Sashe 8
Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ba sa iya ɓoye ma juna komai, tun suna yara tare suka taso, duk da Ummu ta ɗan girme ma Baɗɗon da shekara ɗaya, amma yadda suka taso suka ga aminci mai ƙarfi a tsakanin iyayensu suma haka suka samar da na su misalin aminci a tsakanin su, duk da ita Ummu tana da wata ƙawar da suke kusanci sosai Shamsiya(Bestie) ita makaranta ce ta haɗa su tun da ga primary har gama babban sakandiri, a yayin da ita Baɗɗo ba ta da wata ƙawa Aminiya kamar Ummu Salma
Tare suka yi girkin dare, don Ummu ta hana Baɗɗo tafiya da ta matsa ma sai ta kira Habib a waya ta kai masa ƙaran ta shi kuma ya ce a ba ma Baɗɗo wayar ya yi mata magana da cewa ta tsaya har ya dawo su ci abiinci sai ya ma yar da ita gida tun da itama duk suna cikin garin Jimeta ne a wata anguwa mai suna Nasarawo.
Baɗɗo ba ta da yadda za ta yi dole ta zauna da man in dai ta zo gidan Habib da Ummu ke ma yar da ita gida wata rana kuma shi kaɗai, ta daɗe tana yi ma Ummu murna da farincikin samun gwarzo irin Habib, ta daɗe tana sha'awar irama ta yi aure ta tafiyar da mijinta da gidanta kamar da Ummu ke tafiyar da na ta gidan abin sha'awa abin birgewa, sannan abin da ke ƙara sa take ganin girman Habib girmama duk wani ahalin Ummu, son duk wanda take so shi ya sa ita da Shamsiya Habib ke yi musu hidima da jikinsa da aljihunsa saboda kawai sune makusantan Ummu na sosai ɗin da ba wanda ya san tsakanin su.
Bayan sun gama girkin Baɗɗo ta gyara gidan tas ta goge ta saka turaren wuta yana tashin ƙamshi, Ummu ta matsa mata sai da ta yi wanka kaya ma ta dage sai ta saka nata taƙi, a cewarta na ta ba su yi datti ba tun da ta ƙwabe su da za su fara girki ta saka wata doguwar rigar Ummu sauƙaƙƙa ta zaman gida. Bayan sun yi sallar mangriba ne Ummu ta yi wanka ta ci ado suka zauna a falo suna kallo suna hira a cikin hiran ne Baɗɗo ke faɗa ma Ummu ranar litini su Ummin ikki da Amma za su wuce Daura.
"Au da man tare da Ummin ikki Ammah za ta tafi?
Ummu ta tambaya BaÉ—É—o ta gyaÉ—a kai mata kafin ta ce" Ke ma ai kin sani, suna nan suna shiri."
BaÉ—É—o da Ummu suka kwashe da dariya har suna tafawa.
"To su Daura za su je ko Abuja? Tun da na ga duka events É—in na su a Abuja za su yi É—aurin aure ne kawai a garin Daura fa."
Ummu ta tambaya tana kallon Baɗɗo da dariya a bakin ta.
"To ni ina zan sani, kullum dai dai sai Ammah ta kira Ummi a shige ciki a daÉ—e ana tattaunawa."
A tare ma wannan karon suka kwashe da dariya kafin Ummu ta ce" Wa ya ga su Ammah a tawagan uwar Amarya."
"Sai ki iya ganin su."
Suka sake yin dariya nan Ummu ta fara ba ma BaÉ—É—o labarin karon su da Amma zuwanta gida na karshe.
"Sisna haka fa Ammah ta fitike ta in da take shiga ba ta nan take fita ba wai kawai saboda tana labarin bikin Daura ban tanka ba, shike nan fa ta fara faɗa daga ƙarshe ta ce na bar mata gida tun da ba gidana ba ne, ki ji ƙarfin hali."
Ummu ta ƙarishe faɗa tana, riƙe haba da sigar mamaki.
"Amma hoo. Ammah drama Queen."
BaÉ—É—o ta faÉ—a tana dariya.
"Ba wanda Amma ta ƙyale. Hamma Lamiɗo ne kawai ban taɓa ganin ta yi ma faɗa ba."
"Ke ko wannan ai É—an gaban goshi ne."
Ummu ta taɓe baki kafin ta ce" Ai ni tun da gabda bikina ya taɓa kiran wayar Amma na ɗauka ya ji ni ce, ina fa mgana ya yi banza da ni daga karshe sai ce mini ya yi wai shi ba ya mgana da mara son makaranta .
Ummu ta karishe faɗa hawaye na cika ƙwarmin idanuwanta in ta tuna da cin mutumcin da Hamma Lamiɗo ya yi mata sai ta yi hawaye.
"To ke me ya kai ki É—aga kiran sa? Mutumin da sai ya gan ka ya nuna bai san ka ba, ka gaishe shi yana ji sai ya ga dama zai amsa sai ka ce jinin sarauta hauka ne."
Baɗɗo ta faɗa cikin jin takaici domin itama ya taɓa yi mata wulakanci zuwan farko da ya kawo ma Amma matarsa, sai ya kawo ta wajen Ummin ikki, ta shigo falon tana gaishe shi ya yi kamar bai ji ba sai da Ummi ta ce Baɗɗo na gaishe ka sannan hankalinsa na kan wayarsa ya amsa a ɗakune kamar mai ciwon baki da " lafiya" Wannan abin ya yi mata ciwo tana uwar ɗakin Ummin ta ji yana cewa bai gane ta ba lamarin Hamma Lamiɗo bayan jinin sarauta har da wulakanci da ɗagawa ma a cikin shi.
"Ban san shi ba ne, saboda lambar ba suna, kuma ni na san sai dare ko asuba yake kiran Amma, in da na san shi ne ai ba zan ɗauka ba, ni da lokacin da maganar aurena da Habib ya taso ya kira Amma a waya yana faɗa wai ya za su biye mini na ƙi karatu na ce aure zan yi ina yarinya da ni ban san komai ba? Da shi da Hamma Kabiru da yake shima irin halin su ɗaya ya zo yana ma Baffa kumfar bakin cewa na yi ƙankanta da aure."
BaÉ—É—o ta kalli Ummu ganin har ta fara hawaye.
"Ni yaushe na ce aure na ke so? Ni dai ba na ce ba ne a ƙyale ni bana son cigaba da karatu abin da na san kawai na ce kenan."
Sai kawai Ummu ta fashe kuka BaÉ—É—o da ya ke ta san hali sai ta dafa kafaÉ—anta tana faÉ—in" To ke ma ban da abin ki duk wanda ya ji ba ki son karatu ai zai fassara ki da cewa aure kike so ne SisNa"
KafaÉ—an BaÉ—É—o ta kai ma duka ita kuma sai ta goje tana dariya .
"In kowa bai fahimci halin da na ke ciki ai ke na san za ki fahimce ni. Karatu na daga cikin abin da ke wahalar da ni, tun da ya ke ba ni wahala na yi kuma iya yina na riƙa ganewa na kasa ba gwara na hakura ba, domin ina tsoron na shiga jami'a domin faranta ma su Hamma Kabiru rai kafin na yi nisa a kore ni."
BaÉ—É—o ta kwashe da dariya Ummi na ta ya ta da guntun hawayenta.
"Hamma Saddam ya ce sai ya ga wanda zai aure ni ina low class ban ji turanci mai zurfi, sai ko ga shi ya sha mamaki. Ya ga Noori na, wanda kyau dai na fuska da zati bai isa ya nuna masa ba."
"Bai isa ba."
BaÉ—É—o ta faÉ—a tana dariya.
"Bestie ta ce tana roƙon Allah ya ba ta miji kamar Habib. Ya so ta kamar yadda yake sona."
"Amin."
BaÉ—É—o ta amsa kafin ta ce" Ai Habib miji goma ne, kin gama dacewa SisNa muma Allah ya sa mu da ce irin na ki."
"In sha Allahu za ku samu fiye da wanda ya fi Habib ma."
"Allah ya sa hakan."
BaÉ—É—o ta sake amsa mata, sannan suka cigaba da hiran su, ana haka sai ga Shamsiya ta kira wayar Ummu sai ta saka ta speaker suna fara mgana BaÉ—É—o ta kira sunanta.
"Bestien SisNa."
Tana jin haka ta san BaÉ—É—o ce domin haka take kiran ta, ita kuma sai ta ce mata Sisna Bestie na.
"Wayau kika yi mini Sisna bestie na? Kika taho duba Bestie ba tare da ni ba?
Shamsiya ta faɗa daga cikin wayar, Baɗɗo ta ce mata itama fa ta kwana biyu ban leƙo ta ba sai yau fa kin san saboda makaranta mun kusa fara jarabawa.
Shamsiya ta ce suma sun kusa farawa shi ya sa amfani da wayar ma sai a hankali.
Shamsiya irin yaran nan ne masu ƙoƙari da nacin karatu, kaf gidansu yan boko ne sai kin gama jami'a ko kin kusa gamawa kike da damar fidda mijin aure, ko ba ka son karatu su a gidan su wajibi ne sun ɗauki boko kamar wani zunubi ne in ba ka yi ba. Ita kanta Shamsiyar ɗaliba ce a jami'ar Modibbo Adama University Yola a garin girai can ta ke zama a hostel sai sun samu hutu take zuwa ganin gida.
Sun daÉ—e suna waya suna ta hira, har sai da dawowar Habib ya katse su. BaÉ—É—o sai da ta kauda idanuwanta, saboda rumgumar da ta gudana tsakanin Habib da Ummu in da a ce ana sabo da tuni ta saba da ganin haka tun bayan auran Ummun da Habib.
"BaÉ—É—on mu."
Habib ya faÉ—a yana yi mata murmishi bayan sun gama oyoyon shi da Ummu.
"Noorin mu."
Dariya ya yi, domin Habib akwai harka ko yau kuka taɓa haɗuwa da shi sai ka ji kamar ka yi shekara da sanin shi, yana da magana da harka sosai.
"Na sa ka ki jirana ko?
Bari na yi wanka mu ci abinci sai mu je mu kai BaÉ—É—on mu gida ko Baby?
Ummu ta gyaÉ—a masa kanta lokaci É—aya tana mai saukar da kanta a saman kafaÉ—an sa.
A falo suka bar Baɗɗo suka shiga ciki mintina talatin sai ga su sun fito Habib ya yi wanka ya sanya kaya zuwa jallabiya baƙa a dinning suka zauna Ummu ta yi serving ɗin su jalop rice mai salat, sai zoɓo sauran na jiya ne da ta saka a frizer suna ci jefi-jefi suna hira, hiran kuma tsakanin Habib da Baɗɗo ne yawanci kuma akan karatun ta ne.
Sai can ne Ummu ta kan sako musu baki ko kuma in ya juya ya sako ta a ciki.
Sai wajen tara na dare Habib da Ummu suka tafi kai Baɗɗo gida, da suka isa ƙofar gidan Habib ya ce su shiga ciki su gaisa da Ummu ikki, Ummu ta ce aa suna shiga za ta yi musu faɗa ne.