← Book details Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 92

Sashe 90

Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baɗɗo da su Ummin ikki da matan su Hamma Abdullahi duk sun zo Kaduna taron suna Umma Balki da Umma A'i ma sun zo Umma Balki sai da aka yi arba'in ta koma Mubi ita ta yi ma Ummun wankan jego mai tsada, Baffa ma ya tako har Kaduna ya ga Hanna amma ban da Ammah sai dai ta gan ta a hoto. Kaf yayyenta ba wanda bai kira ta ba, sannan sun tako tare da iyalansa ita da Hanan sun ga gata sosai, kuma ga shi yarinyar ta taso da ƙiriniya kowa na son ta Daddy ko kamar shi ne mahaifinta yadda in dai yana gida tana tare da shi haka ma Mami shi ya sa su ta fara kiran sunayensu bayan ta fara iya magana sai Faruƙu da Ilam wato Islam ko Mahma sai daga baya ta fara iya faɗa, gata na duniya Hanan ta na gani kuma tana kan gani komai na rayuwa ba abinda suka nema suka rasa Daddy ne da Mami ke tsaye kanta ita da yarta.

Har kuma gobe Habib bai nemeta ba, itama ta manta da wanzuwarsa a rayuwanta ba za ta ce ta manta gabaɗaya ba, domin ba zai mantu ba, amma ta kan daɗe ba ta tuna ba  in ta tuna ita kaɗai ta yi ta kuka, Rayuwarta ta ya sauya a Kaduna Mami macece mai kirki da yaƙana kaunar da take yi mata ko rabin shi ba ta nuna ma Lamiɗo, ba ta zuwa ko'ina tana gida daga baya ne ma ta fara bin Mami zamfara in za ta je ganin Dangin Daddy, bikin Baraka ne farko, amma ba ta bin ta Jimeta itama ba ta matsa mata  tunda ga waya tana mgana da kowa daga gida.

Tun kafin ta yaye Hannan Hamma Kabiru ya matsa wai sai ta koma makaranta ita kuma har abada ba ta son karatu shi ya sa a wannan karon ma ta turje, Daddy da Mami suka goya mata baya dole suka ƙyaleta, da ta watsar da girke-girkenta sai dai kawai tana yi a gida, tunda ta hana Mami ɗaukan mai girki tace ita za ta dinga yi, Mami ce ta matsa mata ta dawo dashi, ta kuma ce za ta neme mata catering school ko wani program haka ta shiga domin ta sake ƙwarewa haka ko aka yi Mami ta nema mata ta shiga yanzu haka a Kaduna tana da certifacate sama da huɗu na catering da program kan abin da ya shafi girke-girke kuma da shawaran Mami da na Baɗɗo tare da na Hamma Saddam tare da Hamma Abdulrahim ta ƙirkiri sabon account da sabon suna lokaci ɗaya kawai tunanin yin amfani da sunan Hanan ya zo mata. Hanan Baba Jimeta sai ta ke amfani da Hanan B Jimeta.

Ta fara video tana É—orawa a youtube na girke-girke duka-duka wattani shidda ne da fara abin amma har ta É—an fara tara mabiya da farko har ta sare da karfin gwiwansu ta cigaba a hankali ta buÉ—e sabbin accounts a Tiktok da instagram.

Daddy kuma ya gwangwajeta da sabuwar waya Mami kuma ta siya mata ringlight kayan girki da komai akwai su a kayattacen kitchen ɗin Mami, wanda wasu ma saboda kyan kitchen ɗin ya sa suke kallon Videos ɗin Hanna Delicouis ba a ganin fuskarta in ta ɗora videos ɗon sai dai a hangi rigarta daga ƙasa haka sai maganarta, ga shi yanzu wasa wasa videos ɗinta suna ta tafiya a kafafem sada zumumta mata da dama suna ƙaruwa da ita saboda ta iya koyar da komai a saukaƙe.

A dalilin Mami da Daddy ta je Umra sau ɗaya ta je Niger sun je Ghana, a Nigeria kuma sun je Abuja da Kano. Daddy  na da gidaje a Kano da Abuja haka kawai in yara sun samu hutun makaranta zai kwashe su suje su huta na kwanaki, idanuwanta sun buɗe tunda suna yawan fita yawon buɗe ido, babu in da ba ta sani a garin Kaduna ba.

Wani lokacin ma har cikin makaranta ta sha raka Mami, zuwanta Jimeta wannan karon sai da ta zama abar kallo, BaÉ—É—o ita kanta ta zo Kaduna sau biyu sai da ta yi mamakin ganinta.
Ta yi kiɓa ta sake fari ta zama wata babbar mace lalle kwanciyar hankali ma ni'ima ne.

"Auta ke ce kika zama giwa haka? Ai ke da uwar taki ma sai a rasa uwar da yar."
Ammah ta faɗa domin in suka jera da Mami kamar yaya da ƙanwa a jami'ar da Mami ke koyarwa da suka fara ganin Ummu sun ɗauka kanwarta ce, sai da ta ce ɗiyar yayanta ne suka saki baki, Baffa kam bakinsa yaƙi rufuwa.

"Auta Auta an zama uwa manyan mata."
Haka yake faÉ—a, Hanan ko kiyuwa ta fara yi musu farkon zuwan su, sai da Ammah ta yi mata jan ido sannan ta shiga taitayinta ta yi ta kuka tana rigima Baffa me mai lallashi ya ce shi kan ai ya ga mata, dole ya yi biyayya Ammah ko ya ce kishi take yi ta ga wacce ta fi ta jan fata.

Ammah cikin gatsale ta ce bai ko yi dace ba ana ta dariya.
Hanan kuma ba ta iya kiran sunan Baffa ba sai dai ta ce Bacca.
Ammah ta yi ta masifa tana faɗin ke ba sunan mijina Bacca ba sunan shi Baffa in ba ki iya faɗa ba ki yi shuru ki bar ɓata masa suna, sai suka koma suna ba ma mutane dariya.

Kowa ya zo ya ga Ummu sai ya yi magana haka da ta je gidan su BaÉ—É—o su kaltume suna ta mamakin sauyawarta ta zama wata mai tsada da ita.
Ummin ikki sai da ta ce ina surukin da take jira, Ummu ta yi dariya ba ta ce komai ba, domin ita a zuciyanta ma ba ta son duk wani namiji in dai da aure ne, aure ya fita kanta gabaÉ—aya. Yadda ta tsani Habib haka ta tsani kalmar aure, ta je Mubi saboda an yi rashi É—iyar Umma Salmatu ce ta rasu wajen haihuwa, nan ma suka yo ma ta caa kan maganar aure har da su Baffa Umaru shi ya sa ta baro musu garin ma gabaÉ—aya.

Ita yanzu me za ta sake tsinta a aure da za ta sake yi? Ai tana jin babu sauran wani abun da ba ta gani ba, yanzu abin da ke gabanta kawai ba ma Hanan tarbiya amma a zuciyanta ta yi kudiri ita da aure har gaban abada. Tana ganin ta rasa komai, ba ta da wani sauran wani abu da rage mata da za ta sake takama da shi, Habib ya gama da komai kafin ya cire ta daga rayuwarsa.

***

Sai bayan la'asar ta fito daga cikin ɗakin ta a baya a ɗaki ɗaya suke kwana da tare da Islam amma tun bayan da ta haihu Mami ta gyara mata ɗakinta ita kaɗai, balle ma yanzu da Islam an fara zama yan mata shekarunta sha huɗu, Faruƙu ne goma. Kicthen ta shiga ta duba abin da za ta sarrafa na dare yau ko abincin rana ba su yi ba ita da Basira tea suka sha  Hamisu kuma da kuɗinshi ba zai  jira su ba, Sunusi kuma ya yi aure matarsa na aiko masa da abinci, Mami ma tana maganar za a gyara musu bangaren waje kawai ta dawo kusa da shi.

Alele kawai ya faɗo mata a rai sai ta ce bari ta yi musu mai nama a ciki sai ta yi musu miyar source ɗin ƙwai store ta shiga ta ɗobe waken suna da ƙaramin turmi ta ɗan saɓa shi ta wanke ta niƙa shi a blander wani katon friza ne a kitchen din cike da kayan amfani, nau'ikan nama ba wanda babu sai dai kawai a ɗauka in za a yi amfani da shi.
Tana kitchen ɗin tana aiki Mami ta shigo gidan ba ta sani ba sai da ta leƙo kitchen ɗin ta yi mgana.

"Ya Ummu sannu da aiki."
Haka Mami da Daddy ke kiranta hatta Hanan ta kama wani lokacin haka take kiranta.

"Laa Mami yaushe kika dawo?
Ta faɗa tana kashe blander ɗin tunda ta gama niƙa waken.
"Yanzu na shigo me aka yi mana ne na fara jin ƙamshi?
Mami ta faÉ—a tana É—an shigowa kitchen É—in kaÉ—an.

"Mami alele mai nama zan yi mana ko kina son wani abu ne?

"Aa ki yi mana yaushe rabo na da alala, amma ki yi mana na manja."

"To Mami."

"Ina Hanan yar rigima? Ya zazzaɓin ya sauka?
Ta tambaya tana buÉ—e fridge ta É—auko rowan gora Ummu kuma ta É—auko mata kofin tangaran a wani dirowan kitchen É—in ta mika mata ta tsiyaya ruwa.

"Ta ji sauƙi ta na can bayan Basira."

"Ban gan su a falo ba."

Mami ta faÉ—a bayan ta gama shan ruwan.
"Ƙila suna bangaren Basira."
"To bari na je na watsa ruwa. Kafafuwana sun gaji Ya Ummu."
"Mami za a yi tausa anjuma."
"Yauwa yar albarka."
Mami ta faÉ—a tana dariya sannan ta fita, Ummu ta amsa da Amin tana É—an mirmishi har ta fita sai kuma ta dawo tana faÉ—in" Baffa ya kira ki kuwa?
Ta tambaya tana tsaye a ƙofar kitchen.
"A'a Mami."
Sai ta kalleta ganin ta yi shuru.
"Me ya faru Mami?
Ta tambaya a É—an tsume.

"Aa ba komai, kawai na tambaya ne."
Tana gama faÉ—in haka ta wuce tana faÉ—ib" Na shiga ciki."
Mamaki ya kamata, me ya faru ne? Mami ba ta saba mata irin waɗanan tambayoyin ba, suna waya da Baffa kusan ko da yaushe yana kiranta amma itama tana yawan kiran shi saboda yadda suke daɗewa suna hira, saɓanin Ammah da suna gaisawa da tambayan yara hiransu take katsewa. Sai ba ta saka tunanin komai ba, sai ta ɗauka ko Baffa ne ya kira ta yau shi ya sa take tambaya kanta tsaye ta cigaba da aikinta tana sanye da riga da wando kalan ruwan ƙasa yan pakistan Mami ce ta siya mata su a Saudiya ta ce ma zaman gida ne.

Mami kuma na shiga bedroom É—inta dake saman bene ta watsa jakanta saman gado lokaci É—aya ta ciro wayarta ta kira wata lamba, sai da ta katse ba a É—aga ba ta sake kira nan ma shuru.

"Kai."
Chapter 90 · 0% Book details