Sashe 70
Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Namijin da ba ya iya bayyana ƙololuwar jin daɗinsa ko da daɗin zai kashe shi ne, amma zai yi rawan jiki sannan zuciyarsa za ta tsananta bugu sannan zai ta yin zufa amma ba wai ya yi kuka ko sambatu ko wata alama ba, daga lokacin ta samu salama tunda ta fahimci duk yana yin haka kawai dai sambatu ne da ihu ba ya yi, jiya ma da ta tafiyar da ragamar ya yi ta mata nishi kamar numfashinsa zai kwace daga ƙirjinsa. Shi dai in har wajen zai yi duhu to zai iya sakin jiki a yi komai sai bayan sun natsa ne in haske ya gauraye ɗakin ya yi kamar ba shi ba, kai tana son Lamiɗo domin ta san ta yi ma sauran mata zarra samun namiji mai kama da maza ɗari a waje ɗaya.
Tana so su dinga zama suna hira duk da itama ba ta da surutu amma tana so ta ga tana yi masa hira ko ba zai yi magana ba ya yi ta kallonta da yanayin kallon shi mai narkan mata da zuciya.
Amma matsalan itama ba ta iya hiran ba, da ta fara sai ta rasa me za ta ce, in dai ba hiran can Daura ba shima sama sama, har gwara ma in tana yi masa hiran Ammah har mirmishi za ta ga yana yi mata sannan in ta yi tambaya yana bata amsa jefi-jefi. Ta daɗe da shaida cewa Lamiɗo na kaunar Ammah ninki da yadda yake son mahaifiyarsa Mami ita kuma kowa ya shaida yadda take ƙaunarsa, shi ya sa itama kamar ta lasheta saboda ita ɗin Matar Lamiɗo ce, tana gani in ta je matan su Hamma Abdulrrahaman Ammah ba ta yi ta kan su, amma ita da yaranta da jikinta da komai take yi musu wahala. Da farkon auren su ba ta san dawan garin ba duk da ta san a hannun Uncle ɗin sa ya taso yayan mahaifiyarsa. Ta ɗauka mahaifiyarsa na da tasiri a rayuwarsa sai daga baya ta fahimci komai domin lamarin ma a bayyane yake. Mami da Lamiɗo in suka haɗu ban da gaisuwa ba abinda ke sake haɗa su, a waya ko sai su yi sama da wata ba su yi magana ba in ba wani abu ba ne ya taso ya kirata ba. Musamman ma dai ya fi kiranta ya gaisheta in su Islam na gida ya ce a ba su wayar shi dai yana da son yara duk da baya son hayaniya. Wayar ma da yake yi mata Ammah ce ta ce ya riƙa kiranta yana gaisheta mahaifiyarsa ce, amma mijinta Alhaji Isa akwai girmamawa mai girma a tsakanin shi da Lamiɗo shi har ya fi Mami ma jawo shi a jiki amma ita kamar ba ɗan ta ba, ko da yake da man ta ce ba ɗanta ba ne ɗan Ammah ne.
Da fari har ita tana kira ta gaisheta lokaci bayan lokaci ranar dai Mami ta faɗa mata gaskiya da cewa in za ta yi kamun kafa ne ta je ta kama kafar Ammah ita uwar Lamido ce kawai a haihuwa amma nan duniya ba shi da iyayen da suka wuce masa Ammah da Baffa kuma ta ga haka, domin a wajensa shima ba shi da iyayen da suka fisu, akwai wani zuwan da suka yi Daura ta tambayi Fulani Daura ita ta zaunar da ita ta bata labarin mafarin komai ta kuma shaida mata Mami ta yanke alaqa da duk wanda ya danganci Lamiɗo da su Ammah kawai suke zumunci, kuma ta ga hakan in za su haɗu sau nawa bayan gaisuwa ba ta taɓa ganin sun yi wata magana ko da mintina goma ba ne, Mamin ma kwata kwata ba ta yi ta kansu, ko su Sultan a matsayin jikokinta ba ta taɓa ganin ta ja su jikinta ba. Tun lamarin na ba ta mamaki har yanzu daga baya ya zame mata jiki. Ta riƙe Ammah a matsayin uwar mijinta da Baffa a matsayin uban mijinta, sannan ta riƙe Maimartaba a matsayin uba sannan ta riƙe Gimbiya Shahida a matsayin uwa Fulani Daura kuma a matsayin kaka.
Mami kuma sai ta saka ta a cikin sahun wasu makusanta LamiÉ—onta.
Tashi ta yi tana yanga kamar yadda ta saba ta karisa kujeran da yake zaune ta zauna kusa da shi, kanta ta ɗora saman kafaɗan shi tana sauke numfashi jikinta da gashin kanta suna fitar da wani sihirtattacen ƙamshi mai daɗi.
Ya ɗan motsa amma bai buɗe idanuwansa ba tun da ya san ita ce, hannunta ta tusa cikin yatsun hannunsa guda ɗaya ta jimƙe shima sai ya taya ta suka jimƙe yatsun hannunsu a tare, mirmishi ta yi har yana fidda sauti kafin ta sake lafewa daga gefen kirjinsa.
Sun fi minti goma a haka sai ita ce ma ake jin sauka da hawan numfashinta amma shi ba ko a jin motsin na shi numfashin, in za su kai gobe a haka ba zai ce mata komai ba.
Ta san shi ta san waye Lamiɗo, ko mai za ta yi ba zai taba cewa aa ba, mutum ne mai girmama zamannsu mai daraja aure da sauke haƙƙoƙi.
Ta tuna bayan haihuwan Beena ta faɗa masa ta yi planning tunda ta samu haihuwan a jere da juna, ko faɗa bai yi mata ba ko irin ya ce me ya sa ba ta faɗa masa ba. Shi ba wanda ya isa ya gane ya ji daɗi abu ko bai ji daɗi ba fuskarsa ta iya shanye komai ba ta kuma bayyana abin da ke fuskarsa. Hausawa na cewa wai labarin zuciya a tambayi fuska to shi Lamiɗo labarin zuciyarsa sai dai a tambayi bakinsa, domin komai bin kwafkwafin ka ba ka isa ka fahimci abin da ke cikin zuciyarsa ba.
"Ranka ya daÉ—e."
Ta kira shi kamar yadda ta saba kiran shi.
Bai amsa ba kuma bai buÉ—e idanuwansa ba, ta É—an É—ago ta kalle shi ta san ba zai yi magana ba amma tana da tabbacin yana jin ta.
"Ashe kuma abin da ya faru da Autan Ammah kenan?
Ta faɗa lokaçi ɗaya tana ɗan wasa da gargasa hannun shi, da hannunta guda ɗaya.
Shuru na wani lokaci sannan ya buɗe idanuwansa da suka ɗan ƙanƙance sun ɗan kuma sauya launi.
Kallon shi ta yi, shima sai ya kalleta yadda ya kalletan ne ya sa ta san bai san komai ba.
"Ba ka sani ba?
Ta faÉ—a cikin sanyin murya lokaci É—aya tana goga masa gashin kanta samana kirjinsa cikin wani salo.
Bai yi magana ba amma ta ga ya É—an jinjina mata kai alamun bai sani ba.
Sa sauri ta tashi daga kan kirjinsa tana fuskanshi.
"Jiya da na ganta wani iri na tambayeta ko ba ta da lafiya ne? shi ne fa Ammah ke ba ni labari."
Ya yi mata kuri da ido yana son jin ƙarshen maganar..ita kuma sai ta yi shuru tana nazarin shi, yana so ya ce mata me Ammah ta ce? Amma kuma bakin shi ya gaza furtawa.
"Uhm labarin fa ba daÉ—i ga tausayi yaron nan ya zalunci Autar Ammah"
Ta faÉ—a tana matse hannunta cikin na shii.
Idanuwansa ya ke buÉ—ewa a kanta, zuciyarsa har wani tsalle ta yi amma bai nuna ba, yana nan a yanayin shi tun farko.
Ita kuma Bilkisu ba ta fahimci ya matsu ya ji labarin ba sai ta cigaba da faÉ—in" Ta rame fa duk ta yi wani iri. Ai ka ganta ko?
Ta gama faÉ—a da sigan tambaya.
Ya yi shuru kawai yana kallon ta.
"Ko ba ka gan ta ba?
Ta sake tambaya tana kallon shi, sai da ta ja yatsunsa sannan ya É—an lumshe ido ya buÉ—e lokaci É—aya yana mai jinjina mata kai alamun e ya gan ta.
"To ba ka ga ta rame ba? Duk ta yi fari ashe ma da ciki ya sake ta."
Hannunta dake cikin na shi ya matse har sai da ta É—an kalle shi lokaci É—aya kuma ya zare hannun shi ya yi shuru ba tare da ya yi magana ba.
Bilkisu kuma ta shiga ba shi labarin da Ammah ta ba ta ganin kamar LamiÉ—on ya tattara hankalin shi a kanta.
Har ta gama bai ce komai ba amma hankalinshi da natauwarshi yana kanta ya yi mata kuri yana kallonta kuma yana sauraranta.
"Ammah ta ce hankula sun tashi sun shiga damuwa amma dai yanzu da sauƙi tunda an kwarari wata biyu cikin na uku. Ummu Salman ce sai a hankali har yanzu ba ta daina yan koke koke ba.".
Ta gama ba shi labarin kuma ya saurare ta amma bai ce mata komai ba.
"Wai ko Ammah ba ta faÉ—a maka ba?
Ta sake tambayan shi.
Sai wannan karon ya yi magana
"Ba ta faÉ—a ba."
Kawai ya iya cewa sannan lokaci ɗaya ya miƙe yana kallonta kafin ya ce" zan yi wanka"
Da ga haka ya wuce ta ya fara tafiya a hankali cikin takunsa har ya shige tiolet ta bishi da kallo, ko maganar ta dame shi ne ko ba ta dame shi ba, ba za ta iya sani ba. Amnma ta yi mamakin yadda bai sani ba ko Ammah ba ta faɗa masa ba ta yi tunanin amininshi KB zai faɗa masa, ta wani fannin kuma ba ta yi mamaki ba sanin halin mijin nata, ba ko da yaushe kake samunsa ba. Za ka iya tura masa saƙo sama da wattani bai gani ba, kuma sanda aka yi abun yana can wajen aiki ba lalle ya sani ba, ita dai ta tausaya ma Ummu Salma, ƙaramar yarinya ta haɗu da jarabawa, ita fa ta ga ƙokarin su Ammah yadda suka yi ma Ummu auren wuri haka a lokacin ta yi ta ce ma Lamido ta yi ƙarama da aure bai ce mata komai ba, ga shi nan ya sake ta ya wulakanta ta da ƙananun shekarunta.
Ta shi ta yi ta É—au wayarta ta bar É—akin domin ta san in gogan ya fito ya iske ta ba zai ji daÉ—in shiryawa ba, shi ya sa ta bar masa É—akin ta koma É—ayan bedroom É—in ta É—an kwanta.