← Book details Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 92

Sashe 40

Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Salau-salau haka ta ƙarisa gaban shi, ta zauna a kasan cafet tana mai ƙura ma kwalliyan cafet ɗin idanuwanta, amma hankalinta ba ya wajen in da zai lura ma kafafunta da hannayenta ma rawa suke yi tsabar firgici.

"Kin gama na ki aikin saura nawa aikin kuma Ummu Salma."

Sai ta É—ago tana kallon shi amma ba ta yi magana ba.

"Kin je kin haɗa ni da iyayena, kin yi ƙoƙarin ɓata mini gobe na sai dai burin ki bai cika ba."

Ya sake fada yana mai kallon ta fuskar nan ba fara'a kamar bai taɓa dariya ba.

"Me kuma na yi?

Ummu ta faÉ—a muryanta na karyewa kamar ta fashe da kuka.

"Ni kike tambaya abin da kika yi! Kin manta kin sake kai ƙarana wajen iyayen ki? Ke a tunanin ki za su iya sauya komai ne?

Ta ma kasa mgana bakinta na rawa, shi ya sa kawai ta yi shuru amma har hawaye sun kece mata maganarsa ya ba ta tabbacin Baffa ya ji labarin halin da take ciki, magana ta kai kunnen iyayen Habib.

"Ummu Salma ba ke kaÉ—ai ne ba ki da tunani ba har da iyayenki ma."

Da sauri ta ɗago ta kalle shi cikin mamakin kalaman shi, iyayenta ne marasa tunani?  Yau ita Habib ke faɗa ma iyayenta ne ba su da tunani?

"E haka na ce ba su da tunani, in har suna da tunani ai ya ci ace zuwa yanzu sun fahimci bana ra'ayin ki, na nuna bana son ki a aikace duk domin su fahimta su sauƙaƙa mini aiki amma sun kasa fahimta ban sani ba ko a wajen su ne kika gado wannan kidahumancin na ki ba"

Habib ya gama faÉ—a har yana nuna kanta cikin izgili.

Ummu Salma ta yi ma Habib ƙuru da ido ta kasa mgana, domin sai ta ji kamar an zare mata duka lakkan jikinta.
Yau iyayenta ne kidahumai a bakin Habib? Iyayenta fa? In ita ya zageta ta shanye, to ai bai kama ta ya taɓo bangaren iyayenta ba, domin ya san duk ɗa na gari ba zai zura ido ana cikin zarafin iyayenshi kuma ya yi shuru ba.

"Na gaji da ke, na gaji da auren ki wallahi, ke kika fara cutar da iyayen ki tun da kika ɓoye musu gaskiyan manufata akan ki, su kuma rashin tunanin su da lissafin su yasa suke tunanin ina son ki, sannan iyayena suna da ikon sarrafa rayuwata ne? Ina, rayuwata ce ni ke da ikon zaɓa ma kaina yau n da gobe na ba wani ba, ba kuma wanda ya isa ya saka ni na zauna da abin da bana so, a farko ni ne na yi ra'ayin zama dake saboda ina son cimma burina, yanzu kuma na gama amfana dake, na cimma burina akan ki me kuma ya yi saura a tsakanina da ke?

Ya faÉ—a yana zare mata ido.
Ummu na hawaye har da majina, ta ce" Iyayena ba su yi maka komai ba Habib ka daina zagin su don Allah."
Ta faÉ—a kukanta har yana fitar da sauti.

Sai ya kwashe da dariya kafin ya ce"Oh kina jin zafi ne? To na dai na cewa basu da tunani suna da shi, amma dai ba zan fasa faɗa miki kin turo bagidajen tsohon ki wajen iyayena ba kuma ya zo, sannan kuma har ya bar mini saƙo "

"Haba Habib."

Ummu ta sake faÉ—a cikin kuka tana sakin shessheka domin ji take yi kamar ta shiÉ—e yadda maganganun Habib suke kassra tunaninta da sauran kuzarinta gabaÉ—aya.

"Na faÉ—a wannan bagidajen uban naki ne, wai shi ne yake da zarran zuwa ya faÉ—a ma Abba cewa in na gaji dake ne na dawo masa dake gida"
Ya gama faÉ—a yana wata dariya ta reni da wulakanci.

"Shi yana ɗauka ya yi gwanin ta ne, ko kuma me ya ke takama da shi? Lauyan yayanki? Ko mai aikin filin jirgi? Ko mai fama da gwajin kashi da fitsari ko mai aiki da hukumar ruwa? Ko wannan yayan na ki mai bin tsohon ku saro tsoffin injina? Ko kuma wannan yayan naki mai karatun jami'a? Ko wanda ya tafi ƙasar waje da kuɗin tallafi?

"Habibb.."

Ta faÉ—a muryanta baya fita saboda kuka.
Bai saurareta ba ya cigaba da faÉ—in.

"Oh na tuna ko yana takama da wannan ɗan da bai haifa ba ne? Lamiɗon da dangin ku ke ji dashi, Yariman Daura ko? Wanda uwarki ke zuwa maula gidan sarki ko? Da shi yake taƙama da har zai zo wajen ƙanin mahaifina ya bar mini wannan saƙon?  To in ma gatse yake yi ya yi kuskure, a yau ba sai gobe ba zan cika umarninsa zan mayar masa dake kamar yadda na ɗauko ki daga gidan shi."

"Habib ka bari, ka daina zagin iyayena."

Ummu Salma ta faɗa tana kuka zuciyarta na ƙuna tana wani irin soya da irin wannan cin mutumcin da Habib ya zaunar da ita yana yi ma iyayenta da yan'uwanta.

"Na faÉ—a ko za ki rama musu ne?

Ya faÉ—a yana taso mata kamar zai dake ta sai ta yi shuru ban da kuka ba abin da take yi, yi take yi kamar zuciyarta zai fita, wani É—aci na taso mata É—acin an ci zarafin iyayenka a gaban idanuwanka amma ba ka da hurumin da za ka hana faruwan haka, miyan bakinta har kafewa ya yi saboda yadda zuciyarta ke tafarfasa.

"Ni ce na yi maka laifi ba iyayena ba. Ni ce baka so ba su ba, to kuma su me suka yi maka da za ka ci zarafin su?

Ummu ta faɗa cikin kuka mai ƙarfin da sautin shi yake fita sosai.

"Ka yi mini abin da za ka yi mini zan jure Habib, ka tozartani iya tozartawa ba zan taba mgana ba, amma ba zan jure jin maganganun cin fuska ko na ɓatanci ga iyayena ba, kar ka sake ban zagi naka iyayen ba kai ma ba ka da hurumin da za ka zagi nawa iyayen."

Tana magana yana mata dariya kamar ya ga wata mahaukaciya.

"Me suka yi mini kike tambaya na?

Tasowa ya yi zuwa gabanta ya durƙusa saitin kunnuwanta ya yi magana.

"Saboda sun haife ki, laifin su kenan a wajena."

Ya faɗa yana yi mata dariya, Ummu na tsiyayan hawaye tana kallon Habib tana jin son ta ji ta tsane shi, tana so ta daina jin ko da ɓurɓushin son shi a cikin zuciyarta amma ina, tunda ba ita ke da alhalin sarrafa zuciyarta ba har yau ba ta daina jin son Habib a ƙasan zuciyarta ba.

Miƙewa ya yi ya koma in da ya tashi ya zauna lokaci ɗaya yana faɗin" Tunda har tsohon ki ya bar mini sallahun in na gaji dake ne na dawo masa dake shi bai gaji dake ba, to a matsayin shi na Surukina mahaifin matar da na aura na more albarkatun jikinta ya zame mini kamar wajibi na cika umarninsa."

Kallon ban fahimce ka ba Ummu ke yi masa kamar idanuwanta za su faÉ—o kasa, ga shi suna masu zubar da hawaye.

Takardan ya jawo a gefen shi ya ɗora saman cinyarsa ya ɗora biron a kai lokaci ɗaya yana faɗin" Zan sake ki kamar yadda mahaifinki ya ɓukata, duk da ya ɗan yi gaggawa, da a ce ya jira da ni da kaina zan sako masa ke ba sai ya wahalar da kansa wajen zuwa ya bar mini saƙo ba."

Ummu Salma ta ji kanta ya sara, har É—an dake cikinta sai da ta ji ya motsa saboda firgici da tashin hankali.

"Yanzu Habib sakina za ka yi?

Ummu ta tambaya muryanta cikin kuka kamar za ta shiÉ—e.

"Kina tantama ne? Bari na rubuta na ba ki ki karanta sai ki samu tabbaci "

Kawai sai ta ga ya fara rubutu da sauri ta rarrafa gaban shi cikin kuka tana faÉ—in" Don Allah Habib ka yi hakuri kar ka sake ni, don Allah ka taimaka mini ka rufa mini asiri ka da ka sake ni."

Take faÉ—a tana wani irin gunjin kuka, ga ta duke kan gwiyoyinta tana mai zubar da hawaye tana haÉ—a shi da Allah akan kar ya sake ta.

"Ai abin da tsohon ki ya bukata ne, duk da nima ina da niyyar yin haka amma ba yau ba."

Ya faɗa yana nuna halin ko in kula, yana ma ƙoƙarin cigaba da rubuta abin da ya fara.

Da sauri Ummu ta faɗa kan kafafun Habib ta riƙe shi gam tana wani gunjin kuka.

"Ke miye haka?

Ya faɗa yana fizge kafarsa har tana yin gefe amma ba ta haƙura ba sai da ta sake riƙo kafafunsa da karfi ta rumgume a ƙirjinta lokaci ɗaya tana faɗin.

"Na tuba, don Allah ka yi haƙuri Habib kar ka sake ni."

"Wallahi sai na sake ki, mutuwa ce kawai za ta hana na sake ki, itama sai in yanzu ta zo ta ɗau raina amma in dai ina raye a yau zan yada ƙwallon mangwaro na huta da guda."

Ya gama faɗa yana sake fizge kafafuwanshi ya ɗora saman kujera ya bar Ummu duƙe a gaban shi tana wani irin kuka kamar za ta shiɗe.

"Habib in ka sake ni ina zan je? Wa zai sake kwasa ta? Wa ye zai iya aurena bayan ba ni da komai. Don Allah ka rufa mini asiri kar ka sake ni, kar ka manta da gudan jinin mu dake rayuwa yanzu haka a cikin jikina, kar ka bari ɗan mu ya rayu ba tare da kai ba, ka yi haƙuri don Allah ka rufa mini asiri "

Majina har zuba take yi a ƙasan cafet saboda kukan da Ummu ke rusawa amma ina Habib ba ya sauraranta rubutu kawai yake yi.

"To na ji , wallahi zan yi duk abin da kake so. Na ji zan. Zan zubar da cikin."

Ta faÉ—a cikin fitan hayyaci, har muryanta na dishewa saboda kuka.

Ganin ya É—ago yana kallon ta, ya sa da sauri ta sake rarrafawa gaban shi tana rawan bakin faÉ—in " Da gaske na ji zan zubar da cikin in har zan tsira da aurena."
Chapter 40 · 0% Book details