← Book details Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 92

Sashe 69

Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Sannu da zuwa Hamma, in yini?

Ta faÉ—a daga in da take tsaye.
Amma Hamma LamiÉ—o ya yi kamar bai ji ta ba.
Da man halinsa ne ko a baya sai ka yi ta gaishe shi yana ji ya yi kamar bai ji ba in kuma ya amsa to a gajarce ne.

"Anan kuma! Ƙariso ciki wataƙila bai ma ji ki ba."
Hamma Abdullahi ya sake faÉ—a. Kamar Ummu ta fashe da kuka har hawaye sun kawo mata cikin kwarmin idanuwanta.
Haka nan jikinta a sanyaye ta ƙariso tsakiyar falon ta ɗan rankwafa daga gefe jikin kujera

"Ina yini Hamma".
Ta faÉ—a cikin rawan murya.

"Fatan an zo lafiya?

Ta sake faɗa kanta na ƙasa.
Nan ma shuru ya yi kamar bai ji ba sai da Hamma Abdullahi ya ce ana gaishe shi sannan ya É—ago yana kallon shi, Ummu ya nuna masa yana faÉ—in" Autar Ammah ke gaishe ka."
Kanta na ƙasa ba ta ɗago ba, saboda haka ba ta san ko ya kalleta ba ta ji dai ya amsa da lafiya da muryansa nan na shi a ginshiƙe kamar ba zai yi magana ba.
Zumbur ta miƙe ta bar falon har tana harɗewa da hijabin jikinta sai da ta ɗan laɓe daga can korido tana so ta ji ko zai tambaya me ya sa ya ganta a gida? Duk da ta san ba zai taɓa tambaya ba. Bai yi magana ba suma su Hamma Abdullahi ba su yi masa maganar ba sai ma suka shiga wata hirar ta dabam hakimin yana zaune yana sauraransu yana amsa musu ɗaya bayan ɗaya a ginshike cike da kasaita. Ita dai tunda ta shige ɗakinta ba ta sake fitowa ba, ana yin sallar isha'i ta tashi ta yi Adda Suwaiba ta ɗauko mata ruwa ta sha magungunnan ta, ƙila akwai na barci ne a ciki nan da nan barci ya ɗauketa. Cikin barci sama-sama ta ji Baffa ya shigo duba ta, ba ma za ta iya tuna me ta ce masa ba, shi dai ta tuna yana ce mata Auta ya jikin naki? Daga nan sai asuba ta iya farkawa shima wasu masallatan sun sallame salla.
Gidan shuru ashe tun jiya da daddare da baƙin da suka zo da yan gidan duk sun tafi gidajen su.

Da safen ma Ammah ta yi abin ƙari Hamma Abdullahi ya zo ya ɗauka bayan shi ma Adda Ummu Sulaim ta yo, sannan haka ma Adda Suwaiba ta kawo duka ya haɗa ya tafi da shi gidan Hamma Lamiɗo dake Jambutu haske.

**

*Jambtutu Haske*

Gidan Hamma LamiÉ—o babban gida ne, mai É—auke bangare biyu manya manya. ÆŠayan bangaren an gyara shi amma babu kayan amfanin yau da kullum yana ma rufe ne É—ayan bangaren ne suke sauka in har sun zo garin. Kayattacen gida ne mai kyau wanda ya dace da zamani
Ko da Hamma Abdullahi ya kai musu abin ƙari ya daɗe yana knooking ɗin gidan ba a zo an ɓude ba. Kuma ya yi ta kiran wayar Lamiɗo tana shiga amma ba a ɗagawa.
Har ya yi niyyar juyawa sai ga Sabuwa ta zo ta buɗe gidan ganin shi ne yasa ta rankwafa tana gaishe shi ya amsa lokaci ɗaya yana miƙa mata kwandunan dake hannunsa masu ɗauke da abincin ta karɓa tana yi masa godiya.

"Uwardakina da Ranka shi daÉ—e ba su tashi ba."

Ta faÉ—a tana kallon Hamma Abdullahi
Agogon fatan dake tsitsiyan hannun shi na hagu ya kalla ƙarfe 9:50am  da man ya yi tunanin haka su ai yan Lagos ne ba sa buƙatar tashi da wuri ba irin su da sukan fita ƙwadago da sassafe ba.

"Ba matsala in sun tashi ga saƙo nan daga Ammah."

"Allah ya saka da alheri. Madalla mun gode."
Sabuwa ta faÉ—a sannan suka yi sallama ya wuce zuwa motarsa ita kuma ta rufe gidan ta koma cikin gidan
Duk wanda ya san matar LamiÉ—o ya san ta da amintattaciyar hadimanta Sabuwa tunda duk in da ta saka kafa nan itama take sakawa shi ya sa kowa ya san ta a bangaren Ammah itama tas tasan kowa, haka ma Anitha mai kula da su Sultan duk in tafiya ta kama Balkisu ko na kwana É—aya ne in dai tare da yara za ta yi tafiyar Anitha na tare da ita saboda kula da yaran shi ya sa itama ta san kowa kamar yadda kowa ma in ya ganta ya san amfaninta ba sai ya yi magana ko tambaya ba
Hidiya da Debora kaÉ—ai da su James ake bari a gida.
Hidiya ana tafiya da ita amma sai in Bilkisu za ta je kano haka ganin gida ko kuma in za su je Daura amma yawan cin tafiye-tafiyenta ta fi yin su tare da Sabuwa da Anitha.

Kitchen Sabuwa ta kai kwandunan abincin tunda masu gidan ba su tashi ba sai sha biyu na rana su da Æ´aÆ´an su. Sai da suka yi wanka suka shirya sannan Sabuwa ta jera musu abin karin a saman dinning
Akwai ruwan zafi da kayan tea sannan akwai kunin ɠyaɗa da soyayyen fanke wannan na Ammah ne, sai soyayyan ƙwai da daffaffe, sai soyayyar indomie, na gidan Hamma Abdullahi kenan na gidan Hamma Abdulrrahaman kuma soyyayar doya ce da ƙwai da plantain sai ruwan zafi, Bilkisu ta ba da umarnin Sabuwa ta ɗibar musu ita da Anitha tunda abincin ya yi musu yawa.

Ita dai tea ta sha da soyayyan doya yaran kuma sun ci ƙwai da plantain Lamiɗo kuma kunun ɠyadan shi ya sha da fanke, har wani jin daɗi yake yi domin ya yi kewar abincinka Ammah na'u'i masu daɗi, ta san yana so shi ya sa ta yi masa, shi fa har gobe yana faɗa babu wacce ta san shi dari bisa ɗari irin Ammah, ko bai yi magana ba ta san abin da ya fi so da wanda ba ya so.

Sai da suka gama karyawa sannan suka koma cikin É—akin barcin su, yaran kuma Anitha ta ja su falo ta kunna musu tibi suna kallon cartoon aka bar Sabuwa da gyara in da suka ci abincin.
Tunda suka koma cikin É—akin barcin su, magana ko ta fatar baki ba ta sake shiga tsakanin miji da matan ba, shi yana zaune a wata kujera kwara É—aya dake cikin bedroom É—in ita kuma tana kishiÉ ide a gefen gado tana duba wayarta shi ma É—in ya duba wayar tasa har ya ga Abdullahi ya yi ta kiran shi amma bai bi bayan kiran ba.
Kansa kawai ya É—an jinginar a jikin kujeran ya É—an yi balance kafafunsa na lumshe a cikin tattausan cafet É—in da ke cikin dakin barcin.

Idanuwansa na lumshe kamar mai barci sai dai ba barcin yake yi ba, a halin shi ko awa uku zai iya yi a haka ba tare da ya gaji ba shi dai kawai yana son shuru fiye da komai a rayuwarsa.
Sanye yake da riga da wando bakake, rigar mai gajerun hannu ne tana da É—an taushi sai wandon iyakarsa gwiwan kafarsa, gargasan da ke kafafun nashi duk sun bayyana a waje.
Kansa ba hula sumar kan ta kwanta haka gemunsa da sajensa, Balkisu ta ajiye wayarta kawai tana kallon mijinta tana mai jin wani alfahari.

Da farko ta ɗauka tara gemu da saje ba na manyan mutane ba ne ta ɗauka na talakawa ne irin uztazan nan sai da ta haɗu da Lamiɗo ta san tara gemu ma baiwa ne da ƙasaita saboda shi ya sa take son gemu da saje. Kuma itama ta fahimci yana so, wai a haka ma yana ragewa in yana wajen aiki in suka yi video call gashi duk ya cika masa fuska sai ta ce ranka ya daɗe ya kamata a yi aski kai kawai yake ɗaga mata baya magana, tana so ta riƙa rage masa amma baya barin ta, sau ɗaya ya taɓa bari ta rage masa shima ita ce ta matsa daga ranar kuma ko ta ce za ta ce za ta yi masa sai ya ce a'a. Ita da ta so har private part ɗin sa ta dinga masa sheving amma ina ta san ba zai taɓa aminta ba.

Ko fa kaya ta saka in dai jikinta ya bayyana ba ya son kallonta sai ya dinga wani kauda kai in ta matsa kuma sai ya runtse ido yana faÉ—in
Ki je ki sauya kayan jikin ki mana"
Yau ma wata riga ce a jikinta mai santsi tana da yar ciki da jaket. Da za su fita beakfast sai ta saka jaket din suna dawowa ɗaki ta cire ta zauna daga ita sai ta cikin mara hannu ta ɗan kamata amma tana da ɗan tsawo tunda ta kai wajen gwiwan kafafunta, kanta kuma da man mayafi ne ta saka ta yi rolling shima tuni ta cire, ta bar suman kan nata da ya sha gyara sai ƙamshi yake yi yana ƙyalli.

Mirmishi take yi ita kaɗai tana tuna daran jiya. Ba ta ɗauka zai kula ta ba, ganin sun yini gidan Ammah kuma ga gajiyan tafiya amma suna yin shirin barci ta shige jikinsa ta lafe masa tana sauke numfashi ya birkice mata, in ta tuna irin yadda ya yi mata rawan jiki sai ta ji wani irin daɗi ya kamata. A baya kafin ta fahimce shi sai ta yi ta kuka tana tunanin ko ita mijinta baya jin daɗin ta ne ? Mata da yawa ƙawayenta ƴaƴan sarakuna da abokan karatunta masu aure suna irin hiran yadda ko gyara suka yi irin yadda mazajensu ke ruɗewa har da waɗanda ake yi ma kuka da ihu, amma ita mijinta bai taɓa mata ko sambatu ba, kuma in zai dawo haka za ta yi ta shiri ta gyara ciki da waje, daga can Kano Umma me aiko mata da kayan gyara da yawa ta yi ta sha ammah in ya dawo suka kaɗaice ba ta ganin wani canji. Sai da ta ga wani rubutun wani likitan kan maza yana bayani kan kashe kashe da rukunin maza da ta bi rubutun sa anan ne ta gano mijinta a cikin rukunin maza.
Chapter 69 · 0% Book details