Sashe 74
Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Daga nan sai suka ci burki suma a katon bangaren yar Sarki jikan Sarki, matar Sarki sannan uwar Sarki.
Hajiya Raƙayya(Fulani Daura).
Fulani na da mayan ya'ya mata amma namijinta kwara É—aya ne Mai martaba Muhammad Nasiru Daura, duk da a wancan lokacin maigidanta Marigayi mai martaba tsohon Sarki yana da wata matar kafin ita mai suna Hajiya Rakiya.
Tana da É—a namiji babba amma an haife shi ba shi da lafiya daga karshe ma ya rasu bayan mahaifiyarsa ta rasu ba daÉ—ewa.
Akwai yaranta biyu yayyen Mai martaba ne da Fulanin Daura ta riƙe su.
Hajiya Kilishi ita ce babba kuma tana da sarautan(Magajiyar garin Daura) Tana kuma auren shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin katsina ne.
Sai Hajiya Balaraba(Magajiyar zama Daura) Tana auren wani babban general ne a hafsan sojan ƙasa tana zaune a garin Abuja da iyalanta.
Sai ya'yan Fulani ƙannen Mai martaba mata
Wacce ke bi ma Mai martaba Hajiya Zaliha wacce LamiÉ—o ke kira da Mahma ita ce(Magajiyar sanda mata)
Kuma tana auren madakin masarautar Zazzau ne tana can garin Zariya.
Ita ce kamar 5 and 6 na Mai martaba Sarki komai zai yi sai ya yi shawara da ita ga shi ba ta taɓa haihuwa ba shi ya sa take son Lamiɗo kamar ran ta.
Sai mai bi mata, Hajiya Zeenatu(Magajiyar Gabas)
Tana auren shugaban yan sandan na ƙasa gabaɗaya.
Sai Hajiya Zannura,(Magajiyar Yamma)
Tana auren ɗan sarkin Katsina. Sai ta ƙarshe Hajiya Binta(Magajiyar sha wata Daura)
Tana auren É—an sarkin muslmin garin sokoto ne can take zaune da iyalanta.
Fulani an tsufa amma jinin mulki na nan a jikinta ko da suka shiga tana kishigiÉ—e Sultan da Beena na jikinta kamar za ta mai da su cikin ta saboda so.
sun iske su suna ta hira da Balkisu, wacce Saleem ya rankwafa shi da Amir suka gaisheta ta amsa cikin sakewa.
"Maraba da Yarima. Maraba da Muhammadu LamiÉ—o."
Fulani take faɗa cikin farincikin da ya saka ɓoyuwa a saman fuskarta.
"Ranki ya daÉ—e ga Yariman Daura nan na kawo miki mene ne tukwaici na?
Saleem ya faÉ—a yana zama a shimfidar da take zaune.
"Na baka farin doki na Hakimin Daura."
Ta faÉ—a cikin fara'a shi ko sai ya washe baki yana faÉ—in" Hakimin Daura yana godiya. Allah ya kara tsawon kwana Fulanin Daura."
Tana son farin dokin nan ta ce gadon shi ta yi wajen babanta ba ta bari kowa ya hau in ba Mai martaba ba, amma yau ta yi masa kyautarsa saboda zuwan Yarima Lamido.
"Barka da hutawa ranki ya daÉ—e."
Lamido ya faÉ—a yana mai zama a gefenta cikin ladabi.
"Papa."
Sultan da Beena suka faÉ—a a tare ganin babansu, Saleem ne ya amsa musu yana mai jawo su jikinsu sun san shi tunda ai suna yawan zuwa in Lamido bai zo ba Balkisu na zuwa in ta samu dama.
"Lafiya lau Yarima, ya wajen su Baffan naka?
Ya amsa mata duk suna lafiya cikin girmawawa.
"Barka da zuwa Muhammadu LamiÉ—o. Masarauta ta ji daÉ—in zuwan ka"
Mirmishi kawai ya yi bai yi magana ba
Bilkisu tafiya ta yi ta bar su tare da Fulanin Daura.
Da yaran nan fa ta shiga abin da ta saba tana ta ba su labaran tarihin masarautan Daura da ya shude shi dai LamiÉ—o zaune yake amma ba ya ma jin ta, kanshi har ya fara ciwo Saleem kuma yana ta su Sultan ne Amir ne ke mata tambayoyi.
Kiran mangariba ya fitar da su daga shashen Fulani.
Da suka fita salla har wajen tara na dare Lamido na waje yana gaisawa da mutanen fada.
Goma saura na dare Lamiɗo ya shiga keɓantattacen ɗakin Mai mairtaba na cikin turakansa a shashensa.
In da za su yi ganawar da suka saba daga shi sai shi sai Allah in dai ya zo garin.
Bayan sake gaisuwa.
"Ya wajen iyayen naka na Adamawa?
Maimartaba ya tambaya yana zaune a saman wata darduman dake cikin É—akin barcinsa.
Sanye yake da jallibiya ba rawani a jikimsa sai fuskarsa ta bayyana kamar ta LamiÉ—o, sai dai ya nuna masa yarinta da cikar maza amma har yanayin maganarsu ma iri daya ne, sai dai shi Lamido fari ne yayin da Mai martaba yake da duhu amma ba baki ba ne sosai.
"Duk suna lafiya sun ce a gaishe ku."
"Muna amsawa. '
Daga nan É—akin ya yi shuru na wani lokaci.
Sai da Maimartaba ya kira sunan shi sannan ya dago.
"Muhammad Lamido."
''Allah ya taimake ka."
"Don Allah ka dinga zuwa gida akai- akai. Kar ka manta kai ne Yarima mai jiran gado, ka zo gida domin ka koyi sarauta tun kafin ta Allah ta kasance a kaina."
Mai martaba ya faÉ—a cikin wani irin amo.
Kan Lamido na kasa bai yi magana ba
"Shekaru sun gangara Lamido. Ya kamata ka yi tunani."
"Allah ya kara maka yawancin rai,"
LamiÉ—o ya faÉ—a kafin ya É—an yi shuru.
"Zan din ga zuwa"
" in sha Allahu."
Ya sake faÉ—a a rabe,
Jinjina kai Mai martaba ya yi kafin ya ce" Na ji daÉ—in haka. Allah ya yi ma rayuwarka albarka."
"Amin."
LamiÉ—o ya amsa a kasan lebensa.
"Ya wajen aikin naka?
"Alhamdulillah."
LamiÉ—o ya sake faÉ—a.
"Madallah. Ina ita iyalin naka? Ina takwara na? Ina jiran shi zan yi masa hakimi dawakin Daura nan gaba in ya sake girma."
"Allah ya taimake ka."
"Suna cikin gida,"
"Za su zo gaishe ka da safe in sha Allahu."
"Allah ya tashe mu lafiya."
Maimartaba ya faÉ—a cikin É—an mirmishi.
Sai kuma ya yi shuru.
Dakin ya yi wani tsit kamar ba kowa a ciki.
"Sultan har yanzu yaro ne"
Mirmishi Mai martaba ya yi na manya da masu sarauta yana kallon É—an na shi.
"Na ce in ya kara girma LamiÉ—o."
Ya faÉ—a yana kallon sa.
"Tuba na ke yi ranka ya daÉ—e."
"Ba ka yi laifi ba LamiÉ—o."
Ya sake faÉ—a yana kallonsa. Fuskar Batula na gilma masa.
"Ya wajen Batula?
LamiÉ—o ya dago yana kallon mahaifin na shi.
Ya san wace ce ya ke kira Batula ba kuma mamaki ya yi ba domin in dai suna magana da Mai martaba sai ya yi hiran Batula.
"Ka je wajen ta?
Ya tambaye shi cikin kulawa.
"Ban samu zuwa ba ranka ya daÉ—e."
Ya faÉ—a yana É—an sosa giran shi.
"LamiÉ—o."
Ya kira shi ya amsa.
"Allah ya ba ka nasara."
"Muhammadu."
Ya sake kiran shi a karo na biyu.
"Allah ya ba ka yawan rai."
LamiÉ—o ya sake faÉ—a cikin rusunawa.
"Ka bi Batula. Ka yi ta bin ta domin ita É—in mahaifiyarka ce."
"To in sha Allahu."
"Duk yadda za ta nuna ma duniya ba ta damu da kai da abin da ya shafe ka ba. To ka sani tana sonka. Ta fi kowa sonka."
LamiÉ—o ya yi shuru bai yi magana ba amma a zuciyarsa sai dai ya ce ba ta kai Ammah sona ba.
"Saboda ita ta haifeka. Cikin ka ta É—auka na wata tara ta yi nagudar ka ta haifeka ta kuma rene ka."
"Ammah dai ta rene ni Allah ya ba ka nasara."
Ya yi saurin katse Mai martaba.
Domin shi dai da yawon sa Ammah ya sani a komai na shi ba Mami ba.
Mirmishi Ma imartaba ya yi har tana fidda sauti.
"Saboda tana sonka ne, ta ji zafin abin da aka yi mata shi ya sa ta cire ka daga rayuwarta. Amma Batula tana sonka LamiÉ—o wata rana ko bayan raina za ka ga hakan."
"Allah ya taimake ka,.'"
LamiÉ—o ya faÉ—a sannan ya cigaba da faÉ—in.
"Ammah ce uwata ranka ya daɗe ita ce ba ta taɓa wofantar da sha'anina ba har gobe."
Shurun ya sake yi kansa na kasa kafin ya cigaba da fadin.
"Amma ban musa cewa Mami ce ta haifeni ba. Amma ni Ammah ce na sani a mahaifiyata."
Mai martaba ya sake yin mirmishi cikin kasaita kafin ya ce" Ba shakka duka uwayenka ne LamiÉ—o amma Batula ce ta haife ka "
"Tuba na ke yi ranka ya daÉ—e, in na faÉ—i wata magana ba daidai ba."
Mai martaba ya sake É—an yin mirmishi kafin ya ce" Ba ka yi laifi ba LamiÉ—o "
Sai ta sake kallon shi kafin ya ce" Magana ta shi ne kar don ba ta shiga sha'aninka kai ma ka daina shiga nata. Hakki ne a kanka, ka bita ka yi mata biyayya."
"In sha Allahu ranka ya daÉ—e."
"Allah ya yi maka albarka. Allah albarkaci zuru'anka Muhammadu LamiÉ—o "
"Amin Allah ya kara maka lafiya da yawancin kwana ranka ya daÉ—e."
Shi kan shi LamiÉ—o ba ya sanin a ina ya koyo wasu abubuwan na sarauta sai dai kawai ya samu kanshi cikin aikatawa.
Sun daÉ—e suna tattaunawa sai sha É—aya da rabi Mai martaba ya sallamesa ya koma bangarensa.
Duk ya gaji ga ciwon kai da rashin natsuwa wanka ya yi ya sha tea kawai ya kwanta ko Balkisu bai nema ba saboda gajiyar dake jikinsa rabon shi da ita tun a falon Fulani.
Washe gari ma bai samu zama ba da shi aka yi zaman fada sannan da yamma kuma ya fita cikin gari shawagi a saman doki shi da Saleem da Amir.
Ya yi ta kuma ganawa da mutane, kuÉ—i ne bai san adadin su ba ya fita da su amma duk sun kare tun daga ma'aikatan gidan da dogarai haka ya yi ta musu alheri. Lamido is a giver duk da ba shi da fara'a amma yana da kirki da kyauta.
Tun da suka zo Daura bai zauna ba, kullum yana fada ko sun fita gari gabaÉ—aya ya gaji ya takura amma ba shi da mafita ranar da suka yi kwana huÉ—u ya fita shi da Saleem da wasu dogarai a dawakai ya sha rawani da kayan sarauta yana ta gaisawa da mutane.
Washe gari kuma Balkisu da yara tare da hadimanta suka koma Lagos.
Da shi da Saleem da wasu dogarai suka kai ta filin jirgin katsina.
Ta na so ta rumgumi mijinta saboda ta yi kewarsa amma ba hali yana cikin mutane kuma a halin Lamiɗo in ta rike sa a nan shi ne kunyanta shi na farko da ta taɓa yi a rayuwarsa.