← Book details Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 92

Sashe 49

Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ummu Salma ta ɗauka ta gama dacewa. Ta ɗauka bayan ita da wahala a samu mace irin ta a cikin tsara. Sai ga shi cikin wattani uku Habib ya yi ma rayuwarta juyin waina daga sama ta koma kasa. Cikin wattani tara zuwa goma da auran su ya yi ma rayuwarta katon taɓon da har ta koma ga Allah ba za ta manta ba.

*littafin Fargar Jaji na kuÉ—i ne a manhajar Telegram akan #1k. Tura KuÉ—in karatun ku ta wannan acct É—in 9069067488 JAMILA UMAR OPAY sannan sai ku tura shaidar biya ta waÉ—anan lambobin kamar haka.*

09069067488.
08032773332.

*Yan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajojinku a cikin wannan kayattacen labarin za ku iya tuntuɓata kai tsaye ta wannan lambar 09069067488 Na gode.*

*Janafty*
*FARGAR JAJI.*

*Wattpad:JamilaUmar315*
*Arewabooks:JamilaUmarJanafty*

"To Hajiya Hauwa'u Inuwa Aminu (Anty Hairi) with love and gratitude"

https://chat.whatsapp.com/LsC7Rjmei7J6Hd11e95nNS?mode=gi_t

*12*

Hamma Abdullahi ya ɗauko  Ummin ikki a mazaunin gaba na motarsa sai Baɗɗo da Ummu dake zaune a gidan baya akan hanyar su ta zuwa gidan Baffa. Baɗɗo ne ke ta kuka saboda in ta kalli Ummu sai ta ji rauni ya dabaibaye ta, ita ma Ummin ikki hawayen take yi tana sake rantsuwan ba za su yafe ba sai Allah ya yi ma Ummu sakayya akan tozarcin da Habib ya yi mata.

Hamma Abdullahi ko baya magana tuƙinsa kawai yake yi amma in da za a tona zuciyarsa da wataƙila an fahimci halin baƙincikin da yake ciki, takardan sakin tana cikin aljihun jallabiyan jikinsa har wani ɗaci yake ji a ran shi na tozarcin kalaman Habib yanzu ya ya Baffa da Amma za su ji? Ummu ma ba a maganar ta, tana zaune kawai ta ƙura ma gabanta idanuwana sai ta daɗe ba ta kyafta idanuwana ba kamar wacce ta zama gunki ba ta kuka ba ta motsi sannan babu hawaye sai dai ido kawai yana kallonta, ta cikin madubin motarsa na gaba gabaɗaya jikinsa ya yi sanyi kamar an masa wanka da ruwan sanyi, addu'a kawai yake yi mata Allah ya ba ta ikon cin wannan jarabawan domin jarabawan mai zafi ne sai wanda ubangiji ya so zai iya tsallakewa.

Har suka isa gidan Baffa dake Zone 3 suna cikin wannan yanayin har cikin haraba Hamma Abdullahi ya shiga da motar Baɗɗo ta kama Ummu ita da Ummin ikki suka shiga da ita cikin gida yayin da Hamma Abdullahi ya buɗe boot ya kwaso akwatin Ummun guda huɗu ya bi bayan su da shi. Amma na zaune a falonta tun bayan fitowarta daga wajen Baffa ba ta koma ba, ba ta so ya fahimci tana cikin gigita shima kamar ya sani sai ya bata lokaci tunda suka gama waya da Aminiya take zaune cikin mutuwar jiki da na zuciya na tsawon lokaci kafin ta ji sallama a tsakar gida zumbur ta miƙe jikinta ba in da ba ya rawa ɗago labulen da aka yi ne yasa Amma ta yi saurin komawa ta zauna tana ɗan daidaita yanayin ta.

Lokacin da suka shigo da Ummu a riƙe kallo ɗaya Amma ta yi mata ta ji ta sare, kafafunta sun yi mata nauyi da ta kasa ma miƙewa Ummu ce ta koma haka! Idanuwa sun kumbura fuskarta ta yi wani irin jajir, tana zaune kawai tana kallon su, suka zaunar da ita a saman kujera Baɗɗo ta zauna a gefenta ta jawo ta a gefen kafaɗanta tana ɗan tapping bayanta alamun lallashi, duk in da aka bi da ita can take bi kamar wata doluwa ko yarinya ƙarama.

Ummin ikki ta ƙarisa kusa da Amma ta zauna tana faɗin" Aminiya yau mun tashi cikin jarabawar Ubangiji."
Amma ta kalleta kafin ta É—an motsa bakinta a hankali tana faÉ—in" Allah ya sa hakan ya zame mana alheri gabaÉ—aya"
Ummu ikki ta amsa da Amin kafin ta fara goge ƙwalla tana cigaba da faɗin" Wannan yaro ya cuce mu. Da ikon Allah sai Allah ya saka mana."

Ta faÉ—a tana kallon Ummu har a lokacin kawai waje É—aya take kallo ko kiftawa babu, kafin ta sake cewa wani abu Hamma Abdullahi ya yi sallama ya shigo cikin gida sun amsa sannan ya shigo falon Ammah, sanda suka taho da su Ummin ikki Hamma Jibo ne ya kira wayarsa shi ya sa ya É—an dakata suka yi magana ya sanar da shi ya kawo su gida yanzu. Akwatin hannunsa ya jera anan tsakiyar falon Ammah ko zama bai yi ba ya kalli Ummu na wani lokaci kafin ya É—an girgiza kansa.

"Ina kwana Ammah."

Ya faÉ—a cikin sanyin murya.

"Lafiya lau Baba ya iyalan naka?

Ta amsa masa amma ba ta kalle shi ba kanta na ƙasa ba ta so shima ya fahimci halin da take ciki, ko ba ta fito ta nuna ba ko ta ɓoye Ammah fa uwa ce ga Ummu Salma yadda lamarin nan zai daki kowa barin ita ne.

"Suna lafiya."

Ya faɗa sai kuma ya yi shuru, Ummin ikki na ta sharan ƙwalla Baɗɗo ko hawaye ne wasu na zuba wasu na sake tunkuɗowa.

"Ba komai in sha Allah zai wuce."

Hamma Abdullahi ya faɗa domin a lokacin shima ya rasa kalaman da zai faɗi falon ya yi shuru kamar mutuwa ta gifta tun ballanta shessheƙan kukan Baɗɗo da na Ummin ikki. Ummu dai ba ta kuka da man an ce wani baƙin ciki in ka yi kukan daga baya in kukan ya ɗauke shike nan sai dai zuciya ta dinga ƙuna da raɗaɗi to hakan ce take faruwa da Ummu tunani take yi kamar ba gaskiya ba ne abin da ke faruwa gani take yi kamar komai a mafarki ne in ta farka za ta ganta a cikin ɗakin auren ta, tare da Habib amma ina duk lokacin da ta kifta idanuwanta a falon Ammah take sake ganin ta.

"Ammah Baffa fa?

Ya faɗa ganin Ammah ta yi shuru kanta na kallon ƙasa.

"Yana cikin É—akin sa."

Ammah ta amsa masa cikin ajiyar zuciya.
Ya kama hanyar barin falon ne sai ga Baffa ya shigo da sallama daidai lokacin da Hamma Abdullahi ya É—aga labulen falon Ammah sai ya koma da baya ya ba ma Baffa waje domin ya shigo.

Baffa ya shigo har falon Ammah ya yi tsaye kawai yana kallon Ummu Salma sanye yake da manyan kaya tun da ya saka ne zai je masallaci da asuba.
Tun ɗazu ya ji shigowarsu amma ya kasa tashi ne, bai san adadin hawayen da ya share a ciki kafin ya fito ba. Bai san a wani hali zai ga Ummu ba! Abin da ya faru da ƙanwarsa Fatima ya dawo masa sabo, shi kaɗai ya san dararan da ya ɓata idanuwan shi biyu yana kukan tausayin Fatima tausayin jarabawan rayuwan da ta faɗa sai ga shi kwatan kwacin haka ya sake faruwa da gudan jininsa Ummu Salma, amma bai yi butulci ba sai ya yi ma Allah godiya domin ba wai ba ya son bayin shi ba ne don ya sake jarabtansu, ya yi haka ne domin ya sake jaraba imaninsu, yana fata da tunanin in Habib ya zama mafarin Ummu Allah ya kawo mata wanda zai wanke mata duk wani dattin zuciya da Habib ya sanya mata.

  Ko da yake tsaye a gaban ta, ba ta nuna alamun ta san ma yana wajen ba, kawai gabanta take kallo babu ko ƙyaftawa. Falon ya sake yin shuru kamar ba kowa a ciki Baffa ya duƙa a gaban Ummu yana kallon ta amma ita ba shi take kallo ba kawai gabanta ta ƙura ma idanuwa ba ta ko motsi daga in da take zaune Baɗɗo na rumgume da ita.

"Ummu Salma."

Baffa ya kira sunan ta cikin kulawa na musamman.

Shuru ita ba ta amsa ba sannan ba ta kalle shi ba, ya sake kiranta a karo na biyu nan ma ba ta É—ago ta kalle shi ba sannan ba ta amsa ba.

"Ummu Salma."

Shuru falon ya sake É—auka kowa hankalin shi na wajen Ummu cikin tausayi.

"Kalle ni nan Ummu Salma."

Baffa ya sake faɗa lokaci ɗaya yana riƙo hannunta guda ɗaya, abin mamaki haka ya riƙe hannunta da ya ji sa ya yi sanyi sosai amma Ummu ta kasa iya rike Baffa sai ta ji kamar duka kasusuwan hannun nata ba sa aiki, daƙyar ta iya ɗago idanuwanta ta kalli Baffa. ta ƙura masa ido  ba ko kiftawa tana ta kallon shi.

"Ummu Salma."

Baffa ya sake kiranta yana mai matse hannunta a cikin na shi hannun, yana ji kamar ya fashe da kukan tausayin ta amma in ya yi kuka ita za ta sare a yanzu a wannan kadamin su ne ƙarfin gwiwanta in suka rushe itama za ta rushe.

"Ummu Salma."

Ya sake kiran sunan ta, sai ta motsa idanuwanta. Ta kifta ta sake kiftawa sai ga hawaye sharr sun kwaranyo mata a saman kumatun ta.
Ganin Baffa kawai da ta yi ya duƙa a gabanta yana kiran sunan ta ya sa hawaye ya kawo mata. Ya Baffa zai ji? Wani hali zuciyarsa take ciki? Ta yi aure ta tafi ita kaɗai sai gashi ta dawo  musu da ciki a cikin jikinta, Ammah ma ta san tana cikin firgici kawai tana ɓoyewa ne. Kuka fa ake yi saboda abin da ya same ta. Ita ko in ba ta ce tana cikin bala'i ba me za ta ce?

"Allah ya ba ki dangana Ummu Salma. Sannun kin ji ko?

Baffa ya faÉ—a yana sake jinjina hannanunta dake cikin na shi. Sai ta sake kifta idanuwanta hawaye suka sake zubo mata.

"Ai gwara ta yi kukan ko za ta samu sauki. Tunda muka je yarinyar nan ke cikin wannan yanayin."

Ummin ikki ta faɗa cikin rawan murya. Baffa ya yi shuru kansa na ƙasa kafin ya saki hannun Ummu ya miƙe yana kallon Baɗɗo na saka tafukan hannayenta tana mai share ma Ummu hawaye.

Hamma Abdullahi da tausayin Ummu ya kama shi sai ya ji kamar ya yi mata ƙwalla amma duk da haka idanuwansa sun kala sun yi jajir kamar gwarwashi saboda bacin rai.

"Baffa ina kwana? Ya muka ji da wannan al'amarin kuma da muka tashi da shi yau?
Chapter 49 · 0% Book details