← Book details Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 92

Sashe 57

Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ita dai Ummu Salma jin Mami kawai take yi ba ta san irin yadda zuciyanta ta so Habib ba ne. Ba ta san yadda jikinta da rayuwarta ya saba da shi ba ne, shi da ya fara me ya sa bai ƙarisa ba? Me ya sa ya rabu da ita? Ta amince za ta zauna da shi ya yi ta moran jikinta har illa masha Allah, amma yanzu da ya sake ta ina za ta je? Ji take yi kamar ta rasa komai na rayuwanta ne in ta ce komai tana nufin komai, mafarkin ta burukanta da dukkan wani tanadinta na rayuwa Habib ya yi sanadiyar da yau ita Ummu Salma ta dawo ba komai ba, ya kuma ma yar da rayuwarta kwanko babu wani abin mamora a rayuwarta a yanzu.

Kwanan Mami biyu da zuwa Jimeta sai ga Hamma Mustapha da iyalan shi a rana ɗaya suka zo da Hamma Jibo amma shi kaɗai ya zo bai zo da su Nauwara ba, jirgi ya biyo ma. Suma dai duk haƙuri da nasihan suka yi ta Ummu Salma ganin yadda duk ta faɗe ta rame ba ta mgana. Daman a wannan lokacin kowa haƙuri yake ba ta, domin babu wani abu da za a yi mata.

Zuwan su Hamma Jibo aka yi maganar kwaso kaya. Mami da Ummin ikki ne suka je gidan tun da key É—in gidan da man su BaÉ—É—o sun taho da shi kaf aka haÉ—a kayan ta waje É—aya babban mota mai budaÉ—É—en baya ta zo ta kwashe zuwa gida a É—akin kusa da na Ammah mai ciki da falo aka saka kayan aka rufe, kayan abincin da Hamma Jibo ya siya mata jibgi haka aka kwaso su sai dai aka kai su store É—in Baffa.

key É—in kuma suka ba ma maigadi sallahu in megidan ya zo ya bashi ko masu duba gidan tun da suna zuwa duk sati kayan Habibu ko É—aya ba su samu a gidan ba tun washegarin ranar da ya yi sakin kafin ya tafi sai da ya kwashe duk abu da yasan na shi ne daman iya kayan sawa ne da takalma sai takardunsa duk ya kwashe su.

Ranar da aka kwaso kayan kwana Ummu ta yi tana kuka. Ba kuma wanda ya hana ta Mami ta ce a ƙyaleta ta yi kukanta ko za ta samu suƙuni kar baƙincikin ya ƙume mata a zuciya ta samu matsala. Tunani take yi shike nan komai ya ƙare tunda gashi an kwaso kayan ta, shike nan ta rasa komai ba ta da wani abu kuma da ya yi mata saura. Cikin dake jikinta ne kawai ya rage mata shi kaɗai ne abin da ya rage ta ƙarisa a halin yanzu.
Habib ya cuce ta, Habib ya gama da rayuwanta.
Habib ya yi ma duniyarta kaca-kaca, Habib ya yi sanadiyar da labarinta ya shiga bakin mutane ya mayar da ita bazawara ya sanya kanta a cikin mata masu taɓo a zukatan su, ya jijjiga duniyanta sannan ya bar ta da abin tunawa har na tsawon rayuwarta na har abada.

*Janafty*
*FARGAR JAJI.*

*Wattpad:JamilaUmar315*
*Arewabooks:JamilaUmarJanafty*

"To Hajiya Hauwa'u Inuwa Aminu (Anty Hairi) with love and gratitude"

https://chat.whatsapp.com/LsC7Rjmei7J6Hd11e95nNS?mode=gi_t

*14*

Sai da Mami ta shafe sati ɗaya a garin Jimeta kafin ta koma Kaduna. Kuma zaman ta ya yi amfani tunda Ummu na jin maganarta sannan tana sauraranta, zamanta a gidan kafin ta tafi ya taimaka ƙwarai wajen sake dangana a zuciyar Ummu Salma, tana cin abinci tana kuma samun hutu sannan koke-koken da take yi ya ɗan ragu sai dai abin da ba'a rasa ba.

Mami ta so Baffa ya amince ta tafi da Ummu Salma Kaduna wajenta ta zauna na wani lokaci saboda yanzu garin Adamawa gabaɗaya ya yi mata ƙunci in ta yi nesa za ta fi samun sukuni da jin daɗi lokacin Hamma Jibo na nan shi bai koma ba ya yi na'am da shawaran Mami har Ammah ma ta ce gwara ta ɗauketa su tafi na ɗan lokaci har zuwa komai ya lafa, shi kan shi Baffa ya fahimce su amma sai ya yi tunani a matsayin shi na Babba, bai ba ta Ummu ta tafi da ita da farko ba amma ba wai ya hana ta ba ne.

"Fatima Auta fa ƴ'arki ce, ni ko Amman ku ba mu isa mu hana ki tafiya da ita ba. Sai dai ya kamata mu yi abin hankali, ke fa matar aure ce kina da miji da kike zaune a ƙarkashin ikon sa, bai kamata ba tare  da sanin shi ko izinin shi ba kawai ya ga kin zo da yarinya ba. Ya kamata ki yi shawara da shi in ya amince ki zo ga Auta nan halak malak Fatima ba wanda ya isa ya yi miki iko da ita."

Abin da Baffa ya faÉ—a mata kenan ana gobe za ta koma da ta same shi da maganar son tafiya da Ummu Salma gidanta dake Kaduna.

"Baffa ka fa san Abban Islam ba shi da wata damuwa. Mun yi ma magana da shi a waya shi ya ma kawo wannan shawaran na cewa ko zan taho da ita ne ta É—an samu natsuwa? Shi fa ko har abada za ta zauna damu ba shi da wata damuwa."
Mami ta amsa ma Baffa cikin magiyan ya amince ta tafi da Ummu amma ya hana ta, ba da niyyar ba ta da hurumi ba sai da niyyar ta bi komai a hankali da cewa ta koma su tattauna da mijinta in ya amince daga baya sai ta zo ta tafi da Ummu sun ba ta ita har abada.

Dole Mami ta amince amma ba haka taso ba, ita ma ta ce ba domin wajen aiki ba, da sai ta yi wata a garin Jimeta amma saboda aiki ya sa ta yi shirin komawa. Kafin tafiyarta haka ta zaunar da Ummu  ta sanar da ita za ta koma Kaduna amma ba daɗewa za ta dawo ta tafi da ita can ta zauna tare da ita.

"Mami me ya sa ba yanzu ba?

Ummu ta faɗa cikin raunin murya har ta fara hawaye. Za ta fi son Mami ta tafi da ita, domin garin nan da mutanen cikin ta sun gama fita da zuciyarta, wani ƙunci take ji da duhu daga cikin zuciyarta watakila da za ta yi nesa da gida da garin gabaɗaya za ta fara mantawa da kaddaranta har ta manta da Habib daga zuciyarta gabaɗaya.

"Ni ma haka na so, to amma kin san halin Baffa ya matsa sai na koma gida na yi magana da Abban Islam."

Ummu tana ta kuka har da shessheƙa, Mami ta yi ta lallashinta da ban baki, ba ta so Mami ta tafi tana son zama da ita domin ita ce kawai ta fahimci halin data ke ciki, ita ce kaɗai ta san irin raɗaɗi da zafin da kaddaran take da shi, ita ce kuma ta san irin yanayin da ake shiga in ka rasa dukkan wata dama ko mafitar daka ke tunanin ka kama ko ka dafe tuntuni amma sai daga baya ba ka shirya ba, ba zato ba tsammani komai ya kubce daga hannun ka.

"Ki yi haƙuri Daughter in sha Allahu zan dawo na tafi dake. I promise you in sha Allahu."
Da haka ta samu ta lallasheta ta daina kuka. Sannan ta bi ta da kalamai masu sanyaya zuciya da alkawarin ko bayan ta tafi ba za ta cigaba da damuwa ko kuka ba, sannan ta riƙa cin abinci saboda lafiyanta da inganta abin da ke cikinta kuma ta yi mata alƙawarin duk za ta ji maganarta. Sannan ta umarce ta da duk abin da take so kar ta yi ma Baffa ko Ammah magana ta kirata ta sanar da ita, ita kuma ta yi mata alƙawarin komai take so in dai bai fi karfinta ba za ta yi mata.

Ranar Jumma'a da misalin ƙarfe goma na safe jirgin da Mami ta shiga ya ɗaga zuwa Kaduna. Abdullahi ne ma ya tuƙa ta zuwa filin jirgin, bayan tafiyarta Ummu ta yi ta kuka ba wanda ya hana ta kowa ya san akwai shaƙuwa mai tsanani tsakaninta da Mami, balle itama Mamin lokacin da za su yi sallama har tana sharan ƙwalla kamar kar ta tafi haka take ji.

Bayan tafiyar Mami kamar Ummu ta saduda sai kuma ta koma gidan jiya, ita kenan sai kwanciya tana kuka ba ta cin abinci sai Ammah ta shigo ta yi magana ta tsakura kaɗan, ko Baffa in ya tsaya mata ko kuma ta ji zuwan Hamma Abdulrrahman, ga ta da juna biyu amma ba ta taɓa cewa yau ga abin da take sha'awa ba ko Ammah ta tambayeta ba ta magana sai ta ce komai aka ba ta za ta ci, ita a ganinta ba ta da wani sauran zaɓi kuma a rayuwarta tunda Habib ya sake ta kamar tara sa dukkan wata damarta ne.
Chapter 57 · 0% Book details