← Book details Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 92

Sashe 29

Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kukan ta ya ki tsayawa hawayenta suna zuba tana saka gefen hijabin jikinta tana gogewa.

"Me ke faruwa ne?

Baffa ya sake tambayan ta cikin kyakyawan lafazi.

"Baffa."

Kafin ya amsa ta cigaba da faÉ—in" Da ma, da ma ina da ciki ne."
Sai kawai Baffa ya washe baki yana faÉ—in" Ma sha Allah. Wannan ai abun murna ne ba na kuka ba Autan Baffa."
Kallon sa ta yi kafin ta ce" Baffa Habib ya ce ba ya son cikin fa"
Baffa ya zuru yana kallonta cikin mamaki kafin ya ce" Ban gane ba ya son cikin ba kamar ya ya?

Ummu-Salma ta sake fashe masa da kuka ƙasa-ƙasa ta kasa mgana.

"Kukan kuma dai Auta! In ba ki bar kukan nan ba ta ya ya za ki yi mini bayanin da zan fahimce ki?

Ya faÉ—a cikin damuwa saboda tunaninsa ya tsaya a dalilin kukan Ummu saboda mijinta Habib ne kuma ya shafi cikin jikin ta.

"Baffa kai kaÉ—ai ne za ka iya taimako na. Shi ya sa na zo wajen ka."

Kai ya gyaÉ—a mata kafin ya ce" In sha Allahu Auta sai dai abin da ya gagare ni, sai na bar ma Allah ya yi na shi ikon."

"Baffa ina son Habib."

"Na sani."

Baffa ya ba ta amsa a ɗokance domin ya ƙosa ya ji dalilin Habibu na cewa ba ya son ciki.

"Ba na so na rasa shi, ko na rasa aurena."

"In sha Allahu alheri ne zai biyo baya Ummu-Salma.".
Ya kira sunanta, suna mai darajan da ba ya iya kira saboda sunan mahaifiyar shi ce sai dai ya ce Ummu ko Autan Amma ko Autan Baffa amma tun da ta ji ya kira sunan ta tasan wasa kuma ya ƙare.

"In ba ki yi mini bayanin abin da ke faruwa ba, ai ba zan iya taimaka miki ba Auta"

Tana kuka tana shessheƙa ta labartama Baffa abin da ke faruwa amma ta ɓoye maganganun Habib a kan ta na cewa ba ya son ta auren sha'awa ya yi da ita sannan ta ɓoye hanyoyin da ya bi wajen mata barazanar ta zubar da cikin, ta dai  faɗa ma Baffa zaman su ya lalace domin Habib ya ce in har ba ta bi umarninsa ba, yanzu suka fara yar tsama a tsakanin su.

"Innalillahi wa'innna ilaihirraju'un"

Baffa ya dire salatinsa cikin mamaki yana kallon Ummu yadda take kuka kamar ran ta zai fita.

"Baffa don Allah ka kira Habib ka yi masa faÉ—a na san yana jin maganarka. Ka faÉ—a masa ina son cikin nan ba zan iya zubar da shi ba"

Ta sake faɗa cikin kuka Baffa ya yi shuru lamarin na ɗaure masa kai , ina aka taɓa haka? Ka yi ciki da kan ka sannan ka dawo ka ce ba ka so sai an zubar.

"Don Allah Baffa."

Ta sake roƙon shi, tausayi ta ba shi Ummu ta faɗa cikin kaddaran aure tun tana da ƙananun shekaru.
Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce" Abin da ban gane ba, me ya sa ba ya son ciki? Mene ne dalilin shi na cewa sai an zubar?

"Baffa wai ba yanzu ya tashi haihuwa ba."

"Ka ji wani shirmen banza. Da man shi ke da wannan tsarin ba na Ubangji ba ne? Habibu ya ba ni mamaki ina É—aukan sa mai hankali ashe kallon kitse na ke yi ma rogo ban sani ba?

Baffa ya faÉ—a cikin bayyana mamakinsa domin abin da ya yi, aikin jahilai ne mara sa ilimi da tarbiya.

"Tun yaushe ne kuka cikin wannan yanayin?

"An fi wata fa Baffa."

Ta faÉ—a tana cikin dashewar murya lokaci É—aya tana share hawayenta da gefen hijabin jikin ta.

"Me ya sa tun a lokacin ba ki zo kin faÉ—a mini ko Amman ku ba?

"Baffa na É—auka za mu iya warware matsalan ne da kan mu."

Baffa ya jinjina kai kafin ya ce" Ni lamarin ne ya É—aure mini kai. Ban taba zaton haka daga Habibu ba."

"Nima ban yi zato ba Baffa."

Ta faÉ—a cikin sanyin murya.

"Ki yi hakuri Auta. Amma ba ni ne zan yi ma Habib mgana ba. Ta in da aka hau ta nan za a sauka."

Ya faɗa yana kallon ta, kafin ta yi mgana ya rigata da cewa." maganar ki zubar da ciki ma bai taso ba tun da lafiyan ki lau, saboda haka waliyin shi wanda ya karɓan masa auran ki za a yi ma mgana su za su kira shi su yi masa magana."

"Baffa me ya sa kai ba za ka yi masa da kan ka ba?

Kai tsaye Baffa ya ce" Maganar ba ta ni kaÉ—ai ba ne, dole a sako waliyin shi a ciki "

Ummu ta yi shuru kanta na ƙasa Baffa bai fahimci abin da take tsoro ba. Kamar ya san abin da take tunani ya kalle ta yana faɗin" Ki kwantar da hankalin ki, Baffan ki Umaru zan yi ma waya shi zai kira waliyin na shi mu ji me zai ce."

"Baffa ina son Habib, ba na so a raba mu "

Ummu ta faÉ—a cikin karyewan sauti kamar za ta sake fashewa da kuka.

Baffa na shirin mgana su ka ji sallama, gaban Ummu ya amsa domin ta ji muryan Hamma Abdurrahaman.

"Ammah ko ba ta nan ne?

Ya faÉ—a daga tsakar gida, kafin kuma ya kariso É—akin Baffa tun da ya ga motarsa ya san yana gida, balle ma ya yi waya da Ammah da safe ta ce ya fita tare da Abdullahi amma ba za su daÉ—e ba.

  Jikin Ummu ya fara rawa lokacin da Hamma Abdulrrahaman ya shigo ɗakin Baffa da sallama ta kasa iya ɗago idanuwana ma ta kalle shi, fatan ta ka da Baffa ya sanar da shi abin da ke faruwa.

"Abdulrrahman lale sannu da zuwa."

Baffa ya faÉ—a cikin mirmishi, shima Hamma Abdulrrahaman É—in cikin fara'a ya amsa yana mai zama kusa da Baffa a saman darduman da ya ke zaune sai a lokacin ya kula da Ummu.

"Ke lafiya?

Ya faÉ—a yana kallonta kafin ya juya yana kallon Baffa.

"Baffa me ke faruwa ne?

Saboda irin zaman da ta yi ne ya sa ya ji kamar jikinsa bai ba shi ba.
"Lafiya lau. Ya aiki da wajen iyalan naka?
Baffa ya faÉ—a yana mirmishi, ya amsa da duk suna lafiya yana sake nazarin Ummu da ke dukar da kai kamar munafuka.

"Na zo nan kusa ne kan wata sharia da na kai ne a yanzu."

"Allah ya ba ka nasara."

Ya amsa da Amin.

"Ke jira kike ni na fara gaishe ki?

Hamma Abdurrahaman ya fada a É—an zafafe.
Baffa ya yi saurin tare shi da faɗin". To sarkin ƙorafi yaushe mu ka gama gaisawar ballanta ma ta samu damar gaishe ka?

"Baffa kar ka kare mata, mintina na nawa da shigowa É—akin nan?

"A yi haƙuri."

Baffa ya faÉ—a yana É—an mirmishi.

"Hamma ina yini."

Ummu ta faÉ—a muryanta na rawa, lafiya lau ya amsa sannan yana sake kallon ta.

"Kin yi ciwo ne?

Ya faÉ—a daidai da ta tashi za ta bar É—akin na Baffa.
Sai ta juyo tana kallon shi duk da ya É—an kwana biyu bai gan ta amma ta lalace da yawa.

"Ta yi zazzaɓi kwana biyu."

Baffa ya amsa mishi, kallon shi ya yi kafin ya sake kallonta ya ce" Baffa wannan ya wuce zazzaɓi, idanuwanta da fuskarta sun nuna tana cikin damuwa."
Baffa na dariya ya ce" To lauya."
Shima sai da ya yi dariyan da haka Ummu ta so ta sulale Hamma Abdulrrhaman ya tsare ta da cewa ta dawo ta zauna  jikinta na rawa gabanta na faɗi ta koma ta zauna a in da ta tashi.

"Ke kina da wata damuwa ne?

Ya faɗa yana mai tsare ta da ido, har yana sauke jakar hannunsa a ƙasa, sanye yake da suit ya tsuke, da man Hamma Abdulrrahaman in ya ta saka ka gaba ba ka iya ƙwatan kan ka, aikin lauyancin har a gida yana yi, in yafara jefa maka uban tambayoyi sai ka fara zufa ma ba ka sani ba.

"Ko mijin na ki ne ke ba ki wahala! Kin rame sannan fuskarki ba ta cikin walwala."

Ya sake tambaya kanta na kasa ta kasa mgana sai rawan hannu take fama da shi duk yana lura da ita.
Baffa na so ya yi mgana ya katse shi da cewa" Baffa da wani abu ko! Wani abu na damun yarinyar nan kamar mai depression kalli yadda hannayenta ke rawa?

Baffa na dariya ya ce" Kai ne ka saka ta rawan hannu. Daga zuwan ka, ka fara mata tambayoyi sai ka ce a kotu."

Baffa na so ya ɗan shashantar da maganar amma Hamma ya ƙi yarda saboda ya fahimci akwai wani abu.

"Baffa wani abu na faruwa, kai ma fuskar ka ta bayyana damuwa."

Baffa ya kasa mgana, da gaske ne tun da Ummu ta faÉ—a masa abin da ke faruwa ya rasa abin da ke yi masa daÉ—i.

"Ya kamata na sani Baffa?

Ya tambayana yana kallon shi, Ummu kuma Baffa take kallo tana girgiza masa kai, karaf ko ya ganta da sauri ta mai da kanta ƙasa tana jin hancin jikinta na ƙalawa saboda tsoro.

"Baffa me ke faruwa?

Ya faɗa cikin  muryan da ba wasa a cikin ta.
Baffa ya yi gyaran murya sannan ya shiga sanar da shi abin da Ummu ta gama faÉ—a masa.

"Yanzu nan da ka gan mu, nima ta gama faÉ—a mini abin da ke faruwa kenan."

Hamma Abdulrrahaman ya yi shuru kafin ya ce.
" No wonder na ga yarinyar nan duk ta lalace, ba ma za ta rasa depression ba."
Baffa ya yi shuru bai yi mgana Hamma Abdulrahaman ya kalli Ummu ya fara faÉ—in" Shi don uban shi bai shirya haihuwa ba yanzu ya zo ya aure ki? Ya san bai shirya haihuwa ba ya yi aure? Ji wani rashi tunani don uban shi ba a haihuwa shi aka haife shi?

Ya ƙarishe faɗa cikin ɗaga murya jikin Ummu ya fara rawa kafin ma ta samu damar magana Ammah ta faɗo ɗakin tana faɗin" Waye kuma ba ya son haihuwa?
Ta yi turus ganin Ummu zaune tana rawan jiki ga Hamma Abdulrrahaman na ta bala'i Baffa na zaune a gefe bai yi mgana ba.
Chapter 29 · 0% Book details