Sashe 88
Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Abin da ke bani dariya in na tuna, ta zo gidammu ana jibi bikin mu ta ga hotunan auran mu amma wai ta kasa gasgata gaskiya ne, ta yarda da ni ta aminta da soyayyar da take yi maka a wautar ta tana tunanin wata rana za ka dawo gare ta? Ka daɗe kana ce mini yarinyar nan ba ta da tunani ban taɓa yarda ba sai ranar."
Ta gama faÉ—a tana sake kwashewa da wata dariyan daga gani tana cikin nishaÉ—i da labarin da take bayarwa.
Nan fa ta cigaba da faÉ—in maganganu marasa daÉ—i a kan Ummu Salma labarin zuwanta gidansu da duk abin da ya kwana kullum sai ta tuna ta yi dariya kamar ya zama abun tunawarta ta yi nishaÉ—i.
"Wawancin iyayenta na gani, suka barta da cikin jikinta alhalin wanda ya yi cikin ya ce ba ya so, to mene ne amfanin haihuwar da za ta yi?
Ta faÉ—a tana kallon shi, sai ya É—an juya mata ido alamun bai sani ba.
"Ni dai har abada ba za ka kawo mini jinin da ba nawa a gidana ba, ba mu yi wannan alƙawarin ba."
"Ba ma zan kawo ba? Me zan yi da abin da ta haifa! Ke da za ki yi ta haifa mana yara?
Ya gama faÉ—a yana É—an jan hancinta mirmishi ta sakar masa har tana sumbatar gefen kumatunsa.
"Da gaske na ke yi na bar ma Ummu Salma da iyayenta wannan cikin har abada ba ni da alaqa da shi"
Ta jinjina kai cikin farinciki.
"Wayyo ta ba ni tausayi, "
Ta sake faÉ—a tana sake saka dariya.
"Lokacin har wani É—aga kafaÉ—a take yi. Bestie Allah kuma ya ba ku miji wanda ya fi Noori na ma komai da komai."
Ta gama faÉ—a tana kwaikwayon muryan Ummu Salma daga shi har ita sai da suka sake tsintsirewa da dariya.
"Ko haihu ta yanzu? Domin ganina da ita na karshe na ga cikin ya yi kasa. Ko da yake ina ruwanmu ko Sweety?
Ta tambaya tana kallon shi.
"To ai ke ce ke É—auko maganarta. Ni tuni na gama da babinta."
"Labarinta na sanya ni nishaÉ—i ne."
Ta sake faÉ—a tana dariya.
"Na san zuwa yanzu kowa ya san na aure ka, na san na sha tsinuwa wajen yan'uwanta barin ma uwarta din nan bafullatanar banza, da wannan yayanta na ta lauya masifaffe da shegiyar ƙawar nan nata Baɗdo ba ta da mutumci, ka ga saƙon cin mutumcin da ta turamini ranar biki! Wai duk abin da ya samu Yar uwanta ni da kai Ubangiji ba zai ƙyale mu ba to ina ruwan mu? Daman ai aro na ba ta kai kuma na zo na karɓi kaya na sai aka ga laifina Sweety?
"Bai kamata a ga laifnki ba, ai su ba su nan abin da ya faru ba ne."
Ya faÉ—a cikin sanyin murya.
"Ko da Ummu Salma ta riga ni haɗuwa da kai. Amma ai ni ka zaɓa sama da ita ko?
Ta sake tambayan shi tana É—an kallom shi.
"Tabbas."
Ya faÉ—a abin da ya faru a lokacin yana dawowa masa.
"Wallahi tun a ganin farkon da na fara yi maka kishi da hassada suka kume ni, a raina ina faɗin me ya sa sai Ummu ce za ta fara haɗuwa dakai? Ranar na koma gida da baƙinciki ina ganin kai ne irin namijin da nake burin aure ban taɓa tunanin za ka kawo kanka gare ni ba wallahi tallahi da ka makara ba ka zo ba, ni da kaina zan neme ka na yi maka tallar kaina sannan na sanar dakai na fi Ummu Salma bukatar ka a rayuwata."
Ta gama faÉ—a cikin wani yanayi kamar ta yi kuka.
"Sweety wallahi ina sonka."
Sake rumgumeta ya yi a jikinsa yana faɗin" Na sani, nima ai kinsan ina son ki! In kika yi duba da tsawon lokacin soyayyarmu da yadda na cika alƙawarin kema za ki san bayan ke ba na son kowa a duniyar nan a matsayin matar auran da zan zauna da ita. Na fuskancin komai saboda na mallake ki "
Ta sake ƙamƙame shi tana faɗin" Na sani Sweety na sani wallahi."
Sumbatar sumar kanta ya yi kafin ya ce" Ki bar tuna duk abin da ya wuce, rayuwarmu ce yanzu kawai a gabanmu Sweety, mu zauna mu gina sabuwar rayuwa wacce za ta yaÉ—u zuwa nan da wani lokaci kaÉ—an. Can wait na ga ranar da za ki haifa mini É—a ko Æ´a daga mahaifarki."
Ya faɗa yana kai hannunsa ƙasan maranta ita kuma sai ta noƙe wai tana jin kunya.
"Ke ce na zaɓa ki zama uwa ga ƴa'ƴana. Kuma ba zan sauya miki ba."
Gabaɗaya ya gama kashe mata zuciya da kalamansa. Sai ta sake narke masa cikin shagwaɓa shi kuma yana biye mata sun daɗe a haka domin da ya ce su je ɗaki su kwanta sai taƙi karshenta a saman jikinsa ta yi barci ta bar shi da sake shuga tunani mai zurfi.
Tabbas a ganin farko da ya yi ma Ummu Salma ya ji yana son ta amma lokacin da ya haɗa idanuwansa da na Shamsiya sai ya fahimci ashe ba so ya ke yi ma Ummu ba sha'awanta yake yi, in yana tare da ita burinsa kawai jikinta ne a gabansa amma in yana tare da Shamsiya burinsa kawai ya dauwama tare da ita ko da ba za ta amfanesa da komai ba, tun bai fahimci karatun ba har dai ya fahimta ba shi da mafita illa ba ma zuciyansa abinda take so sai kuma aka yi saa itama shi take so, kawai sai suka jone suka kuma tsara komai. A lokacin a gida ba za a aurar da Shamsiya ba sannan shi kuma yana son auran Ummu Salma saboda ya cire wannan kwaɗayim nata a zuciyarsa shi ya sa ya yi ma Shamsiya alƙawarin zai yi auren shekara ɗaya ya sake ta sannan ya zo su yi aure daga baya ta aminta amma babu sharaɗin haihuwa, kaddara ce ta gifta har wannan cikin ya zama rai a cikin Ummu Salma amma ba shirin su ba ne, bai samu matsala a bangaren iyayen Shamsiya ba saboda dangin mahaifiyarta sun tankwasa mahaifinta, kuma gidan yan boko ne ba wani damuwa aka yi da dogon bincike ba tunda aka fahimci shima yana da iliminsa da aikinsa sannan ko da aka ce ya saki matarsa ta farko ba wanda ya yi bincike mai tsanani akan haka, kuma a cikin ahalin Shamsiya ba wanda ya san shi a matsayin mijin kawarta, shi kawai a san shi ne a matsayin mijinta na yanzu. Ya so ya samu matsala da Alhaji Sheriff shi ne ya ce ba zai sake zuwa ya nema masa aure ba, amma Baba Usman da su Gwaggo duk ya siye su da kyauttuka tuni suka manta da komai, shi ma dai Alhaji Sheriff ɗin da magiyan Habib ɗin da Baba Usman da Gwaggo ya amince ya je ya nema masa auran Shamsiya har aka ba shi amma da sharaɗin in wani abu ya biyo baya kar ya saka shi a ciki.
Shi kuma ya amince a tunaninsa me zai biyo baya? Masoyiyarsa fa ya aura, yana tunanin dukkan wani buri na shi zai cika, ya gama samun farinciki bayan ya watsa farimcikin wata,bai san cewa watakila farincikin na shi na lokaci kaɗan ba ne, ƙila nan gaba kaɗan Fargar jaji zai kama shi ya fara nadaman abin da ya aikata nadama mara amfani alhalin kuma lokaci ya sare masa.
****
*NDC QUATERS KADUNA NAGERIA.*
*BAYAN SHEKARU BIYU.*
"A Yau na koya mana yadda za mu sarrafa shinkafar mu zuwa chinese rice, za ki yin ta da kowani shinkafa amma ta kasance mai kyau ce saboda gudun caɓewa. Uwargida da Amarya har da ma ƴan'mata tare da zawarawa duk a yi pratical ma'ana gwaji domin da gwaji ne ake ƙwarewa ni ce dai taku ɗin nan HANAN DELICIOUS sai mun sake haɗuwa daku a wani sabon video na gode kar ku manta ku yi like in yau kika fara kallon videos ɗina to kar ki manta ki bibiya duka shafukana a Facebook Hanan B Jimeta a Youtube channel ɗina za ku kama ni a Hanan Delicious, in kuma a instergram ne za ku iya kama ni a Hanan B Jimeta, in kuma a Tiktok ne za ku iya kama ni a Hanan Delicious domin samun kayattacen videos ɗina akan girke girke masu kayatarwa tare da snacks na zamani domin jin daɗin ku. "
"Mahmah..."
"Mahmah.."
Ta ji ana kiranta daga falo, ta kuma san yanzu za ta shigo kitchen ɗin in kuma ta shigo za ta ɓata mata Video ya sa da sauri ta ce.
"Bissallam. Sai mun sake haÉ—uwa. Bye."
sannan da sauri ta matsa wajen ringligt ɗin da ta ɗaura a wayarta ƙiran iphone 15 ta yi saving ɗin Video ɗin dai dai lokacin da ƙaramar yarinyar ta ƙariso cikin kitchen ɗin.
"Mahmah."
Aka sake faɗa cikin murya irin ta yara masu shagwaɓa.
Da sauri ta baro in da take tsaye sanye da abaya baƙa ta yi rolling ɗin mayafin J.c mai ruwan madara kyakyawan farar fuskarta da dogon hancinta ta yi kyau sosai.
Sama ta É—aga yarinya tana faÉ—in
"Waye ya taɓa mini Hanan ɗina?
Ta faÉ—a tana share mata idanuwanta ganin hawaye.
Dakyar ta lallaɓata ta yi barci sannan ta zo ta fara Video ɗin nan, da ta kwana biyu ba ta ɗora komai a shafukanta ba Hannan da man akwai rigima balle kuma ba ta da lafiya tana ɗan zazzabi ga zawon haƙori na can gefe da suke fitowa shi ya sa rigimanta ya ƙaru kuma rigiman saboda ta san sun kwanta tare kuma ta farka ba ta ganta a gefenta ba shine ta taso tana kuka.