← Book details Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 92

Sashe 38

Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya faÉ—a a fili yana dafe kai, a cikin kayattacen É—akin hotel É—in da bankin su ta kama musu.
Da man ko ba a kira shi ba ya gama yanke shawaran in har ya koma ya ga yunwa bai saka Ummu tafiya gida ba to zai sallame ta, har ga Allah ya gaji da shiga damuwa akan ta.

**

Hamma Jibo a ranar lahadin da sassafe suka É—au hanya shi da iyalan shi, da yake tafiyar mota suka yi wannan karon shi ya sa suka fita da wuri, sun rabu da Baffa akan duk halin da ake ciki zai kira shi ya sanar da shi, sannan Ummu ma sun yi waya ya sanar da ita ya faÉ—a ma Baffa komai amma bai faÉ—a mata Baffa ya je wajen waliyin Habib ba, shi dai ya jadadda mata ta kula da kanta sannan ta zama jaruma ko da wani abu zai faru ta sani Allah ne ya jarabce ta ba wani ba.

Ta amsa masa da in sha Allahu, domin ita tuni ta san wannan karatun ita da rayuwarta ta yi juyin waina cikin lokaci, Habib ma ba ya kwana a gidan yanzu ba ta san ya yi tafiya ba a tunanin ta tunda yanzu ba ya buƙatar ta shi ya sa ya daina ma kwana a in da take shaƙan numfashi.

Kamar wasa a ranar tana zaune tana cin abinci  da yamma gabda mangariba sai ga Habib ya shigo gidan. Ko kallon ta bai yi ba ballantana ta saka ran cewa zai iya jin tausayinta bayan ya kalle ta, shigewa ciki ya yi ya barta anan tana tsiyayan hawayen da suka zame mata jiki, sai ta ma kasa cin abincin ƙwata-ƙwata sai juya shi cokalin take yi a hannun ta, shinkafa da wake ne da man da dafa sai ta saka allayahu sosai ya ji saboda dokar likita yunwa take ji tana zumuɗin cin abincin amma ganin Habib ya sa komai ya ƙwace mata. Hawaye suka kece mata wasu na gangara wasu na kawowa tana tuna irin rayuwar da suka gudanar ita da Habib tun daga soyayyarsu har zuwa auren su. Ta daɗe tana alfahari da buɗe kafaɗan cewa ba wata macen da ta kai ta dacen miji mai son ta da ƙaunarta. Ba ta taɓa tunanin nan kusa za ta fuskanci kuka da damuwa ba, ba ta taɓa zaton wata rana ita Ummu Salma za ta zama wacce Habib ya tsana ba ya son gani ba sai yanzu da yake faruwa, su Baɗɗo sun daɗe suna fata da ƙwatancen su zama kamar ita domin sun ɗauka tarihin soyayyarta ya kai a ba da labarin shi da zai sa mata da dama su ji suna jin haushi da yadda ta yi dace ta bar su, tabbas za a ba da labarin soyayyarta da na rayuwarta gabaɗaya Habib zai sa ta zama abin nunawa da kwatance a cikin dangi da anguwa gabaɗaya.

Tana nan zaune tana kuka Habib ya sake fitowa, ta kifa kanta a saman hannun kujeran da take zaune tana ta kuka har yana fidda sauti, yadda ya shigo bai kalleta ba haka ya sake fita bai ko kalli in da take ba amma ita ta ɗan ɗago ta kalle shi ya yi wanka ya sauya kaya zuwa manya yana ta tashin ƙamshin turare. A baya in ta kalli Habib wani nishaɗi da alfahari take ji , wani irin son shi ke ƙaruwa in ta kalle shi amma sai ga shi yanzu in ta kalle shi sai ta ji nadama da baƙin ciki yadda in da za a ba da tarihin rayuwarta sai an fara da Habib watakila ma a ƙare da shi tunda Habib ya gama kassara rayuwarta gaba da baya ba ta kuma da sauran wata mamora.

Abincin da ta hakura dashi kenan ba ta ci ba, sai ta mai da shi kitchen ta ajiye ruwa kawai ta iya sha ta koma ciki ta kwanta tana jan casbaha tana kuma kuka lokaci ɗaya. Addu'a take yi ubangiji ya yaye mata ƙunci da damuwar dake cikin zuciyarta Allah ya ba ta ikon cin jarabawanta, cikin da ke jikin ta Allah ya kare shi ta daina ma adduan Allah ya karkato da hankalin Habib kanta, ta yarda kuma ta amince da gaske Habib yake yi bai taɓa son ta ba, shi kuma wanda  ya furta ba ya son ka, to ba zai taɓa son ka ba har gaban abada.

**

Habib na fita daga gidan anguwansu ya nufa yana hanya sai ya ji ana ta kiran sallar mangariba shi ya sa bai shiga gidan na su ba sai da ya tsaya ya yi sallar mangariba sannan ya shiga gidan na su ya gaishe da matan mahaifin shi sannan ya shiga É—akin da mahaifin shi ke jinya ya zauna.

Hatsari ya yi shekaru goma da suka wuce, ya bugu a kansa har ya shafi ƙwaƙwalwarsa sannan ƙugunsa ya samu matsala baya iya zama daga kwanciya sai kwanciya sannan baya mgana sai dai ya yi ta kallo ka kawai da idanuwana sannan kan ma da sauƙi.

Har kusa da shi ya ƙarisa ya riƙe hannun shi yana gaishe shi yana ta dai kallon shi. Gwaggo ta shigo ita ce babba a matan gidan kuma ita ce ta riƙe Habibu, sai dai a gidan shi ne kaɗai ke da ɗan rufin asiri shi ne Namiji babba sauran duk mata ne suna gidan mazajen su shi ya sa duk ɗawainiyar gidansu tana wuyan sa, da laluran mahaifinsa na shekaru goma ana ta fama, a dangin mahaifin na shi ban da Alhaji Sheriff to kowa ma nema yake yi lamarin dai sai godiya.

Gwaggo ta tambayi Ummu da ina tafisu, ya ce tana gida ta ce a gaishe su ya yi ƙarya. Itama ganin ta kwana biyu ba ta zo ba ne ya sa ta tambaya. Tare da Gwaggo suka yi ta hira a ɗakin Mahaifin na shi suna cikin hiran ne Alhaji Sheriff ya kira shi a waya yana tambayan sa ko ya dawo? Sai ya ce ma ga shi a gida kawai sai ya ce su haɗu a gidan bayan an yi issha'i shima zai zo gidan.

Habib ya sha mamakin ganin har da Baba Usman ma ya zo, ya É—auka ya zo duba É—an'uwansa ne tunda yana zuwa amma sai ya ji yana tambayan shi ko sun yi waya da Alhaji Sheriff?
Sai ya ce masa sun yi ya ce zai zo bayan sallan isha'i. Jin da ya yi Baba Usman ya ce to bari su yi sallan su jira zuwan shi ya sa sha jinin jikin shi.

Tare da Baba Usman suka yi salla a masallacin kusa da gidan su suna idarwa suka dawo gidan sai suka iske Alhaji Sheriff ya iso da yake shi a anguwansu sukan riga nan anguwan yin sallan su, tun da Habib ya ga Gwaggo bayan sun gaisa da Alhaji Sheriff ta miƙe za ta fita ya ce ta dawo ta zauna maganar ta shafe ta daga nan ya san lamarin ya yi ƙamarin da ya wuce na shi lissafin.

Ƙansa na ƙasa ya ji Alhaji Sheriff na jero maganganu Gwaggo na salati ya kwashe yadda abin ya faro tun daga farko har zuwan Mahaifin Ummu Salma wajen shi da yadda suka tattauna.

"Habibu ba ka kyauta ba sam."

Gwaggo ta faɗa tana kallon shi cikin mamaki shi dai kansa na ƙasa amma ransa ya ɓaci.

"Ya ci amanar aure, abin na shi har ya kai ya fara yi ma iyalan na shi horan yunwa? Ga juna biyu in wani abu ya same ta iyayenta suka yi ƙaran shi a kotu ba? Yana da kalaman da zai iya kare kanshi da su ne?

Baba Usman ya faÉ—a yana kallon Habibu da ya ji duk ya muzanta. Ga shi a gaban mahaifin shi suna ta maimaita maganar, duk da ba ya magana amma yana jin duk abin da ke faruwa a É—akin.

"To kun ji dai halin da ake ciki, tun da har na yi masa faɗa bai ji ba shi ya sa na ce mu taru anan ga mahaifin shi tare da ke mariƙiyarsa domin kun san halin da ake ciki. Mahaifinta ya ba ni saƙo na ba shi, ya ce in har ba ya son yar sa to ya dawo masa da ita shi bai gaji da ciyar da ita ba."

"Yana da gaskiya."

Gwaggo ta faÉ—a tana mai hararan Habib

"Habibu me ya same ka! Kai fa da kanka ka zo ka ce kana son yarinyar nan aka je aka nema maka auranta, auren ko shekara bai yi ba amma an fara samun matsala, kana ɗan musulmi bafillace ka ce sai an zubar da ciki? An ya kana so ka yi albarka kuwa ba ka san ya'ya rahama ba ne! Ka san wanda zai ji ƙan ka anan gaba ne?

Gwaggo ta faɗa tana kallon shi, ya ma kasa mgana jujjuya saƙon da aka ce mahaifin Ummu ya bar masa yake yi a cikin zuciyarsa. Lalle ko zai dawo masa da ƴarsa gida tunda  haka ya buƙata.

"Kuma yana da tabbacin in ya zubar da cikin ubangiji zai sake ba shi wani damar a gaba ne? Yana da ilimin shi amma Habibu na neman ya yi ma kansa sakarci."

Baba Usman ya faɗa yana zaune kusa da Alhaji Sheriff, amma har lokacin Habib bai tanka ba, ya sunkunyar da kansa kawai yana wani tunani. Ba zai ce komai da zai ɓata musu rai ba saboda nan gaba za su yi masa amfani.

"Ni dai na gama iya ƙoƙarina na zare hannuna akan duk abin da ya shafi Habibu tun da ba ya jin magana. Ya je ya yi duk abin da zai yi amma ya sani in har ya gaji da zama da yarinyar mutane ne gwara ya sake ta zai fi alheri akan ya zauna yana azabtar da ita"

Alhaji Sheriff ya faɗa yana nuna Habibu kafin ya cigaba da faɗin" Shi ya sa na tara ku gwara kun san abin da ke faruwa. Ke Aina'u ki yi masa mgana wataƙila ya saurare ki, ni dai na gama nawa"
Yana gama faɗin haka ya tashi zai fita Gwaggo da Baba Usman suna ta ba shi haƙuri.
Chapter 38 · 0% Book details