← Book details Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 92

Sashe 13

Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk kuma gajiyar nan da Ummu Salma ta kwaso bai saka Habib ya ɗaga mata ƙafa ba, har mamakin shi take yi ba ya gajiya, in har Habib bai kusanceta ba sai dai in tana jinin haila ne, shima ɗin saboda ba shi da yadda zai yi ne ammaa kafin ta samu tsarki duka gabban jikinta sai sun koma suna raɗaɗi saboda yadda suke shan yamutsa ba ya barin ta sukuni ko kaɗan shi ya sa har yau ta saka kumarin nan na masu aure ga shi sun kwarari wattani takwas da yin aure, ko lokacin da ta samu ciki da ga samanta ne kawai ta yi kiɓa amma ban da jikinta, irin yadda Habib ke matsa mata lamba ba lalle ta yi  kumari ba, abu kamar cin tuwo ba ya gajiya.

Kuma har lokacin tana jin wannan sauye-sauyen a jikinta amma tun da ta yi gwaji ta ga ba haka ba ne sai ba ta saka ma kanta tunanin komai ba.
Ta fi danganta hakan da rashin hutun da Habib ba ya bari gangar jikinta ya samu shi ne dalili.

Abin da ba ta sani ba shi ne tana da shigar ciki. Dalilin wannan cikin rayuwarta za ta juye daga farinciki zuwa aƙasin hakan.

****

Jalingo street.

Tun jiya da daddare take fama da tashin zuciya amma ba ta damu ba, ta fi danganta hakan da soyayyen ƙwan da ta ci da safiyar ranar ne, can kuma da rana da ta sha zoɓo sai tashin zuciyar ya kwanta har dare da Habib ya dawo ba ta sake ji ba, da safe kuma da tashi sai kasala duk ya rufeta miyau na taruwa a bakinta sannan da zafin jiki ta kwana, Habib bai sani ba kuma bai hana da asuban ya sake nemanta ba, wani abu ke ba ta mamaki a group ɗin makarantan su na sakandiri mai suna Ahmadu ribaɗu Collage wanda suka buɗe na mata zalla akwai matan aure kuma tana gani suna hira, wata Aisha Iro ta taɓa tambayan cewa mijinta sai su yi kwana biyu bai neme ta ba, hakan ba matsala ba ce, nan fa aka yi ma tambayar caa, kowa na faɗin albarkacin bakinsa.

Mafi rinjaye sun ce ba wani abu ba ne, domin rayuwar aure ba domin saduwa ba ne, zamantakewar aure ibada ne. Wasu ma suna ta cewa sai su yi sati kuma ana zaune lafiya, sai dai a yi romance kawai a kwanta tun lokacin da ta ga maganganun su abin ya tsaya mata arai, ba ta taɓa tattauna wannan matsalan da kowa ba sai Baɗɗo ita kuma ba aure ta yi ba sai ta nuna mata wataƙila Habib na cikin maza mabuƙata, ko Bestie ba su taɓa maganar da ita ba amma lamarin na damun ta, ba ta nemi komai ta rasa ba, ba abin da Habib ba ya yi mata matsalanta da shi kawai wannan bangaren ne, kamar wata machine haka ya ɗauke ta kwata-kwata ba ya barin ta samu hutu, tana haɗa musu abin karyawa tana ta tunane-tunane a cikin ranta, ta taɓa yi masa mgana tun farkon auren su ya ce ta shirya mijinta mai yawan buƙata ne amma ita a ganin ta buƙatar ta shi ta yi yawa ne.

Indomie da ƙwai ta dafa ma Habib ba ta jin daɗin jikinta shi yasa ba ta yi dogon breakfast ɗin da zai ba ta wahala ba, sai ruwan tea da ta dafa masa sai da ta jera komai saman dinning sannan ta koma ciki ta tashe shi, wajen taimaka masa ya yi wanka ma sai da ya maimaita a tiolet, in Ummu ba ta furta ta gaji a baki ba gangar jikinta ya nuna gajiya da jarabar Habib, shi ya fara tsarkake jikinsa ya fito ya bar ta a cikin tiolet tana jin kirjinta da kanta sun yi mata nauyi.

Ko da ta fito har ya shirya kan shi cikin suit, ko yadda ya ganta ta yi wani suku-suku ba fara'a bai damu da ya tambayi dalili ba, faÉ—a mata yake yi ta yi sauri kar ya makara.
Wata riga mai gajeren hannu doguwa ta saka  sai hula ta rufe gashin kanta dake jiƙe sai ta sallame shi ko za ta dawo ta busar da shi.
Tun da suka zauna saman Dinning karnin Dafaffen ƙwan nan ya dame ta, ba ta ma saka ma kanta shi ba, indomie ɗin kawai ta zuba wacce ta dafa tare da su carrot da greenbeans, tana kai cokali na ɗaya biyu, na ukun ne ya gagare ta haɗiyewa tuni ta ji kayan cikinta sun fara yamutsawa da gudu ta tashi ta faɗa tiolet kafin Habib ya samu damar mgana ya ji Ummu na ta sheƙa amai kamar  za ta amayar da kayan cikinta.

Da sauri ya tashi daga zaman karyan da yake yi cikin mamaki ya bita tiolet ɗin amma daga baƙin kofa ya tsaya.

"Baby me ke faruwa? Wani abu kika ci?

Ya faÉ—a cikin bayyana damuwa a muryansa. Kuma damuwar har ya bayyana a saman fuskar shi.

Ba ta ma san yana yi ba, tana duƙe tana sheka amai sai da ta amayar da duk abin da ke cikinta sannan ta samu sukuni, ruwa ta buɗe a famfon sink ɗin ta wanke bakinta sannan ta kora Aman ta ɗago tana haki ta nufo hanyar fitowa jiri ya ɗebe ta za ta faɗi Habib ya yi saurin riƙo ta.

"Baby me ke damun ki ne?
Are you sick?

Ummu da saurin kuka tuni ta lafe a jikin shi ta fashe masa da kuka.

"Ni ma ban sani ba Noori amma ina jin jikina duk ba daÉ—i."

Ta faɗa cikin shagwaɓa, tarairayota ya yi suka dawo falo ya zaunar da ita akan kujera ya zauna a gefenta yana mai ƙura mata ido.
Gabansa ya faɗi kar dai a ce Ummu Salma wani cikin ta samu? Da ko ya shiga uku.
Da sauri ya tallabo fuskarta da duka tafukan hannayensa kafin ya ce" Baby yaushe rabon ki da ganin al'adan ki?

"Tun bayan ɓarin da na yi sau ɗaya na yi Noori."

Ta faÉ—a tana wani lumshe idanuwa har ga Allah jikinta ba ya yi mata daÉ—i so take yi ta kwanta.

"Ummu-Salma ko ciki ne da ke?

Ya faÉ—a cikin wata murya mai cike da fargaba.

"Ban sani ba, nima kwanaki na yi tunanin haka sai da na siyo PT na yi gwaji sai na ga babu komai."

Ta faÉ—a cikin sanyin murya tana mai É—ora kanta a saman kafaÉ—anta.
Duk da haka bai gamsu ba, sake ɗagota ya yi yana sake ƙare mata kallo.

"Noori ka bar ni na kwanta jiri nake gani."

Ta faɗa cikin shagwaɓa shi ba ma ta ita yake yi ba kirjinta yake kallo sai a lokacin ya lura kirjinta sun tasa bai taɓa lura da hakan ba.

"Wani yanayi kika ce kina ji a jikin ki?

Ya tambaya agaggauce.
Ita ko Ummu Salma ta É—auka duk murna ce ya sa cikin sanyin murya ta amsa shin
"Noori ina ji fa ba ciki ba ne, na faɗa  maka na gwada ba komai."

"Ki amsa mini tambaya ta."

Ya katse ta da sauri, numfashi ta fesar kafin ta shiga faɗa masa yanayin da take ciki ai tun kafin ta ƙarisa ya miƙe da sauri ya koma cikin bedroom  ɗin su, da mamaki ta bi shi da kallo ganin ya fito da Hijabin ta a hannun shi da key ɗin motarsa lokaci ɗaya yana faɗin.

"Tashi mu je asibiti a yi gwaji."

Cikin mamaki take bin sa da kallo ba ta samu damar mgana ba har ya zura mata hijabi ya koma ciki ya É—auko mata takalmi jikinsa sai rawa yake yi kamar mazari.
Tausayin shi ya kamata lokacin da ya duka yana zura mata takalmi kansa ta shafa lokaci É—aya tana faÉ—in" Ka kwantar da hankalin ka Noori."

Miƙewa ya yi lokaci ɗaya yana kama hannunta ta miƙe tsaye ba tare da ya amsa mganar ta ba.

"Ka ji ?

Ta sake faɗa bayan ta riƙo hannunsa guda ɗaya kallonta ya yi duk ya firgice a cikin ƙanƙanin lokaci.

"Hankalina ba zai kwanta ba sai an yi gwajin nan."

Ya faɗa da sauri lokaci ɗaya ya ja jakarsa dake gefenta ya rataya, riƙe da key ɗin mota a ɗayan hannun na shi, ɗayan kuma ya jawo hannunta. Ita ce ma ta ce ya tsaya ta kashe kayan wuta sannan ta ɗauko key ɗin gidan suka fita tare ta rufe suka rankaya motarsa ƙirar Benz har suka ɗauki hanya bai sake yi mata mgana ba hankalinsa duk ya tashi sai faman gudu yake yi a titi
Ganin haka ya sa Ummu ta kama hannun shi dake saman sintari sai ya juyo yana mai kallon ta.

"Noori."

Da sauri ya katse ta da faÉ—in.

"Boshon clinic za mu je ko?

Sai ta gyaÉ—a masa kai kafin ta ce" E. Ai can na ke da fayel."

Daga nan bai sake magana ba hankalinsa na wajen tuƙi amma daga ganin shi ba ya cikin natsuwarsa.

"Noori ka kwantar da hankalin ka, in ba cikin ba ne ma in sha Allahu na kusa samu."

Wani irin kallo ya yi mata kallon da ba ta taɓa ganin ya yi mata irin shi ba za ta sake mgana ya ɗaga murya yana faɗin.

"Ki bar ni, ba ki ga ina driving ba ne."

Sai da ta kalle shi cikin mamaki shi kuma ba ya ma cikin natsuwarsa ballanta ya ji ba daÉ—i kan É—aga mata muryan da ya yi.

Idanuwanta suka cika da kwalla, tausayin Habib ya kamata yanzu in suka je asibitin suka ce ba ciki ba ne fa? Wani hali zai shiga sai ta koma addu'an Allah ya sa ciki gare ta, ko domin hankalin Habib ya kwanta daga gani ya ƙwallafa rai akan samun cikin ta.

Abin da ba ta sani ba, tunanin da ke zuciyar Habib kishiyar tunanin da ke zuciyarta ne.

****

BOSHON CLINIC.

Suna isa asibitin sai da suka sake siyan kati saboda sauri sun manta da shi a gida. Bayan Ummu ta ga likita ta yi mishi bayanin duk abubuwan da ta ke ji a jikinta nan take ya saka aka É—ibi jininta zuwa lap, ya ce su É—an jira sakamakon ya fita.
Chapter 13 · 0% Book details