Sashe 35
Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"To yanzu dai ba ni dashi ku fara shan wannan sai na fita na siyo muku."
Ummu ta faɗa cikin yaƙe da dariya.
"Haba. Ƙyale su Auta rigima ce"
"Adda ki bari na fita ko megadi na ba ma saƙo ya siya musu."
Hamma Jibo ne ya saka baki ya ce Aa, yaran ma ya yi musu jan ido ya ce su ɗau ruwa su sha in ba za su sha ba su bar shi, dole suka ɗauka suka sha kaɗan Hamma ma ya sha shi da Nauwara, miƙewa ta yi tana faɗin me za su ci ta dafa musu?
Da sauri Hamma Jibo ya ce" Sai da suka ci abinci muka fito fa, Auta ki yi zaman ki kawai."
"Dad ni egg zan ci "
Ammi ta faÉ—a kamar za ta yi kuka wannan karon Nauwara ce ta balla mata harara kafin ta ce" Ba shi kike taso kika bari a gidan Ammah ba? Zan zane ki fa"
Ta faɗa mata cikin harshen turanci lokaci ɗaya tana hararanta Ummu duk ta zama wata iri sai yaƙe take yi amma da ka ganta tana cikin damuwa.
"Auta taho nan ki zauna kusa da ni."
Ya faɗa mata yana mai nuna mata kusa dashi jikinta a sanyaye ta zo ta zauna kusa da shi kanta a ƙasa.
"Auta me ke faruwa ne?
Ya tambaya yana kallon ta, sai ta ɗago tana kallon shi cikin yaƙe kafin ta ce" Me ka gani Hamma? Lafiya ta lau na yi ta zazzaɓi kwana biyu ne "
"Haka Ammah ta ce sannu?
Nauwara ta faɗa tana kallon ta, Amma ta faɗa mata Ummu na da ciki shi ke ɗan ba ta wahala wataƙila shi ya sa duk ta rame.
Hamma Jibo ya yi shuru yana kallonta ya kasa magana.
"Hamma ba fa komai Allah."
Ummu ta sake faÉ—a tana faÉ—aÉ—a mirmishinta wanda ba ta san bai boye damuwarta ba.
"Megidan na ki ba shi da aiki ne yanzu?
Cikin mamaki ta ce" Yana aiki me ka gani Hamma?
"Na ga kin siyo abinci Auta."
Ya faɗa kai tsaye yana kallon ta cikin nazarin ta. Sai ta kasa mgana, kanta na ƙasa amma hawaye take yi ganin haka ya sa Hamma Jibo ya ce Nauwara ta kwashi yaran su shiga ciki zai yi magana da Ummu Salma. Da sauri ta bi umarnin sa ta kwashi yaran suka shiga bedroom ɗin Ummu suka zauna.
"Auta ki faɗa mini abin da ke faruwa ni fa ɗan'uwan ki ne, zan yi komai domin ganin kin yi farinciki."
Kalamansa sake sake ruguza rauninta ta sake fashe masa da kuka, kanta ya dafa yana ɗan bubbugawa alamun lallashi, sai da ta yi kukan ta ya ishe ta sannan ta warware masa komai amma shima ta ɓoye masa abubuwa da yawa kamar yadda ta ɓoye ma su Baffa, sai dai ta bayyana masa ita ke ciyar da kanta tunda har ya gannin ma idanuwansa ƙarya ba na ta ba ne. Har da haɗa sun da aka yi waje ɗaya kamar an samu masalaha duk ta sanar da shi.
Hamma jibo ya ji wani abu ya kama shi na tausayin ƙanwarsa da jin haushin Habib cikin faɗa ya ce" Kuma kike zaune yunwa za ta kashe ki Ummu ga su Baffa a kusa?
Tana kuka ta ce" Hamma ina son aurena sannan ina son iyayena ba na so na saka su cikin damuwa."
"Ai cutar da kanki da kike yi shi ne zai saka su a damuwa Auta."
Ya faÉ—a yana kallon ta, tana hawaye ta ce" Ka yi hakuri Hamma."
Kanta ya jawo a saman kafaÉ—anta yana lallashin ta.
"Ya nuna ba ya jin maganar na gaba da shi tunda an masa mgana ya nuna ya ji amma bai ji ba, sakarai ne shi? Ta ina aka taɓa haka? Kawai sai ya ce sai kin zubar da ciki saboda ba shi da tunani?
Ya cigaba da faɗa Ummu na ta kuka tana faɗin Hamma ka yi haƙuri.
"Ya zama dole su Baffa su sake sanin halin da ake ciki."
Ya faɗa yana sakin ta lokaci ɗaya yana ƙokarin ɗauko wayarsa.
"In ba haka ba wata rana zaki mutu ba a sani ba, kin ga yadda kika rame? Kuma kina da juna biyu in wani abu ya same ki fa?
Da sauri Ummu ta sauko ƙasa ta duƙa tana faɗin" Don Allah Hamma ka yi haƙuri, kar ka sanar ma da su Baffa ba na so hankulansu ya sake tashi."
Tsayawa ya yi yana kallon ta cikin mamakin ta.
"Hamma ina son na tsira da aurena ba abin da ya rage mini a yanzu. Don Allah kar ka bari su Baffa su san abin da ke faruwa."
Ya rasa yadda zai yi da ita ganin tana ta kuka shi ya sa sai ya mayar da wayar shi aljihu yana faÉ—in" To na ji ya isa."
Ya saka hannu ya ɗago ta yana share mata hawaye miƙewa ya yi yana ce mata bari ya je ya dawo.
"Hamma."
"Zan dawo yanzu."
Yana gama faÉ—in haka ya fice, nan ta zauna tana kuka Nauwara ta fito ta same ta, tana kuka ba ta tambayi ba'asi ba ta zauna tana ta lallashinta Ammi ta yi barci Saudat ne idanuwanta biyu da ya ke akwai wutar nepa sai Nauwara ta kunna mata cartoon zaman shuru suka yi Ummu ta daina kukan amma ba ta daina ajiyar zuciya ba.
Ba daɗewa sai ga Hamma Jibo ya dawo Allah sarki ɗan'uwa. Kayan abinci ne ya siyo mata mai yawa kuma shi ya dinga ɗauka yana shiga mata da shi cikin store, Ummu ta yi hawaye ta yi kuka tana yi masa godiya ba abin da bai siya mata ba har kayan tea sannan ya tura mata 100k ya ce ta riƙe a hannunta. Ba su daɗe ba ya ce su tashi su tafi da alƙawarin zai faɗa ma Baffa halin da take ciki amma ba zai bari a kashe mata aure ba, sai dai za a sake kiran Habibu a ji dalilin shi na yi mata horan yunwa.
*Janafty*
*FARGAR JAJI.*
*Wattpad:JamilaUmar315*
*Arewabooks:JamilaUmarJanafty*
"To Hajiya Hauwa'u Inuwa Aminu (Anty Hairi) with love and gratitude"
https://chat.whatsapp.com/LsC7Rjmei7J6Hd11e95nNS?mode=gi_t
*09*
Suna tafe a mota za su koma gidan Ammah, Nauwara ta fahimci mijinta na cikin damuwa tun fitowan su daga gidan Ummu fuskar shi ta nuna damuwar da yake ciki, ta fahimci akwai matsala amma ba ta so ta yi shisshigi tunda bai sanar da ita komai ba. Ga kukan da Ummu Salma ta yi ta yi, sannan ga kayan abincin da ya siya mata shima wani alama ne da cewa wani abu na faruwa.
Hannunta ta ɗora saman hannunsa dake saman sitiyari, ta riƙe ta ɗan matsa da ya sa ya kalleta lokaci ɗaya yana ma yar da hankalin shi kan tukinsa su Saudat na baya suna ta wasa ba su ma fahimci abin da ke faruwa a gaban motan ba.
"Ina fatan ba wata matsala ba ne game da Auta ba ko?
Nauwara ta faÉ—a cikin kwantar da kai tare da kulawa ga mijinta Jibril Hadi Baba.
Kai ya gyaÉ—a mata kafin ya sauke ajiyar zuciya.
"In sha Allahu komai zai yi dai dai."
"Allah ya sa. In sha Allahu."
Ta amsa masa cikin jinjina masa kai lokaci ɗaya tana yi masa mirmishi, shima sai ya mayar mata da martanin mirmishin nata, amma gabaɗaya baya cikin natsuwarsa halin da ya iske Ummu Salma a ciki ya gama ta yar masa da hankali shi ya sa suna komawa gida sun ci sa'a Baffa ya dawo lokacin ɗakinsa kawai ya shiga Nauwara kuma da yara suka ya da zango a falon Ammah in da suka iske su Hassan da Hussaini na ta wassani isma'il ne ma ya yi barci.
Baffa ya razana da labarin da Hamma Jibo ya sanar da shi, ya yi masa zuru yana kallon sa cikin É—imuwa da mamakin labarin da ya ba shi, wai Ummu na yini da yunwa saboda ba abinci ya tuna yadda store É—in su yake rumbatsa da kayan abinci wani ba ya karewa ake sake kawo wasu, Baffa ba zai iya kirga shekarun da ya É—auka bai siya hatsi ba, haihuwa ce ta yi masa rana har da ma waÉ—anda bai haifa ba suna yi masa, amma a ce É—iyarsa na aure a garin nan amma tana kwana da yunwa saboda son rai da mugunta da zalunci irin na Habibu.
"Innalillahi wa'inna alaihirraju'un."
Baffa ya samu kan shi da furtawa saboda hankalin shi ya tashi matuƙa.
"Baffa wallahi hankalina ya tashi da yadda na ga Auta. Ba zan ɓoye maka ba sam ban ji daɗin ganin ta ba, tunda na baro gidan ta na ke cikin damuwa. Baffa Auta ta sauya tana neman mutuwa a cikin gidan nan ba wanda ya sani."
Ya karishe faÉ—a kamar ya yi kuka, da man shi yana da tausayi da rauni.
"Baffa ina tambayanta sai kawai ta fashe mini kuka, Baffa ka ga yadda Auta ke kuka, kamar ran ta zai fita amma a haka roƙona take yi kar na faɗa muku wai ba ta so hankalin ku ya tashi ni kuma na ce sai na sanar daku domin dole ne a yi wani abu tun kafin Auta ta samu wata matsalan a dawo ana wallahi tallahi Baffa."
Ya dire maaganarsa yana shafa naman goshin sa cikin damuwa.
"Gwara da ba ka rufe ni ba Jibo. Ai wannan ba mganar da za a yi shuru ba ne. Tunda tun farko mun sako waliyin shi a ciki nan aka kira shi ya ce ya bar mganar in sha Allahu ashe yaudaran mu ya yi, ya koma ya sauya wani tsarin to Jibo horon yunwa fa? Kashe mana Auta yake son yi ko mene ne manufarsa?
Baffa ya faÉ—a yana kallon Hamma Jibo cikin damuwa muraranta da ya bayyana a saman fuskar shi.
"Mene ne mafita Baffa?