Sashe 78
Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ammah ta faɗa tana miƙewa.
"Amma dai nace Baba ya yi ma matarsa mgana ya É—an kaita ta je ta É—an gyara gidan kafin ya iso "
Ummu ta ɗan yi yaƙe ba ta yi magana ba.
Ammah ta kasa zaune ta kasa tsaye tana tunanin abin da za ta dafa masa.
"Ummu ko na yi masa tuwo ne? Kin san yana so"
"Kai kuma yamma ta yi gaskiya."
Ita kaÉ—ai take ta maganganunta
Ummu Salma na jin ta ba ta ce mata komai ba shigowar Baffa ne ya katseta sai ta juya tana faÉ—a masa halin da ake ciki.
"Ba laifi ga Ummu nan ta É—an yi masa abinci nan da take yi mana na yan gayu."
Ya faÉ—a yana kallonta, mamakin Baffa ya hana ta magana wannan ne zai ci abincinta.
Ta ma san Ammah za ta ce aa ga mamakinta sai Ammah ta juya tana ce mata ta É—an sama masa wani abun.
"Za ki iya ko?
Ba ta da magana in ta ce ma ba za ta iya ba Ammah ce za ta É—aga hankalinta.
"Zan iya Ammah."
Ta faɗa a fili amma a zuciyanta sai ƙunƙuni take yi tana faɗin sai kawai mutum ya zo ba sanarwa da man halin shi ne ya yi ta abu gaban kansa.
Haka nan ta shiga kitchen chinese rice ta ce za ta yi, Allah ya sa akwai cefanen kayan lambu shekaran jiya Hamma Abdulrahaman ya kawo, amma sai da ta dafa ganyen zoɓo sauran nata ne ma da aka dawo da shi ta fito da shi tana yi musu zoɓo lokaci bayan lokaçi. Girkin kaɗan ta yi tunda suna da sauran taliya da miyan da Ammah ta dafa shi da rana, gogan ne ba zai ci ba tunda shi na musamman ne.
Bayan mangariba ta gama aikinta tunda gas ne Ammah na da gas na tsaye mai uku da electric da shi ake amfani, shi ya sa aikin ya yi mata sauri zobon ta zuba a wani jug na tangaran ta saka a firiza, abincin kuma ta zuba a ƙololin Ammah sabbi ne ma a kwalin su da ta je bikin Autan Umma Salamatu ne ta zo da su ko Baffa ba a taɓa sanya masa abinci a ciki ba amma yau Ammah ta ce ta ɗauko a zuba ma Lamiɗo a ciki.
Ta gama komai ta jera saman faranti sauran kuma ta zuba ma Baffa a ranta tana faÉ—in ai nima sai ubana ya ci tunda Ammah ba ta kanshi take yi ba.
Har ta koma ɗaki ta yi alwala ta yi sallan Mangariba shuru ba Hamma Abdullahi ba ɗan Ammah, sai da Ammah ne da kanta ta leƙo tana ce mata ta kira mata Baba a waya ta ji ko lafiya ba su kariso ba ita wayarta kamar ba kati ta dai ki shiga.
Hakanan ta É—au wayarta ta kira shi sai ga shi ta shiga ta ba ma Ammah suka yi magana.
Ashe Hamma Lamidon bayan an ɗauko shi daga filin jirgi gidan shi ya ce a wuce da shi zai yi wanka. Sannan ya ce ma Hamma Abdullshi ya koma gida in ya gama abin da yake yi zai tuƙo kansa zuwa gida.
Haka Ammah ta ke faÉ—a mata ita da Baffa da bai daÉ—e da dawowa daga masallaci ba.
Abincinsa Ummu ta kai masa É—aki sai ya wuce can Ammah kuma ta bi bayan shi.
Ita kuma sai ta koma cikin ɗakinta da tsinin cikin ta a gaba wayarta na hannunta kamar an ce ta buɗe data sai ta ja sama ta kunna ba wasu saƙonni ne masu yawa take samu ba tunda sabuwar lamba ce ba kowa ya santa da lambar ba.
Sai dai saƙonnin da ta gani a group ɗin makarantar su ne ya ɗan ja hankalinta, kuma ta ga har tagging ɗinta an yi sai ta shiga.
Sai ta ga ana ta fatan alheri da Allah ya ba da zaman lafiya.
"Ga wacce za ta dinga amsa addu'o'in ku nan."
Madina ta faÉ—a bayan ta yi tagging É—inta akan an ce ana ta fatan alheri amarya ta yi shuru ba ta amsa ba.
abin ya sake É—aure mata kai ganin Shamsiya ake tagging ana mata fatan alheri kasa wasu hotuna ne guda uku jikinta har rawa yake yi wajen dannawa ta buÉ—e hotunan domin ta ji suna ta cewa Allah ya sanya alheri ya kuma kai mu lokacin
Zuciyanta ya ba ta cewa auren Shamsiya ya zo ba ta faÉ—a mata ba.
Sai dai me katin biki ne ya fara buÉ—ewa da farko.
Ba ta ko tsaya duba sunan angon ba ta fara duba date É—in bikin jibi ne É—aurin auren. Mamaki ya sake kamata da al'ajabi kenan da gaske ne Shamsiya ta ja baya da ita sannan da gaske ne zargin da take yi a kanta cewa tunda yanzu ta zama bazawara ba ta bukatar ta.
Tana ta hawaye ita kaÉ—ai tana zaune da waya a hannunta.
Jikinta ya fara karkawa ne lokacin da hoton ƙasa suka buɗe. Sai ta ga kamar ko idanuwanta ke yi mata gizo ba gaskiya ba ne. Har sake murza idanuwanta ta yi ta sake ƙura ma wayar idanuwanta cikin fitan hayyaci.
Zuciyanta ne ya tsaya da bugu na lokaci É—aya.
Me take gani haka?
Shamsiya ce da Habib cikin shigar alfarma a cikin hotunan nan guda biyu.
Ɗaya ya kwanto ta bayanta ya haɗe hannayensu a saman cikinta. Dayan kuma tana zaune a kan kujera shi kuma ya tsaya a bayanta suna masu kallon juna suna mirmishi cikin yanayin da amarya da ango kan yi a lokacin yin hotunan pre-weeding pic, tamtama take yi kamar ba Habib ta gani a jikin hoton ba sai dai kuma ina shi ne domin ba za ta taɓa mantawa da kamaninsa ba har abada.
Habib ne mijin da Shamsiya za ta aura?
"Kai gaskiya sun dace."
Ta ga saƙon wata Hamdiya"
Kar dai a ce Shamsiya Habib za ta aura tunanin da take yi kenan zuciyanta na sake tsinkewa.
Ko ba ta san Habib ba ne? Ko ba ta san Habib shi ne mijin da ta aura ba? To ai in mijinta ne a da a yanzu ba mijinta ba ne sun rabu. Ba kuma za ta ce Habib bai san Shamsiya ƙawarta ba ce, ba kuma za ta ce Shamsiya ba ta san Habib ba.
Dukkansu sun san juna, kuma shi ne za su yi aure! Da man shi ne mijin da ta samu lokaci kaÉ—an? Ko da man shi ne dalilin da ya sa ta ja baya da ita. Ta sani ta san Habib ne za ta aura ta sani kuwa.
Zuciyan Ummu ya daina aiki kwata-kwata kanta na sarawa ta ma rasa tunanin da za ta yi, wayar na hannunta addu'oin fatan alheri ke ta shigowa ga Shamsiya da mijinta Habib, tun tana tunanin mafarki take yi har ta gasgata a zahiri ne yake faruwa. Ta kashe wayarta yafi sau uku tana sake kunnawa amma still in ta sake shiga hotunan take gani hoton Habib da Shamsiya a cikin yanayin farinciki.
Ta kasa zama ta kai gauro ta kai mari a cikin É—akinta. Tana jin har abin da ke cikinta yana juyawa tsabar halin datake ciki.
"A'a Bestie ba za ta auri Habib ba."
"Ba za ta aure shi ba."
Take faɗa tana kallon hotunan lokaci ɗaya tana faman girgiza kai. An ce kuka ma Rahama ne ta kasa kuka amma a kasan zuciyanta take jin wani irin zafi zafin da ba ta taɓa jin irin shi ba har ya ninka irin zafin da ta ji lokacin da Habib ya sake ta. Ta kasa gasgata gaskiyan abin da ta gani, in har auren ne da gaske to watakila Shamsiya ba ta san Habib ba ko shi ne bai gane Shamsiya kawarta ba ce, ga shi dai zuciyanta na cigaba da hasko mata hotunan su a lokutan da Shamsiya da Habib suka sha haɗuwa tun kafin aurenta da shi har ma bayan auren amma wani shashi na zuciyanta faɗa mata yake kila dai kuskuren fahimta ne ba abin da idanuwanta ke ganin mata ba ne.
Saboda ma ta samu tabbacin abin da ta gani sai ta sake duba katin bikin ga sunan Habib Idris Mai imani nan raÉ—au a jikin katin tare da na Shamsiya.
"Aa No.."
"Ba gsskiya ba ne."
Ta faÉ—a kamar mahaukaciya. Ba ta yarda ba zuciyanta ba ta aminta da abin da ta gani ba tana bukatar wani ya yi mata karin bayani
Jikinta da hannunta na rawa ta lalubo lambar Shamsiya ta kira ta amma kira sama da sau goma ba ta ɗaga kiran ta ba, in wayar na ringing tafiya yake yi da bugun numfashin Ummu Salma tsabar tashin hankalin data ke ciki.
Ganin da ta yi tana ɓata lokaci a daran nan a wannan lokacin take son karin bayani take kuma son sanin gaskiyan komai tun kafin zullumi da fargaba su saka zuciyanta bugawa. Wani dogon hijabin da take salla ta raruma ta saka a saman bakar doguwar rigar jikinta.
Har ta fito falo sai ta tuna ba ta ɗauki kudi ba sai ta koma da gudu ta yayo mu ƙaramar jakarta dake saman madubin dakin, tunda ta dawo daga asibiti ta ajiyeta a wajen wayarta na hannunta ta fito, takalmin Ammah dake kofar ɗaki wani na roba na zirga-zirgan tsakar gida ta zura ta fice daga gidan ba tare da tunanin komai ba, tana jiyo hiran Ammah da Baffa a turakansa amma ko waiwayowa ba ta yi ba, a lokacin hankalinta ya bar gangan jikinta. So kawai take yi ta buɗe idanuwanta a cikin na Shamsiya ta nuna mata hotunan da ta gani ta ji shin abin da ta gani gaskiya ne ko ƙarya ne?