← Book details Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 92

Sashe 5

Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk da yanayin Ummu-Salma da Habib ya gani bai saka ya ɗaga mata kafa ba, kafin su kwanta sai da ya maimaita. Can cikin dare ma sai da ya tashe ta tana so ta ce ya ƙyaleta ba ta jin daɗin jikinta amma ta kasa, yana dawowa daga sallar asuba ma sai da ya yi duk yadda ya ga jikin Ummu-Salma ya yi laushi a cewarsa jarumatarsa ce ta ƙaru, shi ya sa ta makara sai wajen bakwai saura ta iya ƙarfin halin tashi ta shiga kitchen, da ya ke girki Hobby ɗin ta ne garin fulawa ta iya sarrafa wa, cikin lokaci ta kwaɓa fulawa ta sarrafa shi zuwa Naan Bread.
Tun da tana da kayan lambu, nama ne babu sai ta yi amfani da ƙwai.

Ko kafin takwas ta yi ta jera komai a saman dinning. Ta koma bedroom ta tashi ta Habib ta taimaka masa ya yi wanka, ya tsuke cikin suit masu ruwan  baƙi da ruwan toka. Tare suka zauna zaman ƙaryawan Naan bread ɗin suke ci haɗe da tea Habib na gutsira yana yi mata santi.

"Baby ina son wannan abin. Ya ma sunan shi?

Tana dariya ta ce" Naan Bread Noori, amma wannan mai ƙwai ne ba nama ba."

Sai ya jinjina kai kafin ya ce" A online clases É—in ku aka koya miki?
Bayansa ta dafa kafin ta ce" Noori na santi."
Sai da ya kurɓi tea kafin ya ce" Ba santi ba ne, Allah Baby yana da daɗi, in dai kika yi shi ai ina cewa yana da daɗi ko?

"Yes My Noori."

Hira suke yi, jefi-jefi ita tea ɗin ma kawai ta ke kurɓa saboda zuciyarta ta ji tana tashi tun da safe, shi ya sa ma ba ta ci ba naan bread ɗin ba.

Habib wayarsa ce a hannunsa yana ta dubawa. Lokaci É—aya kuma yana cin abinci.

"Baby."

"Naam"

"Ashe kuna da biki ban sani ba?

Sai ta kalle shi cikin mamaki.

"Noori Biki kuma?

"Yes"

Ya faɗa yana karkata mata wayar ta leƙo da kanta sai ta yi arba da zafafan hotunan Badia'tu yar sarkin Daura.

"Ba bikin gidanku ba ne?

Ya faɗa  yana sake tura abin da ke hannunsa a baki lokaci ɗaya yana korawa da ruwan tea.

"Oh ai fa."

Ummu-Salma ta faÉ—a tana kauda kanta.

"Ammah za ta je?

"Za ta je mana. Kai ma ka sani"

"Mami fa? Itama za ta je?

Sai ta kalle shi kafin ta ce.

"Kai ma ka san Mami ba za ta je ba."

Sai ya jinjina kai yana cigaba da kallon wayarsa kafin ya ce" Baby da kin tambayeni da na bar ki, kin raka Ammah dagaa ganin bikin nan za a sha shagali."

"Uhm"

Ta faÉ—a ba tare da ta sake mgana ba.

Dariya Habib ya yi kafin ya ce" Am just joking. In kika tafi ni kuma ya za ki yi da ni?
Hararan shi ta yi, yana sake yin wata dariyan ya ce.

"I love you Baby."

Juya masa ido ta yi sannan ta yi masa fari, jinjina kai ya yi kafin ya ce" Ki bari kafin na ce mu shiga daga ciki."
Tana jin haka ta yi saurin gyara zama tana faÉ—in.

"Za ka makara fa Noori?.

"Ina sane da time fa Baby."

Sai ta jinjina kai, ba ta yi mgana saboda cikinta ne ta ji yana juya mata.

"Baby."

"Noori."

Sai da ya kalleta kafin ya ce.

"Hamma LamiÉ—on to zai je can Daura É—in ne?

"Ban sani ba Noori."

"Serous fa?

"Allah fa ban sani ba."

Ta faÉ—a tana mai kallon shi.

"Ko Ammah ba ta faÉ—a miki ba.?

"Ba ta faÉ—a mini ba Noori."

Ta faÉ—a cikin gajiya da tambayoyin.

"Noori yau kuma Hamma LamiÉ—on kake son gani?

Ta  faɗa tana kallon shi mirmishi ya yi kafin ya ce" Ba laifi ba ne, kin manta sau ɗaya na taɓa ganin shi, shima daga nesa kafin na karisa ya shige cikin mota."

Baki ta taɓe kafin ta ce.

"Uhm"

"Baby ke dai kawai ki ce jininku bai haɗu ba, kuma saboda kin ƙi karatu ne "

Wani kallo ta yi masa da ya sa ya fara dariya kafin ya ce.
"Baby gaskiya na faÉ—a, nima fa ta shafe ni kamar baya sona saboda ke."

Kai Ummu-Salma ta girgiza kafin ta ce" Shi wannan yana neman dalilin tsanar mutum ne? in dai haka ne kowa ya tsana kenan."

"Me ya sa kika ce haka?

"To ban da Ammah wa ke ganin dariyan mutumin nan! Ko Baffa a ginshiƙe yake masa mgana. To bari ka ji ko su Hamma Jibril a takamance yake yi musu mgana, ballanta irin mu ƙananun ƙwari."

Habib ya kwashe da dariya ganin yadda matar tashi ta haÉ—e rai, tissue ya É—auka yana goge bakin shi kafin ya ce.

"Kuma Ammah tafi son shi da ke ba Baby."

"Ta fi son shi da kowa ma Noori. Ni ai na bar masa ita na kama Mami na da Umman ikki."

Ta faɗa tana juya masa baki, miƙewa ya yi yana faɗin" Baby is time."
Itama sai ta mike, bedroom ta koma ta É—auko masa briefcase É—in sa ta dawo falon suka rumgume juna sai da ya sumbaci bakin ta kafin ya ce.

"Baby take care kin ji ko."

"In sha Allahu"

Ya hana ta masa rakiya a haraba shi ya sa iyakarta kofar falo ya fita tana ɗaga masa hannu har ta za ta rufe ƙofar sai ga shi ya dawo da sauri yana faɗin.

"Baby key É—in mota ko a kafa kike son na je wajen aikin yau?

Sai ta juya da sarssarfa ta koma ciki ta É—auko masa, bayan ta kawo masa sai da ya sumbaci hannun sannan ya wuce yana faÉ—in

"I love you Baby."

"Love you too Noori na."

Hannu ya ɗaga mata, itama ta daga masa sannan ta rufe ƙofar. Dinning ɗin ta koma ta zauna domin ba ta ƙoshi ba sauran Naan bread ɗin da Habib ya rage ta ɗauka ta ci guda ɗaya ta hada da ruwan tea, Allah ne ya sota da ta yi amai saboda zuciyarta ta yi ta tashi sai da ta sha ruwa sai ta ji zuciyarta ta kwanta

Tunani take yi ko dai ciki gare ta? Sai ta fara tunanin yaushen da rabon da ta ga al'adanta? Tun bayan ɗaukewar jinin nan na ɓarin da ta yi ba ta sake wani jini ba, tsalle ta buga ita kaɗai a falo da gudu ta ruga ɗaki ta dauko wayarta Habib ta so kira sai kuma ta fasa kar ta ɗaga masa hankali.
Sai ta mai da alkalan kiran ga Sisna amma ba ta É—auki wayar ba wata kila ta shiga cikin makaranta ne
Sai ta bar mata saƙo.

"Albishirin ki. Ina tunanin ina da wani cikin SisNa."

Ita kaɗai a gaban madubi tana shafa cikinta tana kallo, farincikinta ya kasa ɓoyuwa wani irin murna Habib zai yi in ya san tana da ciki? Ba ta da tabbaci amma alamominta na kwana biyun nan ya fi kama da na masu juna biyu, sai a lokacin ta kula da nonuwanta sun tasa, kuma da man cikinta na farko kafin ta yi ɓarin shi a Nono ya fara nuna kansa kenan wannan ma anan zai fara bayyana kan shi?

Wata zuciyar na faɗa mata kar ta faɗa ma Habib sai ta je asibiti an tabbatar mata sannan sai ta faɗa masa cikin mamakin da tasan murnan da zai yi ba ƙarama ba ce, saboda lokacin da ta yi ɓari ya shiga damuwa sosai har ta dinga mamakin haka yake son haihuwa? Ko da yake in ta yi duba da gidan da ya fito gidan yawa ne shi ya sa zai so shima ya tara yara kamar mahaifinsa.

*littafin Fargar Jaji na kuÉ—i ne a manhajar Telegram akan #1k. Tura KuÉ—in karatun ku ta wannan acct É—in 9069067488 JAMILA UMAR OPAY sannan sai ku tura shaidar biya ta waÉ—annan lambobin kamar haka.*

09069067488.
08032773332.

*Yan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajojinku a cikin wannan kayattacen labarin za ku iya tuntuɓata kai tsaye ta wannan lambar 09069067488 Na gode.*

*Janafty*
*Sat, 05. June 2025.*
5:53pm.
*Posting on 17/04/2026*
*FARGAR JAJI.*

*Wattpad:JamilaUmar315*
*Arewabooks:JamilaUmarJanafty*

To Hajiya Hauwa'u Inuwa Aminu (Anty Hairi) with love and gratitude"

https://chat.whatsapp.com/IF0uPZWtcCOIczsjhdCbIZ?mode=gi_t

https://www.arewapen.com/u/jamilaumarjanafty

*02*
_JIMETA: Zone 3_
*10:30pm.*

Alhaji Hadi Baba na zaune a gefen gadon dake cikin turakan shi, wasu takardu ne a hannun shi yake dubawa sanye yake da jallabiya mai ruwan madara, kansa da tsilintsilin furfura wani siririn farin gilashin ne a idanuwansa wanda in zai karanta wani abu yake amfani da shi saboda raunin ganin sa.

Sallaman matarsa ne ya katse masa nazarin takardun dake hannunsa, ya É—ago kansa lokaci É—aya yana mai amsa mata cikakkiyar sallaman kamar yadda ta yi.

Dattijo ne mai cikar kamala da haiba, fari ne amma ba shi da haske sosai wataƙila ya yi sirki shekarunsa na haihuwa za su kai 66 amma hutu da jin daɗi sun saka fatarsa da yanayin jikinsa suna ƙaryata shekarunsa
mai ɗakin sa yake kallo dai-dai lokacin da ta ƙariso gaban shi.

"Baffa ba ka kwanta ba?

Ta faɗa da muryanta da ta cakuɗe irin na fulani lokaci ɗaya kuma tana nufar can ƙurar ɗakin in da ta ijiye mganin sauron da ta kunno a hannunta a saman wata kwalba lokaci ɗaya tana sake faɗin" Na manta yau ban yi maka feshin magani ba Baffa."

"Sannu da ƙoƙari. Na gode."

Ya faÉ—a da cikin harshen fillanci, dawowa ta yi zuwa gefen shi ta zauna tana kallon shi, itama ita ya kalla amma bai yi mgana ba sai ta fara dariya tana faÉ—in" Baffa me kuma na yi ni Jamila?
Kai ya girgiza kafin ya ce" Ba ki yi komai ba."
Agogon da ke sama ta É—aga kai tana kallo sha É—aya saura daga nan ta gano laifinta.

"Baffa ka san ina da tafiya a gaba na ina can ina ta Æ´'an kimtse-kimtse ne "
Chapter 5 · 0% Book details