Sashe 42
Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta faÉ—a tana jin jikinta na yin wani sanyi, haka kurum take jin faÉ—uwar gaba tun jiya da man kawai Autan ke faÉ—o mata arai ta so ma kiranta sai ta ga dare ya yi tana shirin da man yau ta kirata a waya ta ji lafiyan ta ne.
Baffa ya kasa mgana jin yadda Ummu ke rusa masa kuka a waya gabaÉ—aya jikinsa ya gama yin sanyi amma sai ya yi jarumta komai ya faru daga gare ka ne Ya Ubangijin mu.
"Ki bar kukan nan ki yi mini bayanin abin da ya faru Auta."
Ya faÉ—a cikin lallashi a muryan sa Amma ta sake tsurewa a cikin zuciyanta tana maimaita kalmar kukan da ta ji Baffa ya ambata.
"Baffa."
Ummu Salma ta kira sunan Baffa muryanta a shaƙe da ƙyar ma take fita.
"Naam Auta me ya faru ne?
Ya faÉ—a cikin sauri domin ya kosa ya ji abin da ya faru duk da yana zargin wani abu amma bai yanke hukunci ba.
"Baffa."
Ta sake kiran sunan shi cikin matsannacin kuka duk ta ruÉ—ar da Baffa, ga Ammah ma a gefen shi kamar za ta kwace wayan idanuwanta kawai ya kalla ya ga tsoro da firgici a cikin su.
"Na'am ina jin ki Auta, ki daina kuka maza ki sanar da ni abin da ke faruwa bar kuka Auta kin ji ko?
Ya ƙarishe faɗa muryansa na karyewa shima jin irin kukan da Ummu Salma ke yi a waya kamar ranta zai fita.
"Baffa Habib."
"Me ya samu Habib É—in?
Baffa ya katse da sauri kafin zullumi ya kashe shi.
"Ya sa ke ni..."
Ta faɗa tana sarƙewa cikin matsanancin kuka.
Sai da Baffa ya miƙe da sauri kansa ya sara, idanuwansa suka ciko da ƙwalla hannunsa na rawa haka ƙafafuwansa shuru ya yi yana kiran sunan Allah a cikin zuciyarsa domin ya samu ya tattaro natsuwarsa.
Ammah ta biyo shi a tsayen tana tambayan shi jin ya yi shuru sannan ba su yanke wayar ba, ta san waye Baffa shurun sa na nufin damuwa mai yawa ko a fuskarsa ma ya bayyana haka.
Tana so ta yi magana amma sai ta kasa ta dai tsura masa ido kawai tana bin shi da kallo.
"Baffa Habib ya sake ni, ya sake ni jiya da daddare."
Ummu Salma ta sake faÉ—a cikin kuka jin Baffa ya yi shuru, bai ce komai ba.
"Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un."
Baffa ya samu bakin shi da furtawa cikin wata murya mai cike da tausayin Ummu.
"Allahumma ajirni fimusibatihi. Daga gare ka muke Allah kuma a gare ka za mu koma."
Baffa ya sake faɗa cikin yaƙinin da cewa akwai Allah da sanin sa komai ya faru kuma shi zai kawo sauƙin lamarin cikin gaggawa.
Ummu kuka kawai take rusawa kamar ranta zai fita Baffa ya kasa jure jin kukan ta kawai sai ya kashe wayar, ya ma kasa kallon Ammah wacce ke bin shi da kallo, kansa ya juyar kawai ya koma ya zauna a gefen gado ya dukar da kansa lokaci É—aya ya saka hannayensa duka biyu ya dafe kansa yana sake maimaita salati da muryansa cikin rauni da tausayi.
"Allah ya ba ki ikon cinye wannan jarabar mai zafi da raÉ—aÉ—i Ummu Salma."
Muryansa ta karye da man Baffa akwai rauni ko ciwo mutun yake yi sai ya yi kuka lokacin da Ammah ke haihuwa haka zai yi ta kuka asibiti in tana naguda, ganin yanayin shi kawai ya ba ta tabbacin wani abu ya faru mara daɗi amma ba ta tambaya ba, sai ta bishi ta zauna a gefen shi ta ɗora hannayenta saman kafaɗan shi tana ɗan matsawa alamun lallashi duk da itama ƙarfin hali take yi amma zuciyarta ta yi rauni ba ta so ta nuna ne.
Shuru na wani lokaci kafin Baffa ya fesar da numfashi cikin hikima ya share ƙwallar da ta ɗan siraro masa ta gefen idanuwansa saboda kar Ammah ta gani abin da bai sani ba, ta riga ta gan shi, kukan sa kawai ya sake ba ta tabbacin Ummu ta fsɗa cikin kaddaran aure, kaddaran da take ta yi mata fatan kar Allah ya sa ta faɗa a cikinsa, domin ba ko wacce mace ba ce jaruma, ba ko wacce mace ba ce take iya tsallake wannan jarabawar sai jaruma sai sadaukiya amma Ummu ba za ta iya ba zuciyarta karama ce tana da rauni ba lalle ne ta fuskanci girman jarabawan da ya faɗa mata ba.
Baffa ya ɗago kanshi suka haɗa ido da Ammaj sai kawai ta yi masa mirmishi, ita wai a dole ta nuna masa ba ta damu ba, fillanci na cin ta amma duk wanda ya kalleta ya san a cikin zuciyarta tsoro ne da fargaba ba ta tambaye shi ba shima sai ya kasa faɗa mata, illah hannayenta da ya jimƙe cikin nashi yana kallon ta amma ya kasa mgana a cikin zuciyarsa salati kawai yake yi da kiran sunan Allah.
Itama sai ta jimƙe hannayen na shi cikin nata cikin karfin hali ta kira sunan shi.
"Baffa."
Bai amsa ba amma yana ta kallon ta.
Sai kuma ta yi shuru ta kasa mgana tana so ne ta tambaye shi amma ta kasa, shi kuma ya san halinta ba za ta sake tambaya ba saboda kawaicin ta sai kawai ya yi kumdulan fada mata ita uwa ce ya kamata ta sani ko domin su yi tunanin mafita.
"Jamila."
Tunda ta ji wannan sunan a bakin Baffa ta san maganar da zai faÉ—a mata mai girma ne.
"Habibu ne ya saki Auta jiya da daddare."
Ya faɗa yana kallonta hannayenta na cikin na shi yana matsawa, shuru na wani lokaci yana kallon ta duk da ta tsammaci haka amma ai zato ne ba gaskiya ba yanzu da ta samu tabbacin sai ta ji zuciyarta ta yi duhu wani abu kamar ya sare daga kirjinta kwata-ƙwacin abin da ta ji a lokacin da Fatima ta zo gare su da tsohon dare ɗauke da jaririn da ko jinin haihuwa ba a wanke masa ba, a lokacin da ta ba ma Baffa takardan saki, abin da ta ji a lokacin a wannan lokacin ma shi ta sake ji.
"Ta kira ni tana ta kuka Jamila. Gwanin ban tausayi "
Ya sake faÉ—a muryansa har tana sauyawa, Ammah ta yi ajiyar zuciya kafin ta tattaro kalaman bakinta ta furta."Â Allah ya sa hakan ya zame mana alheri gabadaya "
"Amin "
Ya amsa yana kallon ta.
Shuru na wani lokaci kafin Amma ta yi ƙarfin halin cewa" Baffa wa zai je ya taho da Ummu?
Ta faÉ—a tana kallon shi, sai yanzu ya tuna ya kamata wani ya je ya É—auko ta zuwa gida a yanayin da ta ke ciki tana bukatar wani a kusa da ita.
"Bari na yi ma Saddam magana ya tuka ni muje mu taho da ita."
Baffa ys faɗa yana miƙewa da sauri Amma ta mike ta riko shi ganin duk ya daburce kallon ta ya yi yana cigaba da faɗin" tana ta kuka gwara na je da kaina "
Ya faÉ—a yana laluban aljihun jikinsa
"Ammah ina key É—in mota ta?
Ya faÉ—a yana waige-waige Baffa fa ba ya cikin natsuwarsa shi ya sa ta sake riko shi tana kiran sunan shi.
"Baffa."
Sai kawai ya tsaya yana kallonta
"Jamila Auta tana can tana kuka ba ki ji muryan ta ba."
Ya faÉ—a cikin karyewan sauti, kawai sai ta faÉ—a jikin shi, domin itama in ta cigaba da jin sautin Baffa cikin rauni za ta iya fashewa da kuka ba ta sani ba, jin ta a jikinsa ya sa ya yi shuru kawai yana sauke ajiyar zuciya, bayansa take É—an tapping da hannunta alamun lallashi, kuma ta yi nasara domin sai ya É—an samu natsuwar zuciya.
"Ba kai za ka je ba Baffa."
Ya ji Ammah ta faÉ—a da sauri ya dago ta kafin ya yi magana ta yi saurin cewa" ka kira Abdullahi ka sanar da shi abin da ke faruwa ka ce ya É—au mota ya je ya É—auko Aminiya zan kira ta yanzu na sanar da ita abin da ke faruwa, ita in suka je za ta shiga ciki ta taho da Ummu gida."
Tabbas ya aminta da shawaran ta, gwara mace ta je zai fi akan namiji.
"Hakan ya yi, amma ko na kira Abdulrrahman ne?
"Aa gwara dai Abdullahi ka san halin Abdulrrahman fusattace ne."
Shi saboda tashin hankali duk ya manta da halin Æ´a'yan na shi, wayarsa ya fara laluba Ammah ta É—auko masa ita a gefen gado ta mika masa lokaci É—aya tana faÉ—in" Ka kira shi yanzu, bari na je na kira Aminiya"
Tana gama faɗin haka ta wuce ta fita daga ɗakin, falon ta yana sakaye ne ta tura ta shiga wayarta a chaji ta sakata tun daran jiya hannanunta na rawa kamar yadda zuciyarta ke bugawa.
Tana duba wayar sai ta ga ma Ummu ta kirata sau uku a lokacin da ta kira Baffa kenan, lambar Ummin ikki ta nemo wacce ta yi ma saving da Aminiya, duk da Ammah ba ta yi karatun boko ba amma sun yi yaki da jahilci shi ya sa ta iya karanta hausa, wani lokacin ma da fillanci take yi saving din lambobin wayarta.
Sai dai tana kiran wayar sai ta ji a kashe, har sau biyu ba ta shiga ba sai kawai ta laluɓo lambar wayar Aisha(Baɗɗo). Tana kiranta ita sai ta shiga.
BaÉ—É—o na kwance a É—akin su bayan ta idar da sallar asuba gajiya ne a jikinta jiya wajen takwas na dare ta iso gida daga Mubi, tana idar da salla sai ta É—an kishigiÉ—a barcin ya É—an É—auke ta kenan ta ji ringing É—in wayarta dake gefen filon data ke kwance da barci-barci ma a idanuwanta ta zaro wayar sai dai ta wattsake ganin sunan Ammah tana kiranta, ido ta waro tana sake duban sunan mai kiran da gaske dai Ammah ce.
"Wa ke kira hala ?
Adda Kaltume ke tambaya ganin yadda BaÉ—É—on ta zaro ido kamar ta ga wani abun tsoro.
"Ammah ce fa."
Ta faɗa tana kallon ƙaramin agogon bangon dake ɗakin barcin na su, ƙarfe 6:32am na safe to ba lafiya.
"Topha, É—aga mu ji Allah ya sa dai lafiya"