← Book details Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 92

Sashe 86

Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ammah ta yi wucewarta É—akin Baffa domin ta gyara tana ce ma Mami.
"Ku kuka sani dai Fatima."
Mami ita kaÉ—ai ma faÉ—anta ta dinga yi.
Hamma Abdulrrahaman ya sulale ya gudu shima Abdullahi daga filin jirgi bai dawo gidan ba.
FaÉ—an da Mami ta yi ranar har dare, sai da Ummun ta koma ba ta hakuri.

"Gwara na tattaraki mu tafi can su daina ganinki, tunda Ammah ta daure musu kugu, Baffa kuma ba zaman gidan yake yi ba, balle ya tsaya miki "

Haka da Baffa ya dawo ta tare shi da cewa Ammah ta yi gayyar yayanta sun saka Auta kuka.
"Baffa har da wannan É—an nata kamar basamude, shi ya fara zuwa ya yi mata kerere a gaba yana ta masifa, ashe karyan miskilanci yake yi tunda yana faÉ—a, Ammah na gefe da sauran yayanta suna cewa ya yi daidai."

"Ba su kyauta ba "

Baffa ya faÉ—a yana danne dariyansa.

"Ammah ce fa ba ta tsawarta musu ba."

"Ammah ma ba ta kyauta ba."
Ya sake faÉ—a yana dariya.
Ammah ta shigo ɗakin kawo ma Baffa abinci ta ce" An zo an kawo ƙarana kenan?
"E wai har da basamuden danki kika kira ya zo ya yi ma Auta faÉ—a."
Ammah ta kwashe da dariya Baffa na ta yata.
"Allah ya shirye ki Fatima."
Ammah ta faÉ—a tana ficewa daga dakin.
"Gwara ki dauki yarki ku koma Kaduna sai kun shekara ba su ganta ba, ina ce va shike nan ba, sai na ga wanda ya'yan Ammah za su yi ma faÉ—an"

"Ai Baffa ka bar su da ni, boko ce suke gwada mana, nima yar bokon ce sai dai mu buga ta."
Baffa na dariya sosai ya ce" A gaida Fatima Baba, Fatin Gwaggo. Yau da ma suna raye su ga yadda Ubangiji ya mayar da Fatin su."
Sai kuma suka koma tuna rayuwarsu ta baya tare da yi ma iyayensu addu'a daga karshe ma tare suke cin abincin Ammah ta sake dawowa ganin suna cin abinci ya sa ta rike baki tana fadin" Fatima kin zo kin ƙwace mini Baffa, miye nufin ki?

"Jibi za mu bar muku gidan."

"Umma ta gaida Aisha."
Baffa dariya kawai ya yi yana girgiza kansa.
Ammah itama zama ta yi suna cin abincin su uku daga faranti ɗaya, in ya kalle su sai ya tuna a shekarun baya shikenan raba faɗa a tsakanin Mami da Ammah, amma shaƙuwa ce mai tsanani a tsakaninsu, wacce ma alƙalami ba zai iya rubutawa ba.

*1k on Telegram
09069067488.

*Janafty*
*FARGAR JAJI.*

*Wattpad:JamilaUmar315*
*Arewabooks:JamilaUmarJanafty*

"To Hajiya Hauwa'u Inuwa Aminu (Anty Hairi) with love and gratitude"

https://chat.whatsapp.com/GKzdnJ5Gb62IjjqT6AYpcC

*21*

Washegari asabar Alhaji isa ya iso Jimeta tare da Islam da Faruk. Mami da kanta tare da Hamma Abdullahi suka je filin jirgi suka É—auko su zuwa gida.

A shashen mazan gidan daman ya kan sauka in ya zo duk da in kwana ya kama shi hotel yake tafiya yau ɗin ma a bangaren su Hamma Saddam Mami ta sauke shi sai bayan ya ci abinci ya natsa sannan ya shigo cikin gida suka gaisa shi da Amma, Baffa ba ya nan ya je cikin garin Jalingo sai can yamma ya dawo tare suka yi sallar mangariba da Alhaji isa har isha'in ma daman abokan kasuwanci ne tun a baya sannan megida ne da yaronsa. Yanzu kuma har da surukanta da ya haɗa su dalilin auran Mami, duk da hakan zumumcin da ya haɗa su bai yanke ba yau ɗin ma bayan sun dawo daga masallaci a tsakar gida Ammah ta yi musu shimfiɗa ta kuma haɗe musu abinci waje ɗaya suka zauna suna ci suna hira, irin ta su ta masu kasuwancin ƙarafa da siya da siyarwan motoci daga jin yadda suke magana a tsakaninsu za ka fahimci akwai kyakyawam alaqa a tsakanin su.

Mami kuma da Ammah suna falo suna kallo tare da Faruk jefi-jefi suna taɓa hira a tsakanin su, Ummu kuma tana cikin ɗakin ta tare da Islam sarkin surutu tunda suka iso tana makale da ita tana yi mata zence, ta sha labarai kala-kala har sai da ta gaji, tamboyoyi har ta gaji da amsa mata su. Tun a can Kaduna Babansu ya sanar da su Ya Ummu za ta koma gidan su da zama to fa suna sauka ɗakinta ta fara zuwa tambayanta na farko shi ne.

"Ya Ummu wai da gaske gidanmu za ki koma da zama?
Ummu Salma na mirmishi ta ce.
"In sha Allahu Islam."

Nan fa ta fara murna da tsalle, Islam yarinya ce mai shiga rai, tana da son mutane da mgana kamar Mami yar kimanin shekara sha biyu 12, Faruk kuma É—an shekaru bakwai ne 8, shi bai da surutu sai dai rigima ce da shi sosai kamar yaron goye.
To duk bayan mintina sai ta zagayo ta ce"Ya Ummu da gaske za ki bi mu gidanmu?
In ta amsa mata da E bai hana anjuma ta sake dawowa da irin wannan tambayan har sai da ta gaji da amsa mata. Mami ma cewa ta yi ta kore ta daga ɗakin ta ce a ƙyaleta, ganin ta da surutunta na sanyata nishaɗi, kuma ta tabbata ko can ta je islam da Faruk ba za su barta ta yi kewa ba, domin samun yara a gida yana haskaka gida tare da samar da walwala ga mazauna gidan gabaɗaya.

A can tsakar gida kuwa bayan su Baffa sun gama cin abinci sun wanke hannuwansu a roban wanke hannun da Ammah ta ajiye musu, suka ɗan shiga hiran yadda kasuwancin siyar da tsoffin karafan motoci ya yi kasa yanzu ba kamar a baya ba, Baffa na mganar kasuwancin motocin da sabbin ƙarafan ma sun fi tafiya a yanzu shi kuma Alhaji Isa na sake kora masa jawaban, tun da shi dila ne kamfani guda gare shi na siyar da motoci wani lokacim ma su Baffa kan siya motoci a wajen su in hakan ta kama.

A cikin hiran ne Baffa ya kalli Alhaji isa cikin nisawa kafin ya ce" Alhaji ina son mgana da kai, duk da na san kun gama mgana da Fatima amma amatsayina na wakilin Fatima, uban Ummu Salma ya kamata na yi magana da kai."

"Ina jin ka ina fatan ba kan maganar zaman Ummu a wajen mu ba ne ko Baffa?
Tunda shima Baffa yake kiran shi tun ma kafin aure su da Fatima, abokan kasuwancin Baffa duk da wannan sunan suke kiran shi.

"Akan maganar ne."
Baffa ya amsa masa cikin É—an sanyin magana.

"Haba Baffa, ai ina ce mun wuce haka a tsakaninmu. Ko ban auri Fatima ba ni mai riƙe Ummu Salma ne, ballantana ina auren Fatima. Ba ka da sauran haufi ko tsoro. Ummu Salma za ta samu sauyin rayuwa tare damu na ba ka tabbacin yadda zan yi ma Islam da Faruku haka zan yi ma Ummu Salma. Sannan haka itama Fatima saboda haka ka kwantar da hankalinka ba abinda zai sake faruwa da yardan Allah."
Yana mgana Baffa na ta gyaÉ—a kansa cikin gamsuwa.
Yana direwa ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce.

"Na gode sosai, Ubangiji ya yi ma arziƙin ka albarka. Da man tsoro na ke ji, kar Auta ta sake tunanin kashe kanta a karo na biyu"
"Hakan ba zai sake faruwa ba in sha Allahu."
Alhaji Isa ya sake ba shi tabbacin sa.
"Allah ya sa haka. Ubangiji ya sa tafiyarta ya zama mabuÉ—in alherin rayuwarta."
Suka amsa da Amin a tare, tare da su Ammah daga cikin ɗaki domin sun rage ƙaran talabijin ɗin Faruk ne ma ya matsa sai da aka mayar masa da tashar carttoon, shi ya sa hankulansu ya ɗan karkata kan mganganun Baffa da Alhaji Isa.

Wajen goman na dare Alhaji Isa ya tafi makwanci ya kwanta daman jirginsu karfe sha É—aya na safe zai ta shi zuwa Kaduna.
Shi ya sa sai wajen goma ya zo gidan abin karyawa ma tun a waya ya ce ma Mami kar ta wahalar da kanta, ya riga da ya yi breakfast a hotel É—in da ya kwana.

Ko da ya zo gida cike da yan sallama.
Ummin ikki da BaÉ—É—o, tare da matan su Hamma Abdullahi da yayan su, Hamma Abdullahin ma yana nan tunda shi zai kai su filin jirgi, Hamma Abdulrrahaman ne matarsa ta ce ya yi sammakon fita yana da wata sharia da yake jagoranta.

Ko da garin Allah ya waye daman Ummu Salma ta ji kamar ta buɗe idanuwanta ta ga ta yi nesa da garin Jimeta gabaɗaaya garin ya fita da ga zuciyanta a baya ba ta taɓa tunanin wata kaddara za ta iya raba ta da mahaifarta ba sai ga shi kaddaran Habibu ta sa za ta yi nesa da iyayenta da duka yan'uwanta domin tsira da salamar zuciyarta, ta tsani garin Jimeta da duk wani farincikin da ta samu a cikin ta dalilin Habib..
Sai ga shi suna sallama da BaÉ—É—o tana hawaye itama tana hawaye.

"Zan yi kewar ki Sisna. In sha Allahu in muka samu hutu zan dinga zuwa ina ganin ki."
Baɗɗo ta faɗa tana sharan ƙwallah.
"Na gode Aisha. Ba zan taɓa mantawa da alherinki ga zumuncin mu ba, nima Allah ya ba ni iko da tsawon rayuwa domin na samu damar saka miki."
Ummu Salma ta faÉ—a cikin kuka sannan suka sake rumgume juna.

Dakyar suka saki juna, Ummin ikki ma ta rike hannuwanta tana fadin" Ki je can ki sake sabuwar rayuwa. Kar ki dawo mini sai da sabon suruki kin ji ko Ummu?
Ta faÉ—a cikin mirmishi a zuciyan Ummu Salma faÉ—i take yi wa zai sake sona a haka Ummin ikki? Amma a fili mirmishi ta yi lokaci É—aya tana gyaÉ—a kanta cikin fitan hawaye.
Ammah ce kawai ba ta yi kuka ba, ita da ba a ganin raunin ta.

"Ammah zan tafi, ki yafe mini."
Ummu ta faɗa bayan ta duka a gaban Ammah tana zubar ƙwalla."
Chapter 86 · 0% Book details