Sashe 18
Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya faɗa cikin ta da jijiyan wuya, Ummu ta firgita domin ba ta taɓa jin Habib ya yi mata tsawa irin na yau ba har ta fara hawaye.
"Ba wasa na ke yi ba. Mene ne matsayar ki?
Kanta dake girgizawa tana kwance amma ta kasa mgana saboda kuka ne ya taho mata zuciyarta na wani rawa rawa na ganin ko jin abin da ba ta taba tunanin gani ko ji daga bakin Habib ba.
"Amsa za ki ba ni da bakin ki ba kai za ki dinga kaÉ—a mini ba malama."
Ya sake faɗa lokaci ɗaya yana mai ɗora kafarsa a jikin gado ya ɗan duƙo yana mai kallon Ummu da ta fara rawan sanyi haƙoranta na haɗuwa gap! gap!.
Mirmishi ya yi, mirmishin da iyakarsa fatar bakinsa kafin ya ce" Ko mutuwa za ki yi sai kin faÉ—a mini matsayar ki."
Da ƙyar Ummu ta iya miƙewa zaune tana mai kallon Habib tana hawaye.
"Me kika yanke?
Ya sake tambayanta wannan karon ya É—an É—aga murya.
"Me ya sa kake son sai na zubar da ciki Habib?
Me ya sa? Lafiyata kalau, ba ni da wata damuwa cikin nan kuma na sunna ne to me zai saka ka ce sai na zubar da shi?
Kallonta yake yi amma bai yi mgana ba, ita kuma tana kallon shi hawaye na gudu bisa kumatun ta mamaki take yi? Mamakin Habib? Mamakin me ya sauya shi cikin lokaci ƙanƙani haka.
"Kawai ina so ki zubar da shi ne."
"Saboda mene?
Ummu ta katse shi da sauri cikin kuka.
Sai ya yi shuru bai yi mgana ba amma yana ta kaÉ—a kafa.
"Ba zan zubar da cikin ba, sai ka ba ni ƙwaƙwaran dalilin da zan gamsu da ya cancanta da na zubar ɗin sai na bi abin da kake so."
Kallonta ya ke yi cikin mamaki, bai ɗauka Ummu za ta ba shi matsala ba ya yi tunanin yadda take son shi komai ya ce ta yi, za ta yi ba tare da ta yi masa gaddama ba amma ya ga alamun sai ya fito mata a Habib ɗin sa sannan za ta fahimci ba da wasa yake yi ba.
"In kuma ban faÉ—a miki dalilin ba fa??
Ummu tana mai kallon shi hawaye na zuba ta ce" Ba zan bi Umarninka na saɓa ma Allah ba Habib. Ina son cikina kuma zan rene shi har ya fito Duniya. Ba zan yi ma Ubangiji butulci da kyautar da ya yi mini ba, ya tsamo ni a cikin dubu ya ba ni sai na yi masa butulci a wajen kashe rai?
"Ai bai za ma rai ba malama. Babu zunubi in an zubar da shi yanzu."
Ya katse ta a fusace, Ummu ba ta san tana da ƙarfi ba sai da ta gan ta a tsaye a kan kafafunta.
"Ai daga gudan jinin ne ake busa masa rai. Ka ga ko shima zunubi ne."
Ummu ta faÉ—a kai tsaye tana mai share hawayenta.
"Ban san dalilin ka ba, ko ma mene ne dalilin ka na tsayar da shawaran cewa ba zan zubar da cikin nan ba Habib."
"Ko da na ce ba yanzu na shirya zama uba ba.?
Habib ya katse Ummu lokaci É—aya yana yi mata wani kallo.
Cikin mamaki ta ke kallon shi, amma ta kasa mgana saboda bakinta ya yi mata nauyi.
"Ko da na ce miki ba ke nake so ki zama uwar Æ´a'Æ´ana ba?"
Ya faÉ—a yana mai kafe ta da idanuwansa sannan lokaci É—aya yana takawa zuwa gaban Ummu-Salma da ta kasa mgana sai kallon Habib ta ke yi, domin sai ta ke ganin kamar a mafarki komai ke faruwa.
"Ko da na ce miki ban taɓa son ki ba, ba ke ba ce matar da na shirya ki zamo uwar ƴa'yana ba, a hakan za ki yarda ki haifi cikin da ni ba zan amsa sunan uban shi ba?
Ummu ta ji wani jiri ya kwashe ta, ba domin ta yi saurin jingina da wardrope ɗin da ke gefenta ba da sai ta faɗi saboda yadda kalaman Habib suka ruguza duka saurin kuzarinta. Kan ta ta ji ya sake sara mata har wani duhu-duhu take gani, jikinta na rawa kamar ana mata kiɗan mazari, kallon Habib ta ke yi kamar tana tunanin in ta buɗe ido za ta ga komai da ya ke faruwa ba gaskiya ba ne. Sai dai ta runtse ido ta sake budewa still Habib ta ke gani a gabanta yana sake jadadda mata bai taɓa son ta ba.
"Kin shirya ma hakan!?
Ta kasa mgana hawaye ne kawai ke yi mata ambaliya, duhu duhu ma take iya ganin Habib tsabar yadda ta ji kamar ba a duniya take ba.
"To ki sani in dai kin ƙi bin umarni na , kin yi taurin kai to ina so ki san wasu abubuwa guda uku."
Har wajen fuskarta ya kawo kansa sannan ya nuna ta yatsa kafin ya cigaba da faÉ—in.
"Ki sani wannan cikin ba ni da danganta da shi, tun da kika ƙi bin mganata to ki je na bar miki. Na biyu kuma da man na faɗa miki sai kin yi nadaman jayayya da ni Ummu-Salma. Na uku kuma ba zan ce miki komai ba amma zan sanar da ke daga yau kin fara bankwana da farinciki, kin ƙulla ƙawance da baƙin ciki da tashin hankali a rayuwarki, sannan kin fara rasa komai tun daga yau ɗin nan, kin rasa ni Ummu Salma. Watakila da kin bi umarnina da kin tsira da wani abun tun da kuma kika zaɓi taurin kai mu zuba mu gani."
Yana gama faɗin haka ya juya zai bar ɗakin cikin ƙaraji da ihu Ummu ta ce.
"To ka san ba ka sona me ya sa ka aure ni Habib?.
Ta faÉ—a tana wani irin kuka kamar ranta zai fita.
Kuka take yi da dukkan muryanta da iya ƙarfinta.
Juyowa ya yi ya kalleta kafin ya ɗan cije baki kafin ya yi mgana Ummu ta zuɓe a kasa a kan gwiwoyinta tana sake faɗin.
"Me ya sa Habib? Me ya sa haka? Me ya sa ka je ka nemi aurena a hannun iyayena in dai har ka san ba ka taɓa sona ba? Sannan ka san ba ka san haihuwa da ni me ya sa ka yi mini cikin?
Kuka take kamar ranta zai fita amma bai sa Habib ya ji tausayin Ummu ba, bala'in jin haushin ta ya ke ji, domin taurin kanta adadin ɓacin ran masoyiyar shi, shi kuma duk abin da zai ɓata mata rai yana gudun shi.
"Za ki san dalilin anan kusa."
Yana gama faɗin haka ya fice daga ɗakin har yana bango ƙofa yana jin ƙaran Ummu da sanda ta sake fashewa da kuka mai cike da sauti.
Falo ya fito ya kasa zaune ya kasa tsaye me ya sa Ummu za ta yi masa haka? Bai taɓa tunanin za ta ba shi matsala haka ba, ƙaran shigowan saƙo daga wayarsa ne ya dakatar da shi daga tunanin mafitan da ya ke yi.
"Ya ake ciki? Ta amince?
Wannan lambar dai da ya yi ma saving da M.S ita ne aka sake turo masa saƙo da ita.
Jikinsa na rawa shima ya ma yar da amsa.
"Ba ta amince ba."
Ya tura ba daÉ—ewa sai ga shi an dawo masa da amsa.
"Duk da ka faɗa mata cewa ba ka taɓa son ta ba?
Shi ya sa ba za ka so haÉ—a zuru'a da ita ba?
"Na faÉ—a mata."
"Me ya kamata ka yi a yanzu?
"Na kasa samun mafita."
"Ka sake ta Habib."
Shuru ya yi kafin ya rubuta amsa.
"Zan sake ta. Amma sai na nuna mata kuskurenta sai na saka ta yi nadaman sanina a rayuwarta. Sai na saka ta ji dama ba ta yi mini gaddama ba tun fari. Sannan daga karshe na yi mata sakin wulaƙanci da ƙasƙancin da ba ma ita ba dangin ta ma ba za su taɓa mantawa da ni ba"
"Good Job.. Cikin jikin ta fa?
"Zai fita ko tana so ko ba ta so."
"Ka aiwatar da hakan da gaggawa domin ka san ba mu da lokaci"
"Ki yarda da ni."
"Na daÉ—e da Aminta da kai Masoyi na"
Saƙon ƙarshe ya saka shi farinciki har sai da ya murmusa, wayarsa ya ma yar cikin aljihun wandon jikin shi, ya fara safa da marwa yana tunanin yadda zai yi sanadiyar zubar cikin jikin Ummu Salma ko ta karfin tsiya, yana jiyo kukanta a cikin ɗaki amma ko a jikinsa tunanimsa kawai ta ina zai samar masa da kansa mafitar zubar da cikin nan? Domin bai shirya ba, kuma ba akan Ummu Salma ba.
Abin da bai sani ba, wannan gudun jinin sai an busa masa rai kuma sai ya shaƙi iskar duniya, duk abin da zai yi Ubangiji ya riga da ya gama na shi.
*Janafty*
*FARGAR JAJI.*
*Wattpad:JamilaUmar315*
*Arewabooks:JamilaUmarJanafty*
"To Hajiya Hauwa'u Inuwa Aminu (Anty Hairi) with love and gratitude"
https://chat.whatsapp.com/LsC7Rjmei7J6Hd11e95nNS?mode=gi_t
*05*
Ummu-Salma ta sha jin wata hausa a bakin hausawa. Da sukan ce wai yadda na ga rana haka na dare, ta ɗauka wata mgana ce kawai ta shaɗi faɗi, wacce ba ta da tushe ballanta makama, ita a da in aka ce mutum ya kwana bai yi barci sai ta yi ta mamakin me zai hana shi barci? ta ɗauka sai in an yi maka mutuwa ta uwa ko ta uba, ko ciwo ita bai hana ta barci. Sannan Ammah da Baffa duk suna raye kuma duka yayyenta ba wanda ta taɓa rasawa. Sannan tun tasowarta take cikin farinciki da gata. Har haɗuwarta da Habib da yadda ya shafe wattani takwas ya na nuna mata fassaran so da ƙauna a baki da aikace.
Ba ta taɓa riskan kanta a yanayin da ta kwana a ciki ba ranar. Har aka kira sallar asuba idanuwanta biyu suna kuma masu zubar da ƙwalla ko sun gaji sun haƙura da zubar ƙwalla ba a ɗaukan lokaci za su dawo suna kwarara kamar an buɗe famfo.