Sashe 7
Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce" Za mu je, zan yi ma Abdullahi(Baba) mgana."
"Baffa ka yi ma Abdurrahaman mgana ku zo tare da shi."
Sai ya jinjina mata kai kafin ya ce" Shike nan. Da ma kin sani kin yi ma Abdullahi(Baba) mgana ko da matarsa sai ku tafi."
Baki ta riƙe bakin ta ce" Na sha'afa wallahi bari zan yi masa mgana na ji."
"To Amman LamiÉ—o."
Tana dariya ta ce"Kai kuma Baffan LamiÉ—o ba."
Yana y'ar dariya ya ce" Na bar miki, duka matsayin tuntuni. Wannan LamiÉ—on naki ai sai ke. Ni fa cikin satin nan da ya doka mini kira cikin dare sai da ya sa jinina ya hau na É—auka ba lafiya ba ina É—aukan kiran cikin damuwa na ce" LamiÉ—o lafiya cikin daren nan?
BuÉ—ar bakinsa sai ce mini ya yi" Baffa me ya sa kake tambaya? Ai da man wannan ne lokacin da na ke kiran ku a waya"
Ja'irin yaron nan ko a jikinsa bai ma damu da É—aga mini hankalin da ya yi ba, muna gama gaisawa ya kashe wayarsa shi ya sa ma ko zan je ba saboda LamiÉ—o ba ne sai saboda zumunci da girman mahaifinsa , amma shi LamiÉ—o da na samu zuwa da kar na samu zuwa duka É—aya ne a wajen sa."
Amma na dariya Baffa na taya ta, ya ci gaba da faÉ—in" Ta bakin Fatima ta ce ba zan iya da É—an Ammah ba shegen faÉ—in rai. Ta manta jinin dake gudana a jikinshi."
Amma na gimtse dariyanta lokaci ɗaya tana faɗin" Ni fa bana ganin duk abin da ake faɗa akan Lamiɗo, a wajena yafi kowa sauƙin kai."
"Uhm da yake É—an gaban goshin ki ne ai ba kya ganin laifinsa. Gaskiya Fatima ne ke kika bata LamiÉ—o ya saba da komai ya yi dai-dai ne a wajen ki."
Amma ta dariya ta ce" to ba ta bar mini É—an ba, babu kuma ruwanta da ni balle rayuwar É—a na."
"Allah ya ba da sa'a."
Baffa ya faÉ—a Amma ta amsa da Amin..
"To iyalan na LamiÉ—on za su taho bikin dai ko? Domin shi gogan na san ba zai samu zuwa ba."
Amma ta ce" Gaskiya ya ce mini da wuya ya zo suna can ko wata ƙasa ne ma, sunan da wuyar faɗa Baffa, amma ita Balkisu ya ce za su taho tare da yaran gabaɗaya tun da sun samu hutun makaranta."
Baffa ya jinjina kai kafin ya ce" Hakan ma ya wadatar. Allah ya nuna mana lokacin."
Ta amsa da Amin suna cigaba da tattaunawa har sha biyu saura na dare sannnan suka yi shirin kwanciya sai bayan sun kwanta ne Amma ta ce.
"Baffa ka yi mgana da Ummu ne a kwanaki nan?
Baffa na daga kwance ya ce" Jiya ta kira ni da safe mun gaisa. Tana lafiya ita da mijinta, shima yau da safe sai da ya kira ni muka gaisa."
Amma ta yi kyafci kafin ta ce" Habibu dai ya kira ni da safe amma Ummu ba ta kira ni ba."
"To ai kin yi mata faÉ—a zuwan ta na karshe shi ya sa ba ta kira ki ba."
Baffa ya faÉ—a yana dariya Amma ta kalle shi tana cigaba da faÉ—in" Au har ta faÉ—a maka? Munasiran yarinya."
"Ki rage yi ma uwata faÉ—a, kar ki manta ta girma yanzu matar aure ce."
"Ai ko duniya ta haifa sai na ci mata in ta yi mini ba dai-dai ba."
'"To me ta yi miki kuma?
Ammah ta miƙe daga kwancen da take tana faɗin" Zuwa fa ta yi ina mata hiran bikin nan na Daura ta yi banza da ni, shi ne na danƙwashe ta yarinyar nan ta fara mini kukan shagwaɓa wai ita ina ruwanta da bikin da zan ce sai ta saka baki a hiran? Ka ji fa shi ne na fattatake ta na ce kar ta dawo mini gida ta ce wai gidan ai na Baffa ne, na ce ta ci ubanta Baffan ma a ƙarƙashina yake ballanta ita "
Kafin ta gama bashi labarin ya fara dariya, Ammah dai ba za ta sauya ba, in tana faɗa da yara sai ka ce ba ita ta haife su ba musamman ma ita da Autar ta Ummi, ba sa zama a inuwa ɗaya yanzu nan lafiya anjuma za a ji su suna tafka tsiya ta fattateketa a gidan tun kafin ta yi aure gidan Ummin ikki take zuwa ta yi ma Amman ya ji sai in ta gaji da kanta take dawowa, ita fa Ammah ba ga ya'yanta ba ko na yan'uwa ne ba ta da sauƙi, jikoki kan sun san sauran in ƴa'yan su Jibo suka zo hutu sun ma san hali ba ruwanta da wasan jika da kaka yanzu sai ta ji ƙaniyar mutum, ba a yi mata wargi in aka dame ta ta kira uban ko uwar ta ce su zo su tattara ƴayan su ta gaji, ita da gidan Baffa ba za a bar ta sake ba. Babar ɗiyar Jibo Sauda wancan hutun da suka zo kafin su koma ta ci dundun Ammah, saboda ba ta jin mgana ga son jiki ita kuma Ammah ba ta shiri da yaro mara kunya da son jiki yanzu za ku samu matsala, ba su gama cinye hutun ba ta kira Jibo ta ce ya zo ɗauki sangartatun ya'yan shi ba za ta iya ba sun dame ta. Da yake shi ne babba kuma yana aiki ne Airport na Abuja can yake zaune da iyalansa.
Baffa ne mai wasa da jikokinsa da Æ´a'Æ´an sa amma ban da Ammah kana yi mata wasan za ta ma yar da shi na faÉ—a, Æ´aÆ´an lamido ne kawai jokokin gata a wajenta in suka zo ta rasa ina za ta saka su kamar yadda take yi ma ubansu hidima suma haka take yi musu.
Hatta matar Lamiɗo hidima Ammah ke yi mata, ita kuma sanin Amma ce komai na mijin nata sai ta riƙe ta gam, domin yadda take yi ma Amma hidima da kuɗinta ko Mami da ta kawo Hamma Lamiɗo duniya ba ta yi mata haka, to ina ma ta ga fuska Mami ko a fili ko a sarari ba ta taɓa nuna Lamiɗo ɗan ta ba ne, Islam da Faruk sune duniya ta shaida ƴa'ƴanta. Shima bai taɓa nuna wata a matsayin uwa ba bayan Ammah ba
Sannan matar Hamma Lamiɗo ita ɗin yar masu kuɗi ce ɗiyar sarauta ce domin babanta shi ne Sarkin Kano na yanzu, ita kuma likitar mata ne mai zaman kanta, shi ya sa ko su matan Yaya Jibo ba su isa su haɗa kan su da Balkisu ba, ita ɗin ta musamman ce a wajen Ammah kamar yadda mijin nata yake gangariyan na musamman a wajen Amma.
"Ummu ta raina ni Baffa."
"Ba ruwana ina shiga zan ji kunya ke da Autar ki."
Da sauri Amma ta ce" Ba Auta ta ba ce, Autar Umman ikki ne."
Baffa ya sake yin wata dariyan kafin ya ce" Har da ke me, ni na É—auka har da ita za ki tafi bikin. Na tabbata Habibu ba zai hana ta zuwa ba."
Da sauri Amma ta ce" Wallahi ba zan je da ita ba, kawai ta kunya ta ni, ka manta zuwan da na yi da ita naɗin Sarautan Lamiɗo nan fa na faɗa maka abin da ta yi mini sai da na yi nadamar zuwa da ita, tana ta taɓe taben fuska suna jan ta da mgana sai ta ga dama take amsawa, sannan ta maƙale mini ta ƙi zuwa ko'ina sai na yi mgana sai ta tura baki ta ce ba ta san kowa ba, wallahi ban ji daɗin zuwan da na yi da ita da man na ce har abada sai dai in ita ta kai kanta ba dai ni ba."
Baffa dai na ta dariya bai yi mgana ba.
"Ka san ta da shegen iyayin tsiya, ba ta da wayewa a wajen shiga mutane. In da BaÉ—É—o ta fita kenan da ba domin makarantar ta ba da tare da BaÉ—É—o zan tafi"
Baffa ya gyaÉ—a kai amma bai yi mgana ba.
"Ka dinga yi mata faÉ—a Baffa in kana so mu shirya da Auta nan ta ka."
"Zan yi mata"
Ya faɗa yana riƙo hannun Ammah, sai ta kalle shi, shima ita yake kallo waiwayi ya fara mata sai ta fara dariya tana kiran sunan shi.
"Baffa..!!!
*****
Jalingo Street.
Taa ƙasa faɗa ma Habib canje-canjen da ta ke ji a jikin ta. Tsoron ta kar ta sanya masa rai akan cikin kuma su je a yi gwaji a ga ba shi ba ne, kuma sun yi mgana da Sisna da ta nemi shawaranta sai ta ce kar ta faɗa masa amma ga shawara mai zai hana ta yi gwajin da PT ta fara gani in tabbas akwai cikin?
Sai ta aminta da shawaran Baɗɗo, ita ta bar ma alhakin siyo mata PT ɗin da alƙawarin in za ta zo gidan sai ta taho mata da shi, haka kuma aka yi ranar wata Jumma'a daga makarantar da take karatu wato State polytechnic Yola(SPY JIMETA) ta hayo abin hawa zuwa gidan Ummu.
Tare suka yi gwajin har tsinke biyu amma sai ya nuna babu cikin shike nan murnan Ummu ya koma ciki.
"SisNa kar ki wani damu, soon in sha Allahu za mu samu wani Baby kin ji ko?
BaÉ—É—o ta faÉ—a cikin sigan lallashi ganin Ummu ta É—aga hankalinta.
"To amma yanayin da na ke ji a jikina fa SisNa?
Baɗɗo ta ce" Wata ƙila gajiya ce kawai ba wani abu ba."
Ummu dai duk da ba haka ta so ba amma hakan nan ta haƙura ta cigaba da karɓan lallashi daga wajen yaruwata Aisha(Baɗɗo) wata ƙawarta kwara ɗaya da dangatakar jini bai haɗa su ba amma amincin Amma da Ummi ikki shi ya haifar da wannan kyakyawan dangantar dake tsakaninta da Baɗɗo a yau.