Sashe 6
Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta sake faɗa tana yi masa mirmishi, takardun hannun shi ya adana a cikin dirowan gefen sa, sannan ya mai da hankalin shi a kanta, ba ta damu da jiran amsar shi ba har ta miƙe, farantin kwanukan abincin da ta kawo masa tun bayan dawowarsa ta sumguma tana faɗin" Bari na kai wannan kitchen na dawo Baffa."
Daga haka ta sake ficewa shi dai kawai ya bita da kallo yana mai girgiza kai, lokaci É—aya yana sakin mirmishi.
Mintina huɗu sai ga ta ta sake shigowa da sallama wannan karon har sai da ta tura ƙofar daƙin lokaci ɗaya tana cewa" Baffa ko za ka sake fita ne?
Sai da ya amsa mata da kai kafin ya amsa mata da baki.
"A'a"
Ta fara tahowa zuwa gare shi, shi kuma yana kallonta, Jamila (Ammah) ko da shekaru suka tura kyanta da dirin ta bai samu wani tawaya ba, ko yanzu da yake kallonta yana ganin kyawunta na shekaru sama da talatin da auran su, ita ce dai Jamilar da ya aura yarinya yar shekaru sha shidda a lokacin, ita ce wacce Gwaggo ta yi masa auran gata da ita(Allah ya gafarta mata) ita ce kuma a yau uwar zaratan maza ginannu har guda bakwai, uwa kuma ga Muhammad Lamiɗo, kuma uwar Auta Ummu-Salma, har yau hasken fatarta ba ta dishe ba, da ya ke fara ce sosai mahaifiyarta kafin rasuwarta Nenne tsada ake kiranta saboda tsabar jan ta, sannnan kaf ya'yan su jan fatan ta suka ɗauko a kammani ma ta rinjaye shi, duk da mutane da dama sun sha cewa shi da Jamila suna ɗiban kama, tun da su ɗin jini ɗaya ne, wani lokacin Amma ba uwa ce kaɗai a wajen ƴa'ƴan shi ba hatta shi kan shi uwa ce gare shi, in ta rufe shi da faɗa kamar Gwaggo, shi ya sa ya sha cewa Ammah mata ce, ƙawa ce Aminiya ce sannan uwa ce a gare shi da ƴa'ƴan su gabaɗaya. Da yake kuma ya aure ta da ƙananun shekarun a wancan lokaci yanzu ma take cikin shekarunta na hamsin da shidda, babban yaron su Jibo ya zo duniya tana da shekaru goma sha bakwai, sau tari in suka jera da Jibril kamar ƙaninta yake ba ɗanta ba, yadda tserensu yake kamar a jere da juna. Sannan ta mori jikinta ba da ta kiba kuma ba ta da tsawo, gajera ce tsawon da yaran suke ɗaukowa tsawon uban su ne shi Alhaji Hadi Baaba.
Sai da ta zauna kusa da shi sannan ya sauke ajiyar zuciya.
Ya juyo yana kallonta ita kuma sai ta saka hannu ta zare masa gilashin fuskar shi lokaci É—aya tana faÉ—in" Baffa a cire gilashin hakan nan, ko nima sai da shi kake iya ganina tarwai?
Dariya ya yi har sai da haƙoran shi suka bayyana a waje.
"Ahto Baffa ba amana a ce ba ka gane ni sai ka sanya gilashin ƙara karfin gani."
"Ammah ba ki da dama."
Ya faÉ—a da sautin muryan shi ya saba da kiranta Ammah kamar yadda yaran su, suke kiran ta ba ma shi ba kowa yanzu Ammah ne yara da manya. Shi kuma da man ita ce take ce masa Baffa kafin yaran su su tashi da sunan a bakinta.
Akwai wata rana da ya shuÉ—e Saddam na zolayanta da cewa.
"Amma wai kema Baffa Baffan ki ne?
Dakuwa ta yi masa kafin ta ce. "A'a naka ne mai uba, to ni ce mai Baffan gabaÉ—aya ku duk yan cikon banci ne."
Suna falo ne suna karyawa a wata safiya shi kan shi sai da ya yi dariya da kalamanta
Ammah ce, ba ta da dama mace ce mai jajircewa kan mijinta da ƴa'ƴanta mai son zumunci da yaƙana ce, amma kuma ba ta da haƙuri Amma mace ce da ba ta ɗaukan Nonsense tana da faɗa da zafi, zafin namanta har a jikinta da kazar-kazar ita ce mata ɗaya cal da Alhaji Hadi Baba ya mallaka a matsayin mata anan duniya amma ko yanzu da shekaru suka tura ba ta taɓa jin ta gaza daga hidimta masa ba.
Yanzu É—in ma cewa ta yi ya kwantar da kansa saman filo, ta jawo kafafunsa a saman cinyarta tana matsa masa a hankali cikin kulawa tana faÉ—in.
" Baffa ya kamata ka huta. Kwana biyun nan ba ka samun zama sosai."
Sai da ya dan muskuta kafin ya ce" In na zauna gida na huta sauran harkokin nawa wa zai yi mini?
"Ka bar ma Baba"
"Ban da abin ki ai ko a yanzu shi ke yin harkokin, shima abin a tausaya masa ne ba ya cikakken sati tare da iyalansa."
Amma ta jinjina kai kafin ta ce" To shi yanzu jininsa yake Baffa kai kuma jiya ba yau ba, ni dai ka dinga hutawa kar wata rana aga tsoho na ya faÉ—i."
Ta ƙarishe faɗa tana masa dariya da man in tana jin nishaɗi ɗan tsohona take kiran shi, kai ya jinjina kafin ya ce.
"Tun da haka kike bukata ai haka za a yi uwar LamiÉ—o "
Ta sake faÉ—aÉ—a mirmishinta ba ta dai ce komai ba tana cigaba da matsa masa kafafuwansa.
Idanuwan Baffa na lumshewa domin akwai gajiya a jikinsa Ammah dai sai dai Allah ya yi mata albarka ta san shi fiye da yadda shi ya karance ta. Mubi ya je shi da Abdullahi duk da ba shi ya yi driving ba doguwar tafiya yanzu na bashi wahala ko don shekaru sun tura ne? Shi da a shekaran baya a jihohin Nageria ba in da kafarsa ba ta ka da sunan kasuwanci ba. Kasuwanci ma irin na shi na siyan injinan manyan motoci ƙananu da manya da kuma wasu part-part na jikin mota ya daɗe yana wannan harkan kafin daga baya ya fara sirkawa da harkokin siyar da motoci sanadin haɗuwar shi da Alhaji Isa Ɗanmarke.
amma yanzu saboda girma da shekaru in ya yi doguwar tafiya a mota sai ya ji duk ya gaji sauƙi sauƙin ta ma in a jirgi ne.
"Saddam ya dawo gidan nan kuwa?
Ya tambaya cikin sanyin murya.
"Tun ɗazu fa ya dawo muna tare da shi, ya so ma ya jira ka har ka shigo sai ya ce mini kansa na ciwo zai shiga ya sha mgani, wataƙila lokacin da ka shigo ya kwanta ne."
"Me ya sa yake jira na?
Ya tambaya har lokacin idanuwansa na lumshe.
"Gobe ya ce yake so ya koma makaranta."
Sai a lokacin ya buÉ—e idanuwansa kafin ya ce" Gobe kuma? Ya fasa raka ki Dauran ne kuma?.
"Aa bai fasa ba ya ce akwai abin da zai yi ne a can, satin da za mu tafi zai dawo."
Ɗan miƙar da kansa ya yi yana gyara kwanciyarsa kafin ya ce" Allah ya ba da sa'a."
Ta amsa masa da Amin Amin.
"Bayan Umman ikki, sai kuma suwa kika shirya tafiyar da su?
Ya tambayeta yana kallonta, kai tsaye ta ce" Umma A'i tunda na fara yi ma mgana sai ta ce ba ta nan É—iyar mijinta ta haihu a kano za su tafi, Umma salamatu kuma kasan ba ta son doguwar tafiya. Yanzu daga ni sai Umma Balki, sai Saddam da Ummin ikki."
Kai ya jinjina kafin ya ce"Kun isa ma, Allah ya nuna mana ya sa a yi biki lafiya a gama lafiya."
Ta amsa masa da Amin tana cigaba da faÉ—a masa sun yi waya da LamiÉ—o ya ce Abdulrahaman zai siya musu tiket jirgi za su bi zuwa katsina daga nan motocin gidan Mai martaba sarkin Daura suna jiran su za su É—auke su zuwa masarauta.
"Allah ya sa albarka."
Ta amsa da Amin kafin ta ce" Baffa ba za ka je ko É—aurin auran ba?
Kai tsaye ya ce" Zai yi wahala. Ban dai sani ba, bari mu gani."
Tana jin ya ce haka ta san bai yi niyyar zuwa ba.
"Kai Baffa ban san ka da riƙo ba fa. Ai komai ya wuce yanzu mun zama ɗaya silan Lamiɗon mu."
Shuru ya yi na wani lokaci ba tare da ya yi mgana ba. Ya manta sannan ya yafe, kara yake yi ma Fatima, shi ya sa bai cika tusa kansa a wannan bangaren ba.
Janye kafafunsa ya yi daga cinyar Amma ya sauke a ƙasan cafet ɗin da ke ɗakin.
Sannan lokaci ɗaya ya yunƙura ya miƙe zaune yana mai kallon Amma.
"Na san zuwan ba zai gagare ka ba, sai dai in Fatima ce ta ce maka kar ka je ko?
Baffa Mai martaba fa da kansa ya kira ka ya sanar da kai bikin ɗiyarsa me ya sa ba zaka yi masa kara ba! Sannan Gimbiya Shahida ba ka ga yadda ta ke yawan kirana tana tambayana yaushe za mu taho ba, a ƙalla dai sun nuna mana ƙauna hatta Fulani ta kira ni, ta ce ba ta ɗauke mini zuwa wannan bikin ba."
Mirmishin gefen baki ya yi, a cikin ran shi yana faɗin sai yanzu? Da ma ace za su iya mayar da hannun agogo baya wataƙila da sun gyara kuskuren su na baya da Fargar jaji bai kama su a yanzu ba amma a sarari sai ya kalli Amma kafin ya ce" Ni wallahi ban taɓa rike su a raina ba Ammah kin sanni kin san halina. Kawai dai."
"Kawai dai me?
Ta katse shi tana kallon shi sai ya kasa amsa mata, domin ai ta san amsar tambayar nata.
"Fatima ce! Saboda Fatima ce ya sa kake yin wannan baya bayan ko Baffa?
TafaÉ—a tana sake matsawa gare shi lokaci É—aya ta tsare shi da kaifaffun idanuwanta masu sanya shi ya yi laushi bai shirya ba.
"Baffa don Allah kar ka biye ma wannan ƙanwar taka mai zuciyar rashin yafiya, yadda na sanka mai yi ma zumumci hidima ne. Ko saboda Lamiɗon mu ko sabo da shi, kar ka manta har abada Lamiɗo ɗan mu ne."
Ta gama faɗa tana mai riƙo duka hannayensa a cikin nata, ta kuma kafe shi da idanuwanta da ba ya iya mata gaddama in dai ta kafe shi da su.
"Za ka je ko Baffa?
Ta faɗa har tana kasa-ƙasa da murya.