← Book details Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 92

Sashe 2

Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta tambayi kanta a zucci da sarari, miƙewa ta yi da hijabin jikinta saboda ta na jin sanyi-sanyi, kwana biyun nan ta fara jin canje-canje a jikinta kamar samun kanta cikin kasala, ciwon jiki, ciwon kai ciwon mara da yanayi mara daɗi ta ji ba ta jin cin komai, ga yawan barci in za ta tashi da ƙyar jikinta ya yi ta ciwo kamar ta yi wani aikin wahala mai tsanani, tun tana jin yanayin kaɗan-kaɗan har yanzu yanayin na yin yawa, daman niyar ta yau in Habib ya dawo ta sanar da shi ba ta jin daɗi ya kamata ta je ta ga likita.

Falo ta koma ta zauna a saman kujeran da ta tashi, falon babba ne yana da faɗi da tsawo, daga can ta sama akwai bangaren Dinning amma ƙarami ne mai kujerun zama guda uku, sai falon da kujeru guda huɗu suka yi masa ƙwanya sai cafet da ya malale tsakar ɗakin mai ɗauke da santer table.

Daga gabas kuma ƙaton tibi ne akan tv stand, sai agogo dake sama babba yana ƙirga lokaci ɗit!ɗit. Kujerun falon black and milk ne, shi ya sa har labulayan suma colour ɗin su kenan, wayarta ta jawo saboda ta ɗauke mata hankali daga tunanin rashin dawowar Habib yau da wuri data ta buɗe ta shiga Tiktok tana ta kalle-kallen abubuwan girke-girken zamani, saboda in dai bangaren girkin ƴan gayu ne na zamanin nan za ka gan su a wajen Ummu-Salma kala-kala, tun tana gida in tana sarrafa wani abun sai ka ce in ta gama ba zai ciyu ba ne, amma in ta gama haka za a yi ta santi musamman ma Baffa da ke supporting ɗin ta a komai na rayuwarta.

Amma ce sarkin faɗa ta yi ta masifa tana cewa Ummu na yi mata ɓarna da shegen iyayin nan nata, saboda ita Amma yar gargajiya ce gani take yi duk abin da Ummu ke yi wahalar da kanta ne kawai da iyayi, a cewarta abincin gargajiya shi ne sahihin abinci ba kayan ƙwalama da Ummu-Salma ta ɗauka abin birgewa ba.

Amma ta sha ce mata in ta yi aure za ta gani in wannan ƙwalamar da ta fi ƙwarewa akai za ta riƙa girka ma mijin yana ci. A lokacin baki ta tura kafin ta amsa mata da cewa" Ammah ke fa ba ki gane ba, ko an yi abinci ana buƙatar irin haka saboda zamani ne ya zo mana da hakan"

Baffa ya sha kashe kuɗi akan online clasess da na training akan burin Ummu na ƙwarewa a girke-girken zamani da sarrafa fulawa ta kowacce hanya kuma ta yi nasara ta koya kuma ta iya kuma har gobe tana kan koya. Yanzu haka ma tana cikin wasu guda uku, kuma a wayarta girke-girke ne sun fi guda dubu, shi ya sa ko tiktok ta shiga abin da za ka yi ta gani kenan ta kalla ta yi like in kuma tana so sai ta yi saving Vedio ɗin, sannan tana da karambani, duk abin da ta gani sai ta gwada shi, shi ya sa a wajen Ummu-Salma fulawa ba ta bata tsoro za ta iya sarrafata fiye da nau'ika goma a lokaci ɗaya.

Daga Tiktok, WhatsApp ta koma charting bai wani dame ta ba tun da ba ta da yawan surutu a waya kafin ta duba chart sau goma ta lalace a wajen kallon status ɗin jama'a.  Ummu Salma sai ta yi watanni ba ta kira wayar mutum ko ta yi masa mgana ba amma kullum tana nan tana duba status ɗin ka sai dai in ba ka saka ba. Za ta duba kuma ta gani amma ba za ta yi mgana ba, ko da rashi aka yi ma mutum ko abin ƙaruwa a cewarta charting ba wajen jaje ba ne ko murna wajen nishaɗi ne, shi ya sa sau tari sai dai ta kira ka a waya ta yi maka jaje ko murna amma ba dai ta charting ba. In za ka jira ta yi maka mgana sai dai ku daumana a haka, yayyenta maza har sun saba da halinta in ka ga tana charting a waya mai tsawo da mutane uku ne. Mutum na farko Mami ce ta biyu kuma Bestie ta uku kuma Sisna, ban da mutanen nan guda uku Ummu Salma ba ta doguwar mgana da kowa, Habib ne lokacin tana gida suna yawan yin charting bayan sun yi aure suna yi amma ba sosai ba shi ya sa a saman chart ɗin ta ba ta kuskure ma waɗanan mutanen guda uku.
Bestie, Mami, Sisna.
Bestie da SisNa ƙawayenta ne Mami kuma wata mace ce mafi daraja a rayuwarta bayan Ammah.

Yanzu haka ma tana cikin duba status ɗin Hamma Abdulrrahaman ta ga ya saka wasu hotuna shi da abokan aikin sa sun sha Suit, da alama a wajen aikin shi ne aka yi wani abun tun da lauya ne, sai ta ga saƙon Sisna ya faɗo da sauri ta fita ta je ta duba.

"Sisna."

Ta turo mata da emojin kuka.

Wani farinciki ya kamata jiki na rawa ta ma yar mata da amsa itama.

"Naam Sisna ya aka yi ne? Wa ya taɓa mini ke yau na ta da garin Jimeta da kewayan ta?

Daga ƙarshen maganarta ta sirka da fullanci, ta tattara emojin wukaƙe da hannu zai kai naushi.
Vioce note ta turo mata na sakwan talatin tana buɗewa ta ji muryanta cikin shagwaɓa tana faɗin.

"Sisna, na gaji da karatun nan na yi matukar gajiya, ni dai kawai ki zo ki ce ma Umman ikki a yi mini aure kamar yadda aka yi miki."

Ummu-Salma ta kwashe da dariya kafin itama ta danna Vn ta fara mgana.

"Uhm ai ni da man na sani akwai abin da ya kai karatu wahala ne Sisna? Wallahi babu shi shi ya sa na ce na gama kuna ganin laifina. Yarinya ki zo ki yi aure a cikin aure akwai Nii'imaaa."

Ta ƙarishe faɗa tana jan maa ɗin da dariya.
Sannan ta tura.

"Wai ke me ya sa in dai mutun ya kawo miki damuwarsa akan karatu sai ki sake ƙarya masa gwiwa? Sisna ki ƙarfafa ni tun da na saka kaina kuma na fara ki karfafa ni, ki ce Sisna ki jure keep fighting za ki iya."

"SisNa Fight.!!!*

Ta tura mata tare da emojin É—aga power hannu da jinjina.

"Yes Maa"!!

Itama ta sake dawo mata da amsa, har da emojin kai biyu da love a saman su.

"Ina Habib?

"Bai dawo ba Sisna.".

Ta bata amsa da gayyar emojin kuka.

"Dilla ke kuma. To kin kira shi?

"Ba ya É—agawa."

"Kar ki damu Sisna. Ƙila ya biya ta gidan su ne zai dawo yanzu kin ji ko?

"To"

"Smile my beautiful Baby."

Sai ta tura mata emojin heart, da na dariya sun fi goma.

"Good night. Ki yi mini addu'a kin san upper week za mu fara exams."

"Ubangiji Allah ya ba ma Sisna Sa'a. Allah ya sa Aisha(BaÉ—É—o) ta fi kowa maki da samun nasara."

"Amin Amin Sisna, sai mun yi waya."

"Bye"

Itama ta tura mata Bye ɗin amma bai yi marking sau biyu ba hakan ya ba ta tabbacin ta sauka daga online, numfashi ta fesar tana kallon window an fara ruwa duk da bai yi ƙarfi ba sosai, ta shi ta yi ta sake gyara labulen da kyau kar ruwan ya yi ƙarfi ya yi mata feshe duk da ta rufe window ɗin, kichen ta shiga da ya ke da ƙofa ta wajen dinning, kitchen ɗin shima Babba ne yana da space sosai ɗaya daga cikin drowers ɗin kitchen ɗin ta buɗe ta dauko wani ƙaramin mug, akwai ƙaramar buta a saman gas cike da ruwan tea da ya ji gayayyanki shi ta ɗaga ta tsiyaya bayan ta saka ƙaramar rariya ta tace, siga ta ɗan saka kaɗan sannan ta samu ƙaramin Bowl, ta buɗe wani kwali ta ɗebo doughnuts guda uku manya ta zuba a ciki sai da ta ma yar da komai a muhallin shi sannan ta ɗauki mug ɗin da Bowl ɗin ta koma falo ta jawo santer table ɗin dake tsakiyar falon ta ijiye saman ta isa gaban Tv ta kunna soket ɗin sai ta ɗauko remot ta dawo ta zauna ya kawo amma a tashar ƙwallo ne
Habib ke kallo in dai yana gida sai ta ma yar da ita tashar Arewa24 suna maimacin kwana chasa'in sai ta bar shi amma ta rage sautin duk da kallo bai dame ta amma tana yi jefi-jefi.

Kan kujera ta koma ta naɗe har da tankwashe kafa, ta ja mug ɗin tea din ta, tana kurɓa lokaci bayan lokaci tana gutsiran doughnuts ɗin dake saman cinyarta, har wani lumshe ido take yi saboda daɗi.

"Ashe ya fi ma daÉ—i in ya yi kwanaki."

Ta faÉ—a tana sake gutira a bakinta, Bowl É—in ta sauke a saman kujera ta sake jawo wayarta chart ta shiga ta duba Habib tun 5.40pm ya sauka daga online, sai ta je ta duba Bestie itama tun safe ba ta damu ba sanin tun da suka kusa fara jarabawa Bestie za ta yi wuyar gani.
Sai ta rubuta mata.

"Bestie kina lafiya? Ya karatun? Da wahala ko. Ayya sannu Allah zai ba ki nasara Bestie na"

Ta tura mata kuma ya tafi amma ba ta online tun da bai yi marking sau biyu ba.
Sai ta koma ta duba Mami sai ta ga tana online da sauri ta tura mata.

"Mami na."

Ba daÉ—ewa Mami ta dawo mata da amsa.

"My first Daughter me kike yi da waya da daren nan? Ina mijin ki?

"Mami bai dawo ba"

"Is he Ok?

Mami ta tambaya sai ta amsa mata da lafiya lau ya biya ta gida ne.

"Good, nima ina duba test É—in É—alibai ne, gobe zan kira ki. Good night."

"Good night Mami na."

Ta rubuta tana tura baki kamar tana ganin ta.

"Kowa sai ya ce mini wai Good night"
Chapter 2 · 0% Book details