Sashe 15
Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bayan sun gama wayar Data ta buÉ—e ta shiga tiktok tana kallon girke-girke akan account É—in Maryama Kitchen. Duk yadda ta ke son abin da ya shafi girki, in tana kallo ma wani nishaÉ—i take ji amma yau kwata-kwata ba wannan nishaÉ—in sai ta ji ma komai ya fita daga kanta kawai sai ta kashe datan, saboda kar ta zauna shuru ya sa ta fara duba contact É—in ta. Lambobin da ba su da amfani take bi tana faman gogewa domin wasu lambobin ma sai su shekara ba su yi waya ba. Wasu ma duk sun daina amfani da layukan.
Lokacin da ta iso jerin sunayen Yayyenta da ko wanne ta yi masa saving da Hamma sannan da sunan mutum a gaba. Tsayawa ta yi tana kallo Hamma Mustapha ne suka ɗan jima ba su yi mgana ba. Kuma yana da ƙoƙarin kiranta lokaci bayan lokaci, ba za ta iya tuna last da suka yi waya da shi ba. Ita kuma ta sha'afa ganin bai kira ta ba, kuma ita ba ta kira shi ta gaishe shi. An ce ka gaida mai gaishe ka duk cikin yayyenta ta fi son Hamma Mustapha yana da sauƙin kai da sanyin hali ga haƙuri da kawaici hallayan Baffa kaɗan ne bai deɓo ba.
 Yana da son ƴan'uwan shi sosai, saɓanin irin su Hamma Kabiru da bashi da kula kwata-kwata, duk a cikin su Hamma Mustpaha ne da Hamma Jibo suke ji da ita, to sai gwara ma Hamma Abdulrrahaman, shi Hamma Abdullahi in ya gan ka dai zai yi murnan ganin ka amma don bai gan ka baa zai damu da neman ka ba. Kar su Hamma Kabiru su ji labari, shi a motor ɗin shi cewa yake yi in ka ji shuru lafiya ne. Baya neman mutane in kuma ya gan ka ba zai yi murna ba in ma bai gan ka ba zai damu ba kuma ba zai tambaya ba. Shi ya sa Ummu ta sha faɗin cewa suna da kamanceceniyar halayya da Hamma Lamiɗo, wataƙila saboda tare suka yi wasan ƙasa suka kuma girma tare shi ya sa wasu hallayan na su marasa kyau suke kamanceceniya da juna.
 Hamma Mustapha ta latsa ma kira, ringing ɗaya ana biyu ya danna mata busy, ta sani da man ba ya ɗaga kiranta. Shi zai kashe sannan ya kira ta. Cikin minti ɗaya sai ga shi ya biyo bayan kiran da sauri ta ɗauka cikin zumuɗi.
"Hamma ka manta da ni "
Ta faɗa cikin yar shagwaɓa kamar za ta yi masa kuka.
Daga can bangaren ya yi dariya har tana fidda sauti.
"Wane Hamma ya manta da Autan Ammah. Kina raina ayyuka ne suka yi mini waya a kwanaki nan. Kina lafiya?
Ya faɗa daga ƙarshe yana sirka mganar shi da yaren fillanci.
Ta amsa mishi itama cikin harshen fillancin, sun gaisa cikin fara'a da tambayan iyalan shi, da ya ke shi Gombe yake aiki can ya ke zaune da iyalansa.
"Ina Adda Aisha? Ina su Mahma da Baffan mu?
Duk ya ce sun yi barci saboda makaranta gobe Adda Aisha yanzu ta bar É—akin sa.
"Ka gaishe mini da ita sosai."
"Zan faÉ—a mata Autan Ammah. Ya wajen megidan na ki?
Tana shafa cikinta cikin mirmishi ta ce" Duk muna nan lafiya Hamma. Yaushe za ka zo?
Sai da ya yi tunani kafin ya ce.
"Kin san ga aiki sannan yara suna makaranta itama Aisha tana makaranta ko?
"E na sani Hamma."
"To sai mun samu hutu za mu zo mu yi ko sati É—aya ne in sha Allahu."
Cikin murna ta ce" Allah ya kawo ku lafiya Hamma."
Ya amsa da Amin.
"Ba dai wata matsala ko?
Ya tambaya sai ta amsa mishi da babu wata matsala ya É—auka za ta yi masa sallama ne tun da dare ya yi sai ya ga ta fara zaro wata hiran.
"Auta dare ya yi, kar ki bar megidan na ki shi kaÉ—ai."
Sai ta kasa mgana, jiki a sanyaye suka yi sallama in ta ce Habib bai dawo ba zai saka ayar tambaya, ko ba ma haka bai kamata ta faÉ—a mishi wani abu ba, yau dai zumumci take jin yi wayar Hamma Jibo ta kira shi, shi dai ba ta same shi ba Adda Nauwara ta É—auka ta ce ya shiga wanka.
"Ummu yanzu da daren nan? Ko kewar mu kike ji ne?
Nauwara ta faɗa tana dariya, sai Ummu ta rufe fuska kamar tana ganinta itama tana dariyan, yara ta tambaya itama ta ce duk sun kwanta dare ya yi, suna ta hira da Nauwara har Hamma Jibon ya fito ya karɓa shima suna gaisawa sai da ya ce.
"Autan Baffa ko akwai damuwa ne?
"Ba komai Hamma kawai na kira ka ne na gaishe ka."
"To na gode. Ki kwanta kin ga dare ya yi, da safe za mu yi waya."
Da haka shima ya sallame ta, sai bayan sun gama wayar ne ta ga Hamma Mustapha ya tura mata 10k, duk da ya san ba ta buƙatar komai amma shi mai kyauta ne da alheri shi kafin ta yi kukan wani abu ya ba ta saƙon godiya ta tura masa da addu'an Allah ya sa ya gama da duniya lafiya.
lambar Hamma Abdulrahim ta gani shi da ya ke ba ya ƙasar sai dai in shi ya kira ka ko da yaushe wayarsa ba ta shiga. Amma suna mgana a chart sosai har Vadeo call suna yi wani lokaci in karatu ya yi musu sauƙi tana kewar shi ko bikinta bai samu zuwa ba ya fi shekara rabon shi da zuwa gida amman ya ce ya kusa kamallawa gabaɗaya shi ya sa zai jima a can kafin ya dawo gida.
Da har ta wuce lambar Hamma Kabiru, sai ta dawo bari dai ta kira shi, ko ba komai ɗan'uwanta ne kuma ba za ta biye ma halin shi ba, in ta duba ma ai akwai jininsa roba biyu a cikin jikinta. Sai ta latsa masa kira har ta katse bai ɗauka ba taɓe baki ta yi a cikin ranta ta ce ka huta.
Agogon wayarta ta sake kallo sha É—aya har da mintina ta gota. Tagumi ta sake yi cikin bugawar zuciya sake kiran lambar Habib ta yi amma ba ta shiga ba.
Niyyarta ta kira ko ƙaninsa Maharazu acan gida ta ji ko yana gida ne tana cikin neman lambar ne kiran Hamma Kabiru ya shigo mata sai ta ɗauka.
A ginshiƙe ya yi mata sallama da muryan nan ta shi a cunkushe kamar mara lafiya ta amsa ita ta fara gaishe shi ya amsa da lafiya jin ya yi shuru itama sai ta yi shuru sai ta rasa ma abin da za ta ce masa, ba wani shaƙuwa sosai a tsakanin ta da shi ba kamar sauran yayyen nata.
"Mene ne haka, na zo na ga kiran ki ba na kusa. Na zo na gani na kira kuma kin yi shuru."
Tana so ta yi magana kamar an É—inke mata baki ta kasa.
"Ke in ba ki da abin cewa zan kashe wayata. Kin san aikin da na katse ne na kira ki?
Ya faɗa cikin faɗa shi da man ko mganar arziƙi ce ta faɗa ce a wajen shi.
"Hamma."
Ta faÉ—a a sanyaye tana jin hawaye suna cika kwarmin idanuwanta.
"Me ya faru?
Ya faɗa a hankali jin muryanta ta yi sanyi alamun kamar za ta yi kuka, duk da ya san Ummu da shagwaɓan tsiya sai dai ganin dare ya yi yasa ya yi tunanin ba lafiya.
"Ki yi mgana mana."
Ya faÉ—a da karfi.
"Hamma."
Ta sake kiran shi a raunane lokaci É—aya hawaye na zubo mata muryansa kawai da ta ji sai ta ji wani irin abu ya sauko mata mai kama da rauni, sai ta ke jin kamar ta yi tsuntsuwa ta ganta a gaban shi kawai shi take son gani domin ta fi wata uku ba ta saka shi a idanuwanta ba, tunda shima a Jalingo ya ke aiki can ya ke zaune da iyalansa yana zuwa amma ita tana gidan ta in dai ba hutu suka zo shi da iyalansa ba ba ta samun ganin shi.
"Lafiya wai kike ta kiran sunana kuma ƙin ki mgana."
Hawayenta ta yi saurin sharewa.
"Mijin naki ne ya yi miki wani abu?
Ya faÉ—a kai tsaye domin shi abin da zuciyarshi ta kitsa masa kenan.
"Aa Hamma."
"To A'a me ye? Ke ba na son fa shanshanci in ba ki da abin faÉ—a zan kashe waya ta ina da abun yi."
Jin abin da ya ce ne ya sa cikin yar shagwaɓa ta ce" Hamma na kira ne fa na gaishe ka "
"Ƙarya ne"
Ya faÉ—a kai tsaye.
"Wallahi Hamma."
"Gaisuwan ne sai da daddare za ki kira ni Ummu?
Kanta ta sosa kafin ta ce" Ni ban ma lura da dare ya yi haka ba Hamma."
Kai ya jinjina kamar tana ganin shi kafin ya ce" Ko dai ba ki da kuÉ—i ne? Kin talauce ne?
"Kai Hamma."
Ta faÉ—a tana rufe bakinta.
"To ni dai ba saba kira na ki gaishe ni kika yi ba Ummu Salma."
Ya faÉ—a kai tsaye saboda haka É—in ne suna daÉ—ewa ba su yi mgana ta waya ba.
"Ina kiran ka mana Hamma."
"Ba na son ƙarya kina dai kiran su Mustapha amma ba ni ba. Ko da ya ke kin ce kin fi son su ni ina da mugun hali irin na Lamiɗo ko?
Ummu ta rasa in da za ta saka kanta saboda kunya da nauyi. Ashe ya ji wannan mganar? Amma abin mamaki wa ya faÉ—a masa?.
"Kin yi shuru ko ba haka na ji kina faÉ—a ma BaÉ—É—o ba."
Tabbas an yi haka tun kafin ta yi aure ne. Suka taɓa hiran a ɗakin Ammah ne su ba su taɓa sanin ya ji ba in ba za ta manta ba yana garin lokacin wataƙila ya zo shigowa ɗakin Ammah ne ya ji suna hiran
"Duk mugun hali na ina da kirki Ummu. LamiÉ—o ma don ba ki zauna da shi ba ne he is a nice person."