← Book details Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 92

Sashe 58

Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Koda Baɗɗo ta koma gida saboda makaranta tana yawan leƙewa duba Ummu Salma, wata rana ma in ta yi dare nan take kwana da safe ta wuce makarantan daga nan haka ma Ummin ikki koda yaushe tana kan hanyar zuwa domin duba Ummu, kuma in dai ta zo sai ta zaunar da ita tana yi mata nasihan haƙuri da ɗaukan kaddara zuwa lokacin tuni Ummu Salma ta yarda da kaddaran Habib ya sake ta amma ta kasa gasgasta kaddaran cewa ya rabu da ita har abada, gani take yi zai zo gare ta ko da take gida zai dawo gare ta, ta kasa ba ma zuciyarta hakuri da fahimtar cewa Habib ya yi mata nisa har lokacin ba ta sare ba, saboda tana son shi duk abubuwan nan da suka faru ba ta jin haushin shi sai ma soyayarsa dake sake kassara tunaninta kuma ko yanzu ya dawo gare ta, za ta iya yin komai domin itama ta koma gare shi. Habib kaɗai ta sani shi ne fa Duniyarta ya za a yi ta fara yin wata sabuwar rayuwar da ba shi a cikin ta. Gaskiyan da Ummu Salma ta kasa karɓa kenan gani take yi ba ta da wani sauran jin daɗi kuma tunda dai ba tare da Habib, ta lamkaya jin daɗin ta da samun komai na duniya a lokacin da take Matar Habib ba a yanzu da ta ƙare ba ta da komai ba.

Tafiyar Mami da kwana goma sai ga Shamsiya afufujan tana kuka wiwi tana faÉ—in ita ba ta san abin da ke faruwa ba kenan ta yi tafiya zuwa Taraba gidan Sister É—in ta, tun a can take faman kiran wayar Ummu a kashe kuma ba ta ganin ta a chart hankalinta ya tashi shi ne fa ta kira BaÉ—É—o ita ke faÉ—a mata wannan mugun labarin mara daÉ—i.

"Bestie Habib ya sake ni."

Ummu ta faÉ—a hawaye suna kece mata.
"Ya sake ni Bestie."
Ta sake faÉ—a tana mai kwantar da kanta saman cinyar Shamsiya dake zaune a saman gadon É—akin da Ummu Salma take.

"Na yi komai domin na tsira da aurena amma na kasa Bestie. Na kasa na faÉ—i.."

Take faÉ—a tana wani irin gunjin kuka Shamsiya na É—an bubbuga bayanta alamun lallashi take faÉ—in" Sai da na ce ki bi umarninsa Bestie amma kika yi taurin kai, da a ce kin zubar da cikin da yanzu kina gidan mijin ki, da yanzu ba ki zauna kina kukan nadama da dana sani ba."
Take faÉ—a tana sharan kwalla itama, amma ba ta fasa faÉ—a ma Ummu ita ce ke da laifi ba, ita ba ta ganin laifin Habib a wannan maganar.

"Bestie su fa iyayenmu tunanin su da namu ba É—aya ba ne. Ban so ki kawo maganar gida ba, da kawai kin bi umarninsa kin zubar da cikin da yau duk ba a yi haka ba. Da kina can gidan mijin ki ba wanda ya san abin da ya faru."

"Besite ko na zubar da cikin nan ko ban zubar ba Habib ya gama samun duk abin da yake so a wajena. Ba zai É—aga mini kafa ba sai ya sake ni, da man kawai cikin ya zo a gabar da ya fake da dalilin shi ne, amma ba ya so na ya ma faÉ—a mini da bakin shi."
Ummu ta faÉ—a tana cigaba da kukanta.

"Ni fa ban yarda Habib ba ya son ki ba Bestie kawai kin ɓata masa rai ne da kuma shigowar su Baffa cikin maganar, amma ke kanki kin san cewa Habib na son ki Bestie."
Shuru kawai Ummu ta yi mata, ba za ta gane ba ne, amma tunda har ita ta furta mata cewa Habib ba ya sonta to ai ya kamata ta yarda da ita. Itama da fari ba ta gasgasta ba amma daga baya da abubuwa suka yi ta faruwa dole ta aminta ta kuma gasgasta cewa Habib ba ya sonta , sannan saboda jikinta ya aureta kuma tun da ya gama biyan bukatar shi ai ba ta da wani amfani a wajen shi kamar yadda ta faÉ—a.

"Shima ya yi kuskure me ya sa ya yi saki uku? Ai da ya yi É—aya ne in iyaye suka shiga ciki sai a gyara lamarin. Ni fa har kiran shi na yi ta yi bai amsa kirana ba daga karshe ma kamar ya rufe ni ne kwata-kwata bana samun shi."

Ta faɗa tana kallon Ummu Salma wacce ta miƙe daga kwancen da take, tana kallon Shamsiya da mamakin maganganun ta.
Ta buÉ—e baki za ta yi magana kenan Shamsiya ta katse ta.

"Ban ji dadin faruwan wannan lamarin ba Bestie. Na yi miki kaico domin da wahala ki samu kamar Habib. Ba ma tamtama ba za ki taɓa samun kamar sa ba har Abada Ummu Salma."

"Za ta samu, za ta samu wanda ya fi shi komai da komai in sha Allahu."
Suka ji magana a bayansu, suna juyawa gabaɗayansu suka ga Ammah ta shigo da kulan abinci ba da niyyar laɓe ba ne, amma ta daɗe tsaye a kofar ɗakin tana jin irin maganganun da Shamsiyan ke faɗi.

"Ammah."

Shamsiyan ta faÉ—a lokaci É—aya tana saukowa daga saman gadon. Kulan abincin hannun Ammah ta amsa tana faÉ—in" Sannu da aiki Ammah."
Ta sakar mata lokaci É—aya tana cewa" Yauwa."
Sai kuma ta kalli Shamsiya da take sauke kulan a saman side drower É—in gadon tana mai É—agowa, Ummu Salma ta kalla ita kuma tana ta kuka har da sauti.

"Shamsiya."

Ammah ta kira sunanta sai ta É—ago tana amswa cikin ladabi.

"Don Allah ki daina tuna ma Auta da wani Habibu. Ba shi da wata amfani yanzu a sabuwar rayuwarta. A matsayin ki na ƙawarta ki lallasheta ne ba wai ki zaunar da ita kina nuna mata kamar ta ci baya ba. Habibu da man bai cancanta da zamowa abokin rayuwar Auta ba, kaddara ce ta aura mata shi kuma yanzu ta raba su. Ina mai baki tabbacin shi ne ya yi asara shi ne kuma har abada ba zai taɓa samun madadin ta ba, amma a gare ta za ta samu ire-iren su masu tarin yawan da sai ta zaɓa ma, kuma ni na faɗa miki Ummu Salma za ta sake yin farinciki fiye da irin farincikin da ta yi a farkon rayuwarta da Habibu."

Ammah ta gama faÉ—a tana mai kallon Shamsiya, ta ma É—an kausasa maganganunta, amma har cewar da ta yi da Ummu Salma ta bi umarninsa ta zubar da ciki duk ta ji, kamar a mganganunta ita ba laifin Habibu take gani ba, laifin Ummu ne ita da su iyayenta. Ai ko ba ta san Ummu bai kamata ta faÉ—i haka ba, ballanta Ummun ce silan da ya sa ta ma san Habibun gabaÉ—aya.

"Haka ne, in sha Alkahu Ammah ba zan sake tayar mata da maganarsa ba."
Shamsiya ta faɗa kanta na ƙasa cikin jin nauyin Ammah.

"Yauwa na gode da kika fahimce ni, ga abinci nan bari na kawo muku farantai da ruwa."

Tana gama faɗin haka ta juya har za ta fita sai kuma ta sake juyowa tana kallon Shamsiya. Duk da suke ƙawance da Autar ta ba ta taɓa jin ba ta natsu da ita ba sai yau, haka kurum yau sai ta ji maganganunta sun bambamta da yanayinta.

"Maganar zubar da ciki kuma."

Sai ta dakata tana kallon Shamsiya da ta yi tsuru tsuru.
Ummu ma ta daina kuka tana kallon Ammah ta san halin ta ba ta É—aukan wani reni ko sakarci ko waye kuwa sai ta faÉ—a masa gaskiya ita kanta ta ji maganganun Bestie yau sun É—an yi tsauri amma ba ta ga laifinta ba yanayi ne da tsarin gidan da ta taso kowa abin da ya ga dama yake yi babu takura.

"Na jinjina ma Auta da ta yi wannan jarumtar. Har yau mu iyayenta ba ma cikin nadaman dawo mana gida da ta yi da ciki a jikinta. Tunda dai cikin  kowa ya san uban shi to ai an gama magana. Da Ummu Salma ta tashi a ranar lahira cikin waɗanda Allah zai tuhuma da kashe rai gwara ta mutu wajen haihuwa a tashe ta a matsayin shahidiya."
Ammah na gama faÉ—in haka ta fice daga É—akin ta bar Shamsiya da ajiyar zuciya.

"Kamar Ammah ba ta fahimce ni ba Bestie"
Ta faÉ—a lokaci É—aya tana zama a gefen gadon tana kuma kallon Ummu Salma.
"Ki yi hakuri. Watakila ba ta fahimci maganarki ba ne"
Ummu ta faÉ—a cikin wani irin amon mai sauti mai cike da rauni.

Sai Shamsiya ta yi mirmishi kafin ta ce" Ba damuwa. Na san anan gaba za ta fahimci in da maganganuna suka dosa."
Ta faɗa  tana sake kallon Ummu cikin mirmishin da ya kasa ɓacewa a saman fuskarta
Sai ga Ammah ta dawo É—akin É—auke da filet da cokula guda biyu sai ruwan gora guda biyu ta kawo ta ajiye tana faÉ—in Shamsiya ta sauko ta zuba musu.

"Sannan ki matsa ma ƙawar ta ki ta ci abinci."

"To Ammah."

Ta faɗa cikin ladabi, kuma ta yi abin da ta saka ta,ta matsa ma Ummu ta ci abinci taliya da miyar jajjage ne. Ummu ta ji daɗin taliyan nan saboda miyan na ta ƙamshin kayan kamshi ta kuma soyu sosai, ga cikin ta ya cika amma bakin ta bai daina son ci ba sai ta koma tana lasan miyan saboda ta yi mata daɗi a bakin ta.

"Bestie ki bar lasan miyan nan kar ki yi amai ko cikin ki ya lalace fa."
Shamsiya ta faÉ—a tana kallon Ummu Salma na ta lasan miya
"Bar ni na sha, na ji daÉ—inta ne sosai "
Jin haka yasa sai ta ƙyale ta, sai da ta shanye duka miyan da ta rage kuma Allah ya taimake ta, ba ta yi amai ba.

Shamsiya na gidan har yamma sai gabda kiran mangariba ta tafi lokacin Baffa ya dawo tun safe daman suka fita da Abdullahi har ɗaki Ummu ta kai Shamsiya ta duƙa ta gaishe shi.

"Lafiya lau Shamsiya, ya kwana biyu ya makaranta?
Ta amsa da lafiya lau mahaifinta ya tambaya Dr. Nura babban ma'aikaci ne a minitary of Education na Jahar Adamawa.
"Ashe kuma abin da ya faru da ƙawata kenan?
"Wallahi Kuwa Shamsiya "
Baffa ya ba ta amsa.
Chapter 58 · 0% Book details