilaUmar315*
*Arewabooks:JamilaUmarJanafty*
"To Hajiya Hauwa'u Inuwa Aminu (Anty Hairi) with love and gratitude"
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/L6zUax648eTERbvw8Bqyie?mode=gi_t
*15*
*DUALA ROAD. APAPA LAGOS NIGERIA*
*NO:447.*
Teusday, 2:30pm.
Wata baƙar mota ƙiran TOYOTA(PRIUS) ta fito daga General Hospital dake Apapa Lagos (C9R9+QG7 Abaraham adesanya road) da misalin ƙarfe biyu da rabi na ranar talata gabaɗaya gilasan motan tintec ne shi ya sa ba lalle na waje ya iya ganin na ciki ba. Gudu motar ta yi ta shararawa a kan shararen titunan da ke Apapa na garin Lagos ba daɗewa sai ga shi motar ta iso anguwan Duala road a bakin wani katafaren gida mai blue ɗin get lambar gidan 447.
Hon motar ta yi ba ɓata lokaci kawai get ɗin gidan ya wangale motar ta sulala cikin haraban gidan, kusa da wata mota itama kirar toyota amma camry dake fake a haraban gidan motar ta tsaya.
Daga can cikin parking space kuma akwai wata ɓakar RAVA ita ma ƙirar Toyota.
Yanayin parking É—in da ta yi ba ta daidaita tsayuwar motar ba
Da gudu bayarben megadin tare da wani matashi suka rugo a guje har suna bangazan juna wajen buɗe murfin motan sannan bayan sun buɗe suka rankwafar da kawunansu a ƙasa a tare suka haɗa baki wajen faɗin.
"Welcome Mah."
Haka suke faɗa, kuma ba su daina faɗa ba, sannan wacce suke kira da Mah ɗin har a lokacin ba ta sauko daga motar ba, sai da tafi mintina goma sannan kafaarta ɗaya ta fara saukowa farar kafa da wani takalmi mai igiya baki hill mai tsini sannan ta sake sauko da ɗayan kafar nan ma sai da ta ɓata lokaci kafin jikinta da ita kanta su bayyana a waje.
Farar mace ce doguwa mai kaurin jiki jikinta sanye da riga da wando suit na mata masu ruwan toka, wondon yana da buɗewa ta ƙasa, saman rigar jikinta rigan likitoci ne, a jikin ɗan wani anini da ke jikin rigan an rubuta DR. BILKISU BAYERO.
Sannan kanta ta yane shi da wani baƙin mayafi mai santsi idanuwanta ɓoye cikin wani baƙin glass. Kyakyawa ce domin fuskarta doguwa ce ga dogon hancin ta har baƙa yanayin fuskarta ba wani fara'a, hannunta riƙe da jakarta na hannu ƙarama baka yatsunta sanye da zabban gold guda biyu masu kyau da tsari.
Taku ta fara yi cikin taƙama da isa kamar yadda ya zame mata jiki da daɓi'a, ko kallon ma'aikatan da suke rankwafe suna yi mata sannu da zuwa ba ta yi ba ta yi wucewarta ta nufi wata ƙofa babba mai kyau da tsari sai da ta saka password sannan kofar ta buɗe ta shige kuma ta rufe kanta, sai da ta ɓace ma ganin su sannan Maigadi Baban Adila ya koma wajen aikin shi da sauri ya yin da James mai kula da tsaftan haraban gidan sannan kuma shi driver ne shi ke kai yara makaranta ko ya kaisu wajen wassani ko kuma in fita ya kama ma'aikatan gidan, Uwar ɗakin na su ba kodayaushe take yadda a tukata ba ita ke tuka kanta wani lokacin Megidan kuma ba mazauni ba ne, in ma ya dawo ba ya fita ko'ina in kuma fita ta kama shi ba na kusa ba sai dai na nesan da filin jirgi kawai ake kai shi.
Shi ya tsaya ya shiga cikin motar ya gyara parking É—in sannan ya ciro makullin É—in lokaci É—aya yana fitowa ya kuma rufe motar.
Ita kuma tana shiga makeken falon gidan mai ɗauke da kayattatun kujeru saiti biyu, sallaman ma da ta yi a ciki- ciki ta yi amma ƙaran tsinin takalminta ya bayyana shigowarta falon yan aikin ta suka rugo zuwa gare ta.
Sabuwa wata yar dattajiuwa ta karɓi jakar hannunta sannan ta duƙa tana faɗin" Barka da dawowa Uwar ɗakina."
Hadiya kuma yar yarinya ce matashiya itama duƙawa ta yi tana faɗin" Barka da dawowa ranki ya daɗe."
Ma'aikatan cikin gida huɗu ne Sabuwa da Hadiya daga masaautarsu ta taho da su tun auranta da Lamiɗo aka ba ta su, sai Anitha da Debora anan garin ta ɗauke su, Anitha ce mai kula da Sultan da Beena duk abin da ya danganci abincin da za su ci, kwanciyar su ta shin su, aikin makaranta da shirya su komai da komai dai yana sarƙe a wuyan ta ne,
Karatu na musamman ta yi
akan sanin kula da yara.
Ita kuma Debora mai kula da girkin gidan gabaÉ—aya cikakkiyar Chef ce da ta karanci nau'in girki a jami'a ita ce ke da alhakin kula da duka wani abinci a gidan.
Sabuwa kuma amintattaciyar hidiman Dr. Balkisu ce, duk wani abu da ya shafe ta yana wuyan Sabuwa ne, gyaran É—akin ta gyaran kayan ta, cin abincin ta da duk wani abu da za ta bukata Sabuwa ke kula da shi, ita kuma Hidaya ita ce mai kula da share share duka gidan da tsabtace ko'ina har É—akin mai gidan ita ke da alhakin tsabtar gidan ko'ina ya yi kal yana tashin kamshi wannan nauyin yana wuyan ta ne.
Har ta zauna a saman ɗaya daga cikin kujerun falon ba ta amsa musu gaisuwar su ba. Debora ce ta ɗibo ruwa mai sanyi daga despenser a wani kofin tangaran mai kyau da tsada ta kuma ɗora shi saman wani kyakyawan faranti mai kyau ɗan caras da shi. Shi ta kawo mata bayan ta rankwafa ta miƙa mata tana faɗin" Welcome Mah."
Sai da ta yi kamar ba za ta miƙo hannu ba sannan ta mika ta karɓa ta ɗan kurɓa kaɗan ta miƙa mata da sauri ta tashi cikin girmamawa ta bar falon.
Da kai kawai ta amsa ma Hidaya da Anitha da ke faman gaishe ta sannan ta É—aga musu hannu alamun su watse, ba sai ta yi magana ba zaman su da ita na tsawon shekaru uku ko sama da haka ba sai ta yi magana ba sun san abin da take nufi.
Sabuwa ce kawai ta rage a wajen itama tana jiran uwar ɗakin nata ne, sai da ta gama zamanta shuru kawai idanuwanta a lumshe tana ɗan hutaawa sannan ta miƙe da sauri Sabuwa ta rigata mikewa ta yi gaba da sauri wani korido suka shiga, Sabuwa ta buɗe wata ƙofa tana biye da ita a baya suka bayyana a wani ƙaramin falo kayattace. Nan ɗin ma ba su tsaya ba wata ƙofa Sabuwa ta sake buɗewa sai ga su a wani babban bedroom mai ɗauke da gado wanda ya ji shimfiɗun alfarma da wawaken wardrope daƙin very neat, sannan yana tashin wani ƙamshi mai daɗi ga wani sanyi sanyi mai shiga ƙashi yana saka natsuwa da jin daɗi.
komai dai na cikin muhallinsa tana shigowa a gefen gado ta zauna lokaci ɗaya tana warware mayafin da ta yane kanta da shi, ita kuma Sabuwa sai ta isa ma'ajiyar jakunkunanta ga su nan a jikin wani ɗan katako dogo sama da guda ashirin ta ajiyeta a muhallinta sannan ta koma da sauri ta duka a gabanta ta cire mata takalmin kafar nata shima ta koma ta ajiye shi a wani ɗan dirowa mai faɗi in da takalmin suke a jere resas ba adadi ga su nan kala kala iya kallon ka har ka ɓace ƙirgawa.
Sai da Sabuwa ta kwashe komai da Balkisu ta watsar a saman gadon mayafinta da jaket É—inta tare da glass É—in ido ta shiga clotheset ta mayar mata a jikin hanger sannan ta rankwafa tana faÉ—in" A fito lafiya UwarÉ—akin"
Ta faÉ—a cikin ladabi da kai ta É—an amsa mata lokaci É—aya tana É—an mikar da kafafunta a saman tattausan cafet É—in da ke malale a kasan Bedroom É—in. Alamun gajiya a tare da ita har Sabuwa ta buÉ—e kofa za ta fice Balkisu ta kira sunanta a hankali.
"Sabuwa."
Da sauri ta juyo ta dawo da gudu ta duka a gabanta tana faÉ—in" Uwar É—akina"
Ta faɗa cikin ladabi da ƙaskantar da kai kallonta ta yi na wani lokaci idanuwanta manya suna mai lumshewa suna buɗewa cikin sanyin murya ta ce" Bai fito ba?
Ta faÉ—a tana É—an sauke kallon ta akan Sabuwa.
"Bai fito ba, tunda kika fita bai fito ba UwarÉ—akina."
Sabuwa ta faÉ—a cikin ladabi, Balkisu ba ta bukatar ta yi magana ko hannu ta nuna sun san abin da take nufi
Ajiyar zuciya ta É—an sauke kafin ta ce" Na sallame ki Sabuwa zan huta"
Ta faɗa cikin sanyin murya kasa ƙasa kamar ba ta son yin magana
"To to a huta lafiya Uwar É—akina."
Tana gama faɗin haka ta miƙe da sauri ta fice lokaci ɗaya tana rufo ƙofar saboda Uwar ɗakin nata ba ta son sauti ko ƙara ko hayaniya hatta ƴa'ƴanta sun san yanayin gidan duk da suke yara suna da natsuwa sai gidan ya yini tsit ba ka cin motsin kowa, kowa na bangaren shi yana gudanar da rayuwarsa suma ɗin ma'aikatan gidan suna shashen su luf, sanin masu gidan duka ba sa son hayaniya sun fi son su ji ko'ina shuru.