Sashe 54
Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abdulrrahman ya sake faɗa yana ta da jijiyoyin kansa saboda ɓacin rai.
Mirmishi Baffa ya yi kafin ya ce" Abdulrrahman"
Ya kira sunan shi yana mai kallon shi.
"Ba za mu je kotu ba, ba za mu je mu buɗe ma duniya cikin mu ba. Shi fa namiji ne ita kuma Ummu mace ce, ita ce za ta zama abin nunawa ba shi ba. Gwara mu kai shi kotun da ba wanda ya isa ya kwace daga zaluncin da ya yi ba wannan mahaluƙin in dai ka yi zalunci sai ka karɓi sakamakon ka, daidai da abin da ka ka aikata."
Hamma Abdulrrahman ya kalle shi cikin mamakin kalaman shi shi kuma Baffa ya jinjina masa kai kafin ya cigaba da faÉ—in" Kotun Allah Abdulrrahman. Mu bar shi da Ubangijinsa shi zai yi ma Ummu faÉ—a shi zai saka mata in sha Allahu."
Sai ya yi shuru yana sauraran Baffa ta wani fannin gaskiya ya faÉ—a.
"Za mu iya kai shi kotu mu yi nasara amma zafi da baƙin cikin dake zukatan mu ba za su gushe ba Abdulrrahman. Kuma ba za mu iya sauya cewarsa na baya son yar mu ba, duk abin da za mu yi sai dai mu yi ba mu isa mu ƙanƙarema Ummu bakin cikin zuciyarta ba amaimakon mu saukaka mata sai mu sake dagula mata lissafi."
"Haka ne Baffa."
"To ka yi hakuri da maganar shigar da ƙara. Ba wai don ba za mu iya sharia da shi ba ne. Aa sai domin mu taimaka ma Ummu wajen mantawa da shi, shi kuma Allah ne ya hana zalunci kuma ya yi, to ko Ummu ba ta furta Allah ya saka mata ba wallahi sai Ubangijin adalci ya yi mata sakayya ko a nan duniya ko a ranar gobe ƙiyama.".
"In sha Allahu."
Ammah ta faÉ—a cikin sanyin murya Hamma Abdulrrahman ya yi ajiyar zuciya kafin ya yi magana Baffa ya dafa kafaÉ—an shi yana faÉ—in." Ina fatan ka fahimce ni yanzu ko?
"Na fahimta Baffa. Allah ya kyauta na gaba."
Ya faÉ—a yana jin fushin sa na sauka.
"Allah ya yi maka albarka "
"Amin Amin Baffa "
Ya amsa a sanyaye shuru na wani lokacin kafin Baffa ya tambaya Ummu.
"Na yi mata faÉ—a, Baffa ba a lallashi a irin haka, ba ta da hankali sai zuciya ta zuga ta."
"To yanzu dai ka koma ka matsa mata taci wani abu. Amman ku ta ce tunda suka zo ba ta ci komai ba, kuma ka ga ba ita kaÉ—ai ba ce "
"To Baffa."
Ya amsa yana kallon shi.
"Baffa cikin fa? Mu za mu riƙe shi ko bayan ta haihu za a mayar da shi wajen uban shi?
Baffa ya girgiza kai kafin ya ce" A'a ba ka ji abin da ya ce a takardan ba ne?. Ba ya bukatar cikin shima "
Nan Baffa ya sanar da shi yadda suka yi da waliyin Habib da hukuncin da ya yanke.
"Baffa saboda dai ka ƙi yarda ne amma ai Ummu kaɗai muka aura masa ba da ciki ba. Bai isa ya ƙi karɓan abin da yake nashi ba ne ƙaryan shi tasha ƙarya"
"Ba komai. Ai Ummu ce za ta haifi koma mene ne, saboda haka ba za mu ƙi jinin ta ba."
Hamma Abdulrrahman ya jinjina kai amma da ace Baffa zai bari wallahi ba za su karɓi cikin nan ba sai an je kotu alƙali ya yanka mai kuɗin ɗaukan ciki da reno tana haihuwa bayan ta yaye ya zo ya karɓi abin ya ɗiga shi. Rayuwar Ummu ba za ta kare wajen wahala ba tunda ba shi da mutumci.
Umarnin Baffa ya bi ya koma ciki ya iske gabaɗayan su har da Saddam sun tasa Ummu kowa yana bata baki amma ba ta ji ba kuka kawai take yi tana gunji ko tsayawa ma jin kukanta bai yi ba ya ce a haɗo mata tea mai zafi a kawo masa ba musu Baɗɗo ta mike ta je ta haɗo mata daman akwai ruwan zafi a fulas ta ciko wani jug ta kawo ma Hamma Abdulrrahman ba wasa a fuskar shi yana miƙa ma Ummu jug ɗin ta karɓa hannunta na rawa.
"Shanye shi duka ki ba ni Jug É—in ina jiran ki "
Ya faɗa ba wasa a maganarsa jiki da hannu na rawa ta karɓa ba ko gaddama ta kafa kai ta kwankwaɗe shi ta dire kofi su Baɗɗo na ta murna.
"Yauwa ko ke fa Ummu Salma yanzu ai kya ji dama-dama"
Ba ta gama rufe baki ba Ummu ta yunkura da sauri kafin ta iya miƙewa amai ya biyo baya duk kuma ruwan shayin da ta sha sai da ta amayar da shi a wajen nan Hamma Abdulrrahman ya matsa baya yana rufe hancin sa, saboda ba ya son ganin amai ko ya shaƙa yanzu nan shima zai fara fita ya yi ya ce in sun gyara wajen su sake haɗo mata wani shayin. Hamma Saddam ma ya bi bayan shi aka bar Ummin ikki ta kama Ummu zuwa tiolet ita kuma Baɗɗo tana gyara in da Ummu Salma ta yi aman.
Sai da aka gyara wajen aka kunna turaren tsinke ɗakin ya ɗau ƙamshi ita kuma Ummu Salma wanka Ummi ikkin ta yi mata domin jikin na ta ba karfi sannan duk ta ɓata kayan jikinta kawai sai ta taimaka mata ta yi wanka bayan ta fito Baɗɗo ta ɗauko mata wata doguwar riga cikin kayanta da suka zo da shi. Hamma bai tafi ba ya sake dawowa da wani kofin cike da ruwan tea ya ce Ummu ta sake shanyewa sai ta fara hawaye tana faɗin.
"Hamma zan yi amai."
"Ko sau É—ari za ki yi amai sai kin sha, in dai zai zauna a cikin ki."
Ta san halin shi in yana magana da lalama a yi abin da yake so in ya birkice bashi da kyau dole ta karɓa ta shanye.
Ya karɓi jug ɗin yana faɗin" Good. Ki riƙa cin abinci sosai kar ki bari na ji labarin kina zama da yunwa kin ji ko ba ki ji ba?
Sai ta gyaɗa kanta tana mai zubar ƙwalla
"Ba ki da baki ne?
"Na ji."
Ta faÉ—a tana danne kukanta.
Sai ya miƙe lokaci ɗaya yana faɗin" In ma kina so ki mutu ne ki yi mutuwar da Allah ya tanadar miki, amma in har saboda wancan ne to ki sani har abada rayuwarki ba ta da wata amfani a wajen shi. Ki riƙa tuna hakan a cikin zuciyarki."
Daga haka ya fice ya koma falo ya yi ma su Ammah sallama da cewa zai tafi.
"Ka tsaya ka ci abinci mana."
"A'a Amma bana jin cin wani abu."
Jakarsa ya ɗauka ya rataya ya ce zai shigo gobe da safe kafin ya wuce wajen aiki in dai ba ta ci abinci da yamma ba Ammah ta yi masa waya zai sake dawowa da haka suka yi sallama ya fice Baffa ya koma ɗakin sa can ya bi shi suka yi sallama sannan ya fice daga gidan cikin tausayin Ummu har da su Baffa gabaɗaya gwara Baffa na bayyana damuwarsa Amma ce ke ɓoye abu kallo ɗaya ya yi mata ya fahimci ta rame a tsaye cikin yini ɗaya.
 Ranar sai dare Abdullahi ya kai Ummin ikki gida. Daman da ya dawo da yamma tare da matarsa Adda Suwaiba da Madibbo ya zo. Ita ce tare da Baɗɗo suka zauna da Ummu suna ta ɗan ba ta baki ta daina kuka sai dai suyan zuciya kawai. Baɗɗo nan ta kwana tare da Ummu matar Abdullahi sai wajen sha ɗaya na dare suka koma gida.
Washegari ma wajen ƙaryawa sai da Baffa ya zauna ma Ummu ta ɗan sha tea kaɗan shi ma ba daɗewa sai da ta yi aman shi, da rana faten wake Amma ta yi mata amma ba ta iya ci ba sai da Hamma Abdulrahman ya zo ya tsaya mata sannan ta tsakura haka da daddare ma sai da ya tsaya mata tunda suna gidan har dare tare da Adda Suwaiba kowa Ummu yake tausayawa. Habib kam ya sha tsinuwa da mugun baki Ummin ikki ma tana gidan har dare ita da Kaltume washegari kan Ammah ta fara karɓan baƙi masu zuwa mata jaje, yayyen Baɗɗo dukkansu sun zo Iklima har dare sannan ta tafi. A waya ma Ammah tana ta samun wayoyin sauran yaranta da matan su.
Hamma Jibo ya ce sai karshen sati Hamma Mustapha dai ya ce sai karshen wata za su shigo har Baffa duk sun kira suna mai jajanta musu da wannan lamarin da ya faru su da yake suna da sauƙin kai sun ce hukuncin Baffa ya yi daidai. Kuma duk sun yi magana da Ummu Salma ta wayar Ammah suna ta bata baki amma har yanzu Ummu ba ta daina kuka da damuwa ba.
Hamma Kabiru ne ya yi ta masifa a waya yana faɗin ba za su karɓi wannan cikin ba, ba wanda ya saurare shi daga AmmaH har Baffa sanin halin shi shi ma dai ya ce yana tafe a karshen satin nan.
Saboda hankula ba'a kwance yake ba shi ya sa Amma da Baffa suka manta da maganar kwaso kayan auren Ummu Salma. Sai da su Umma Balki suka zo daga Mubi suke maganar kwaso kayan tunda duk Ammah ta sanar da su, abin da ke faruwa.
Da Ammah ta yi masa mganar kwaso kayan Ummu sai Baffa ya ce za a je a kwashe in zukata sun samu natsuwa. Kwanan su É—aya suka juya cike da alhini.
Baffa ma ya sanar da su Baffa Umaru kowa ya ji labari sai jikinsa ya yi sanyi barin ma in suka zo suka ga yadda Ummu ta koma cikin kwana biyar ta faÉ—e ta rame ta lalace abinci in ba Baffa ko Hamma Abdulrrahaman suka tsaya mata ba, ba ta ci in kuma ta ci ba ya zama a cikin ta za ta amayar da shi. Sannan BaÉ—É—o ta ce Ummu ba ta samun barci da daddare.
Abdullahi shi kan shi ya ga É—ashewar Ummu Salma ya ce ya kamata a kaita asibiti a duba lafiyanta. Shima Baffa ya ga haka saboda komai ta ci baya zama a cikin ta.