← Book details Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 92

Sashe 75

Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunda suka zo bai samu lokacinta ba sai jiya da daddare da za su yi sallama.
Mamah ma ta zo daga zaria, ba ta kwana ba ta juya sannan shi kuma ya je katsina gidan Hajiya Kilishi shi da Saleem da wasu hakiman Mai martaba daga nan suka karisa masarautar Katsina suka yi gaisuwa Hajjya Zannura ba ta kasar ta raka mijinta domin a duba lafiyansa.

Ya ji maganar Mai martaba ya nemi Mami, da man kuma Ammah ta matsa masa ya je Kaduna ya gaisheta.
Sai dai ko da ya kira ta sai ta ce ba sa nan suna Zamfara ita da megidan da ya ce ya zo ne zai zo ya gaisheta kafin ya koma sai ta ce ta yafe masa gaisuwan

Bai damu ba domin ta ma hutar da shi, sai da ya shafe kwanaki goma a Daura sannan ya samu ya komawa Jimeta.

Gabaɗaya tunda ya je Daura bai huta ba, da ya dawo Jimeta ya yi hutu sosai domin akwai ranar da tun safe har dare bai zo gida ba Ammh ta ɗaga hankalinta gashi ana ta kiran wayarsa ba ya ɗauka.  Ta kira Hamma Abdullahi sai da ya je gidan ya gano mata, lafiyansa lau kawai yana barcin gajiya ne. Sannan hankalinta ya kwanta.

Bai koma Lagos ba sai da ya yi hutun wata É—aya cur duka a haÉ—e da zuwa Jimeta da Daura.
Washegarin ranar da ya koma Hamma Abdullahi ya kawo atamfofi guda hamsi cur daga LamiÉ—o Ammah ta raba ma yan'uwa da dangi sannan an cika store din Baffa da kayan abinci sannan an siya masa sabuwar mota camry, Amma kuma ya siya mata waya sabuwar kiran samsumg sannan ya ce ta shirya za ta je Umra.

Ammah sai kuka kukan farinciki, da man in zai yi musu abu sai ya bar garin a cewarsa ba ya son godiya.
Da Ammah ta kira shi a waya tana ta masa addu'a.
Ya dinga amawa da Amin yana faÉ—in" Ammah ki je Madina ki yi addua'a sannan ki samu natsuwa."
Shi duk ƙokarinsa tana cikin damuwa ta tafi can ta samu natsuwa.

"Na gode Lamido. Ubangiji ya yi maka albarka "
"Amin Ammah ta."
Baffa ma da ya kira shi sai ya ce masa" Na gode LamiÉ—o amma ni ba Ammah ba ce godiya zan yi ba sai na yi kuka ba."
Baffa na ta dariya shima sai da ya murmusa.

"Na gode Baffa. Allah ya kara girma."

Kalamansa kenan domin har abada ba zai iya biyan abin da suka yi masa.
Hamma Saddam ma dake makaranta an shaka masa kuÉ—i tunda Ummu Salma ta ga yana ta yin status yana wasa Hamma Lamido, har su Hamma Abdulrahaman duk sun samu kyautar ban girma Ummu Salma ce ko abin da ba a so bai ma nuna ya san tana gidan ba.
Itama ba ta damu ba, wani abun duniya yanzu duk ba ya gabanta halin data ke ciki kawai ya ishe ta.
Har kuma ya gama zaman shi ya koma ba ta yarda sun sake haÉ—uwa ba.

Tuni Ammah ta shiga rabon zannuwa, na mutanen Mubi sama da guda ashirin Ummin ikki da yayanta matan su Hamma Jibo duk ta aje musu, har Ummu an ba ta turmi ɗaya ta karba domin in ta ce ba ta so Ammah za ta yi mata masifa shi ya sa ta karɓa ta ajiye.
Addu''oin godiya da fatan alheri kam Hamma LamiÉ—o na shan su.

Mami ta aiko ma da Ummu Salma waya sabuwar samsumg iri É—aya da ta Ammah har da sabon layi.
Da ta fara amfani da wayar amma ban da lambar yayyenta da ta Mami sai ta Baffa da Ammh sai na BaÉ—do da shamsiya ba ta da ta kowa, wayar ma da komai duk sun fita kanta ita dai gata nan ne tana dai rayuwa. Ba ta buÉ—e whatsApp ba balle tiktok wayar ce kawai a hannunta.

Ta fara zuwa awo Hamma Abdullahi ke kai ta tare da Ummin ikki. Karfin addu'a da kulawan mutane ya ke riƙe da Imanin Ummu amna fa zuciya ta raunana, wani rami ne a zuciyarta wawake da Habib ya yi mata haƙon shi, taɓo ne da ba zai taɓa warkewa ba.

Tafiyan Ammah zuwa Umra ya tashi sannan ta Lagos za su tashi ana ta shirye-shirye.
An yanke shawaran Mami za ta zo ta tafi da Ummu, tuni har ta haÉ—a kayanta tana murnan tafiya Kaduna.

Ana cikin haka ne mijin Mami Alhaji Isa ya yi hatsari  ya samu karaya a kafarsa an ba shi gado a asibitin 44 dake Kaduna. Mami ba ta da natsuwa sai kawai Baffa ya ce Ummu ta yi zamanta duk da Mamin ta so ta je amma Baffa ya hana wannan karon da cewa tana da majinyaci ta zauna ta kula da shi.
Shikenan tafiya Kaduna ta sha ruwa, Ummu ta so ta yi nesa da garin Jimeta amma tunda Allah bai so ba sai ta hakura. Da Hamma Abdulrrahman har cewa ya yi ta koma gidan shi da zama har Ammah ta dawo sai ta yi tunanin ai ga Baffa a gida gwara ta yi zamanta kawai.

Ammah ma ta kawo ƙorafin a asibiti an ce ta huta kar ta yi aikin wahala ita kuma ta dage za ta iya domin tana ganin cewa har zuwa yaushe ne za ta yi ta zama takura da lalura ga yan'uwanta da iyayenta,? Shi ya sa ta ɗau niyyar canzawa domin samar ma da zukatan dake zagayeta da ita salama.

Hamma Abdullahi ne ya raka Ammah har lagos gidan Hamma LamiÉ—o ta sauka baya ma nan ya fara aiki da sabon kamfaninsa, amma an gama dukkan komai kwana biyu Hamma Abdullahi ya yi a Lagos sannan ya dawo bayan a safiyar ranar jirgin su Ammah ya daga zuwa Jidda.

Da man da Hamma Saddam na nan ne shi zai rakata to in baya nan Hamma Abdullahi ne komai na gida duk wanda zai yi sako ma ta hannunsa ne. Kafin tafiyar Ammah Ummu ta roke ta da in ta je ta yi mata addua a ka'aba Ammah ta ce tana daga cikin dalilin da ya sa ta yi farinciki da LamiÉ—o ya biya mata Umra. Ta tafi da niyar za ta yo ma Ummin addu'an Allah ya ba ta dangana ya sauketa lafiya sannan ya sauya rayuwarta daga kunci zuwa farinciki.

Sannan ta bar ma Ummin ikki amana duk da ga Baffa a gida. Kuma ta karɓa tunda kullum za ta zo ta duba Ummu, Baɗdo ma tana zuwa sosai kuma tana jin daɗin ganin yanayin Ummun na sauyawa.
Makaranta ne ma yasa ba ta kwana tunda bayan ta gama ND Sai wannan shekaran ne ma ta É—ora Degree É—in ta(HND).

Tun bayan tafiyar Ammah Ummu ce ke da alhakin gyaran gida da yin abincin Baffa na ganin ba za ta iya ba sai ga shi ta ware, kuma sai aikin ya É—an rage mata damuwa balle ma da take yiin girke-girke kala kala, abin da ba ta gane ba ta É—au wayarta ta faÉ—a Youtube ta duba.

In Baffa na gida ya yi ta kambama ta komai ta yi ta bashi ya yi ta santi.
"Auta shi kuma wannan abin da me kika yi shi?
Ita kuma tana jin daÉ—in in yana santi sai ta zauna ta yi ta faÉ—a masa yadda ta yi.
Haka ma Hamma Abdullahi in ya zo gidan ta yi wani abin ta zuba masa.

"Ummu da me wai kika yi wannan?
Haka yace ranar da ya zo da safe ta yi musu Naan bread, mai nama a ciki shi da Baffa suna santi ita kuma tana jin daÉ—i.

Haka ko su Adda Suwaiba suke cewa in suka zo gidan, ita ce yi musu kosan rogo, wainar fulawa, gurasa fanke cake da su samosa tunda duk abubuwan baking É—inta suna nan É—akin cikin kayanta kawai buÉ—ewa ta yi ta É—auko su tana amfani da su.

Cikin wata É—ayan da Ammah ta yi a Saudiya Ummu ta sauya ta ware ta fara maida jikinta ga cikinta ya turo wattani biyar har da wasu kwanaki tana kuma zuwa asibiti in lokacin awonta ya zo.

Zirga-zirgan da take yi da kai da kawo sai ya rage mata tunani, sannan ta dage da addu'a in ta ji damuwa ko tunanin Habib yanzu za ta kunna karatun Qur'ani tana bi tana saurara tana aikinta.
Kowa ya zo ya ganta sai ya ji daÉ—in ganinta. Haka ma Ammah ranar da ta dawo ta ce Auta ta sauya ta yi kumari kamar ba ita ba.

Ta Lagos din Ammah ta sake sauka, sai da ta huta a gidan Hamma Lamido sannan ta dawo Jimeta. Itama ta yi shar kamar ba ita ba.
Tana cewa me Baffa ke ci da ba ta nan ta ga ya yi kiba ne.
Shi kuma ya ce itama da É—anta ya biya mata Umra ta tafi ta barshi, to ai shima Auta nan nan na jiyar da shi kayan daÉ—i ana ta dariya.
Sai bayan Ammah ta dawo ne suka je Kaduna ita da Ummin ikki duba mijin Mami su Baffa tun lokacin da aka yi hatsarin suka je.

Bayan sun dawo Ammah ta ce Ummu ta haÉ—a kayanta ta je Kaduna. An sallami mijin Mami yana gida.
Lokacin Ummu ta ji ma gwara ta yi zamanta gabansu Baffa sai kawai ta ce ita ba ta son zuwa yanzu watakila sai nan gaba. Mami ta fahimceta ba ta matsa mata ba, suma su Baffa ba su matsa mata ba sun kyaleta ganin ta fara dangana da komawa kamar Ummu Salma farko kafin Habib ya shigo rayuwarta.

*Janafty*
*FARGAR JAJI.*

*Wattpad:JamilaUmar315*
*Arewabooks:JamilaUmarJanafty*

"To Hajiya Hauwa'u Inuwa Aminu (Anty Hairi) with love and gratitude"

https://chat.whatsapp.com/GKzdnJ5Gb62IjjqT6AYpcC

No. 1 online shopping kenan inda zaku sami duk wani kaya da ku ke buƙata, tun daga kan kayan kicin, laceses, atamfofi, shaddoji kayan yara maza da mata ,da uwa uba magungunan supplements wadanda ba su da illa na manyan mata inda zaki fito ki yi das da ke ki zama abin sha'awa, ga kuma Arabian sabaya powder wacce baki taba cin karo da irin ta ba, ke dai maza shigo ki kwashi romon arziki a gidan mutunci da karamci a kai Miki kaya har inda ki ke babu fargaba.

*19*

*BAYAN WATA BIYU*
Chapter 75 · 0% Book details