Sashe 43
Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Adda Kaltume ta faÉ—a, daidai lokacin da BaÉ—É—o ta É—aga kiran Ammah bayan ta sake kiran ta a karo na biyu.
"Ammah ina kwana."
Daga can bangaren Ammah ba ta tsaya amsa gaisuwar BaÉ—É—o ba da sauri ta ce" Aisha ina Aminiya?
"Tana É—akin ta "
"Kai mata wayar zan yi magana da ita."
Amma ta faÉ—a muryanta cunkushe, BaÉ—É—o ta mike tana amsawa da to Adda Kaltume tana ta mata tambaya me ya faru da hannu, ita kuma BaÉ—É—o tana É—aga mata hannu alamun ba ta sani ba.
Ummin ikki na cikin É—akinta, itama da carbi a hannunta tana ja ne barci ya É—an sace ta tana zaune tana ta gyangaÉ—i sai ta ji BaÉ—É—o a saman kanta tana faÉ—a mata ga Amma na son magana da ita.
"To Allah ya sa lafiya "
Ta faÉ—a tana leken waje ganin har lokacin gari bai ida sa wayewa ba.
Tana karɓan wayan ta saka a kunnenta lokaci ɗaya tana faɗin" Aminiya Allah ya sa lafiya."
Ummi ikki ta faÉ—a cikin fargaba kira da sassafe haka ba na lafiya ba ne.
"Wayarki a kashe Aminiya ?
Ammah ta faÉ—a, da sauri Ummin ikki ta ce" Tun jiya ban ga wayar ba, waya sani ma ko ta mace ba chaji ne."
Amma tace" To ƙila."
"Lafiya Aminiya? Na ji muryan ki wani iri ne"
Amma ta yi ajiyar zuciya kafin ta ce" Ki shirya ga Abdullahi nan zai zo ya É—auke ki zuwa gidan Ummu"
"Me ya faru da Ummun?
Ummin ikki ta tambaya har tana waro ido, BaÉ—É—o na gefe tun da taji an ambaci sunan Ummu ta matso kusa da sauri tana son jin abin da ya faru.
"Ya sake ta ne."
Ammah ta faɗa tana runtse ido, kafafunta sun fara rawa da ya sa dole ta lalubi gefen kujeran dake gefenta ta zauna tana ƙoƙarin daidaita yanayin ta.
"Ya sake ta fa ta kika ce Aminiya! Shi Habibun ne ya saki Ummu Salma?
Ummin ikki ta faÉ—a da karfi da ya sa BaÉ—É—o ta yi zaman yan bori a gaban Ummin tana faÉ—in" Habib ya saki Ummu?
Ta sake maimaitawa hannunta a saman ka cikin tashin hankali.
"Ya sake ta Aminiya, Abdullahi na hanya za ku je ku taho da ita "
"Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un amma dai Habibu ya cuce mu Allah ya isa tsakanin mu da shi."
Ummin ikki ta fada sai ga hawaye Ammah kashe wayarta kawai ta yi ta bar Ummin tana ta salati da tsine ma Habibu.
BaÉ—É—o ta fashe da kuka tana faÉ—in" Innalillahi Ummi Habib ne ya saki Ummun? Ummun tawa?
Take faÉ—a tana kuka, Ummin ikki ta ce" Wannan yaron ya gama cutar mu Allah sarki Ummu."
Da man kuma Ammah ta sanar da ita zaman da aka yi na farko ta dinga zagin shi tana cewa mara albarka, to amma daga baya Ammah ta ce mata an daidaita ashe bai hakura ba sai da ya mayar da ƙaramar yarinya bazawara.
Kukan BaÉ—É—o da hargagin Ummi ya fiddo da duka yaran gidan har mahaifin su BaÉ—É—o duk wanda ya tambaya aka faÉ—a masa abin da ya faru sai ya girgiza.
"Subhanallah lamarin bai yi daÉ—i ba me ya faru ne?
Baban su Baɗɗo na tambaya Ummi ba ma tsaya masa bayani ba ta miƙe tana faɗin Abdullahi na hanya zai zo ya dauketa za ta je ta taho da Ummu zuwa gida Baɗɗo na jin haka ta ce itama za ta je Ummi ta ce ba za ta je ba.
"Ummi ki je da ita in Ummu ta gan ta za ta ji daÉ—i "
Adda Kaltume ta faÉ—a cikin damuwa ta girgiza da jin wai Habib ya saki Ummu Salma, duk wanda ke gidan nan ya san waye Habib domin zuwa goma in Ummu za ta yi shi zai kawo ta ya kuma zo ya É—auke ta kuma duk zuwa sai ya shigo ya gaida Ummi da Baba, tun kafin auren su ma bayan auren ma sai ya zama É—an gida nan zai zo É—aukan Ummu su zauna a falon Ummi da shi da BaÉ—É—o da Ummun suna ta hira suna dariya.
Kowa sai jinjina lamarin yake yi, abin mamaki abin tausayi ga rayuwar Ummu, da wayar da Ammah ta yi da Ummin ikki ko minti talatin ba a yi ba sai ga Hamma Abdullahi bakwai saura mintina ya iso gidan yadda ya shigo kawai za ka san shima labarin ya dake shi, jallabiya ce a jikinshi a baibai ya sako ta ma domin yana barcin nan na bayan asuba ya samu wayar Baffa labarin da ya faÉ—a masa ne ya sa ya diro daga kan gado bai shirya ba, ya razana da jin wai mijin Ummu ya sake ta! Har ya kariso gidan Ummin ikki yana tunanin to me ya sa zai sake ta? To ta yi masa wani abu ne?
Daga Ummin har Baɗɗo da hijaban jikinsu suka bi Abdullahi takalma kawai suka saka, suna tafe a mota Ummin ikki na sake kwashe ma Habib albarka Baɗɗo na daga baya tana ta sharan ƙwalla tausayin halin da Ummu take ciki a daidai wannan lokacin.
"Ummi to wai me ya sa zai sake ta? Ko ta yi masa wani abu ne?
Abdullahi ya tambaya jin yadda Ummin ke mgana da alamu ta san wani abu.
"Ba ka san abin da ya faru kwanaki ba ne Abdullahi?
"Ban sani ba Ummi, Baffa bai faÉ—a mini ba, haka ma Ammah."
Nan fa ta warware masa komai mamaki ya kama shi sai ma ya kasa mgana wato shi ya sa kenan ya ga Baffa Umaru ya zo har da mijin Ummu da ita kanta ashe lokacin duk matsalan ne ya ta so.
"Wai ba ya son ciki ka ji fa, sai ka ce shi uwarsa ba cikin ta yi ta haife shi ba wataƙila daga sama ya faɗo"
Ummin ikki ta faÉ—a cikin takaici da haushi.
"Allah ya kyauta."
Kawai Abdullahi ya ce amma maganganu na yawo a cikin ranshi, ta ya ya mutum zai auri macen da yake so kuma ya ce ba ya son ciki? Cikin kuma na shi ne, daga karshe hadda saki? Kai gaskiya yana tamtama an ya mijin nan na Ummu Salma yana son ta kuwa? Domin wanda ke son ka ba zai yi maka wannan tozarcin ba.
Bai sake magana ba har suka isa gidan, a bakin flat ɗin Ummu suka yi parking ɗin motar, dukkansu kuma suka firfito, abin mamaki ƙofar falon Ummu ma a buɗe take har ga labule nan a waje shi ya sa kawai suka faɗa, Baɗɗo ce ta shige gaba da sauri Ummi a bayanta Abdullahi kuma sai ya tsaya daga waje bai shiga ba, a tunanin shi ko Habib ɗin na gidan abin da ba su sani ba tun wajen shidda da rabi ya tattara kayan shi kaf ya bar gidan a motar shi baya son ma wani cikin yanuwan Ummu su gan shi tun da abin da ya haɗa su ya raba baya fata ko son sake haɗuwa da duk wani abu da ya shafi Ummu Salma. Tunda ya ce ya gama da ita, to har abada ya gama da shafin ta.
Yadda BaÉ—É—o ta ga Ummu Salma ya sake tsinke mata zuciya tana zaune a in da ta yi salla kanta jingine da wardrope, ta yi kuri kawai ba ta magana ba ta kuma kuka amma fuskarta da idanuwanta sun kunbura babu kyan gani.
Rumgumeta ta yi ta fashe da kuka tana faÉ—in" Allah ya saka miki Ummu, da ikon Allah Habib sai ya ga sakamakon shi."
Â
Ummu ba ta mgana tana dai kallon Baɗɗo kawai, Ummin ikki ta kasa mgana saboda tausayin Ummu har tana ƙwalla.
"BaÉ—É—o kamata ta tashi, ki kaita falo ki zo ki É—an haÉ—a mata kayan sawan ta."
Da to Baɗɗo ta amsa, ta taimaka ta miƙar da Ummu tsaye ta riƙe ta zuwa falo, ta zaunar da ita a saman kujera ta zauna kawai tana kallon ta, bakin ma ya ɗinke ba mgana sai dai kawai ido.
Baɗɗo na kuka ta juya ta koma ciki tare da Ummin ikki suka cika akwatin Ummu huɗu da kayan sawan ta, Ummin ikki ta ce duk a cire zannuwan gadon kar su yi ƙura a tusa su cikin wardrope kafin a ga abin da Ubangiji zai yi, Baɗɗo ce ta yaye zanin gado sai ga takarda ta faɗo ta ɗauka ta buɗe ta karanta.
"Ummi."
Ta faɗa cikin ƙaraji lokacin da ta gama karanta takardan sakin Ummu Salma.
"Mene ne ya faru?
Ummin ikki ta faÉ—a cikin tashin hankali tana kallon BaÉ—É—o..
"Ummi saki uku fa Habib ya yi ma Ummu."
Ta faÉ—a tana nuna mata takardan hannunta
"Innalillahi wa'inna alaihirraju'un."
Ummin ikki ta faÉ—a kanta har yana sarawa.
"Wannan wani irin sakin wulakanci ne da tozarci?
Ta faÉ—a tana hawaye, BaÉ—É—o ba saki ukun take yi ma kuka ba illa maganganun da Habib ya rubuta masu alamu da tozarci da wulakanci bayan sakin
Karɓan takardan Ummin ikki ta yi ta ce bari ta kai ma Abdullahi bayan ta umarci Baɗɗo da ta yi sauri ta naɗe zanin gado ta kuma jawo akwatunan Ummu zuwa falo.
Abdullahi na tsaye jikin motar shi yana waya da Hamma Jibo.
Jiya sai wajen goma na dare suka isa, yana shirin zuwa wajen aiki ne Abdullahi ya kira shi yana sanar da shi mugun labari, shi ne suke tattaunawa yana ba shi labarin halin da ya je gidan Ummu ya same ta a ciki har zuwan da suka yi shi da Baffa gidan waliyin Habibun ashe duk bai ji ba shi ne ya yi mata sakin wulakanci, sai a lokacin Abdullahi ya tuna wato ranar da ya ga Baffa da Hamma Jibo sun tafi ashe can suka je.
"Ni fa Hamma duk ban san abin da ke faruwa ba, kwanaki dai na ganta a gida duk ta rame to ni ban kawo cewa mata matsala ba ce."
Abdullahi ya faÉ—a yana nusar da hannunsa a cikin sumar kansa.
"An É—auka za a iya gyara lamarin ne ashe bai zai gyaru ba."
Hamma Jibo ya faɗa daga can bangaren cikin damuwa da tausayin ƙanwar tasu.
Kafin Hamma Abdullahi ya sake magana Ummin ikki ta fito wajensa tana mika masa takardan hannun ta.