← Book details Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 92

Sashe 24

Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baɗɗo ta faɗa lokaci ɗaya tana miƙewa. Ummu ta kalle ta a sanyaye kafin ta ce" Nima ina son na je asibiti ba ni da lafiya sosai."
"Yanzu za ki tashi mu je."
Ummu ta sake kallonta kafin ta ce" Habib bai sani ba."
Baɗɗo ta ji kamar ta rufe Ummu da duka saboda baƙin ciki da takaici.

"Kina ganin in na fita bai sani ba, ba matsala.?

Ta sake tambayan ta a sanyaye.

Sai da BaÉ—É—o ta ya fa mayafin ta sannan ta kalli Ummu tana faÉ—in" Yana gidan kike fama da ciwo amma bai damu da ke ba, kin ga kenan in kin fita domin neman lafiyarki hakan ba matsala ba ne."
Ummu ta girgiza kai kafin ta ce" A'a bari dai na kira shi na sanar da shi."
Kasa ma mgana BaÉ—É—o ta yi sai ma ta koma ta zauna tana kallo Ummu ta tashi tana dafe dafen bango ta koma bedroom É—in ta sai ga shi ta fito da wayarta a hannu tana ta kiran wayar Habib amma sai a saka kiran na ta a forwording.

"Ba na samun shi."

Ta faÉ—a a sanyaye

BaÉ—É—o ta yi kamar ba ta ji ta ba haushi duk ya ishe ta.

"Ya zan yi yanzu?

"Ki zauna sai lokacin da kika same shi a waya, in ya ce ma kar ki je ki zauna ki mutu"

Ta faɗa cikin haushi jin haka 
Ya sa jikin Ummu ya sake yin sanyi ta zauna kusa da BaÉ—É—o tana mai marairaicewa.

"Ya zan yi to? Na rasa tunanin da zan yi?

Ta faɗa hawaye suna taruwa a ƙwarmin idanuwanta.

"Ki ta shi na raka ki asibiti a duba lafiyarki Ummu-Salma."

Baɗɗo ta faɗa tana mai sake miƙewa tsaye wannan karon har tana rataya jakar da ta zo da ita ba yadda Ummu ta iya haka ta ɗauko hijabi ta da ƙaramar jakarta da Atm ɗin ta ke ciki ba ta da kuɗi a hannunta, kulle ɗakin suka yi suka fita zuwa bakin titi sannan suka hau Keke Napep zuwa asibitin da Ummu ta ke da fayel, boshon clinic da taimakon Baɗɗo dake  riƙe da ita. Suna zuwa suka ga likita da ya ke ta je da katin ta, likitan na ta faɗa cewa babu wadattacen ruwa a jikinta sannan akwai maleria mai zafi a tare da ita.

Riƙe ta suka yi bayan sun saka mata drip sun yi mata allurai har da na barci ta samu barci sannan likita ya ce Ummu ba ta cin abinci sannan ga jinin ta ya ɗan hau shi ya sa za su rike ta zuwa yamma su gani. Baɗɗo ce ta zauna da ita a asibiti nan tun kafin azahar sai gabda mangariba kuma ba ta kira kowa ba, Ummin ikki dai ta kira ta ganin duhu ya shiga ba ta dawo ba sai ta ce mata ta samu Ummu na fama da zazzaɓi ta ɗan taya ta ayyuka ne amma in dare ya yi sosai ba ta dawo ba to za ta  kwana tare da ita, ta yi ma Ummin ƙaryan cewa Habib ba ya nan ya yi tafiya.

An sallami Ummu tare da magunguna da dokokin likita bayan ta sha leda uku na ruwa sai kuma ta ji daɗin jikinta ta daina jin jirin nan da ciwon kai, ya ce ta samu hutu sosai ma'ana sun ba ta bedrest sannan ta riƙa cin abincin domin inganta jaririn dake cikin ta. Ba su suka shigo gida ba sai ana kiran sallar isha'i kuma har a lokacin Habib bai dawo ba, Ummu wanka ta yi ta shiga  rama salollin da ke kanta ita kuma Baɗɗo bayan ta yi sallar isha'i ta zage tana gyara gidan duk ya yi ƙura tun da Ummu tana ta kanta ba ta gyaran gida ba, har fashasshen kwalban da ke saman dinning Baɗɗo ce ta kwashe shi ta gyara wajen lemun da Habib ya saka ma mganin ita ta kwarara shi a tiolet ta saka kwalayen exotic ɗin a dusbin
sannan ta yi ma Ummu faten wake ta so ta saka allayahu amma babu, kuma  in da ake siyarwa sai kasuwa.

An ci sa'a kuma Ummu ta ci faten waken bai dawo mata ba sai ta ɗora da ruwan lipton mai zafi ya samu ya warware mata ciki sannan Baɗɗo ta ba ta magungunar ta tasha, ta ji daɗi da Baɗɗon ta ce mata sai gobe da safe za ta tafi in ta ga jikin na ta da sauƙi. Suna zaune a falo Ummu na kwance kanta na saman cinyar Baɗɗo suna kallo gefe ɗaya kuma suna hira sama sama sai aka kira Baɗɗo a waya wata class mate ɗin ta ce, ganin suna mgana ne ya sa Ummu ta shiga tunani mai zurfi tsoron ta in mganar nan ta je kunnen Baffa har yayyenta suka ji labari sai Habib ya gane ba shi da wayau sannan tana da tabbacin sai sun raba auran nan da nan a cikin su akwai waɗanda ba su so auren nata ba, ba wai don ba su son Habib ba, a cewar su karatu ya kamata ta cigaba da yi ba aure ba ita kuma ba saboda haɗuwarta da Habib ba. Tun tana ƙarama da ta fahimci ba ta da ƙwaƙwalwar karatu ta ce ita daga sakandiri ba ta son ta cigaba da karatu.

A lokacin ba tasa aure a lissafin ta ba domin ba ta ɗauka za ta haɗu da Habib a gabar ba, shi ya sa son auren ma baya cikin lissafin ta, ba ta taɓa tunanin za ta haɗu da Habib a lokacin ba ballanta har aure ya shiga tsakanin su ba. Abu ne da ya faru lokaci kaɗan haɗuwarsu da auren su wattani biyar ne a wancan lokacin Hamma Kabiru ya yi ta faɗa da cewa an yi gaggawa ya kamata a ɗan sake jira, shi kuma Baffa ya ce tunda dai Ummu tana so kuma shima Habib ɗin ya shirya bai ga amfanin ɓata lokaci ba. Tsoron ta ɗaya in suka ji mganar ba ta san yadda lamarin zai ƙare ba, wataƙila ya yi lalacewar da kafin lamarin ya gyaru za a ɗau lokaci.

Ta yi nisa cikin tunaninta ba ta san shigowar Habib ba, sai da ta ji ƙamshin turaran shi sannan ta farga, tana ɗagowa suka haɗa ido huɗu da shi yana tsaye yana kallon su. Da sauri ta miƙe zaune tana kallon shi, jikinta har rawa ya ke yi saboda ganin Habib ba ta san ta yi kewarsa ba sai da ta gan  shi, ta ji wani irin sanyi a cikin ranta.

"Sannu da zuwa Noori."

Ta faɗa lokacin da take miƙewa tsaye. Baɗɗo na zaune tana ganin ikon Allah. Sai da ta ga Habib sannan ta san a ɗazu ba haushin shi take ji ba, yanzu ne ta ke jin kamar ta rufe shi da duka da ta gan shi. Barin ma yadda yake bin Ummu da wani kallon banza ita ko baiwar Allah hannu ta miƙa za ta karɓi jakar hannunsa da sauri ya kauce ya kuma raɓa ta zai wuce ciki Baɗɗo ta ga ba za ta iya jurewa ta miƙe a fusace.

"Habib."

Ta kira sunan shi a kausashe, sai ya tsaya kafin ya juyo fuskar nan kamar bai taɓa dariya ba. Yadda ya yi ma kamar bai taɓa ganin Baɗɗo ba.

"Ina son mgana da kai."

Tana kallon cikin idanuwansa ta faÉ—i haka.

"SisNa kar ki ce masa komai don Allah."

Ummu ta faÉ—a tana mai rike hannun BaÉ—É—o cikin magiya.

"Bar ta ta faÉ—i abin da ke bakin ta, in tana tunanin za ta iya sauya tunanina ne akan mganar da za ta yi Bismillah."

Ya ba ta amsa har yana wani É—aga hannu, BaÉ—É—o ta kalle shi cikin wani yanayi shima kai tsayen yake kallon ta.

"Na san ta faÉ—a miki abin da ke faruwa, in har ke yar'uwata ce da gaske gwara ki ba ta shawaran ta bi umarnina in tana so ta tsira da sauran abin da ya rage mata."

Ya faɗa cikin gadara sannan yana nuna Ummu kamar ya ga abin ƙyama.

"Domin ba ta da wani sauran wani abin da ya rage a tsakanin mu yanzu."

Ba Ummu ba, hatta BaÉ—É—o sai da ta ji ta muzanta idanuwanta suka kawo ruwa sai ta yi saurin shanyewa.

"Habib Allah ya fika."

Haka kawai Baɗɗo ta faɗa ta ja hannun Ummu suka raɓa ta gefen shi, Ummu tirjiya take yi amma Baɗɗo ba ta sake ta ba sai da suka shiga cikin bedroom ɗinta ta kuma ma yar da kofa ta rufe, suna jiyo dariyan Habib na tura haushi.

"Ki bar ni na je na ba shi haƙuri."

Ummu ta faɗa tana nufar ƙofar Bedroom ɗin da ƙarfi Baɗɗo ta ce" Wallahi in kika fita daga ɗaki nan, sai na kira Baffa na faɗa masa duk abin da ke faruwa."
Kalaman Baɗɗo suka sarƙe ta, ta kasa gaba ballanta baya, kuma yadda Baɗɗo ta ɗau alwashi ba za ta fasa abin da ta ce ba shi ya sa ta koma kawai ta kwanta a saman gado ta fashe da kuka.

"Ina son Habib. Ina so na bashi hakuri mu dawo kamar baya."

Dole Baɗɗo ta sauko ta fara lallashin Ummu domin ta fahimci tana son Habib kuma tana son cikin ta, ba ta da wata mafita ne a yanzu. Sun daɗe ba su yi barci ba Baɗdo na sake ba ta baki sai dai ta ba ta tabbaacin in har Habib bai daina yunƙurin zubar mata da ciki ba to ta koma gida kar ta sake zama yana wulakanta ta alhalin tana da gata.
Chapter 24 · 0% Book details