← Book details Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 92

Sashe 27

Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamar zai dake ta haka ya taso mata da hargagi yana faÉ—in.
"Ke wai har yanzu ba ki ba ma kan ki wannan amsar ba?
Sai na faÉ—a miki dalilin da ya sa na aure ki da bakina sannan za ki yarda?

Ya faÉ—a yana zare mata ido, Ummu ta runtse ido hawaye suka ke ce mata.

"Sabo da ina so na ji daga bakin ka."
Ta ƙarishe faɗa cikin kuka har da shessheƙa.

"Sabo da ba ke na ke so ba, ban kuma aure ki domin ki zo ki haifa mini yara ba."

Sai da ya kalleta sannan ya yi wata dariya kafin ya ce" Kawai ni jikin ki na ke so, auran sha'awa na yi da ke kuma Alhamdulillah na samu biyan buƙatata a wajen ki, ko a haka kasuwa ta watse na ci riba."

Idanuwanta a runtse amma hawaye na ƙwaranya, kukan zucci ta ke yi, da Baɗɗo ta faɗa ta ji zafin mganar ta kuma kasa gasgasta hasaahen ta, sai da Habib ya faɗa sannan ta fahimci yadda komai yake, maganganunsa sun yi zaman da'ira a cikin zuciyarta cikin lokaci kaɗan suka fara yi mata illa, shi ya sa ashe take ta mamakin me ya sa kullum abu ɗaya? Ashe dalilin da ya sa ya aure ta kenan saboda jikin ta, kuma kamar yadda ya faɗa ne ko a haka kasuwa ta tashi shi ke da riba, tunda duk ya gama more wani albarkatun jikinta ya cuci rayuwarta ya lalata mata mata goben ta, tuni ta ji zuciyarta ta yi baƙin ƙirin ɗin da ta ji gwara da ba ta zubar da cikin jikin ta ba, wataƙila da shi ne kaɗai za ta iya tsira a rayuwarta da Habib ya lalata.

Tana jin shi yana ta mganganu ya sake ba ta tabbacin shi bai taɓa son ta ba auran sha'awa ya yi da ita ba auren soyayya ko ta zo ta haifa masa yara ba. Akwai wacce ya yi ma wannan tanadin amma ba ita ba
Daga ƙarshe ya ce ba zai sake ce mata ta bi umarninsa ba amma ta sani sai ta yi nadama daga nan ya bar mata ɗakin har yana banko mata ƙofa.

Yana fita ta saki kukan ta a fili, kuka take yi kamar ranta zai fita, ji ta ke yi kamar zuciyar ta za ta fito waje saboda yanayin da ta ke ciki, mutumin da ta ɗauka a masoyin ta da bayan iyayenta  ba ta da kamarsa, mijinta sirrin rayuwarta wanda ta aminta da shi ashe ashe shi a zuciyarsa ba haka ya ɗauke ta ba, yana da manufarsa a kanta. Ta daɗe tana kuka kafin ta iya tashi ta faɗa tiolet ta tsarkake jikinta sannan ta fito ta saka wata doguwar riga, ta shimfiɗa darduma tana salla tana kuka, bayan ta idar da sallar isha'i ba ta san awannin da ta shafe a saman darduma tana kuka ba.

Abu ɗaya ta sani ba ta ji ta tsani Habib ba, sai ma ji ta yi yanzu take son shi, amma dai ta yanke shawaran gobe za ta je gida ta samu Baffa ta faɗa masa halin da ake ciki. Sai dai za ta za ta roƙe shi ya kira Habib ya ba shi haƙuri, za ta faɗa masa tana son shi kuma ba ta son wani abu ya samu auran ta.

*Janafty*
*FARGAR JAJI.*

*Wattpad:JamilaUmar315*
*Arewabooks:JamilaUmarJanafty*

"To Hajiya Hauwa'u Inuwa Aminu (Anty Hairi) with love and gratitude"

https://chat.whatsapp.com/LsC7Rjmei7J6Hd11e95nNS?mode=gi_t

*07*

Washegari.

Ummu-Salma ta ƙulla ƙawance da kuka. Ta kwana yi ta yini yi, jiya ma kwana ta yi kuka shi ya sa ta tashi idanuwanta sun kumbura sun yi luhu-luhu, fuskarta ta yi jajir abin ka ga farar fata.
Ba ta fito daga cikin É—akin ta ba sai da ta ji fitan Habib daga gidan sannan ta fito domin tsoron haÉ—uwa da shi take yi. Ba ta iya tsinana komai ba, ga ciwon kai ga jikinta duk ba daÉ—i ruwan zafi ta dafa ta sha ruwan lipton saboda za ta sha magani sai da ta sha mgani ta É—an ji ya kwanta mata sannan ta shiga ta yi wanka tana cikin shiryawa ne Hamma Sadam ya kira wayarta. Tana É—auka ta ji yana faÉ—in.

"Ke wai kin mutu ne? Ko an yi miki magana a WhatsApp ba kya dubawa. Sai yau na sake duba ki na ga kin kwana biyu ba ki hau ba."

Mirmishi Ummu ta yi kafin ta ce"  Zan mutu ba ka sani ba ne Hamma?
Ta ƙarishe faɗa cikin sanyin murya.

"To na sani,"

Ya faÉ—a cikin Æ´ar dariya. Dariyan Ummu ta taya shi kafin ta ce" Ba ni da lafiya ne fa Hamma."
"Oh haka ne kwanaki mun yi waya da Amma ta ce ba ki jin daÉ—i, shi ne har yanzu?
"E."
"Me ke damun ki?

"Zazzaɓi ne Hamma."

Ta faÉ—a cikin kasalan da ta ji ya sake rufe ta bayan ta yi wanka.

"Sannu. Allah ya ƙara lafiya."

Ta amsa da Amin. Shi kuma ya tambaye ta ko ta je asibiti.

"E mun je"

"Allah ya ƙara afuwa sannu."

Ta amsa masa da yauwa. Habib ya tambaya ta ce ya fita aiki.
"Allah ya ba mu sa'a."
Daga nan ba daÉ—ewa suka yi sallama da juna kowa ya kashe wayarsa.
ÆŠan wayar nan da suka yi da Hamma Sadam ya É—an rage mata damuwa. Shi fa É—an'uwa daÉ—i ne da shi.

Ballatana Hamma Sadam irin mutanan ne masu amfani da social media sosai, duk gidan su ba kamar sa, komai na shi kowa ya sani, shi ne instagram shi ne Twitter, shi ne Facebook kullum ba shi da aiki sai posting ɗin hotunan shi komai yake yi sai duniya ta sani. Shi ya sa duk wani labarin da ke faruwa Hamma Sadam na da labarin shi da har hoton Baffa da Amma yana kafewa a Facebook Hamma Abdulrrahaman  ne ya yi masa faɗan akan ya daina posting ɗin hotunan su Baffa in zai saka na shi ya saka amma ban da na Ammah da Baffa shi ya sa ya daina amma na shi kam bai daina ba, a ko wani hali ya ke ciki kafin ya yi mgana posting ɗin shi ya bayyana halin da ya ke ciki. Kuma shi ba ma'abocin kiran waya ba ne amma za ku yini kuna chart bai damu ba. Shi ya sa ai Hamma Sadam kodayaushe yana online ne.

Sai da ta ɗan kwanta domin sai ta ji amai yana ta so mata, sannan kasala duk ya rufe ta sai wajen goma da wani abu ta iya rarrafawa ta fita. Doguwar riga ta saka na wata Atamfa sai ta yi amfani da bakin mayafi, ƙaramar jakarta ta ɗauko in da ATM ɗin ta na Banki yake tun da ba kuɗi a hannunta sai ta cire, sai da ta biya ta wani shago ta cire 5k sannan ta samu mai Kekenapep ta yi drop zuwa gida.

Bai sauke ta ko'ina ba sai ƙofar gidan su dake tsakiyar anguwan Zone 3. Ta sauka ta biya shi kuɗin shi sannan ta fara takawa ta tunkari baƙin get ɗin gidan na su, a baya ba baki ba ne da Hamma Lamiɗo ya sa aka gyara gidan ne a lokacin aka sauya get ɗin gabaɗaya. Ba ta tsaya ma ƙwanƙwasawa ba ta tura ta shiga sanin da ta yi get ɗin a buɗe yake, tuni Ammah ta ce a riƙa barin shi a buɗe saboda ba za ta iya wahalan kai da kawo tsakanin get da cikin gida ba shi ya sa a buɗe yake sai dai za a tura shi amma ba za a rufe ba tun da ba maigadi, tun tuni da man gidan Baffa ba mai gadi ballatana yanzu da rayuwa ta gangara.

In ka shiga gidan haraba za ka fara gani, daga yamma kuma akwai wani flat ɗakunan mazan gidan ne falo ne da ɗakuna huɗu kuma kowanne da banɗaki a ciki. Hamma Sadam ke zaune a ciki yanzu amma in su Hamma Mustapha suka zo su kan sauka a wajen ko baƙi daga Mubi dangin Ammah ko Baffa. Daga nan sai bangaren kudu akwai ɗan korido da za ka bi zuwa cikin gida wanda ke ɗauke da tsakar gida daga gefe kuma kitchen ne Babba sai yamma kuma ɗakin Baffa sai daga gabas kuma Ɗakin Ammah ne mai ɗauke da falo da ɗakuna huɗu a ciki. Sai gefen can kuma falo ne sai ɗaki ɗaya a ciki da banɗaki. Ɗakin da Mami ta yi rayuwarta kafin ta yi aure sannan anan Ammah kan sauki baƙin da za su fi sati kafin su tafi. Ɗakin a gyare ya ke, tsab kamar yadda bangaren Ammah ya ke shima kamar ɗakin wata Budurwa. Kusan duk shekara Hamma Lamiɗo sai ya sauya mata tsarin falo, Amma ta yi ta faɗa tana cewa ya bari ita ya gama biyan ta tunda ya kai ta Hajji sannan ya kai ta Umra amma ba ya ji ba ta ma sani sai dai ta ga Hamma Kabiru ya zo yana zuwa to kamar shi ne ya zo tun da duk wani abu da Hamma Lamiɗo zai yi ma Amma na suprising ɗin ta, to da Hamma Kabiru zai fara tattauna maganar sannan Hamma Abdullahi ya gabatar.

Tsakar gidan duk shimfiɗe yake da interlock. Tsakar gidan tas Amma ta share shi Ummu na ta sallama da ƙaramar muryanta ta ji shuru ta dai ta san Baffa baya nan tunda ba ta ga motar da ya ke hawa a haraba ba, ɗayan ta gani Benz ce tana lulluɓe da tamfol ya jima ma bai yi amfani da ita ba.

  Jikinta ba karfi shi ya sa ta kasa ɗaga murya ƙarisowa ta yi kofar falon Ammah ta ɗaga labulen tana leƙen cikin ɗakin.

"Ammah."

Ta faÉ—a a hankali tana zagaya idanuwanta a cikin É—akin amma shuru kamar ba kowa ashe ba ta sani ba Ammah na dakin Baffa.
Amma ta fito daga É—akin Baffa ita kuma Ummu Salma ta juyo sai suka yi ido huÉ—u.
Mamaki ya kama Amma cikin mamakin a muryanta ta ce.

" Ke kuma daga ina kamar an jeho ki?
Chapter 27 · 0% Book details