← Book details Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 92

Sashe 36

Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baffa ya yi shuru yana tunani kafin ya ce" Wannan karon ba zan jira ma Baffan ku Umaru ya zo ba, zan kira shi na ce ya tura mini lambar shi waliyin Habibun zan kira shi na ce masa ina son mu haÉ—u ni da kaina zan warware masa komai sannan na faÉ—a masa ya sanar da É—an shi in har ba ya son Ummu ne ya dawo mini da ita gida ni ina da abincin da zan ciyar da ita ba wai ya gagare ni ba ne"

Yadda Baffa ke magana kaɗai ya isa ka fahimci ya kai makura a takaicin Habibu, ba abin da ya fi ƙona masa rai  a ciki irin horan yunwa ga ciki a jikinta amma ya barta tana wahala saboda wata manufarsa ta banza da wofi. To shi ba zai ɗauka ka ba, ba a dole ya sako masa yarsa in ba zai iya rike amana kamar yadda ya ɗau yaƙini ba.

"Baffa na lura Auta na son mijinta. Kar a yi gaggawan raba su a tsaya dai a sake samun masalaha."

Baffa ya yi ƙaramin tsaki kafin ya ce" To son banza Jibo? Me son ya tsinana mata balle mu iyayenta! Kuma ni na ma fara tamtama in har yanzu yaron nan Habibu na son Auta. Domin mai son ka zai so haɗa zuru'a da kai, sannan ba zai taba wulaƙanta ka ba, ballanta har yana da shi da gangan ya yi maka horo da yunwa."

"Haka ne Baffa"

Hamma Jibo ya faɗa cikin gamsuwa da mganar Baffa amma yadda Ummu ke kuka har yanzu hoton ya kasa ɓace masa.

"Ko tana son shi, in shi ya nuna baya ra'ayin ta ai dole ta haƙura."

Hamma Jibo ya yi shuru duk jikinsa ya yi sanyi. Nan take Baffa ya kira É—an'uwansa Baffa Umaru bayan sun gaisa ya ce masa yana son ya tura masa lambar waliyin Habibu mijin Auta Ummu Salama.

"Hadi lafiya kuwa?

Baffa Umru ya tambaya daga can bangaren cikin mamaki, domin shi a tunanin shi an samu masalaha tsakanin Auta da mijinta tun bayan zaman da suka yi.

"Zan sanar da kai daga baya. Yanzu dai ka turo mini lambar ina jira.'

Sai bai matsa masa ba ya amsa masa da to zai tura masa, suna yanke wayar mintina biyar tsakani ya turo masa lambar, Hamma Jibo ya ba ma wayar ta sa ya ciro masa lambar ya saka a cikin wayar sannan ya ce ya kira ya ba shi zai yi mgana da shi.

Kira É—aya ba ta ko daÉ—e tana kara ba Alhaji Sheriff ya É—aga wayar da sallama Baffa ya amsa bayan gaisuwa sai Baffa ya gabatar da kansa.

"Sunana Alhaji Hadi Baba ni ne mahaifin Ummu Salma, matar yaron wajen ku Habibu."

Nan da Alhaji Sherif ya washe baki kamar yana ganin shi, suka sake gaisawa tunda ba su da lambar juna, daman da Baffa Umaru ne suke magana tun neman auren.

"Alhaji lafiya kuwa? Ina fatan ba wata matsala ce ta sake tasowa daga bangaren yaran ba?

Alhaji Sheriff ya tambaya daga can bangaren, domin ya ji mamakin kiran na sirikin Habibu a wannan lokacin.

"Lafiya lau, in ba damuwa adireshin gidan ka za ka turo mini zan zo har gida da safe na same ka, akwai mganganun da za mu tattauna ne."

Baffa ya faɗa cikin dattaƙon sa.

"Haba Alhaji ai ba sai ka zo ba. Ni zan zo na same ka a gobe da safen in sha Allahu."

Amma Baffa ya ce aa shi ya yi niyar zuwa saboda haka ya bar shi kawai ya zo, dole ya amince suna gama waya da Baffa nan take ya tura masa adireshin gidan shi da ke At Unit cikin gari, ya yi zuru shi kaÉ—ai yana tunanin me kuma ya sake faruwa? Amma jikinsa ya ba shi koma me zai kawo surukin Habibu wajen sa to ba zuwan lafiya ba ne, in ko haka ne Habibu ya gama kunyata shi da girman shi.

Bangaren Baffa kuma, da shi da Hamma Jibo suka shirya za su je gidan Alhaji Sheriif da safe Baffa ya ce kar Hamma Jibo ya sanar ma da Ammah komai sai zuwa nan gaba har sua ga abin da zai je ya dawo. Shi ya sa ya yi shuru bai faÉ—a mata ba shima Baffa ko a fuska bai nuna mata wani abu ba, tausayin Ummu ya dame shi
shi ya sa ko a waya ya kasa kiran ta, baya so ya ji muryanta sai ta saka shi kuka.

Ammah ko ba ta san abin da ke faruwa ba, da ta tambayi Nauwara yadda suka baro Ummu sai ta ce tana nan lafiya Hamma Jibo ma haka ya ce mata su Saudat kuma Allah ya sa yan surutun ba sa kusa da ta ce ta ga Anni na kuka kamar Allah ya rufe mata baki ita da Ammi ba su yi surutun ba.

Baffa kwana ya yi bai yi barci ba. Ba kan Ummu farau zawarci ba ya san shi take tsoro, shi ko da ya bar yarsa ta mutu a gidan wanda ba shi da asara gwara duniya ta zage shi , zai ajiye wani fillanci ya tsaya mata. Shi me ye bai gani ba? Nan ƙanwarsa Fatima ta dawo masa da yaro a cikin jinin haihuwa da takardan saki kuma ya karɓeta ya riƙe ta gam, to ba wani sabon abu ba ne in Ummu ta dawo masa da ciki gida, a wannan karon ma godiya zai yi ma Allah ya karba duka kaddaransa, daga karshe da ya gaji da juye juye sai ya tashi ya shiga tiolet ya ɗauro alwala ya yi nafilfilu, tare da addu'o'i ma su yawa akan in har babu alheri a auren Auta da mijinta Allah ya sauƙaƙa mata kaddaranta.

Da Ammah ta farka ta gan shi yana ta salla, sai itama ta mike ta shiga tiolet ta É—auro alwala ta zo ta jera a gefen shi, ta tayar da salla ba su suka koma suka kwanta ba sai wajen uku na dare, asuba na yi Baffa ya ta da Ammah shi kuma ya yi alwala zuwa masallaci.

Nauwara da yara suna bangaren Ammah, Hamma Jibo na can bangaren haraba, Baffa na fita sai ga shi ya fito tare suka fita zuwa masallaci.

Wajen shidda na safe suka dawo tunda sun ɗan tsaya liman ya yi tunatarwa kan riƙo da zumunci da yaƙana ko da suka dawo Nauwara ta share gidan tas ta gyara ɗakin Ammah sannan ta yi ma yaran wanka Amma kuma na kitchen tana sama musu abin ƙaryawa.

Fanke ta soya sai ta dama kunun tsamiya, ta dafa indomie saboda yan biyu da dafaffen ƙwai, kawai sai Ammi ta saka rigiman sai an soya mata ƙwai, Amma ta ce ta yi abin da za ta iya  uwarta ta fito ta soya mata Baffa da Hamma Jibo suna ta dariya Ammah ko ta haɗe rai tana faɗin yara sai iyayin tsiya.

Suna gama karyawa Baffa ya yi wanka shima Hamma tuni ya shirya. Jibi yake so su koma saboda aikin sa shi ya sa yau ya ce Nauwara da yara su shirya su je su gaishe da Ummin ikki, da gidajen su Hamma Abdullahi da Abdulrrahman
har Mubi ya so su je su gaishe da su Ummu Balki, amma ba lokaci watakila sai hutun karshen shekara.

Ammah ta ɗan yi mamakin ganin Baffa da Hamma Jibo za su fita tare amma sai Baffa ya ce mata fitan na shi ne Jibon zai tuƙa sa ne, ba daɗewa za su yi ba sai ta yi musu fatan dawowa lafiya.

Hamma Jibo na fitowa da mota waje Baffa na shirin shiga sai ga Hamma Abdullahi ya kariso a mashin É—in da ya siya, yana da mota amma in ba tafiya mai nisa ba ya fi yawo a mashin.

Mamaki ya kama shi na ganin Baffa sun fita da Hamma Jibo saboda kafin ya kariso da mashin É—in kofar gida har Baffa ya shiga mota sun bar wajen agogon hannun shi ya duba tara ta gota shi kaÉ—ai yana mamakin ina za su je da safen nan haka?
Ya shanye mamakinsa ya ƙarisa cikin gida bayan ya shiga da mashin ɗin sa har haraba.

Tun kafin ma Ammah ta ce masa Baffa baya nan ya ce mata ya gan su za su fita tare da Hamma jibo a ƙofar gida.

"Ammah ina su Baffa za su je ne?

"Bai faÉ—a mini ba Baba "

Da yake yana da sunan mahaifin Baffa shi ya sa Amma ba ta iya faÉ—in sunan shi har gwara ma Baffa yana kiran shi da Abdullahi wani lokacin.

Ta ba shi amsa da harshen fillanci, bai sake tambaya ba, yana cikin falon ne zaune su Saudat na ta yi masa hira yana biye musu Nauwaran ma ta fito sun gaisa Ammah ta ce ai duk yau za ta leƙa gidajensu shi  Abdulrrahman.

"Itama yau take yi mini mganar tana so ta zo su gaisa."

Ya faÉ—a yana kallon Ammah.

"To ai ta yi zaman ta yau Jibon ya ce duk ta leƙa ku."

Sun É—an taba hira ya so ya jira su Baffa ne sai aka kira shi a waya wani abokin shi ya zo gida nemansa sai ya yi ma Ammah sallama da cewa zai tafi.

"Ba za ka jira Baffan ba?

"Amma na yi baƙo a gida. Zan dawo zuwa anjuma da man magana za mu yi kan injinan mu da zan je kwatano na taho da su."

"To ko Nauwara za ta taho ka sauke su tun da gida za ka koma?

Da sauri ya ce" Da mashin na zo Ammah ba da mota ba."
Sai Ammah ta yi shuru, har su Hassan suna rigiman sai sun bi shi.

"To ku jira baban ku wannan uban na ku bai zo da mota ba"

Yara sai suka fara kuka suna sai sun bi Bobo, haka yaran Hamma Jibo ke kiran duka ƙannen ubansu maza.

"Bari kawai Ammah na tafi da su Hassan sauran Mamansu sai ta taho da su."
Chapter 36 · 0% Book details