← Book details Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 92

Sashe 20

Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana mai ƙara kecewa da kuka da ƙarfi har yana fidda Sauti a cikin zuciyarta ta ke jin wani zafi da radaɗi, gani ta ke yi kamar ba rayuwarta ba ce, ita fa ce Ummu-Salma wacce Habib ya nuna duk duniya ba shi da kamarta amma kalle ta a cikin gidansa kashi ma ya fita daraja, duk da ya ce bai shirya zama uba ba, sannan ba ya son ta shi ya sa ba zai iya haɗa zuru'a da ita ba. Ita tana son shi har kuma gobe ba ta ji ta cikin nadaman auren shi ba wallahi tana son Habib kuma za ta yi komai domin ta ga ta tsira da mijinta da auran ta.

**

*3:45am*

Habib ne a cikin ɗakin sa ya kasa zaune ya kasa tsaye,  kansa har sara masa yake yi saboda damuwa da tunanin mafita? Wani amsa zai ba ma Masoyiyar shi in ta tambaye shi labarin cikin da ke jikin Umma-Salma? Ya faɗa mata cikin na nan bai zube ba, ya saɓa alƙawari domin ba haka suka yi ba, shi kuma duk wata hanya da zai bi domin Ummu ta saduda ya bi amma taurin kanta ya wuce tunanin shi, ya ɗauka matakin da ya fara ɗauka akanta zai yi tasirin da za ta neme shi ta bashi hakuri, salim alim a zubar da cikin nan ya gama more sadakin sa sannan ya kaɗa ta amma ta nuna masa ita ɗin mai taurin kai ne, saboda rasa mafita ya sa ya je ya siyo mganin barci sleeping pills ya saka mata da yawa a cikin zoɓon da ya san tana so sosai amma ya fahimci kamar ko ta sha bai yi mata komai ba. Sannan ya duba bai ga roban zoɓan ba in da a ce tasha yana da tabbacin ba a gida zai gan ta  ba sai dai a kira shi a ce tana asibiti amma yanayin da ya ganta ya ba shi tabbacin wannan karon bai samu mafita ba.

Hannun shi guda ɗaya ya buga a ɗayan, lokaci ɗaya yana mai dafe kan shi cikin matsanancin damuwa na rashin mafita,  me ya sa Ummu-Salma ta kasa gane wa ne?  Ita duk maganganun da ya faɗa mata ba ta yarda ba ya son ta ba? Ba ta yarda ba ita ce zaɓin sa ba, ko kuwa sai ya zauna ya yi mata gwari-gwari ne sannan za ta  gane manufar auran shi da ita, yana cikin wannan tunanin wayarsa dake yashe saman gado ta fara vibration yana kai idanuwan shi wajen sai da gaban shi ya faɗi.

"M.S..!

Ita ce ke kira, a kuma yanzu ba shi da amsar da zai ba ta, ya na ta falling ɗin ta yana ta gazawa. Me ya sa ya yi wannan wawancin tun farko bai kai Ummu Salma an cire mata cikin nan ba tare da ta sani ba? Ba ya bukatar barin wani abu na shi a rayuwar Ummu Salma, bukatar shi in ya gama biyan buƙatar shi da ita ya sake ta shike nan babu wani sauran alaqa, sannan ba haka suka yi da Masoyiyar shi ba ya riga ya yi mata alƙawarin ba wata macen da za ta fara haifa masa zuru'a sai ita, kuma ba ya son saɓa wannan alƙawarin a matsayin shi na namiji, kwata-kwata ya rasa mafita duk yadda ya ɗau lamarin kamar wasa ba wasa ba ne, lamarin na bukatar ya yi aiki tukari akan haka in ba haka ba daga baya zai zo ya yi fargar jaji alhalin lokaci ya riga ya ƙure masa.

Ganin ba za'a daina kiran ba ne, ya san halin mai kiran da saka damuwa , kuma so ta ke ta ji yadda labarin cikin jikin Umma ya tsaya shi kuma ba shi da wata amsa mai daÉ—in da zai iya sanar da ita.
Kiran na ƙarshe da ya katse ba a sake kira ba sai can ba daɗewa sai ya ji ƙaran shigowan saƙo hannunsa na rawa ya jawo wayar ya buɗe saƙon

"Habib ko ka É—aga kirana ko gobe na zo gidan ka, koma me zai faru sai da ya faru. Ka amsa kirana."

Haka aka rubuta a jikin saƙon, jikinsa na rawa yana ƙokarin kiran lambar sai ga shi an sake kira a sanyaye ya ɗaga amma bai yi mgana ba.

"Habib me ya faru ne?

Aka tambaye shi, daga can cikin sanyin murya kuma muryan ta mace ce.

Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce"  Ina tunanin cikin yana nan"
Ya faÉ—a lokaci É—aya yana mai shafa kansa cikin damuwa.

"Kana ma tunani ne ba ka da tabbaci Habib?

Aka sake faÉ—a wannan karon cikin É—aga murya.

"Walahi na saka mata kamar yadda na faÉ—a miki. Sai dai..."

"Sai dai me?

Ta katse shi a fusace.

"Ina tunanin ba ta sha ba."

Wani É—an ihu aka saki acikin wayar daga can bangaren.

"Ki yi hakuri zan samo wata mafitar."

"Wata mafitar! Ai ka daɗe da rasa damar ka Habib. Tun farko kai ka jawo mana wannan matsalan tun farkon auran ku na ce ka sa a yi mata planning yadda wanzuwar ciki a jikinta ba zai ba mu matsala ba, ba ka aminta da shawarana ba ka zauna a tunanin shekara ɗaya ya yi kaɗan ɗin da za ta samu ciki, ka manta da yanzu aure ma ba a shekara ake haihuwa, cikin ta na farko ba domin Allah ya yi zubewar shi da shi ma ya bamu matsala wannan ma Habib ka kasa yin wani tunani? Sai da na ce maka kar ka sanar da ita komai ka ɗauke ta ka kai ta asibiti a zubar da cikin ka kuma sake ta daga can amma ka ce ba haka ba na ka tsarin za a bi yanzu ga in da na ka tsarin ya kai mu. Haba Habib ina jin kamar na haukace in na tuna jakar yarinyar ce ta riga ni aje ƙwan haihuwarka a mahaifarta ji na ke yi kamar zan suma saboda baƙin ciki."

Ta karishe faɗa cikin ƙaraji, jikinsa har rawa yake yi wajen zayyano mata kalaman ban haƙuri da rarrashi.

"My love kin ga kwantar da hankalin ki, ni na yi miki alƙawarin bayan ke babu wata macen da ita isa ta fara haɗa zuru'a da ni. Ki kwantar da hankalin ki dole cikin nan ya zube a goben nan in sha Allahu."

Ya faɗa cikin sigan lallashi, daƙyar har yana ɗan ɗaga hannu kamar tana ganin shi.
Shuru na wani lokaci daga can bangaren kafin ta sauke numfashi ta ce" Habib ka san ina son ka shi ya sa na ba ka damar yin abin da kake so ko?

"Na sani."

"To kar ka ba ni kunya. Kar ka saka na cire yaƙini na a kan ka."

"In sha Allahu, gobe zan É—auke ta mu je asibiti a cire cikin nan ko tana so ba ta so."

Dariya aka yi daga can bangaren kafin ta ce" Habib kar ma ka fara, in ka yi haka za ka yi nadama. Yadda Ummu ta san manufarka akan cikin jikinta ko Saudiya ne ba za ta sake aminta da kai ba balle har ta haÉ—a tafiya da kai. Ka samo wata mafitar dai."

Sai da ta faÉ—a kuma ya fahimci haka yadda ya bayyana munafarsa ba lalle Ummu ta sake aminta da shi ba amma duk da haka ba zai sare ba zai sake jaraba sa'ar shi sun daÉ—e suna waya yana faÉ—a mata kalaman soyayya cikin lallashi har sai da ya tabbatar da hankalinta ya kwanta sun rabu da cewa duk yadda zai yi zai yi na ganin cikin nan ya zube a gobe in sha Allahu.

Su sun gama na su tsarin, abin da kuma ba su sani ba Ubangiji shi ya riga ya gama nashi. A cikin zanen kaddaran su Ubangiji ya rubuta cewa Habib da Ummu za su samar da gudan jini, daga gudan jini zuwa rai.

***

Wani abu ya ba ma Ummu mamaki da ya sa kuma ta fara shakku, lamarin Habib yanzu ya zama abin tsoro da taka tsan-tsan a wajen ta.
Shigowa fa É—akin ta ya yi da safe kafin ya wuce wajen aiki yana tambayan ta ya jikin ta yana fatan ba ta da wata matsala.
Tsabar mamaki sai ta kasa mgana, tana kallon shi yana yi mata mirmishi, mirmishin da har cikin zuciyarta ba ta yarda da shi ba.

"Sannu, Baby zan tafi wajen aiki, amma ina so ki yi mini girki da kwalliya yau in na dawo za mu yi mgana."

Har ya fice daga ɗakin tana bin shi da kallo bakin ta sake ta kasa mgana wata zuciyar na faɗa mata Ko dai ya saduda ne, wata ƙila ya gane kuskuren shi ne zai ba ta haƙuri, da ya ke tana son Habib ta kuma aminta dashi shi ya sa wata zuciyarta ta rinjaye ta da cewa hakuri zai ba ta, ayayin da wata zuciyar a can gefe tana ɗan ɗari-ɗari alamun ba ta aminta da saukowan Habib lokaci ɗaya ba. Sai dai duk da haka ba ta fasa yin abin da ya ce ba, yamma na yi ba ta ko jin daɗin jikinta ta miƙe ta fara aiki Baɗɗo ma ta kira ta a waya ta ce tana tunanin za ta shigo sai ta ce mata ta bari sai gobe, acikin ranta tana murna da farinciki na daidatawar ta da Habib ko da Baɗɗo za ta zo gobe ba za ta fahimci komai ba.

Farar shinkafa ta dafa da miya sai salat. Har da kunun aya ta yi duk da tana yi tana faman hutawa domin sai ta ke jin numfashin ta na yin sama sama kamar zai ɗauke. Ko kafin mangariba ta gama komai sai da ta idar da salla sannan ta rarrafa ta yi wanka tana jin jikinta ya yi zafi zazzaɓin jikinta ya dawo, ammma haka nan ta yi masa kwalliya cikin wata doguwar riga baka mai kwalliyan ja a jikinta shi ya sa ma mayafin rigar ja ne, ta yi kyau duk da ba kwalliya ta yi ba amma fuskarta ta yi mata fayau kamar wacce ta shekara tana jinya.
Chapter 20 · 0% Book details