← Book details Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 92

Sashe 81

Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali a hankali ganin ta ya fara washewa. Daƙyar ta iya ɗan waiga damanta da hagunta, daga lokacin ne ta fahimci kamar tana asibiti ne domin a yanayin ɗakin ita kaɗai ne a kan ƙaramin gado sannan ta ga tsitsiyan hannunta guda ɗaya da ƙarin ruwa.

Me ya same ta? Me ta sa take kwance  a asibiti?
Tana so ta yi tunanin yanayinta na ƙarshe amma ta kasa, kanta ya yi mata nauyi kamar ba na ta ba.
Tsil ta ji daga gefen cikin ta, sai ta É—an daga idanuwanta, ciki ta gani ya yi tsini a jikinta gabanta ya faÉ—i ras! A lokaci É—aya kuma tunanin abin da ya sameta ya fara dawowa cikin kanta daki daki.

"Hasbunallahi wani'mal wakeel."

Hawaye ne masu zafi suka fara gangaro mata ta gefe da gefen idanuwanta masu raɗaɗi sai a yanzu ta samu damar kuka sai a yanzu ne nadama da dana sani suka rufeta sai a yanzu ta ke tunanin da a ce ta mutu fa? Shike nan ta mutu a kafira sai a yanzu ta tuna da Baffa da Ammah, sannan sai a yanzu ne ta tuna da sauran yan'uwanta amma a lokacin idanuwanta sun rufe zuciyanta ta ƙuntata fatan ta kawai ta yi nesa da jin zafin zuciya da raɗaɗi burinta ta samu salama da raɗaɗin dake taso mata a cikin kasan zuciyanta. Amma ina haƙanta bai cimma ruwa ba, ga in da ta kare nan, wataƙila Allah ne yake son ta shi ya sa ya ba ta wata damar.

Ƙokarin tashi take yi amma ta kasa tana cikin wannan yanayin ne aka buɗe kofar ɗakin lokaci ɗaya wata nurse da fararen kaya ta bayyana a cikin ɗakin.
Cikin ruwan hawaye Ummu Salma ta É—ago kanta tana kallon Nurse É—in da ta shigo.

"Laa kin farka?

Nurse ɗin ta faɗa tana kallon Ummu kafin lokaci ɗaya ta juya da sauri ta fice daga ɗakin. Ummu ta bi ta da kallo a tunaninta in ta ƙariso za ta ce ta taimaka mata ta zauna sannan ta cire mata wannan igiya mai takumkumi da yake hanata numfashi da magana.

Tana cigaba da ƙoƙarin tashi zaunen aka sake buɗe kofar aka shigo. Wannan karon ba iya mutum ɗaya ba ne,  likita ne akan gaba sanye da rigansu na likitoci da zugan wasu Nurses guda uku daga bayansa ciki har da wacce ta fara shigowa da farko.

"Ma sha Allah"

Ta ji ya faɗa lokaci ɗaya yana ƙarisowa gaban gadon da take kwance.
Kallon shi ta yi da idanuwanta da suka shige ciki mamaki ta yi da jin abin da ya faÉ—a ba ta yi tunanin ma musulmi ba ne sai da ya sake magana sai ta sake shan mamaki.

"Sannu ko?

Ya sake faÉ—a yana kallonta da É—an mirmishi a saman fuskar shi.
Bayan musulmi ne, ashe ma yana jin hausa ba ta É—auka ma yana ji ba ganinsa jajir kamar bature.
Idanuwanta ta ɗan motsa tana cigaba da ƙokarin tashi ta zauna.

"Kina so ki zauna ne?
Ya tambayeta. Ita kuma sai ta lumshe idanuwanta ta sake buÉ—e domin ba zata iya É—aga kan ta ba, ji take yi kamar kanta zai rabe gida biyu.

"Okay.."

Ya faɗa lokaci ɗaya ya kalli Nurse ɗin dake gefensa da ido kawai ya yi mata magana nan da nan sai gata ta nufo ta,  ta saka hannu ta cire mata abin da ya tare bakinta daga magana da shakar numfashi da kyau.
Sannan kuma ta cire mata zaren karin ruwan dake tsitsiyan hannunta na hagu, amma ba ta cire canula É—in ba sai a lokacin ma ta lura hannunta ya kumbura sosai watakila an yi ta fama kafin a samu jijiyar ne.
Hannunta na dama Nurse ɗin ta kama za ta ɗan dago ta, ita kuma sai ta yi amfani da hannunta na hagu ta ɗan dafa gefen gado lokaci ɗaya ta ji wani mugun zafi ya ziyarce ta har ƙwaƙwalwa.

"Wash..!

Ta faÉ—a cikin fitan hayyaci murya a dashe.

"Sorry, ki yi a hankali kin san left hand ɗinta akwai  rauni."
Sai da ya faÉ—a haka sannan ta iya duba hannun nata na hagu, dai dai ta É—an É—agota ta zauna tana jin bayanta na sagewa saboda kwanciya.

Rabin hannunta na hagu yana nannade da bandeji ne, ƙura ma hannu ido ta yi tana kallo hawaye na sake biyo kumatunta kamar an buɗe famfo.

"Sannu ko?

Ta ji an sake faÉ—a sai ta É—an dago tana kallon likitan lokaci É—aya ta na É—an gyaÉ—a kanta dakyar.
Kujera suka matso masa da shi wata fara ya zauna a gabanta, ɗaya Nurse ɗin ta miƙa masa Fayel ɗin Ummu Salma a hannun shi ya buɗe yana dubawa.

"Ummu Salma Hadi Baba right?

Dr. Ahmad ya faÉ—a yana sake kallonta ta cikin farin gilashin dake fuskarta.
Nan ma kai ta gyaÉ—a masa cikin karfin hali, jin ta take yi kamar ba ita ba komai na jikinta ya yi mata kamar ba nata ba.

Doguwar rigar dake jikinta ne na ranar da abin ya faru amma an yanke duka hannuwanta watakila da aka kawota asibiti ne wajen sauƙaka ma likitoci aiki ne ya sa suka yanke sannan mamaki take yi anan ta kwana ne? Tunda dai dai ta san lokacin da ta yi ma kanta illa, dare ne amma yanzu tana facing window ɗin ɗakin tana kuma ganin haske alamun kamar yamma ne ko rana.

"Ba abin da ke damun ki ko?

Ta ji likitan ya sake faÉ—a yana kallonta kuma da harshen hausa yake yi mata mgana.

Idanuwanta ta lumshe ta sake buÉ—ewa alamun babu abin da ke damunta, sai nauyin jikinta da ciwon kai.
Dakyar ta iya buÉ—e baki ta ce" Kai na "

"Sannu."

"Da jikina kamar ba nawa ba."

Ta faÉ—a lokaci É—aya hawaye na kece mata wasu na zubowa wasu na sake tunkuÉ—owa.

"Sorry duk zai bari in sha Allahu."

Ya faÉ—a yana mai kallonta.

"Ya hannun ki? Ba wani pain?

Sai ta É—an bi hannun da kallo kafin ta É—an gyaÉ—a masa kai.

"Babu."

"Ya kike jin cikin jikin ki? Ba wata matsala dai ko?

Ya tambaya yana mai sake nazarinta.
Yana kallonta a matsayim mai sa'a a halin da aka kawo ta, bai É—auka za ta tashi ba.

"Babu,"

"Amma ina jin motsi."

"Lafiyan jaririyan dake cikin ki ne, mun yi miki scanning mun gamsu da cewa jaririn dake cikin ki bai shiga hatsari ba."

Ya faÉ—a yana É—auko biro daga gaban aljihunsa ya fara rubutu a cikin fayel É—in dake hannunsa.

"Ummu Salma."

Ya kira sunanta yana cigaba da rubutunsa.

"Naa'm"

Ta amsa cikin dashewar murya.

Shuru ya yi bai sake magana ba, ita kuma tana hawaye tana tunanin ita kaÉ—ai ne? Ina Ammah ina Baffa? Ina sauran danginta? Ba ta gansu ba.

"Ina iyayena?

Ta faÉ—a gashin idanuwanta jike da ruwan hawaye.
Sai da ya gama rubutun shi sannan ya É—ago yana kallonta lokaci É—aya yana mika ma Nurse É—in dake gefen shi fayel ta rankwafa ta amsa cikin ladabi.

"Duk suna waje."

Ya faÉ—a yana nuna mata kofa.
"Suna jiran mu gama aikin mu sai mu ba su damar su shigo su duba ki."

Ya sake faÉ—a yana É—an wasa da biron hannunsa.
Kuka kawai Ummu take yi hawaye har sun jika mata gaban riganta, wannan ɗacin da zafin da ta so ta kashe kanta saboda shi, shi ne yanzu ya taso mata yana yi mata maƙakin a kasan zuciyarta ga shi yanzu ta sanya iyayenta da yan'uwanta a cikin damuwa.

"Ummu Salma."

Ya sake kiran sunanta.

"Za ki iya tuna dalilin da ya sa kika tsinci kanki a asibiti?

Ya tambaya kai tsaye yana mai kallon ta.
Hawaye suka sake kece mata zata tuna mana. Za ta tuna cin amanar da ƙawarta Shamsiya ta yi mata tare da Habib, wadanɗa suka ba yar da guddumuwa wajen gurguta yau ɗinta da gobenta. Har a yanzu kalaman Shamsiya na yi mata amsa kuwwa a cikin kanta ba za ta taɓa mantawa da abinda ya same ta ba, domin wannan baƙin cikin watakila in bai yi ajalinta ba, to har ta koma ga Allah yana nan a cikin zuciyarta kuma yana saka ma gangar jikinta ciwo.

"Kiin tuna?

Ya sake tambayanta

Kai ta gyaɗa masa cikin kuka da hawaye, shessheƙa take yi tana jin zuciyanta na bugawa da sauri da sauri.

"Kin san cewa tun shekaranjiya da daddarre aka kawo mana ke ba kya numfashi?
Ummu ta kalle shi cikin mamaki.
"Tun shekaranjiya?
Ta maimaita a saman laɓbanta.

"Daƙyar muka iya ceto rayuwanki, ga shi kina da juna biyu ga shi kin zubar da jini kin shiga hatsari sosai da yasa ko bayan mun ceto numfashin ki, mun sanya miki oxygen amma ba ki farfaɗo ba sai yanzun nan."
Majina ta ziraro ma Ummu amma ta kasa iya wani numfashi.

Kuka kawai take yi hawaye suna zubowa wasu na sake kwaranya.
Nadama take yi, dana sanin me ya sa ta aikata abin da ta aikata? Lalle Allah na son ta da ya sake ba ta wata damar a karo na biyu.

"Kin yanka hannun ki sau biyu kuma yanka mai zurfi. Kin zubar da jini sosai da ya sa sai da ɗan'uwanki ya ba ki jininsa leda biyu muka sanya miki. Ba domin shi ba, da wataƙila wajen neman jinin lokaci ya ƙure har ki mutu bamu samu damar ceto rayuwarki ba."

"Allah sarki É—an'uwa. "
Ta san ma Hamma Kabiru ne ya bata jininsa kamar yadda a baya ya taɓa bata jininsa.

"Me ya sa kika yi yunkurin kashe kanki Ummu Salma?

Dr Ahmad ya tambayeta kamar yadda yake a rubuce a jikin É—an aninin dake jikin rigan likitancin jikinsa.

Kuka Ummu Salma ta fashe da shi muryanta baya fita, bai hana ta ba gwara ta yi kukan ko zuciyanta za ta samu salama.
Yadda take rera kukan ne, abin tausayin duk wanda ke kusa da ita yake kuma sauraranta. Kuka ne mai taɓa zuciya kukan nadama da bakin ciki.
Nurses ɗin dake gefensa har akwai wacce ta yi ƙwalla jikinsu duk ya mutu.
Chapter 81 · 0% Book details