Sashe 23
Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
 Baɗɗo kuma kukan tausayin Ummu take yi. Tausayi mai yawa ganin irin halin da take ciki, gani ta ke yi kamar a mafarki ba domin Ummu ce da kanta ta e faɗa mata wannan labarin ba sai ta ƙarya ta ko ma waye, Habib ne fa? Ba ta taɓa tunanin zai iya aikata haka ba, ba ta taɓa tunanin Habib jahili ba ne mara ilimi sai da Ummu ke ba ta labarin shi.
"Ya zan yi? Na rasa yadda zan yi BaÉ—É—o gani na ke yi kamar a mafarki, gani na ke yi kamar ba Habib ba ne."
Ummu Ta sake faɗa tana gunjin kuka kanta a saman cinyar Baɗɗo ya yin da ita kuma take shafa kitson da ke kanta alamun lallashi amma ita ma kukan take yi, hawaye sun kasa tsaya mata saboda tausayin halin da Ummu take ciki? Lalle ta ƙara sarewa da lamarin mazan wannan zamanin masu sauya launi a duk lokacin da suka ga dama, za su kuma iya juya rayuwar wanda ya yarda da su daga sama zuwa ƙasa.
"Ya ce ba ya sona sannan ba ya son haɗa zuru'a da ni. Ƙarya yake yi ko? Ke ma ai kin shaida irin son da ya ke yi mini ko Baɗɗo?
Ta sake faɗa cikin kuka tana mai riƙo hannayen Baɗdo a cikin nata. Baɗɗo ta kalli Ummu kafin ta share hawayenta duk da ta fahimci Ummu na son Habib ba za ta fasa faɗa mata gaskiyan da soyayyarsa ta rufe mata idon da ta kasa fahimtar manufarsa ba.
"Ummu-Salma ta so nan ki saurare ni ki ji."
Ta faɗa lokaci ɗaya tana taimaka mata ta tashi zaune suna fuskantar juna hannayenta Baɗɗo ta riƙe duka biyun kafin ta sake kiran sunan ta.
"Ummu-Salma."
Ta amsa mata cikin shaƙewar murya saboda kuka.
"Ki kalli gaskiyan dake gaban ki. Da gaske ne duk abin da Habib ya faɗa, domin wanda ke son ka shi ke ƙaunar haɗa zuru'a da kai, kin ce ya faɗa miki da bakin shi sannan ya yi ƙokarin aikata hakan a aikace, kin ga kenan zaman ki tare da shi ma hatsari ne, tun da ya sha alwashi zai iya miki lahani domin ya ga ya cimma burin shi."
Ta ƙarishe faɗa cikin ƙura ma Ummu ido tana so ta ga yadda ta ƙarɓi mganar, tun da ta ce mata tana cikin halin wannan laulayin amma bai damu da ita ba, shi dai burin sa ta zubar da cikin jikinta da kuma yadda ta faɗa mata matakan da ya bi domin ganin ya cimma manufarsa ta tsoraci Habib da lamarinsa ta kuma tabbatar da yadda yake son cimma burinsa zai iya komai in ta ce komai tana nufin komai domin ya ga cikin jikin Ummu ya fita ko da ita za ta shiga haɗari ne.
"Ya zan yi.! Ina son cikina BaÉ—É—o sannan ina son Habib."
Baɗɗo ta taɗe tana kallon ta kafin ta ce" Ni ma ban ba ki goyon bayan ki zubar da cikin nan ba domin ba ki sani ba ko shi ne kaɗai ƙwan ki a duniya ba. Shi ma jahilci ne da rashin tunani sannan da manufarsa ta auran ki, mganar kina son shi duk ki cire shi Ummu tunda da bakin ki kika faɗa mini ya ce shi bai taɓa son ki ba, sannan bai aure ki domin haihuwa ba."
"Habib ne fa BaÉ—É—o. Habib na sona ke ma kin sani?
Ummu ta katse ta cikin kuka hawaye sun kece mata da ƙarfi kuma tana yin kukan mai fidda sauti. Baɗɗo ta yi mata uziri domin ko ita tantaman Habib ta ke yi, in ta yi nazari duba da tun daga lokacin da suka haɗu da Ummu da irin soyayya da ƙauna da tattali da ya nuna mata suma saboda ita duk ya ƙaunace su, ita kanta ba domin Ummu ce da kanta ta ga zahirin Habib ba za ta iya ƙaryata wannan labarin, Ummu na cikin damuwa ta kasa gasgasta Habib ne zai yi mata haka? Tunani ta ke yi kamar ba zai iya nuna haka ba saboda ya gurɓata rayuwarta cikin so da ƙaunarsa tare da kuma Aminta da shi.
"Mun sani a baya yana son ki ayadda ya nuna mana a aikace Ummu. Yanzu kuma ya fito da zahirin manufarsa a kan ki."
BaÉ—É—o ta sake faÉ—a tana jijjiga hannayen Ummu dake cikin na ta.
"To ya san ba ya sona me ya sa ya zo ya nuna mini so da ƙauna har ya aure ni?
"To wannan kuma manufarsa ce tun da bai faɗa ba, ba za mu iya yanke masa hukunci ba. Amma duk namijin da ya ce ya aure ka ba domin yana son ka ba sannan ya nuna ba zai iya haɗa zuru'a da kai ba to dalili biyu ne, na farko ko ya yi auran fansa dake domin rama wani abu da kika yi masa na biyu kuma ko ya yi auren sha'awa da ke Ummu."
Ummu ta ƙura ma Baɗɗo ido tana mai tsiyayan hawaye. Ta fi amin ta da auran sha'awan da Baɗɗo ta ce in ta yi duba da yadda Habib ya tsara zamantakewar su ta aure, yadda ya mai da abin cin tuwo ba dare ba rana ko ba ta da lafiya bai damu ba sai ya aikata abin da yake so da ita.
"Ni na fi tunanin auren sha'awa ya yi dake Ummu."
Baɗɗo ta faɗa hawaye na sake kece mata Ummu ma ta sake fashewa da kuka suka sake curewa waje ɗaya suna kuka kamar wasu ƙananun yara. Baɗɗo ce ta fara haƙura da kukan ta koma tana mai lallashin Ummu da kalaman ban haƙuri da cewa ta yi hakuri Allah na sama kuma yana sane da ita zai saka mata.
"Ya zan yi BaÉ—É—o? Zuciyata zafi take yi ji na ke yi kamar na rasa komai a duniya"
Ummu ta faÉ—a muryanta ma ba ta fita saboda dishewar da ta yi.
BaÉ—É—o ta sake share hawayen ta kafin ta ce" Kina da yadda za ki yi ko Ummu, kuma ke ce kike da kowa. Wannan mganar ba shuru za ki yi ba dole ne su Baffa sun san abin da ke faruwa"
Da sauri Ummu ta waro jajayen idanuwanta tana kallon BaÉ—É—o jin ta ambaci su Baffa in mgana ta kai wajen su Baffa ai shike nan kuma.
"E dole su sani saboda mgana ce da ta wuce tsakanin ku. Neman fa cikar burin sa ya ke yi saboda haka zai iya yin komai saboda haka. A dalilin haka ma zai iya yi miki illa Ummu."
Kai Ummu ta ke girgizawa lokaci É—aya tana faÉ—in" Habib ba zai iya cutar da ni ba. Ba zai iya ba."
Baɗɗo ta yi kasaƙe tana kallon ta kafin ta ce" Nima na yi tunanin haka a baya. Amma yanzu kam ban yarda da shi ba. Ke da kan ki kika ce ya saka miki mganin da zai lalata cikin jikin ki har sau biyu a lemu bai yi nasara ba, na ƙarshen ma kin ce da karfin tsiya ya so ya yi miki ɗure, kina da tabbacin maganin ba zai yi miki lahani ba ke a karan kanki bayan cikin dake jikin ki? Ko kina da tabbacin ke ɗin za ki tsira?
Sai jikin Ummu ya yi sanyi ta koma ta yi lakwas tana tsiyayan hawaye.
"To kin gani dole iyaye su shiga ciki Sisna, in sha Allahu komai zai daidai ta."
Ta faÉ—a tana mai share mata hawaye da hannayenta duka biyu.
"Ina tsoro, ina tsoron kar su Baffa su ji wannan abun su raba ni da Habib."
Ummu ta sake faɗa da har sai da Baɗdo ta ji kamar ta sake fashewa da kuka saboda tausayin Ummu, wata kila ya yi kusa zuciyarta ta aminta da cewa Habib ba masoyin ƙwarai ba ne a gare ta, ba yanzu za ta tantance girman yaudaran da ya yi mata ba wataƙila sai anan gaba.
"Ba raba ki da shi za su yi ba. A matsayin su na iyaye za su shiga su gyara ta in da aka samu ɓaraka ne"
Ummu ta jinjina kai kafin ta ce" Ba yanzu zan sanar da su ba BaÉ—É—o "
"To sai yaushe?
Ta tambaaye ta cikin mamaki."
"Mu sake ba ma Habib lokaci. Wataƙila wasa ya ke yi, wataƙila yana gwada ni ne ya gani."
Kallon ba ki da hankali Baɗɗo ke yi mata ta ma kasa mgana saboda mamaki, mutumin da a cikin idanuwan ki ya ce ba ya son ki ba domin ki haihu ya aure ki ba, sannan ya yi ƙokarin lalata cikin jikin ki da karfin tsiya amma har a yanzu kare shi Ummu ke yi! Tana tunanin wai wasa Habib ya ke yi?
"Kin ga kar mu yi gaggawan sanar ma gida, in ya zo muka daidaita fa ?
BaÉ—É—o ta kasa mgana saboda ta rasa ma abin cewa saboda tausayin Ummu da mamakin ta.
"Kin ji? Mu sake ba shi lokaci na yi miki alƙawarin in bai sauya ba da kaina zan je gida na faɗa ma Baffa duk abin da ke faruwa."
BaÉ—É—o ba ta da cewa tun da Ummu na ta mata magiyan kar ta faÉ—a ma kowa, ita da kanta za ta je ta faÉ—a ma su Baffa in har Habib bai sauka daga kan gudirin shi ba.
"Na ji ba zan faɗa ma kowa ba. Sai dai ina tunanin yadda za ki cigaba da rayuwa a haka da shi, ina tsoron kar ya sake yunƙurin cimma burin sa ya yi miki lahani wata rana."
"Allah ba zai ba shi sa'a ba"
Tunda ta ce Allah sai jikin BaÉ—É—o ya yi sanyi amma jikinta da zuciyarta suna cike da tausayin Ummu ne, ganin yadda ta koma duk ta lalace sannan daga ganin ta, tana bukatar ma ganin likita. Ummu ta faÉ—a mata magungunar da aka rubuta mata a asibiti Habib bai siya ba sannan ga yanayin da take kwana tana ta shi a ciki.
"Gaskiya ya kama ta mu je asibiti."