← Book details Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 92

Sashe 62

Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan fitan Sabuwa ta daɗe zaune tana ɗan daidaita jikinta kafin ta miƙe tiolet ta shige  bayan mintina goma sai ga ta ta fito sanye da rigan wanka fara sama sama ta ɗan shafa lotion a saman fatarta wacce ke wani irin shining ds glowing na jin daɗi da hutu clotheset ɗin ta buɗe ta shiga ba daɗewa sai ga shi ta sake fitowa sanye da wani riga da wando pick, wando dogo ne ya na da ɗan faɗi ta kasa rigar ma haka ba ta kama ta ba amma kayan suna da laushi da ɗan shara shara tunda har ana iya ganin farin pant ɗin jikinta da brazeya ɗin da ta sanya. Gashin kanta a tsife yake yi ba ta da wani suma amma saboda yana shan gyara yana nan mai kyau da shi, ta ɗaure shi da band sannan ta saka wata hula pick tsakiya a buɗe daga saman ne an yi tuntu na kwalliya mai zanen heart. Ta manta da wayarta a jikin jakar da ta shigo da shi sai ta isa wajen kafafunta na lumshewa a cikin lausasan cafet ɗin da ke Bedroom ɗin mai buzu buzu, ta isa wajen jakar ta ɗauko a hankali ta ciro wayarta ƙiran Iphone 16, sannan ta sauke jakar a in da ta ɗauke ta.

Kan makeken gadon da ke bedroom É—in ta kwanta sannan ja jawo farin bargo mai laushi ta rufe kafafunta, ta É—an duba wayar na wani lokaci kafin ta sauke ta a gefenta ta juya ta sake juyawa sannan idanuwanta suka fara lumshewa a hankali a hankali kafin barci mai nauyi ya É—auke ta na gajiya domin tun safe yau take asibiti tana ganin patients.

***

Ƙarfe 3:45pm Balkisu ta tashi daga barci, har an fara kiran salla a wasu masallatan dake kusa da su har da ma waɗanda ke nesa. Duk nauyin barcinta lokacin salla na yi kamar tana ji a jikinta za ta tashi. Shi ya sa in za a tambaye ta a zamanta da Lamiɗo na shekaru shidda wani hali mai kyau ta koya daga gare shi za ta ce tsaida salla a kan lokacin ta. Tunda take da Lamiɗo ba ta taɓa ganin lokacin salla ya wuce sa da gangan ba. Mutum ne mai kiyayewan lukatan salla duk abin da yake yi koma mene ne salla na gaba da komai, ta taɓa tambayan shi ya ya yake yi in lokacin salla ya shiga kuma sai aka yi rashin sa'a yana tuki a lokacin? sai ya ba ta amsa da cewa in ya zo bakin gaba zai tsaya ba zai cigaba da tafiya ba sai ya yi salla, ko ya san wannan ka'idar shi ne in dai a lokacin tukinsa ne.

Tun ba ta saba ba har itama yanzu daɓi'an ya zame mata jiki, tana kokarin kiyayewa lukatan salla. Yanzu ma mika ta yi sannan ta sauko da fararen kafafunta daga saman gado lokaci ɗaya tana mikewa. Tiolet ta shiga ta dauro alwala sannan ta fito ta daidaici gabas ta shimfiɗa darduma babba a ɗan koridon cikin bedroom ɗin nata, ta ɗauki dogon hijabin da take salla da shi a goge a saman side drower ɗin gadon. bayan ta idar da sallar ta ɗan ɓata lokaci tana kirga yatsun hannunta kafin ta shafa adduar'ta a fuskarta lokaci ɗaya tana mikewa ta ninke darduman da hijabin jikinta ta mayar da su ma'ajiyar su. Wayarta ta ɗauka ta sake duba lokaci.
HuÉ—u har da mintina goma,
wani takalmi ta saka mai taushi na zaman cikin gida sannan ta buɗe kofar bedroom ta fita ba ta zauna a falon bangarenta ba sai ta fita can main falo in da ta iske Debora na faman kwashe lunch ɗin da ta dafa tun ɗazu amma daga matar gidan har Maigidan da ya dawo jiya ba su sauko ba, kuma a ƙa'ida ba za su ci ba sai dai a kwashe a sake jera Dinner wanda aka sake dafawa.

Cikin ladabi Debora ta rankwafa tana yi ma Balkisu barka da fitowa cikin harshen turanci.
Ba ta amsa ba sai da ta zauna saman kujera mai zaman mutum biyu.
Sannan ta É—aga mata hannu.
Wayarta ta É—auko tana É—an dubawa ita kuma Debora ta gama kwashe komai zuwa katon kitchen din da ke can yamma da falon sannan ta dawo ta duka gaban Balkisu tana tambayanta ko akwai abin da take so cikin harshen turanci, domin gidan ba a cika yin hausa ba, matar gidan turanci take yi haka ma yaranta. In har ta yi hausa sai dai in za ta yi magana da Sabuwa ko Hidaya su da suke yan kauye ba arabi babu boko.
Amma kaf ma'aikatan gidan masu ilimi ne, kamar yadda ma mallaka gidan suke da tarin ilimi da nasaba.

"Coffea."

Haka ta faɗa kamar bakinta na ciwo, in da sabo sun saba da yanayin ta. Gidan nan kamar wata masarauta ce ta yan boko domin sarauta da ji da kai tare da takama da ƙasaita masu gidan sun iya shi, to yar Sarki ce fa jinin sarauta a jininta yake yi, maigidan ma jinin sarauta ne, kamar ma ya fi matar gidan ji da sarauta komai na shi na dabam ne.
Da sauri Debora ta koma kitchen ta haɗo mata coffea a cikin wani karamin jug mai kyau sannan ta ɗauko wani karamin faranti fari ta ɗora akai sannan ta kawo mata ta kuma jawo mata ƙaramin table din tangaran ɗin da ke falon ta ɗora komai a kai sannan ta duka ta zuba mata ta zuba kaɗan ta ji Balkisu ta ce

" Is ok."
A hankali.

'Yes Mah."
Debora ta faɗa lokaci ɗaya tana mika mata, sai da ta yi sama da sakwan goma sannan ta miƙa dogon hannunta ta karɓa ta rike a hannunta amma hankalinta na wajen wayarta sannan duka kafafunta suna miƙe a saman kujeran da take zaune ne.

Har Debora ta kwashe komai ta koma kitchen mug É—in na hannun Balkisu ba ta fara sha ba sai can sama da minti uku sannan ta iya kai shi bakinta ta É—an kurba sau É—aya ta mayar da shi saman É—an teburin gabanta ta ajiye ta cigaba da duba wayarta.

Gidan ya yi wani irin shuru sai wucewar iskar A.C ko tibi ba a kunnawa a gidan yara ne kuma suna da shi a É—akin su, suma ba sosai suke kallon ba in ma za su yi volume kaÉ—an ne ko na falo ba mai jiyowa, Balkisu ba ta son hayaniya shi ya sa duk abin da zai saka ta ta ji ta takura ba ta yin shi, to ita data ke ma kwana a gidan koda yaushe kenan ba maigidan da sai ya yi wattani biyu uku ba shi a gidan ba.

Ta yi zaman sama da awa ɗaya a falon nan bayan Debora ba wanda ya sake giftaawa. Sau uku ta kurɓi coffea ɗin da aka kawo mata daga nan ba ta ƙara ba.
Agogon wayarta ta duba biyar da mintina an kusa tashin su Sultan daga makaranta.

Dan ajiyar zuciya ta sauke sannan ta sauko da ƙafafunta ta sauke su a saman wani cafet mai taushi da kyau a ido. James ba ya bukatar sai an tunasar da shi lokacin tashin su Sultan ya fi kowa sani tunda alhalin kai su da ɗauko su yana wuyansa ne, tana zaune ta ji an buɗe get an fita daga gidan ka'ida ne da wuri yake zuwa yana bakin makaranta yana jiran su za a tashe su sannan ya ɗaukosu su dawo gida.

Karfe ,5:30pm na yamma ake tashin su kuma tun 7am suke tafiya makaranta tana haÉ—e da boko da islama ne mai suna AL.TASLEEM ISLAMIC SCHOOL.
Suna karatu tun daga saturday har Wednesday. Thurday ne da Friday ba sa karatu.

Miƙewa tsaye ta yi ɗauke da wayarta a hannunta sannan ta fara takawa cikin wani irin taku na ɗaya bayan ɗaya kamar ba za ta taka ƙasa ba, lokaci ɗaya ƙafafunta dake sanye cikin tattausan takalmi suna nitsewa cikin lallausan cafet ɗin daya malale falon gabaɗaya wata kofa ta nufa daga kudu, sai ka ma lura sosai sannan za ka fahimci akwai ƙofa a wajen tana zuwa ta buɗe a hankali ta shiga, sai ga ta a wani dogon korido tana zuwa karshen koridon sai ga wata ƙofa itama tana buɗewa ta shiga sai ga ta cikin wani falo mai girma da ya ji kayan alfarma sai dai falon ya yi duhu tunda gabaɗaya labulanyan falo da windows ɗin suna rufe ne, ba ka jin motsin komai a falon sai dai na sanyi-sanyi da ƙamshin turaren wuta mai shiga hanci sannan kuma mai sanyaya zuciya.

Daga gabas da falon akwai wata ƙofa ita ta nufa ta ɗan tsaya sannan ta ɗan ƙwanƙwasa shuru ba wani motsi na wani lokaci sannan ta murɗa handel ɗin ta shiga cikin ɗakin.
Bedroom ne shima kamar falon ya yi duhu dum, tunda shima duka windows É—in a rufe suke sannan labulayan a sake suke.

Tana tafiya takalminta na taka cafet din da ya malale bedroom É—in idanuwanta na hango masa shi sambal cikin bargo, ba a ganin fuskarsa tunda ya yi kwanciyar gefen dama ne ya danne fuskarsa da filon da ya rumgume a hannun shi da shi.

Har ta iso gaban shi bai sani ba domin barcin sa kawai yake yi, amma fa ko hucin numfashin sa ba ka ji hakan zai alamta maka ko barcinsa cikin natsuwa yake yi
Ta É—an jima tsaye tana kallon shi, kafin ta É—an matsa baya ta isa jikin window É—in É—akin ta zage labule gefe da gefe sannan ta buÉ—e glass É—in haske ya shigo.
Chapter 62 · 0% Book details