← Book details Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 92

Sashe 55

Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ranar Jumma'a da Safe Baɗɗo da Ummin ikki da Hamma Abdullahi suka kai Ummu Salma asibiti Boshin clinic in da take da fayel, suna zuwa likitoci suka riƙe ta acan suka ba ta gado likita na ta faɗa jininta ya hau ga maleria ga rashin cin abinci. Yana ta faɗan cewa yanayin zai iya zama barazana ga cikin jikinta.

BaÉ—É—o suka bari da ita, Ummin ikki da Abdullahi suka koma gida suka sanar da su da halin da ake ciki sannan suka zo da mata da wasu kayan sawa sai fulas É—in ruwan zafi da kayan tea. Kwanta É—aya a asibitin sai ga Hamma Kabiru ya zo shi kaÉ—ai ya shigo garin daman BaÉ—É—o ne ta kwana tare da ita da safe Ummin ikki ta je tana taya ta zama sai Adda Suwaiba da Adda Ummu Sulaim da suka zo da rana su É—an taya su zama.

Hamma Kabiru ya zo har asibitin ya duba Ummu Salma shi da Abdulrrahman da Saddam nan suka bar ma Saddam É—in suka tafi, tana ta barci saboda an yi mata alluran barci tana ta samun barcin da ta yi kwanaki ba ta samu ba.
Hamma Kabiru da Hamma Abdulrrahman suka koma gida suka samu Baffa shi Hamma Kabiru faɗa yake yi don mai Baffa zai ce a karɓi ciki ai tun da dai ya amince shi ya ɗiga shi to bai isa ba.

"Baffa Ummu ta koma kamar wata horror tsabar rama da fari."
Ya faÉ—a cikin damuwa.
"Nima na ce Baffa ya bari a yi ƙararsa amma ya ce ba za mu yi ba."

"Baffa ka bari mu yi amfani da kuɗinmu mu jijiga duniyarsa kamar yadda ya jijjiga rayuwar ƙanwar mu."

Baffa dai ya yi shuru yana jinsu suka gama bambamin faÉ—an su suka sauka sannan ya yi magana da su kalaman dai da ya faÉ—a ma Abdulrrahman shi ya faÉ—a ma Kabiru ya dai bar maganar ne amma ba wai don ya fahimci Baffa ba, ai tunda ya nuna shi ba shi da mutumci gwara suma su nuna masa yan zamani ne, bai karanta takardan sakin ba amma duk kalaman dake ciki Abdulrrhaman ya karanta masa tun yana Jalingo.

Ba kwana zai yi ba a ranar yake so ya koma amma ya ce zai dawo tare da Adda Safinatu da yara su duba Ummu su ɗan kwana biyu. Hamma Abdulrrahman ya tafi saboda akwai in da zai je shi kuma sai ya shiga falon Ammah su sake gaisawa tun da lokacin da ya shigo gidan tana da baƙi, labari kamar ana ta aike maƙota duk sun ji labari ana ta shigowa yi ma Amma jaje har Baffa in ya fita haka za a tsayar da shi ana masa jaje, to ai tunda lamarin ya faru ba wanda ya isa ya hana a yaɗa labarin

Ko Ammah abin da Hamma Kabiru ya ke faɗa mata kenan ta lallashi Baffa ya bari su yi ƙaran yaron nan.

"Baffa ba zai amince ba Kabiru ku bar maganar nan kawai."

"Ammah to sai ya kashe mana ƙanwa! Kin ga yadda Ummun ta koma ne?
Amma ta yi shuru tunda ita dai ba ta je asibitin ba Baffa ma ya kasa zuwa amma dai sun yi waya da Ummin ikki ta ce mata ta samu sauƙi tana ta barci dai. Gwara ta samu barcin ko za ta samu yar natsuwa.

"Kawai Baffa ya koma gefe ya bar mana faɗan nan. Wallahi ko ba mu tura yaron nan gidan yari ba sai ya gane ba shi da wayau sai ya san ba a taɓamu a zauna lafiya. Ɗan iska kawai ni da man bai yi mini ba yana wani sunkunyar da kai kamar nagari Ammah ki tsoraci mutum mai kirki da surutun tsiya daga baya sai ya aikata mugun abu. Nonsense kawai"

Amma ta É—an murmusa ba ta yi magana ba, in dai Kabiru ne da man karatun sa kenan ta kiyayi mutumin da ya cika kirki ba shi da gaskiya. Sake gyara zama ya yi yana kawo maganar da ta wuce wai bai so da man a yi ma Ummu aure ba kamar ya san abin da zai faru daga karshe kenan.

"Yanzu Ammah ina daɗin abin da ya faru? Ummu ƙaramar yarinya ta zama bazawara ga ƙaramin ciki. Haba don Allah in da a ce yarinyar nan ta ji maganar mu da yanzu ta kusa gama Degree ɗin ta da yau ba ta can akwance rai a hannun Allah saboda wani stupid irin yaron da ta aura"

Amma dai ta yi shuru tana sauraran shi yana ta faÉ—a yana nuna mata harda kuskuren Baffa da itama ma kanta tunda Baffa na jin maganarta ba ta hana a yi ma Ummu aure a wancan lokacin ba.

"Kabiru ka ishe ni fa. Baffan ne ke da laifi? In ya tara sani  zai aura ma ta shi? Kaddara ne kuma mu duka musulmai ne musan karɓan kaddara gare mu wajibi ne."

"Amma ki gane magana ta mana. Me ya sa aka goya mata baya! Da a lokacin ke da Baffa kun dage mata wallahi da ta koma makaranta ta bar ra'ayin aure. But kalli abin da ya faru at the end Ammah Rayuwarta ta da dawo baya fa."

"Haka Allah ya hukunta Kabiru ni ko Baffan ka ba mu isa mu sauya faruwan haka ba"

Shi dai sai wani kawo na shi tsarin yake yi Ammah ta gaji ta yi masa tsawa tana faÉ—in" Kabiru zan ci maka mutumci ba za ka bar ni na ji da damuwata ba, ka zo kana damuna da turancin ka na banza da wofi."
Domin daga karshe sai ya koma yana yi mata mgana da turanci sai da ya ji Ammah ta buÉ—e masa wuta sannan ya É—aga hannuwa sama yana dariya.

"Afuwan Ammah na yi shuru."

Ya faÉ—a cikin harshen fillanci wata uwar harara ta maka masa da ya sa ya É—inke bakin shi, shuru na wani lokaci sai da ta sauka don kanta ta tambayi Safinatu da yara, duk da ta kira ta waya ta yi mata jaje, ya ce duk suna lafiya yana tunanin za su zo karshen wata su yi musu ko kwana biyu ne Ammah ta ce Allah ya kaimu ya amsa da Amin.

"Ammah gaskiya ya kamata in Ummu ta haihu ta koma makaranta."

"To Baffa."

Ta faÉ—a cikin gatse tana hararan shi sai ya yi shuru yana dariya.
"Amma shawara ce fa."
"Ba'a son shawaran naka"
"Allah ya ba ki haƙuri Amman mu."
Ya faÉ—a yana É—an mirmishi, sake maka masa harara ta yi shi kuma sai ya kwashe da dariya.

"Allah ya huci zuciyar Amman LamiÉ—o"

Kamar ya sani sai ko ga shi ta yi mirmishi dariyan ya sake yi kafin ya ce" Da man na sani sunan Amini ne kaÉ—ai zai saka ki dariya."
Amma ta yi mirmishi kafin ta ce" Kwana biyu ma ba mu yi waya ba. ya ko san abin da ya faru na Auta?
"An ya! Kamar bai sani ba don ko shekaranjiya mun daÉ—e muna waya kuma ban ji ya yi mini magana ba ina tunanin bai sani ba."

Amma ta jinjina kai kafin tace" Ko jiya na gwada lambarsa ba ta shiga. Haka ma Fatima itama ba na samun ta a waya."
"Mami fa kamar ba ta ƙasar, kwanaki mun yi chart da ita tace mini suna Paris."
Amma ta ce" An yi haka na manta Baffa ya faÉ—a mini sun yi tafiya. LamiÉ—on ne na damu amma tunda har ka yi magana da shi yana lafiya Alhamdulillah."

Hamma Kabiru ya ce" Lafiyan shi lau Amma ga ma wani labari mai daÉ—i."
"Me ya faru?
"Kin kusa fara ganin É—anki yanzu akai,-akai."
Amma ta washe baki tana fafin" Kai don Allah?
Hamma Kabiru ya gyara zama yana faÉ—in." Wallahi a shekaranjiyan da muka yi waya yake faÉ—a mini kamfanin Chevron da ya nemi aiki da su daman can kwanaki ya faÉ—a mini sun yi online interview. To sun ba shi aiki nan da wattani biyu zai fara aiki da su in sha Allahu."

Amma ta washe baki kafin ta ce" Ma sha Allah. To shi wannan kamfanin anan ne ko? Ba sai ya yi ta yawo a cikin jirgin ruwan ba ko?
Hamma Kabiru ya yi dariya kafin ya ce" Ammah duka kamfanonin na gida Nigeria ne, sai dai shi wanda Lamiɗo ke aiki da su yanzu kamfanin Nigerian Port Authority su jirgin da yake tuƙawa suna jigilan mutane ne da kayan masarufi suna zuwa ƙassashe da yawa kuma suna ɗaukan lokaci shi ya sa yake daɗewa bai zo ya ga mutane ba. Ammah ko a can Lagos ko Balkisu ba ta cika ganinsa ba sai su zo Tashar jirgin ruwa dake Apapa Lagos sau nawa bai je gida ba saboda aikin yana da ɗan tsauri shi ya sa na bashi shawaran gwara ya sauya kamfani wanda zai dinga zuwa gida bayan sati biyu ko uku in ya daɗe ne wata ɗaya."

Ammah ta gyaÉ—a kai tana faÉ—in" Haka ne, ya fara tara iyalai bai kamata yana yin nisa da gida lokaci mai tsawo ba gaskiya ka ba shi shawara mai kyau Kabiru."
Hamma Kabiru ya karɓa da cewa" Shi ne fa har sun ɗauke shi aiki yanzu ya rubuta takardan ajiye aiki da kamfanin da yake yi ma aiki yanzu sun ƙi saka hannu. Kin san Lamiɗon naki gifted ne suna son shi duk cikin matuƙan jiragensu ba kamar shi, yana musu aiki tukuru sannan yana da jajircewa akan aikin shi aiki yake yi musu tukuru bai damu da jikinshi ko gajiya ba shi ya sa ba sa son rabuwa da shi."

"To ai sai dai su yi haƙuri mu ma muna son ganin shi sannan muna son ya riƙa hutawa"
Ammah ta faÉ—a tana dariya.
Tun bayan faruwan al'amarin Ummu sai yau Amma ta saki ranta hiran LamiÉ—on da suka yi da Hamma Kabiru.
Chapter 55 · 0% Book details