← Book details Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 92

Sashe 53

Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Mu je na ganta. In ta fasa kashe kanta saboda wani banza ta ci ubanta."

Ya faÉ—a yana yin gaba zuwa cikin falon Ammah cikin fushi da fusata. Saboda wani banza sakarai ne za ta zo tana yi ma mutane sakarci in ta fasa kashe kanta ta ci bura uban ta in ji shi Abdulrrahman Hadi Baba, in ba ta kashe kanta ba ta ci uban ta.

*littafin Fargar Jaji na kuÉ—i ne a manhajar Telegram akan #1k. Tura KuÉ—in karatun ku ta wannan acct É—in 9069067488 JAMILA UMAR OPAY sannan sai ku tura shaidar biya ta waÉ—annan lambobin kamar haka.*

09069067488.
08032773332.

*Yan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajojinku a cikin wannan kayattacen labarin za ku iya tuntuɓata kai tsaye ta wannan lambar 09069067488 Na gode.*

*Janafty*
*FARGAR JAJI.*

*Wattpad:JamilaUmar315*
*Arewabooks:JamilaUmarJanafty*

"To Hajiya Hauwa'u Inuwa Aminu (Anty Hairi) with love and gratitude"

https://chat.whatsapp.com/LsC7Rjmei7J6Hd11e95nNS?mode=gi_t

*13*

Ammah ta bi bayan Abdulrrahman da sauri zuwa cikin ɗakin, dukkansu sun dukufa kan Ummu Salma har Baffa shi ne mai yi mata addu'a yana tofa mata, Saddam da Baɗɗo da Ummin ikki sun rirriƙeta tana ta fizge-fizge tana wani gunjin kuka har a lokacin ba ta daina maganganu ba kamar wacce ta fita daga hayyacin ta.

"Baffa zuciyata zafi take yi. Baffa ba zan iya rayuwa a haka ba. Ku bar ni na kashe kaina na huta."

Haka take faÉ—a tana rera wani irin kuka wanda ke kassara zuciyar mai sauraranta.
Ummin ikki haka take hawaye Baɗɗo har da majina Hamma Saddam ma idanuwansa sun kala saboda tashin hankali Baffa kam har da ƙwalla kwance a idanuwansa.

"Ummu ki daina faÉ—in haka. Ki yi ta maimaita Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un.."

Baffa ya faɗa lokaci ɗaya yana dafe kanta yana karanto mata addu'o'i Fatima kawai yake tunawa da irin wahalan da ta sha kafin ta iya karɓan kaddaranta amma Fatima ba ta taɓa cewa za ta kashe kanta ba. In har aka bar Ummu ita kaɗai wata rana za ta iya yin abin da hankalinta zai gushe ba a sani ba.

"Ku sake ta "
Suka ji an faÉ—a daga bayan su.

Gabaɗayansu suka juya cikin mamaki sai suka ga Hamma Abdulrrahman tsaye shi da Ammah a bakin ƙofar ɗakin.

"Na ce ku sake ta don Allah.".
Ya sake faÉ—a lokaci É—aya yana shigowa cikin É—akin sanye yake da suit masu ruwan toka ya matse wuyan sa da tie. Gefen kafaÉ—ansa kuma jakarsa ce ta aiki.

"Cewa take yi za ta kashe kanta fa Hamma."

Saddam ya faÉ—a yana kallon yayan na shi cikin mamaki.

"To ku saketa ta kashe kan nata mana"

Ya faÉ—a cikin halin ko in kula ba su Baffa ba har Ummun dake fizgewa sai da ta natsu idanuwanta na lumshe sai da ta buÉ—e su ciike da hawaye tana kallon Hamma Abdulrrahman tsaye a gaban su fuskar nan ta sa babu fara'a ko kaÉ—an hannayensa duka suna cikin aljihun wandon suit É—in sa.

"Haba Abdulrrhaman me ya sa za ka ce haka! A wannan yanayin da take ciki za ta iya yi ma kanta illa ba tare da ta sani ba."

"To ku kyaleta Baffa ta yi ma kanta illa saboda wani wanda ya cire ta daga rayuwarsa cikin tozarci da wulaƙanci. Ku barta in ba ta kashe kanta ba, ba ta haifu ba."

Baffa ya yi shuru kawai yana kallon É—an nashi.
"Kai sake ta."
Hamma Abdulrrahman ya ba ma Saddam umarni.
Da sauri ya saki Ummu ya miƙe tsaye, tun kafin ma ya sake magana Ummi da Baɗɗo suka saki hannayen Ummun Salma suka matsa gefe suka bar Baffa kaɗai a durƙushe a gaban ta.

"Baffa kai ma don Allah ka tashi daga durƙushen nan."

"Abdulrrahman."

"Baffa don Allah."

Hamma Abdulrrhaman ya faɗa lokaci ɗaya yana kallon Baffa cikin ɓacin rai,  ba lallashi take bukata ba fata fata za a yi mata sannan za ta dawo cikin hayyacin ta.
Baffa ya ƙi tashi sai da Ammah ta shigo ta kira sunan shi.

"Baffa."

Kallonta ya yi kawai sai ta gyaÉ—a masa kai, dole ya tashi jiki a sanyaye amma sai da ya kalli Abdulrrahman yana faÉ—in" Ka yi mata a hankali."
Ya faÉ—a yana dafa kafaÉ—an shi ya É—an bubbuga.
Fita ya yi daga É—akin ya koma falo Ammah ta bi bayan shi ganin shi cikin damuwa.

Hamma Abdulrrahman ya yi tsaye a gaban Ummu Salma da ta natsu kamar ba ita ce ya shigo ya ga ana rirriƙeta ba, amma yanzu ta yi shuru sai dai kawai hawaye take yi wasu na zuba wasu na karanyowa.

"Kin fasa kashe kan na ki ne?

Ya faÉ—a yana kallon ta, kawai sai ta fashe masa da kuka.

"Ban hana ki ba, go ahead ki kashe kanki Ummu Salma.".
Ya faÉ—a yana sassauta fushinsa.

"Hamma.."

Ummu Salma ta kira sunan shi cikin kuka da fitan hayyaci.

"Na ce ki kashe kan naki don Uban ki."
Ran maza ya ɓaci a gabanta ya duƙa lokaci ɗaya yana kallonta.
"Ai sai kin kashe kanki za ki nuna mana kaf É—in mu ba mu da amfani ko matsayi a wajenki Ummu Salma."
Ya faÉ—a cikin É—aga murya. Ta É—ago jajayen idanuwansa tana kallon shi, bai dagata ba ya cigaba da faÉ—in.

"Ammah da ta yi cikinki na tsawon wata tara ta kawo ki duniya ta rene ki, da Baffa da ya yi É—awainiyar rayuwarki tun daga ranar farkon ki a duniya har zuwa girman ki. Da mu y'an'uwanki da muka yi rayuwa dake sama da shekara ashirin duk yau bamu da muhimmanci, wannan dai banza a banza da ba ki da amfani a wajen shi, wanda kika haÉ—u da shi a baya baya shi ne kike ikirarin kashe kanki saboda shi Ummu Salma?

Hawaye kawai ke shatata ta kasa magana, tana so ta yi ma Hamma bayanin yadda take ji amma ta kasa wataƙila ba zai saurareta ba, saboda bai taɓa riskan kansa a cikin halin rayuwar da take ciki a yanzu ba.

"Are you stupit? Ko kuwa kin rasa tunanin ki ne saboda wanda ko shekara biyu ba ki yi da sanin shi ba?  Da kin san shi? Ba ki san shi ba kuma kin yi rayuwa Ummu Salma ba ki mutu ba to yanzu ma haka za ki cigaba da rayuwa ba za ki mutu saboda wani wanda bai dace ya fita daga rayuwarki ba."

Ya karishe faÉ—a yana kallon ta, duk da tausayinta na kama shi amma ba zai nuna mata ba gwara ya yi mata jan ido domin ya ga ba ta da hankali.

"Za ki cigaba da rayuwarki kamar yadda kika fara tun farko. Bai hallata ki cigaba da kuka ko damuwa akan wanda bai damu dake ba, wanda ya yi miki sakin wulakanci har uku sannan ya sake ki da cikin shi a jikin ki ba tare da ya damu ba. To ki sani in kika sake cewa za ki kashe kanki saboda shi, to kin nuna ma duniya cewa ke ba y'ar halas ba ce."

Shuru ya yi yana kallonta tana ta kuka har da gunji.
"Wanda ke son ki ba zai ƙi haɗa jini dake ba Ummu Salma."
"Ai ya ma ce ba sonta yake yi ba mara mutumcin."
Ummin ikki ta katse shi ya É—ago yana kallonta.

"A takardan sakin abin da ya rubuta kenan maganganu masu muni ai tsakanin mu da wannan yaron sai Allah ya isa."

Ummin ikki ta sake faɗa tana matsar ƙwalla.
Hamma Abdulrrahman ya miƙe cikin mamaki yana faɗin" Ina takardan sakin?
"Ko yana hannun Baffa?
Ya sake faÉ—a.
Sai Ummin ikki ta amsa mishi da cewa yana hannun Baffa. Da sauri ya bar ɗakin yana zuwa falo ya ga Ammah da Baffa, yana ganin shi ya miƙe yana kallon shi.

"Baffa ina takardan sakin?

Ya tambaya yana miƙa masa hannu, bai yi musu ba ya laluba aljihun rigan shi ya ɗauko ya mika masa. Ya karɓa daga tsayen ya fara karantawa bai ko kai ƙarshe ba ya yi wurgi da jakar hannunsa da takardan yana faɗin.

"Wannan yaron so yake mu nuna masa matsayin mu Baffa."

Ya faɗa a fusace lokaci ɗaya yana ɗauko wayarsa daga aljihun wandon shi, da sauri Baffa ya riƙe shi yana tambayan shi abin da zai yi sanin halin shi rudaɗde ne in ran shi ya ɓaci.

"Abokin aikina zan kira. Baffa dole fa mu yi ƙaran wannan yaron mara tarbiya."

Ya faɗa har jijiyon kansa na miƙewa raɗau saboda ɓacin rai.

"Aa"

"Baffa za mu shigar da ƙara sai  mun yi shari'a da shi sai kotu ta karɓo ma Ummu Salma haƙkin ta."
Ya faÉ—a cikin É—aga murya.

"Na ce maka A'a."

Shima Baffa ya katse shi a tsawa ce lokaci ɗaya yana ƙwace wayar hannun shi, Abdulrrahman ya fusata kawai sai ya fara zagayen falon yana ciccijewa saboda ɓacin rai, Baffa ya bishi ya riƙo shi yana faɗin ya je ya zauna ya samu natsuwa.

"Baffa wai ba ka karanta maganganun dake cikin takardan nan ba ne? Raina mu ya yi da zai rubuto mana haka?

Ya faÉ—a yana kallon Baffa cikin fusata.
Ammah na gefe zaune ba ta yi magana ba daman ta san sai an yi haka don ma É—ayan fusattacen bai zo ba Kabiru ai da Baffa ba zai iya da su shi kaÉ—ai ba.

"Zo ka zauna ka natsu mu yi magana."
Da lallashi da ban baki ya amince ya zauna Baffa ya zauna a gefen shi.
"Kwantar da hankalin ka Abdulrrahaman."
Baffa ya faɗa yana kallon sa ganin yadda yake huci ba abin da ke yi masa yawo wai sai don jikinta ya aure ta kuma tunda ya gama mora shi ya sa ya yada ƙwallon mangwaro ya huta da kuda.

Tuna hakan da ya yi ya sa ya sake miƙewa a zuciye yana faɗin" Kai ina! Bai isa ya ci bulus ba, dole ne mu nuna masa kuskurensa yadda ko nan gaba ya ji an ambaci sunan gidan nan sai ya fara mazari don uban sa."
Da sauri Baffa ya sake riko shi yana ba shi haƙuri.

"Baffa ka bari mu koya masa hankali. Ko nawa zan kashe daga nan har kotun ƙoli so kawai na ke yi na ga ya wulakanta."
Chapter 53 · 0% Book details