Sashe 79
Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ba ta ko ganin gabanta kafin ta isa titi ba ta san adadin sau nawa ta ci tuntuɓe ba, amma ba ta damu ba Kekenapep ta tsayar ta shiga ta ce ya kai ta barraks road suna tafe amma ji take yi kamar ta yi tsuntsuwa ba ta taɓa ganin nisan gidan su Shamsiya ba sai a ranar suna isa tun daga kofar gidan ta san ana sha'ani domin get ɗin gidan ma yana buɗe ne ga motoci nan birjit a haraban gidan wasu har waje, ba ta damu da kowa ba, ita dai ta san ta fiddo kuɗi da ba ta san ko nawa ba ne ta mika mai nepep ɗin daga nan sai kawai ta tsinci kanta a falon gidan su Shamsiya akwai mata ga sunan da yawa amma idanuwanta ba su tsaya tantance fuskokinsu ba. Waige-waige kawai take yi ba wacce idanuwanta ke son gani irin Shamsiya.
"Wa nake gani kamar Ummu Salma."
Ta ji an faÉ—a daga bayanta tana juyowa sai ta ci karo da Anty marikiyar Shamsiya.
Mirmishin dole ta yi mata wanda ya tsaya iya saman fuskarta.
"Ni ce ina yini Anty"
Ummu ta faÉ—a tana sauke numfashi.
"Lafiya lau sannu Ummu Salma."
Ta faɗa tana kallonta daga sama har ƙasa.
"Ai na yi ta cewa Shamsiya za ta rako ni gidanku na yi ma Umman ki jajen abin da ya faru ban samu dama ba."
Ummu ta sunkyar da kai, amma tana ta kalle kalle domin hango ta in da za ta ga Shamsiya.
"Allah ya kyauta na gaba. Allah ya zaɓa mafi alheri."
Ko amsata Ummu ba ta yi ba domin ba ta ita take yi ba.
"Kin samun kin rarafo kenan? Da man da na ga ban ganki ba Shamsiya ta ce ai kin yi nauyi."
Da gaske kenan Shamsiya za ta yi aure, amma dai da tabbacin Habib za ta aura ne ba ta sani ba kuma shi ta zo ta sani daga bakin ita Shamsiyar.
"Shiga ciki tana cikin É—akinta ba ta ma daÉ—e da dawowa daga wajen gyaran kai ba"
Ko kafin Anty ta gama magana Ummu ta wuce ta zuwa cikin É—akin Shamsiyar da dama ta san É—akin.
Kofar ma tana buÉ—e suna ta hayaniya ta san ta shiga cikin É—akin kuma ta ga harda yayyen Shamsiyar a ciki amma wacce idanuwanta ke son gani ta nema sai ko suka haÉ—a ido tana zaune gefen gado ta buÉ—e kanta yan'uwanta na duba gyaran kan da aka yi mata.
"Kai Ummu kin rarrafo kin zo?
Badawiyya yayar Shamsiya ta faÉ—a bayan duk hankula ya dawo kanta.
Ita dai kawai tana yaƙe ne amma hankalinta da natsuwarta na kan Shamsiya.
Wato ta ce ba za ta samu zuwa ba ne saboda ta yi nauyi to ai ba ta yi ƙarya ba tabbas ta yi nauyi tunda ga nauyi nan a gabanta tana fama da shi.
"Bestie sannu da zuwa."
Shamsiya ta fada bayan ta taso zuwa gare ta har tana riƙo hannunta.
Ta kuma ja ta har gefen gado ta zaunar da ita, ita kuma kamar gaula ta zauna.
Suna ta yi mata sannu ta kasa amsawa kawai Shamsiya take kallo ko a jikinta sai jikinta ya bata wata kila ba gaskiya ba ne Shamsiya za ta yi aure amma ba Habib ne mijin da za ta aura ba.
"To mu je ko mu bar Bestie ta gana da Bestien ta."
Badawiyyya ta faÉ—a tana tattara sauran yan matan dake É—akin, wasu ta san su yan'uwan su Shamsiya ne wasu kuma ba ta ma tsaya iya gane su ba. Tunda in dai na kusa da Shamsiya ne ta san su kamar yadda itama ta san duk wani da ya shafe ta. Kamar yadda Shamsiya take zuwa gidansu itama haka take zuwa nan gidan wajen Shamsiya tun ma kafin ta yi aure.
Dukkansu suka fita sannan suka rufe ƙofar, suna fita Shamsiya ta kalle ta, tunda daman ita Ummu tunda ta shigo take kallon ta.
Mirmishi ta yi mata irin mai ƙayatarwa nan kafin ta ce" Tunda na ganki na san cewa zuwa yanzu kin ji komai ko kin ga komai."
Ta faÉ—a tana mai yi ma Ummu wani kallo.
Cikin wani yanayi Ummu ta ce" Na ji mana, na ji za ki yi aure amma ba ki faÉ—a mini jibi ne bikin ki ba."
Ta faÉ—a kafin ta É—an ja fasali.
"In ba ki so na zo bikin ki Bestie ba sai kin ɓoye mini ba nima a wannan halin ba zan zo ba ballatana har na na ɓata miki bikin ki."
Ta faÉ—a cikin rawan murya, tunani kawai take yi ba gaskiya ba ne , ko dai ita ce ba ta gani daidai ba ko kuma an samu wani kuskuren.
Shamsiya ta sake kallonta kafin ta kwashe da dariya.
Ummu ta yi jagale tana kallonta ganin tana yi mata dariya
"Wai akan me kike magana?
Ta faÉ—a lokaci É—aya tana mikewa..
"Kin ce ma su Anty na yi nauyi shi ya sa ba zan samu zuwa bikin ki ba, alhalin ni ba ki faÉ—a mini ranar bikin ba."
Shamsiya ta sake kwashewa da dariya tana nuna Ummu kafin ta ce" Wai da man ba abin da nake tunani ya kawo ki ba?
"Me kike nufi?
Ummu Salma ta tambaya cikin shan jikin jikinta.
"Ba ki san abin da na ke magana akai ba?
Ko dai kin sani kin zo ki tabbatarwa ne kina yi mini alaye"
Ta faÉ—a tana mai kallonta cikin kurullah.
"Me me kenan?
Ummu Salma ta tambaya har bakinta na harÉ—ewa.
Shamsiya ta dauko wayarta a gaban madubi ta yi danne danne ta miƙa ma Ummu wacce ta yi tsai tana kallonta.
"Karɓi ki duba."
Hannunta na rawa ta karɓa. Tana dubawa, sai gata ta sake ƙamewa a zaune.
Ba sabo ba ne a idanuwanta hotunan nan ne dai da ta gani É—azu ta kasa gasgatawa.
"Ki yi ta yin gaba, hotuna ne ne ni da mijina in sha Allahu"
Hannun Ummu na rawa zuciyanta na bugawa, haka ta rika wucewa tana kallon hotuna kala kala sama da kala goma ba ta ko gama gani ba ta É—ago idanuwanta cikin wani yanayi tana kallon Shamsiya.
"Da ma. Da ma da gaske ne?
Ta faÉ—a cikin rawan baki da na zuciya.
"To da kin É—auka karya ne?
Shamsiya ta faÉ—a tana É—an dariya.
"Habib ne fa! Ko ba ki gane shi ba ne?
"Habib ne, na gane shi Sweety ba."
Shamsiya ta katseta cikin ba ta tabbaci.
Ummu ta kasa magana bakinta na rawa, tare da jikinta Shamsiya kuma ta ɗaure fuska tana kallon Ummu kallon kasƙanci.
"Ga shaida nan na nuna miki. Jibi uwar haka ina gidan Habib a matsayin matarsa in sha Allahu."
Ta sake faÉ—a tana sakin wani mirmishi.
"Habib fa! Habib miji."
"Kul É—inki. Kar ki sake kiran shi da mijin ki domin Habib ba na ki ba ne nawa ne. Ummu Salma."
Ta faÉ—a tana taso mata a fusace
Kafafun Ummu har gara suka yi saboda jin abin da ba ta taɓa tsammani ba.
"Ban karya ta cewa ke kika fara sanin Habib kafin ni ba, amma zan baki tabbacin ni na baki aron shi har kika aure shi kika kuma yi zaman aure da shi."
Ta dawo gaban Ummu Salma ta tsaya sannan ta nuna cikin jikinta da yatsunta guda É—aya.
"Ni ce har na baki damar da kike da wannan cikin a jikin ki. In da na so da baki aure Habib ba, in da na so da yau ba ki rigani É—aukan cikin shi ba"
Ummu ji take yi kamar mafarki amma da ta runtse ido sai ta sake ganin ta a gidan su Shamsiya kuma ga ta a gabanta tana faÉ—a mata wasu maganganu waÉ—anda ta kasa yarda da su.
"Ke Habib ya fara gani yana so, ranar da kika nuna mishi a matsayin saurayin ki na ji dama ace shi ɗin nawa ne, bani na fara kai kaina ga Habib ba shi ya kawo kansa gare ni da cewa sai da ya ganni ya san ba sonki yake yi ba sha'awarki ya ke ji, tun a lokacin muke tare muna soyayya a ɓoye, saboda ke ba zan hana zuciyata abin da take so ba Ummu Salma."
"Me ya sa to ya aure ni baI aure ki ba?
Ummu ta samu karfin gwiwan tambayan Shamsiya domin ko hawaye ma ba ta ji ya kawo mata ba zuciyarta ke suka tana hasaso mata wasu abubuwan, au da man Shamsiya ce masoyiyarsa da yake ta magana a kanta ita ko me ta yi ma su Habib da suka zaɓi su yi mata wannan yankar ƙaunar.
"Ina son Habib ina son abin da zai saka shi farimciki. Yana tsananin sha'awarki kuma yana so ya kauda wannan sha'awar ni kuma a gida ba za a bari na yi aure a lokacin ba. Shi ya sa na ba shi daman ya aure ki amma na shekara ɗaya ya yi amfani dake son ranshi ya sake ki zuwa lokacin ni kuma na shawo kan matsalata a gida. Mun yi da shi ba zai bar ki ki samu ciki ba, amma sai da kika ɓata mana plan din mu."
Nan ta shiga ba ta labarin duk yunkurin zubar da cikin da Habib ya yi mata da saninta domin tare suke shirya komai.
"Ki ma gode ma Allah na baki aron shi, ki kuma jinjina mini yadda na bari kika fara ajiye ƙwaan Habib a mahaifarki kafin ni, saboda haka godiya ya kamata ki yi mini Ummu domin na ba ki aron abin da na fi so a duniya."
Ta gama faɗa tana fuskanta ta. Ummu ta yunƙura ta miƙe tana jin ɗan cikinta na haɗewa waje ɗaya saboda halin da ta ke ciki, cikin ido ta kalli Shamsiya kafin ta ce" Ai ban neme da ki ba ni aron shi ba Shamsiya. Me ya sa kuka yi mini haka? Riban me za ku samu?
Ta faÉ—a cikin soyewar zuciya.
"Na samu riba, domin Masoyina ya biya bukatarsa, ni ma kuma na samu nawa biyan bukatar, ga shi za mu yi aure."
"Shamsiya mijin da na au"