← Book details Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 92

Sashe 91

Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta faÉ—a tana cije baki, tiolet ta faÉ—a ta yi wanka ta fito kenan É—aure da babban towel a ka kira wayarta ganin mai kiran yasa ta É—auka da sauri.

"Na ji shuru har yanzu."

Magana aka yi mata daga can bangaren sannan ta gyaÉ—a kai tana faÉ—in.
"To ka tabbata dai cikin satin nan, ba fa da wasa  na ke yi ba da gaske nake yi."
Daga haka ta katse wayarta tana É—an wani nazari kafin lokaci É—aya ta saki mirmishi ita kaÉ—ai.
Daga ita sai Allah sai zuciyanta sai wanda suka yi waya suka san abin da take ƙullawa.

****
*Sunday*

Daddy bai dawo ba, Mami ta ce akwai wasu sabbin shigowan motoci ne da zai yo oder shi ya sa ya ɗan jima, sun saba duk karshen sati su kan ɗan fita yawo cikin gari tare da Mami da Barira da Faruƙu, yau ma ko da Daddy baya nan sun fita bayan la'asar suka je Shoprite su ɗan biya store suka yi tsince tsince, suna mota a hanyar dawowa gida Hamisu ne ke tuka su a wata mota ƙiran toyota RAV4, Baffa ya kira wayar Mami sun daɗe suna mgana abin da ma yasa Ummu ta gane Baffa ne ta ji Mami na ambaton sunan shi duk da ba ta fahimci kan me suke magana ba, tunda ita Mami faɗi kawai take yi" Kuma ka yarda da maganansa Baffa? Ni dai Allah ban yarda da shi ba."
Abin da kawai taji tana faÉ—i kenan.

Sai kuma in da ta ce" Baffa ni fa ba wai na ƙi mganar ba ne, sam shi da ƴata ba su dace ba. Ba za ta iya da halin bamuden ɗan Ammah ba."
Kamar ta so ta É—au saunar mganar, Hamma LamiÉ—o ne Mami ke kira da wannan sunan amma kuma yarta ta fa? Wacce take nufi.

"To Baffa muna hanya ne, zan kira ka in mun koma gida"
Bayan ta katse wayar kuma ba ta ba da wata kafa da za a fahimci wani abu ba, sai ta bige da jan Ummun da wata hiran da ya sa ma ta manta da wayar Mamin, bayan sun koma gida kowa ya shiga É—akinsa, daga nan ba ta sake jin wata mgana ba.

Bayan isha'i sai ga Baffa ya kira Ummu Salma a waya bayan sun gaisa kamar kullum ya ce ina amaryansa Ummu ta ce ta kwanta.

"Ummu Salma."
Tunda ta ji Baffa ya kira sunanta  ta san akwai magana a bakinta.
"Naam Baffa."
"Wane ni a wajen ki?
"Kai mahaifina ne"
"Alhamdulillah kin san duk abin da zan yi ga rayuwarki ba nufin na cutar dake ba ne ko Auta?

"Na sani Baffa."

Har idanuwanta sun fara tara ƙwalla saboda ba ta son me ya faru ba.

"A lokacin auran ki na farko ban yarda an yi miki dole ba. Duk abinda kika nuna baki so ni ma zan ce bana son shi. Har kuma yanzu da kike bazawara kina da haƙƙin sake yi ma kanki zaɓi a karo na biyu."
Baffa ya yi shuru yana jan nunfashi.
Ummu har ta fara kuka, tsoro take ji kar Baffa ya ce ta yi aure, ba za ta iya masa gaddama ba amma tabbas hakan cutuwa ne a gare ta.

"Ummu Salma."

"Naam Baffa."

"Jiya an zo neman auran ki a wajena."
Gabanta ya amsa ras!
Jikinta har ya fara rawa.

"Kuma wamda ya zo É—in ba zan iya hana shi ba, na hango miki kyakyawan rayuwa tare da shi."
"To Baffa."
Ta iya faÉ—a tana kuka.
"Ba dole zan yi miki ba, amincewarki  nake nema Auta, in har kin amince gobe da safe ni da yayyenki dake kusa zamu jagoranci ɗaurin auran ki."

Wannan ba amincewa ba ne, Umarni ne Baffa ke ba ta amma a fakaice duk yadda ta tsani aure ba ta isa ta yi ma Baffa gaddama ba su suka tsaya ma rayuwarta kuma ba ta isa ta bijire ma mganarsa ba.

"Kar ki damu in ba ki amince ba, ba komai sai na bashi haƙuri."

Ya faɗa cikin wani yanayi a muryansa akwai zumuɗi daga a farko, daga karshe shurunta sai ya sanyaya ma muryansa ƙarsashinta.

"Baffa."

Ta kira shi cikin muryan kuka.
"Naam Auta, kuka kike yi ne?
"Aa Baffa."
Ta faÉ—a tana share hawayenta da hannunta.

"Kar ki damu na ce in ba ki amince ba sai na ba shi haƙuri."

"Aa Baffa."

"Kin amince?

"E Baffa."

"Kin tabbata?

"Na amince Baffa, in dai ka amimce nima ba ni da ja."

"Na amince da shi Auta, wallahi ina mai yi miki rantsuwan da cewa yadda zai kula da kansa haka haka zai kula da ke Auta."

"To Baffa."

Ta faÉ—a tana danne kukanta

"Allah ya yi miki albarka Ummu Salma, yadda kika karɓi tayina Allah ya wanzar da farimciki a rayuwarki ta har abada. Na gode miki Allah ya gode miki Auta."

"Amin Baffa."

Ta faÉ—a tana jin sanyi a zuciyanta.
Baffa kuma jin ba ta tambayi ko waye ba shi ya sa bai faÉ—a mata ba suka yi sallama suna gama waya ta tashi da gudu ta fita ta haura sama zuwa É—akin Mami tana kuka, Mami na zaune gefen gado waya take yi sanda Ummu ta faÉ—o tana gunjin kuka ai sai ta saki wayar saman gado ta nufeta cikin rawan jiki.

"Subhanallah Ummu me ya ke faruwa ne?

"Mami."

Ta faÉ—a cikin gunjin kuka lolaci É—aya tana faÉ—awa jikinta.

"Shi, bar kuka yi mini bayanin abin da ya faru."
Ta faÉ—a tana janta gefen gado suka zauna.

"Mami aure Baffa zai yi mini"

Mami ta zaro ido kafin ta ce" Aure kuma? Da wa?
"Ban sani ba Mami"
Ta faÉ—a tana tsiyayan hawaye.
"Yanzu Baffa bai bar mganar nan ba? Na ce nima ban amimce ba. Yanzu ma da Abban Islam muke mgana shima ya kira shi ya faÉ—a masa, kuma da alamu ya goya ma Baffa baya."
Kukan Ummu ya É—auke kenan kowa daman ya sani? Har Daddy ma ya amince kenan

"Bar kuka, in dai ba ki so ba wanda zai yi miki dole."
Wayarta ta jawo za ta kira Baffa.
"Baffan zan kira."
Da sauri Ummu ta riƙe mata hannu lokaci ɗaya tana mai girgiza mata kai.

"Ki bari na kira shi na ce ba ki so."

"A'a Mami, ki bar shi kawai."

"Me ya sa? Kin amince kenan?

Ummu na hawaye ta ce" Na amince Mami, ba tilas ba ne sai da Baffa ya nemi zaɓina."
"Tilasa ne mana ai ba ki ga wanda za a aura miki ba, ballatana ki ji kina son shi har ki amince da shi."
"Mami ba komai in dai Baffa ya amimta da shi a wajena Amintattace ne."
Mami ta yi shuru tana kallonta.
"Kin tabbata? In dai ba ki so zan ta da auran nan"
Da sauri ta sake girgiza kanta.
"Aa ina so Mami kar ki yi mgana."
Sai Mami ta sake yi mirmishi.
"To share hawayenki, É—iyar albarka"
Sai ma ta taya ta ta share hawayenta.

Sannan ta riƙe hannuwanta tana faɗin" Ki natsu kin ji ko? Ki yi ta addu'a in sha Allahu kin samu sauyin rayuwa. Ina tare dake har numfashina na ƙarshe."
Sai Ummu ta fashe da kuka ta faÉ—a jikin Mami.
"Mami Allah ya bar min ke."
"Amin É—iya ta."
Ta daɗe a ɗakin Mami suna ta hira, sai daga baya ta koma ɗakinta, ranar ta sha kuka amma ta kwana salla da addu'an neman zaɓin Allah.

Kuma da garin Allah ya waye ta samu natsuwa amma tana cikin fargaba, tun safe Mami ta fita Faruku ma na makaranta daga ita sai Baraka.
Ba wanda ya kira ta ballatana ta ji ko an É—aura auren ko ba a É—aura ba

Can wajen huɗu da wani abu na yamma tana ma zaune ne ta idar da sallar la'asar ne  Daddy ya kira ta da lambarsa tana ta mamakin yaushe ya dawo?
Amma abin da ya tambayeta ne ya sa ta fara rarraba ido.

"Ummu Salma gamu a masallaci za a É—aura auran ki, nawa kika yanke Sadakin ki?

"Naam"

Ta faÉ—a cikin rashin sanin madafa.
"E nawa kika yanke masa?
"Daddy duk abin da ka ce."
"Aa haƙƙin ki ne."
"Dubu dari."
Ta ji bakinta na faÉ—a.
"Tana jin Daddy na maimaita ta ce Dubu É—ari daga nan ta ji mganganun mutane ta cikin wayar sannan Daddy ya kashe wayar, abin mamaki yaushe Daddy ya dawo? Ba daÉ—ewa Mami ta dawo da ta ba ta labarin Daddy ya kirata kamar fa yana Jimeta.

"Yana can, Baffa ya ce sai ya dawo shi zai ba da auran ki."

Mami ta faÉ—a cikin fara'a. Daga gani abun ya yi mata daÉ—i.

"Shi ne ya ta so a yau, saboda shi ne ma ya sa daurin auran ya kai bayan la'asar."

Ta sake faÉ—a tana kallonta.
Ummu dai ta kasa magana saboda yadda jikinta ya yi wani sanyi ƙalau Mami ta shiga kiran Basira wacce ta fito tare da Hanan biye da ita tana ganin Mami ta nufeta tana kiran sunanta.

"Mami oyoyo."

"Oyoyo Hanan."

Mami ta faÉ—a tana cafe ta, tare suka zauna saman kujeran falon tana shafa kanta.
"Barka da dawowa Mami."
'Yauwa basira."
Sai ta kalleta yadda ta É—an rankwafa cikin ladabi
Ummu ta juya za ta bar falon kenan Mami ta kalli Basira tana faÉ—in" rangwaÉ—a ma Ya Ummu guÉ—a yau an É—aura mata aure Basira."
Ai Basira na jin haka ta miƙe ta rangwaɗa guda har sai da Uummu ta toshe kunnuwanta ta bar falon da gudu Mami ta bi ta dariya Hanan ma na ta yata.

"Ma sha Allah, Allah ya sanya alheri Mami."
"Amin Basira.  Yau ki shiga kitchen Amarya ba yanayi gobe ayi abinci da yawa Hamisu zai kawo takeway, za a fita a yi sadaka."
"Allah ya biya ki Mami."
Ta amsa da Amin nan ta bar falon tana ta ya Ummun Murna domin ta É—an san wani labarinta, tana tausayin kanta amma tana tausayin Ummu Salma duk da tana cikin gata.
Chapter 91 · 0% Book details