Sashe 11
Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta shiga kiran ta wacce aka kira da Baraka, da fito da sauri daga wani koridon dake yamma, matashiya ce domin ba za ta wuce 20's ba har gabanta ta ƙariso ta durkusa lokaci ɗaya tana faɗin.
"Barka da fitowa Mami."
"Kin tashi lafiya Baraka?
Ta amsa mata, muryanta da É—an asset na fillanci, lokaci É—aya tana ciro wayarta daga cikin jakar dake gefenta.
"Lafiya lau Mami."
Jinjina kai ta yi kafin ta ce" Kin gama gyara ko'ina ko?
"Na gama Mami, saura na kitchen ne kawai."
"Da kyau Baraka shi ya sa nake son ki saboda zafin naman ki."
Dariya ta yi kanta na ƙasa itama Mamin murmusawa ta yi kafin ta ce" Yau na ga mutumin naki bai yi rigiman tafiya makaranta ba"
"Bai yi ba Mami, na lallashe shi da cewa zan goya sa in ya dawo."
Mami ta yi dariya har haƙoranta suka bayyana farare, da haƙoran makka a bakinta.
"Baraka ina ta ya Faruk kewa ranar da Iya tace a maida ke gida."
Baraka sai ta dukar da kai ba ta yi mgana ba Mami na ta dariya kunya take ji domin an saka ranar auranta karshen shekara nan za su ma yar da ita gida, daga can garin megidanta suka É—auko ta ÆŠan marke, ta fi shekaru biyar tare tasu tun ba ta kai haka girma ba.
Miƙewa ta yi, kafin ta ɗau jakarta Baraka ta yi saurin riga ta ɗauka lokaci ɗaya tana faɗin" Mami ba ki karya ba za ki fita?
"Sai na dawo Baraka."
Sai ta jinjina mata kai, suna tafe har habaran gidan makeke mai cike da motoci ga su nan kala kala sun kai guda biyar, duka na kamfanin Toyota ita ma wata fara ta nufa camry da ita za ta fita yau, jakarta ta karɓa lokaci ɗaya tana cewa.
"Baraka ki kula da gidan sai na dawo."
Sai ta jinjina kai kafin ta ce" To Mami Allah ya dawo dake lafiya."
Lokaci ɗaya tana mai ɗan ramƙwafawa alamun ladabi, tana ƙoƙarin buɗe mota wani matashi ya rugo da gudu ya zo ya buɗe mata.
"Barka da Safiya Mami."
Sai da ta shiga cikin motar ta zauna sannan ta amsa masa.
"Ka tashi lafiya Hamisu?
Ya amsa cikin ladabi kafin ya ce" Lafiya lau Mami.. za a fita ne? Allah ya tsare ki ya sa ki dawo lafiya."
Mami na mirmishi ta amsa kafin ta ce" Ba wata matsala ko Hamisu?
Yana sosa kai ya ce"Hajiya Baraka ba ta ba ni abin karyawa ba goma ta kusa ta san ni mutumin kauye ne da wuri na ke karyawa amma Baraka sai sha biyu na rana take kawo mini abin karyawa fisabillahi fa Mami."
Kafin ya dire maganarsa ya fara sha harara wajen Baraka, Mami tana ta dariya diraman Hamisu da Baraka. Kuma duka daga gari É—aya suke Abban islam ne ya É—auko Hamisu yana kai yara makaranta sai É—an aike-aike da kula da fulawoyin gida.
"In ka matsu sai ka shiga ka dafa."
Baraka ta faÉ—a sannan ta yi tsaki ta kama hanyar komawa cikin gida.
"Mami kina dai jin ta dai ko?
Mami na dariya haƙoranta a waje kafin ta ce" Na ji ta Hamisu ƙyale ta."
Jakarta dake kan kujeran mai zaman banza ta buɗe ta ɗauko masa 5k yan dubu dubu ta miƙa masa ya rankwafa ya karɓa.
"Ka siya wani abu ka ci, ka rabu da ita lokacin da ta kawo maka sai ka ƙara"
Washe baki ya yi kafin ya ce" Na gode Mami, Allah ya tsare gaban ki da bayan ki. Allah ya raya miki yaran ki cikin aminci, yadda kika É—auke mu da mutumci kina saka mana da dukkan alheri ke ma Allah ya saka miki da alheri."
Mami ta amsa da Amin kafin ta ce" To sai na dawo Hamisu."
"A dawo lafiya Mami Allah ya tsare."
Ya rufe mata ƙofar motar ya ruga da gudu wajen Sunusi maigadi, itama sai ta kunna motar ta yi riverse ta dumfari get tana zuwa da man Sunusu ya buɗe mata sai ta tsaya ta ɗan sauke gilashi bangarenta suka gaisa cike da mumtatawa.
"Sunusi ina sane da mganar mu. Jibi Abban islam zai dawo za mu yi mgana da shi in sha Allahu."
Ya jinjina kai kafin ya amsa" Allah ya dawo da shi lafiya Hajiya. Na gode sosai da karamcin ki."
Kai ta gyaÉ—a masa kafin ta ce" Ba komai, sai na dawo"
"Allah ya tsare ki Hajiya."
Ta zuge gilashin sannan ta taka mota ta fice shi kuma ya rufe get É—in ya koma saman farar kujeran da ya tashi kusa da Hamisu suka cigaba da hiran su, kuma duk na yabon kyawawan hallayan Mami ne na kirki.
Sannu sannu tana ta tafiya har zuwa cikin garin kaduna, daga nan ta ɗauke hanyar jami'ar ta Kaduna, Kaduna state University KASU. In da anan take koyarwa a Department ɗin Biology. Har cikin department ɗin su ta shiga da motar ta, ta yi parking ɗin ta in da aka tanada domin parking ɗin motoci, tana ƙoƙarin fitowa daga motar ne ta ji wayarta dake jikin jaka ta ɗan yi ƙara alamun an tura mata saƙo da kamar ba za ta duba ba, saboda ita saƙonni ma sun isheta a waya ba ta dubawa gwara mutum ya kirata da ya yi mata saƙo.
Jakarta ta jawo ta ɗauko wayar na ta iphone 14 ce, tana dannawa haske ya kawo sai ta ga saƙo ne daga My First Daughter, sai da ta murmusa ta manta yau Jumma'a da man ƙa'ida ne duk ranar irin ta yau Ummu Salma tana tura mata saƙon barka da Jumma'a kuma tana jin daɗi sosai.
"Barka da Jumma'a Mami na. Allah ya tsare ki da tsarewarsa. Allah ya ba ki abin da kike nema duniya da lahira. Ubangiji ya yi ma rayuwarki albarka. Happy Jumma'at mubarak."
 Â
Har ta gama karantawa da mirmishi a saman fuskarta, latsa lambar Ummu ta yi, jiya da daddare ta so kiranta sai ta sha'afa gwara ta kira ta yanzu kar ta sake mantawa.
Ringing É—aya zuwa biyu Ummu-Salma daga can garin Jemeta ta É—aga kiran.
"Mami na"
Ta faÉ—a daga can bangaren cikin murna da bayyana har a muryanta.
"Naam Daughter kuna lafiya?
Ummu ta amsa mata, suka gaisa daga can bangaren Ummu ta ce" Mami na ina su Islam?
"Suna makaranta."
"Yaushe za su zo?
"Sai sun samu hutu za mu taho gabaÉ—aya Daughter."
Daga can bangaren Ummu ta yi tsalle kafin ta ce" Mami na da man na yi kewar ki."
"Nima na yi kewar É—iya ta."
Habib ta tambaye ta sai ta amsa mata da cewa ya tafi wajen aiki.
"Ki gaishe mini da shi."
"In sha Allahu Mami na."
"Daughter na siya miki kayan measurement É—in fulawa, har spicess na kayan girki suna nan in zan taho zan taho miki da su in sha Allahu."
"Na gode Mami na. Allah ya saka miki da alheri."
Ta faÉ—a muryanta cike da murna, Mami ta amsa da Amin kafin ta ce" Take care na shigo cikin makaranta ne
"To Mami Allah ya ba ki sa'a."
Daga nan suka yi sallama.
Tana shirin mai da wayar cikin jaka ne, sai kuma ta fasa saboda wajen messages ɗin ta 99 ta gani alamun tana da saƙonni da yawa nufinta ta shiga ta yi delete all, duk MTN ne sai na bankun nan ta, amma sai me tana shiga sai ta bige da ɗan dubawa, tana ɗan jan ƙasa ta ga wata lamba ta turo mata saƙo, yanayin lambar ne ya sa dole ta shiga saƙon domin special number ce.
"Za a yi auran É—iyarki Batula. Ko ba ki zo dan ni ba ki zo don LamiÉ—o, in shi ma ba za ki zo domin shi ba to ki zo domin gudan jinin da Allah ya haÉ—a a tsakanina da ke. "
Na farko kenan na biyu kuma cewa aka yi.
"Tun da ba za ki samu zuwa ba Batula ba, ko yaran mu ki bar su su zo don Allah Batula."
Ko bai saka sunan shi ba, ko bai ambaci wata magana da za ta nuna shi ɗin ba ne, to shi ne domin nan duniya mutum ɗaya ne ke kiranta Batula ko Baffa Fatima ya ke kiranta, tuni fara'an dake saman fuskarta ya gushe cikin lokaci ƙalilan fuskarta ta sauya ta yi wani ja saboda bacin rai.
Hannunta na rawa ta goge saƙon gabaɗaya daga wayarta. Tana mamakin yadda aka yi ya same ta? Ita dai ta san ta rufe duka layukan da ya ke kiran ta da su, sai daga baya ta duba sai ta fahimci ya sauya wata lambar ne me ya rage tsakanin su? Ɗan shi ne kuma ba ya tare da ita, yana tare da shi me ya sa ita ba zai ƙyale ta ba? Ta ce ta yafe masa amma ba za ta bari mu'amalan wai Uba da uwa ta haɗa su ba. Tana da miji shima yana da matan shi, ɗan shi kuma ya san in da yake ba to bini-binin na mene ne? Ita fa har abada ba za ta yi wani aminci da su ba, babu sauran wani aminci har abada atsakanin su.
 Sai yanzu ne ya san da gudun jinin da ya haɗa su? Sai yanzu? Ai lokaci ya kure musu, kurewan da ba za su iya gyara abin da suka lalata shi sama da shekaru talatin ba. Sai yanzu ne Fargar jaji ya kama su? Ba su da sauran abin da za su iya yi a yanzu, gabɗaya ta rasa natsuwarta in ta fita a haka ma ta je aji ɗalibai za su fahimci yanayin ta ba daɗi shi ya sa ta yi zamanta cikin mota tana faman sauke ajiyar zuciya.