Sashe 82
Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ke fa musulma ce, kin ta so gidan tarbiya da gata, ko daga yadda yan'uwanki suka cika asibitin nan saboda ke na shaida ke yar gata ce, wani dalili ne zai sa ki yi yunkurin kashe kanki? Kin manta duk wanda ya kashe kansa kafiri ne? Ko kin manta cewa da kin mutu a lokacin wutar jahannnama za ki shiga?
Tsoro da wani irin imani suka sake kama zuciyar Ummu, ba ita kaÉ—ai ba hatta Nurses É—in dake É—akin.
"Komai ya faru dake ki gaya ma Allah Shi zai yi miki mganin komai. Mu musulmai ne mun san yarda da kaddara mai kyau ko mara kyau yana cikin imani ne. "
Ya sake faÉ—a yana mai kallonta.
"Ina so ne, ina so ne na daina jin zafi da radaÉ—in dake cikin zuciyata."
Ummu ta faÉ—a cikin matsanancin kuka majina da hawaye na kwanraya.
"Me ya sa ba ki karanta Qur'ani ba? Me ya sa ba ki kira sunan Allah ba! Yana sane da halin da kike ciki, da kin daga hannun kin roƙesa salama da amimci da ya sama miki ba sai kin yi tunanin kashe kan ki ba Ummu Salma."
Kuka kawai take yi tana jin kamar ta mayar da hannun agogo baya.
"A lokacin da kika yanke shawaran kashe kanki ba ki yi tunanin wannan ran dake motsi a cikin ki ba ? Da kin mutu fa? Da kin kashe rai biyu? Sannan kin manta da iyayenki da dangin ki? Kin yi tunanin yadda za su dauwama cikin kuka in har kika bar rayuwwansu?
Ummu ta fara girgiza kanta tana cigaba da kuka.
"Mahaifiyarki ana taho dake ta faÉ—i, kina ciki muna ceto rayuwarki ita kuma tana kwance ana daidaita numfashinta."
"Wayyo Ammah."
Ummu ta faÉ—a kamar za ta shiÉ—e."
"Mahaifinki duk da ya yi dauriya amma kuka yake yi yana fargaba rasa ki, yayyenki maza duk da suna da jarumta sun shiga damuwa saboda ke, yau da ace kin mutu kina tunanin za su manta irin mutuwar da kika yi? To har abada ba za su taɓa mantawa ba."
Ummu na kuka tana numfarfashi, ba ita kaɗai ba hatta Nurses ɗin nan suna ta goge ƙwallah
"Kin yi sa'a. Allah na son ki ya sake ba ki wata dama. Ina so ki sani ki yi ta neman gafaran Allah ki kuma tuna kowani tsanani akwai sauƙi a wajen Allah."
"Astagafurullah"
"Allah na tuba."
Ummu ta faÉ—a cikin matsanacin kuka kamar ranta zai fita.
"Daga yau in tunanin kashe kanki ya sake zuwa cikin tunaninnki. To ki tuna da abubuwa guda uku, na farko yadda za ki koma gaban Allah a matsayin asararriya na biyu kuma halin da iyayenki za su shiga saboda ke. Na uku kuma ki tuna ke musulma ce, kuma duk musulmin kwarai yana da imani sannan ya yarda kaddara mai kyau ko mara kyau."
"Na tuba Allah ka yafe mini."
Take faÉ—a tana jin wani irin tsoro na sake shiga cikin zuciyanta.
"A matsayina na likitan da ya karɓi case ɗinki har ya ceto rayuwanki, shi ya sa na baki shawara sannan a matsayina na musulmi na tunasar dake abin da kika manta, in kin shiga damuwa ko baƙin ciki ki yi kuka har sai kin gaji amma ki yi addu'a ki karanta Qur'ani ki samu salama, kar ki yadda ki bari tunanin sake aikata irin haka ya sake shigarki, ki sani in a wannan karon kin rayu watakila na gaba ba za ki rayu ba Ummu Salma."
Ya gama faÉ—a lokaci É—aya yana mai mikewa tsaye.
"Na gode Dr."
"Sunana Ahmad Salisu."
Ya faÉ—a yana kallonta.
"Ya isa haka, ki sassaita kukan ki saboda yanayin jikin ki."
Kai ta gyaÉ—a masa hawaye na kece mata.
"Allah ya ba ki lafiya."
Ta amsa da Amin
Kafin ya wuce nurses É—in suka bi bayan shi jiki a sanyaye.
"Ku ba ma Family É—inta damar ganin ta."
Ya faÉ—a ma Nursea É—in kafin ya fice daga É—akin su bi bayan shi.
Bayan fitan shi kuka Ummu Salma ta cigaba da yi har da shessheƙa.
Sai dai kukanta ya tsaya ne lokacin da ta ji an buɗe kofa ta ɗago jiƙakkun idanuwanta tana kallon kofar shigowa.
Sai da ta ga yan'uwanta suna shigowa. Wani na ture wani, Mami ce akan gaba sai BaÉ—É—o bayan ta Adda Suwaiba ce, sai Adda Ummu Sulaim, Sai iklima sai Umma Balki sannan mazan suka biyo bayan su.
Hamma Abdullahi ne ya shigo bayan sa kuma Hamma Mustpaha, Hamma Abdulrrahman sai Hamma Kabiru ne ya zama karshen shigowa. Ba Ammah ba Baffa haka Ummu ta faɗa a cikin zuciyanta, a tunaninta ko suna baya ne ba su shigo ba amma sai ta ga Hamma Kabiru da ya zama karshen shigowa ya rufe ƙofar sannan ba ta ga Hamma Jibo ba, sannan ba ta ga Hamma Saddam ba, shi da man baya nan ya koma makaranta.
Baɗɗo da Mami suna rige-rigen ƙarisawa gare ta cikin wani yanayi a saman fuskokinsu.
"Ma sha Allah. Sannu Daughter."
Mami ta faÉ—a tana zama gefen gadon data ke kwance har tana rumgumota ta gefen hannunta na hagu.
Jin ta a jikin Mami kawai sai ta saki kukanta wiwi kamar karamar yarinya nadama ya sake kamata ta.
Ta saka kowa ya zo, zuwam kuma ba na lafiya ba, ba kuma zuwan shiri ba.
"Shii is ok. Mun gode ma Allah tunda kin farfaÉ—o, kukan ya isa haka."
Mami take faÉ—a tana bubbuga bayanta.
BaÉ—É—o ma kusa da Mami ta zauna tana mai kallon Ummu idanuwanta cike da hawaye ga shi sun kumbura.
Tun shekaranjiya take kuka ba ta daina ba.
Sai aka koma ita ake ba hakuri ana lallashi.
"Sisna"
Baɗɗo ta faɗa tana mai riƙe hannun Ummu wanda aka cire ma ƙarin ruwa.
"Sisna me ya sa?
BaÉ—É—o ta sake faÉ—a lokaci É—aya tana mai fashewa da kuka.
Ummu ma hawaye suka sake kece mata kamar an ɓude famfo.
"Ku yi haƙuri."
Ta faÉ—a a hankali bakinta na rawa.
"Shii. Ya isa nan asibiti ne."
Mami ta faÉ—a tana mai share ma Ummu hawaye da mayafinta jikinta har da majina.
"Bar kuka kin ji ko? Mun gode ma Allah da kika rayu."
Mami ta sake faÉ—a tana share mata hawaye.
"Mami."
Ta kira sunanta cikin dashewar murya da kuka.
"Naam My First Daughter."
"Ku yafe mini Mami."
Ta sake faÉ—a lokaci É—aya tana mai fashewa da kuka.
Sake rumgumota Mami ta yi, itama hawaye sun kawo mata saboda tausayin halin da Ummu ke ciki.
"Ya isa, is ok kin ji.?
Ta sake faÉ—a tana mai É—an tapping É—in bayanta alamun lallashi.
Sannan ta sake É—agota tana mai share mata hawaye da gefen mayafinta.
"Sannu Ummu kin auna arziƙi."
Umma Balki ta faÉ—a cikin wani yanayi.
"Amma dai abin da kika yi sakarci ne, gabaÉ—aya kin É—aga mana hankali? Haka ake yi? Kan ki farau mutuwar aure?
Ta faÉ—a cikin faÉ—a, da man ita da Ammah ne a É—akinsu suke da faÉ—a
"In da kin mutu fa? Wani hali iyayenki za su shiga! Jamila tana ganin halin da aka kawo ki rai ƙwai kwai ta yanke jiki ta faɗi yanzu in da ya zo da karan kwana fa? Me za ki faɗa ma Allah, ke kin kashe kanki bakincikin ki ya kashe uwar da ta haifeki duk saboda namiji? Namijin banza, namijin ƙanin ajali to ni a matsayina ta uwarki na ce in kika sake ma tuna wannan maci amanan ba mu yafe miki ba shashasha kawai."
Ta gama faÉ—a har tana nuna ma Ummu Salma É—an yatsa wacce ta lafe a jikin Mami tana ta kuka.
"Umma ku yi haƙuri."
"Kaniyarki da haƙurin, sakarya, ba ki da tunani ne! Ina ilimin ki da hankalin ki yake Ummu Salma? Kawai ki yanka kanki kamar a wasan ƙwaiƙwayo"
Ummu kuka take yi har yana ba da sauti ga hawaye ga majina.
"Na yi nadama."
Ta ke faɗa muryanta na shaƙewa.
Mami ke lallashinta amma faɗan Ummu Balki ne ya sa kukanta yaƙi tsayawa.
"Umma Balki don Allah ki yi haƙuri a bar maganar nan tunda dai ya faru kuma an ci sa'a abin ya zo da sauƙi ba sai a yi hakuri ba."
Mami ta faÉ—a tana kallon Umma Balki.
"Ke ma Fatima kaniyarki? Ke ce ke É—aure mata kugun ta yi sakarci sannana za a yi mata faÉ—a ba? Kenan ma abun da ta yi mai kyau ne."
Mami ta yi shuru jin an zage ta.
Su Hamma Mustapha da suke É—akin sun yi shuru kamar ruwa ya ci su.
"Ki yi haƙuri Umma tunda muna asibiti ne."
Adda Suwaiba ta faÉ—a, itama tsaraban hararan ta samu da ya sanya ta kama bakinta ta yi shuru.
"Ai Umma abin da kika yi ya yi daidai. Ni ba domin na lallashi kaina ba, na so ne ina shigowa na falla mata maruka goma sannan na taka wuyanta sai ta kusa mutuwan da gaske sannan zan ƙyaleta."
Hamma Kabiru ya faÉ—a cikin kaushin sa.
"Yauwa, faÉ—a mata ina daÉ—in shi ai ko ba a mare ta ba, a yi mata faÉ—a shi dukan in ta warke a yi mata tunda ba ta da tunani haka kurum, kin tayar mana da hankali mun kasa sukuni da fargaba."
Umma Balki ta sake faÉ—a cikin yanayin faÉ—an ta.
"To a dai yi haƙuri tunda muna asibiti ne."
In ji Hamma Mustapha da ya faÉ—a yana kallon Ummu dake kuka kamar ranta zai fita duk tausayin ta ya gama kashe masa jiki.
"Ni ban taɓa tunanin Ummu za ta iya yin wannan sakarcin ba wallahi."
Hamma Abdullahi ya faɗa yana ɗan cije leɓensa na ƙasa.
"Ni wallahi wani takaici na ke ji in ma tuna akan wani sakarai wanda rayuwarta ba ta da amfani a wajen shi ta so kashe kanta. Wallahi ji nake yi kamar na kamata da duka."
Hamma Abdulrahaman ya faÉ—a yana mai jin takaici na taso masa.
"Don Allah ku bar wannan maganar har mu koma gida."
Mami ta sake faÉ—a tana kallon su Hamma Abdullahi.
"Gaskiya ko don natsuwar ita Auta."
Ummu Sulaim ta faÉ—a tana kallon Ummu cikin tausayawa.