Sashe 85
Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ah Mami ki ce dai kawai kishi kike yi da mu kawai."
Hamma Abdullahi ya faÉ—a yana dariya.
"Ku dai kuke kishi da Auta, ku ana kula da ku, tun shigowarku Ammah ta ba ku abinci ita mai yaron ciki ta manta da ita."
Ammah na dariya ta ce" To ba kin fanshe ni ba, ina nan ina ji da mazan ke kiji da macen ba shike nan ba."
Mami ta yi wucewarta ta bar suna mata dariya.
Lamido na zaune a gefe ko tak bai ce ba, dukkansu shigar fararen kaya suka yi. A saman cafet din Ammah suka baje suna cin abincin LamiÉ—o salat kawai ya ke ci da miyan shinkafan kaÉ—an yake É—ibaa, duk hiran da ake yi ba kasafai yake saka musu baki ba.
Ko Mami sun gaisa irin gaisuwan da suka saba, ya tambayi su Islam tace ai za su haÉ—u gobe za su taho tare da babansu, ya kasa ce mata shi yau zai koma Lagos, sai kawai ya yi mata shuru.
Baffa kuma ba ya nan ma ba a masallaci É—aya suka yi sallar Jumma'a da shi ba, da wuri ya tafi yace akwai wanda zai gani ne.
Ita dai Ummu sai da ta gama cin abincin ta sha ruwa sannan ta ji ta ta dawo daidai, sai cikinta ya sake yin ƙasa saboda ta ci Abinci kwanciya ta yi ta gefe tana ɗan sauke numfashi ta kasa zama saboda tana jin cikinta ya cika.
Mami ne ta sake shigowa ta shiga tiolet tana yi ma Ummu sannu ta amsa dakyar.
Shigan ta ba daɗewa Ammah ta leƙo ganin Ummun kwance ya sa ta ce" ke kuma daga ci sai kwanciya."
Ummu ta yunkura ta tashi zaune kafafunta a kasan cafet duk sun kumbura.
"Ammah na kasa zama ne."
"Da dai kin daure."
Ta faÉ—a tana É—an kallonta ganin tana É—an cije baki.
"Sannu."
Ammah ta ce cikin tausayawa tana kallonta.
"Ga LamiÉ—o nan zai wuce ya ce zai shigo ya sake duba ki.'
Sai Ummu ta fara kifta idanuwana saboda mamaki.
Hamma Lamiɗo ne zai ce zai shigo ya duba ta, abin da ba ta taba zato ba. Ta tuna wani lokaci a baya can tun ba ta yi aure ba, ta taɓa wani irin ciwo kamar za ta mutu na typiod , kowa ya yi mata sannu ya duba ta amma ban da shi, ita tana jin ma sannu na ciwo bai taɓa shiga tsakanin su ba.
Kafin ma ta yi wani yunkuri Ammah ta fita, ta miƙe dakyar domin ta nemi hijabi ta saka sai ga Ammah ta dawo bayanta kuma Hamma Lamiɗo ne ya sawo kai cikin ƙwarjininsa.
"Gata nan ai hannu ya É—auko warkewa."
Ammah ta faɗa tana nuna masa Ummu Salma da ta sandare a tsaye ga ciki a gaba kanta ba ɗan kwalli wani tujajjan kitso ne da ba ta san ma daɗewar shi ba, tun dawowarta gida tana jin sau ɗaya ta taba yin kitso shima Baɗɗo ce ta ga kan ya tsufa ta tsefe ta ɗan yi mata duka baya guda goma kitson bai wani kamu ba, shi ya sa duk ya zare da wuri.
Ummu kunyar duniya duk ya kamata sai kawai ta dukar da kanta ta koma tana wasa da zaren adon rigan jikinta doguwa mai kalan purple.
"Auta ba ki gaishe da yayan na ki ba, jininsa ya cece ki daga mutuwa don kaniyarki"
Ammah ta faÉ—a cikin É—an zolaya.
"Ina yini Ha. Hamma."
Ta faÉ—a cikin É—an rawan murya.
"Lafiya."
Ya amsa a saman leɓensa.
Hamma Abdullahi ne ya kira Ammah daga falo sai ta fita ta bar Ummu da LamiÉ—o a É—akin. Tuni ta ji jikinta ya fara rawa, haÉ—a inuwa É—aya da Hamma LamiÉ—o ma tashin hankali ne zuciyanta taji tana tsinkewa kamar kasa ta tsage ta shige.
Shuru na mintina biyar ta ma ɗauka ya bar ɗakin ne tana ɗagowa suka haɗa ido, ya kafeta da kaifaffun idanuwansa hannayensa duka zube a cikin aljihun wandon farar shaddar jikinsa. Kafarsa akwai safa amma bai ɓoye zarazarab yatsun kafafunsa ba.
Da sauri ta sake sadda kanta ƙasa jikinta na sake ɗaukan bari, har ɗan cikinta sai da ya motsa.
"Ashe ba ki da wayau."
Ya faɗa cikin muryansa cike da ƙasaita
"Ban sani ba "
Ya dire maganarsa yana mai kafe ta da idanuwansa.
Ummu ta kifta ido ta buÉ—e sai hawaye sharr suka kece mata ba ta son ana tuna mata shirmen da ta yi, ba ta so.
"Kin san abin da kika yi."
Numfashi ya ja kafin ya dire.
"Ya saka Ammah Suma."
Ya dire maganarsa abin na sukan zuciyansa. Yana tuna lokacin da Ammah ta zube a kasa a bakin emergency, ya ji tsoro ya kuma ji fargaban in wani abu ya same ta ya zai yi??
"Kina so ki kashe mini uwa ne.?
Ya faÉ—a ya É—an É—aga murya.
Wai uwa, itama ai mahaifiyarta ce.
Tuni har ta fara kuka har yana sauti
"In kin shirya mutuwa saboda wani rubbish, "
Ya dakata yana ɗan sauke numfashi domin ya fara harzuƙa in ma ya tuna dalilin da yarinyar nan ta nemi kashe kanta
"To ki mutu, amma kar ki bari sanadin haka ya taɓa Ammah ko Baffa."
Ummu ta fashe da kuka sai ga ta duke ganin ta ƙasa durƙusawan zai yi mata wahala sai kawai ta baje a zaune tana kuka har da gunji. Mami na makewayi sai faman Uhm uhm take yi amma Lamiɗo bai saurare ta ba, bai ma nuna yaji ba.
"Hamma ka yi.."
"Will you keep your mouth shut."
Lamiɗo ya faɗa cikin murya mai amo da ta yi sanadiyar shigowar su Ammah ɗakin cikin mamaki, kafin ka ji muryan Lamiɗo a sama ahaka ana daɗewa sai in ranshi ya ɓaci ganin Ummu durkushe tana kuka ya ba su amsar tambayar su.
"Ai gwara kai ma ka yi mata faÉ—a yarinya kamar wacce ba ta yi makaranta ba? Har gobe in na tuna da abin da ta yi sai na ji kamar na mutu saboda bakin ciki. Baffa da Mami sun yi tsaye sun hana a yi mata faÉ—a."
Hamma Abdulrrahaman ya faÉ—a cikin jin haushi, shi ya ji daÉ—i domin har gobe bai huce ba tunda ba a bari ya yi mata duka ba.
"Me ya sa kike kuka?
Ya cigaba da mgana cikin kaushin muryasa.
"Me ya sa lokacin da za ki aikata ba ki tuna da komai ba.?
Ummu dai ta daina kuka ta haÉ—iye shi, tun tsawar da ya yi mata da farko.
"Tunda ya ce ba ya sonki ya sake ki."
"Dole ne."
"Za ki yi pushing kanki in to a relatioship É—in da ba ki da amfani ne a wajen ne?
Are you Stupid? Ko ke ba ki da wata daraja matsayinki ta Æ´'a mace ne?
Ya gama faɗa a jere yana haki cikin ɓacin rai.
"FaÉ—a ma ta dai LamiÉ—o "
Ammah ta faɗa cikin bacin rai, ba ta ma son tuna abin saboda ɓacin ran da ta ke shiga
"Ki sani kina da komai ba ki kuma rasa komai va saboda haka ki sani wannan abin da kika yi is a stupidity, kuma kar ki sake."
Ya faÉ—a har yana É—aga murya.
"Domin in kika sake ba mgana zan tsaya ina yi dake ba. I will deal with you. "
Ya faÉ—a yana É—an jinjina kansa.
Ummu kuka har da majina.
"Ku yi haƙuri."
Take faÉ—a, tana kuka Hamma Abdulrrahman ya cigaba da faÉ—a yana masifa.
Daidai lokacin Mami ta fito daga tiolet, cikinta ne ya karta tun É—azu take Allah Allah ta fito, saboda ta ga an yi ma Auta taron dangi.
"A'a Lauya bari, shi ya yi na shi ya gama kai kuma sai ka É—ora naka! Wallahi ku fita daga idanuwana na rufe."
Mami ta fada tana isa gaban Ummu ta duka tana fadin" is ok ya isa yi shurun ki"
Hawaye take share mata da hannayenta.
"Fatima ki bari a yi mata faÉ—a don Allah."
Ammah ta faÉ—a da ya sa Mami ta tashi a fusace tana fadin" To duk ba an yi mata ba, kuma ta yi nadama don Allah ku ko kukan da take yi bai ba ku tausayi ba?
"Wani tausayi? Mu ma ai haka ta É—aga mana hankali."
"To ta ji, ku fita kawai."
Mami ta katse Hamma Abdulrraahman tana nuna musu hanyar fita, LamiÉ—o ya juya zai fita Mami ta jawo hannunshi tana fadin" Kai ne ka fara ko? Kai ba ka san na saka dokar kar wanda ya yi ma Auta mgana ba? Kalli yadda ka sanya ta kuka juna biyu gare ta ba fa"
Mamaki ya kama shi sai kawai ya tsaya yana kallon Mami bai yi magana ba.
"Ammah ja zugan yayanki ku je falo. Ganin su ma firgita mini yarinya yake yi "
Ta faÉ—a tana sakin hannun Lamido ta juya ga Ummu.
Ya daÉ—e yana kallon hannun shi da ta rike, kafin ya juya ya bar É—akin.
Ammah ta ce su fita kawai.
"Ke ma dai Fatima ki zama mai gaskiya "
"Gaskiyan kenan Ammah."
Ta faÉ—a bayan sun fice.
Nan suka bar Mami da zaman lallashi, Ummu ta yi ta kuka tana ce ma Mami ta yi nadama ba za ta kara ba..
Haka Mami ta yi ta masifa, da hamma Abdulrahaman shi dai Lamiɗo ya gudu Hamma Abdullahi ya tafi kai shi filin jirgi.
"Wai ina ganin Basamuden É—an Ammah da ba ya magana, shi ne zai zo ya tasa ya'ta yana yi mata faÉ—a, wallahi da ina kusa bai isa ba."
"Kar ku manta dai ya ba ta jininsa, ba domin shi ba da yanzu kina zaman makoki.,"
Ammah ta faÉ—a tana dariya.
"To sai me! Ai don Allah ya yi kuma ba a saka shi ba, da sai ya bari a saka mata na siya "
Ammah na ta dariyan Mamin ganin ta da karfin hali.
"Shima É—ana taimako ya yi, kuma fadan da ya yi mata na ta so kanta ne."
"To ina ruwan shi? Sai da ta warke ne zai zo da wani tsawonsa kamar falla waya yana yi ma mutane faɗa "
Mami ta sake faÉ—a cikin kufululewa.