Sashe 16
Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta aminta da kirkin shi tun da shi uwa É—aya ce ta haife su amma gwara shi akan wancan, ita dai ba ta yarda da cewa wai Hamma LamiÉ—o is nice person ba.
"Ka yi haƙuri Hamma. Ba.."
Ya katse ta da sauri yana cigaba da faɗin" Hallaya ce Ummu. Wani haka Allah ya hallice shi ba ya son shiga rayuwar kowa. Kamar ni nan na fi son shuru fiye da komai, kamar Lamiɗo ya fi son rayuwa kamar yadda kika ga yana rayuwa, amma duka muna da kirki ba mugaye ba ne kamar yadda kika ɗauka ba."
Tana danne bakinta kar ta yi dariya ta ce" Na fahimta Hamma."
"So ko gobe ki daina yanke hukunci kan mutumin da zama mai tsawo bai haÉ—a ku ba."
Ta amsa masa da toh, suna ma cikin wayar ne ta ji ana taɓa kofa.
"Sai da Safe Hamma a gaida Adda Safina da su Yusra."
"Za su ji, da safe zan saka miki ko na kati ne domin na san dalilin kiran kenan."
Tana so ta ce ba haka ba ne sai har ya kashe wayarsa dai-dai lokacin da Habib ya shigo falon da sauri ta miƙe tana kallon shi cikin mirmishi, shi ko gogan kallo ɗaya ya yi mata bai sake ba, yana rataye da jakarsa ya fara takawa zai wuceta zuwa bedroom.
"Sannu da zuwa Noori."
Ta faÉ—a tana nufarsa, bai tsaya ba amma ya amsa da yauwa a É—akune yadda ta bar fuskar shi a cunkushe É—azu to a yanzu ma haka ya shigo
Tana ƙoƙarin karɓan jakar hannun shi ya wuce ta da sauri zuwa cikin bedroom tana jin ƙaran yadda ya rufe ƙofar da ƙarfi. Ummu salma ta yi sansarairai a tsaye ta kasa motsi saboda mamaki da al'ajabi a wattani takwas ɗin da suka yi da aure ita da Habib ba su taɓa riskan wannan matakin ba sai yau.
Ajiyar zuciya ta sauke, komawa ta yi ta zauna tana sake karfafa ma kanta gwiwan ba komai yana fushi ne ya ɗauka ta san tana da ciki ne ba ta faɗa masa ba. Tana nan zaune sama da mintina talatin sha biyu saura na dare sannan Habib ya fito daga cikin Bedroom, ya sauya kaya zuwa wani gajeron wando da farar singlete da alamu wanka ya yi ko kallon ta bai yi ba ya wuce kitchen ya ɗauko ruwan gora ya fito da shi a hannu ita kuma ganin haka ya sa ta miƙe jikinta har yana rawa.
"Noori."
Â
Ta faÉ—a cikin sanyi da karyewan murya.
Sai da ya sha ruwan rabin goran sannan ya ɗago yana kallonta cikin wani irin kallo da ya sanyaya mata jiki.
"Ga abinci."
Ta faÉ—a tana nuna masa Dinner É—in da ta gama shirya masa komai tun É—azu.
"Na ƙoshi."
Haka kawai ya faɗa lokaci ɗaya yana sauke goran hannun shi a saman dinning ɗin ya wuce ta ya koma ciki, da sauri ta bi bayan shi ta ci sa'a bai rufe ƙofar ba.
Yana zaune a gefen gado yana duba wayarsa ta shigo gefensa ta zauna tana neman kwanciya a saman kafaɗan shi ya yi saurin matsawa gefe, Ummu ta saki baki tana kallon shi.
"Noori."
Ta kira shi da mamaki a muryanta bai amsa ba ya dai kalleta a tsaye da idanuwansa fuskar nan ba fara'a.
"Me ya faru ne?
Banza ya yi da ita sai ma ya cigaba da duba wayarsa.
Sai ta yi mirmishi kafin ta ce.
"Wai akan mganar ciki ne?
Ga mamakin ta sai ya amsa mata da cewa.
"E."
Ta É—auka tunanin ta gaskiya ne yana fushi ne akan yana tunanin ta sani ba ta faÉ—a masa ba, ba ta san tunanin Habib a lokacin ba.
"To ka yi haƙuri Noori na, wallahi da gaske na ke yi nima ban san ina da ciki ba."
Har ta gama mgana bai É—ago ba, yana cigaba da latsa wayarsa.
"Ka ji Allah ban sani ba ka yarda da ni."
Matsowa ta sake yi kusa da shi tana mai riƙe hannun shi guda ɗaya tana sake marairaicewa da muryan tare da shagwaɓan da ta san yana kunna shi.
"Am sorry Noori na.
Baby ce fa? Za ka iya fushi da ni?
Ta faÉ—a tana mai kwantar da kanta a saman kafaÉ—an shi.
Sai ya sake matsawa da mamaki ta sake ɗagowa tana kallon shi kafin ta samu damar mgana ya miƙe tsaye.
"Ummu-Salma ina son na yi mgana da ke."
Ya faÉ—a lokaci É—aya yana mai kallonta a mganar shi da yanayin shi babu wasa ko kaÉ—an.
"Magana kuma? Wata mgana?
Ta faÉ—a cikin mamaki gabanta na faÉ—i kaÉ—an-kaÉ—an.
Bai amsa mata ba sai ya koma can farko gado ya zauna sannan ya juyo yana kallon Ummu-Salma da ta daskare a zaune saboda ita fa ba ta gane ma yanayin Habib ba gaskiya
"Ki natsu ki fahimci umarnin da zan ba ki."
Kallonsa kawai take yi amma ta kasa mgana sai dai ta kasa haÉ—iye miyau a bakinta saboda faragaba da tarardadi
"Ina sauraran ka."
Ta faɗa dakyar cikin rauni har idanuwanta sun fara cikowa da ƙwallah tun kafin ma ya faɗi mganar.
"Ummu-Salma."
Ya kira sunan ta a kausashe, sunan da ba taɓa jin ya kira ta ba tun tana gida da Baby yake kiranta har bayan auran su bai sauya mata suna ba shi ya sa jin yau yana kiran ta da sunan ta cikin kaushi ba tausasawa jikinta ya fara rawa cikin tsoro ta amsa.
"Na'am. "
A muryan ta kamar saura ƙiris ta fashe da kuka.
"Umarni na ke so na ba ki, ta wani fanni kuma ba Umarni ba ne."
Ita dai ta ƙura masa ido, ta kasa cewa komai amma ta matsu ya faɗi abin da zai faɗa kafin zullumi ya ɗauke mata numfashinta.
"Ina son a zubar da cikin jikin ki Ummu-Salma."
Ya faÉ—a yana mai kallonta domin ganin yanayin ta.
Ita ta ko sai ta ji kamar ba ta ji da kyau ba ya sa ta sake tambaya.
"Naam me ka ce?
Ta faɗa tana mai ƙura masa ido, kamar ta ji Habib na maganar ciki, me ya ke cewa ne?
"Na ce ina so a zubar da cikin nan."
Ido ta zaro kafin ta ce" Wa ni ci ki.?
Ta faÉ—a a rarrabe cikin tashin hankali.
"Wanda ke jikin ki."
Ya faÉ—a ba tare da É—ar ba, kuma babu nadama a mganarsa.
Sai Ummu ta fara mirmishi kafin ta ce.
" Haba Noori ka bar irin wannan wasan don Allah ba na so."
Ta faÉ—a lokaci É—aya tana girgiza kanta. Domin a tunanin ta wasa ya ke yi, ita kuma ba ta son irin wannan wasan, duk duniya a yanzu ba wanda ya isa ya raba ta da cikin jikinta sai wanda ya ba ta, amma ba dai wani mutum ba.
 "Wasa ka ke yi ko Noori?
Ta sake faÉ—a tana kallon shi.
Amma sai Habib ya miƙe a fusace har yana nuna ta da hannu.
"Kin ga wasa a mgana ta! Ko kin ga fuskata da alamun wasa?
Ya faɗa a fusace, jikin Ummu na rawa ta miƙe, cikin mamaki da aljabi ta ce" Cikina zan zubar Noori?
"E haka na ce"
"To saboda mene? Cikin yana da wata matsala ne?
"Ba shi da wata matsala, amma ni ne zai iya kawo ma matsala a rayuwata nan gaba."
Ummu cikin rawan baki da na murya ta ce
"Ban ga ne ba?
"Ai ba za ki gane ba. Malama ni dai ga abin da na ce. Ciki za a zubar da shi."
"Aa"
Ummu ta faÉ—a hawaye na zubo mata cikin kuka ta ce" Me ya sa zan zubar da cikina? Cikin sunna ne ba na shege ba."
Ta faÉ—a cikin zubar hawaye
"Ni haka na ce za a zubar da shi."
"Ba zan iya ba. Ba zan iya zubar da cikin nan ba, haka kawai sai ka ce na zubar da ciki kuma ba da wani ƙwaƙwaran dalili ba"
Ta faɗa tana share ƙwalla kafin ta matsa kusa da shi tana cewa" Noori ni ce fa, ka tuna lokacin da ka shiga damuwa da na rasa cikina na farko me ya sa ba za ka yi murna da samun cikina a karo na biyu?
Me ya sa ka canza? Ciki fa ka ce na zubar? Zunubi fa kake so mu aikata."
Ta ƙarishe faɗa tana ƙoƙarin riko shi da sauri ya kauce yana faɗin
"Ni ba damuwa na shiga don cikin ki ya zuɓe ba, ko bai zube ba za ki zubar da shi. Murna na yi lokacin da ya fita ba baƙin ciki ba.".
Ya faɗa yana kallon ta, cikin ɗimuwa da firgici Ummu ta zare ido, kafin ta kifta idanuwanta amma ta kasa mgana domin sai ta ji wani abu ya tokare mata maƙogwaro
"Kin ji da kyau, saboda haka na ba ki kwana uku ki yi shawara. Duk da Umarni ne ba zan miki dole ba amma ki sani zubar da cikin nan kamar makullin auran ki ne, taurin kai kuma na ƙin zubarwa dai dai ya ke da rasa komai na ki, in na ce komai ina nufin komai. Kuma wallahi sai kin yi nadaman saɓa ma umarnina."
Yana gama faɗin haka ya fice ya bar mata bedroom ɗin. Ummu ta rasa wani tunani za ta yi, sai take ganin kamar a mafarki gaskiya ne abin da ke faruwa ko ƙarya, amma kuma kamar da gaske, ganin ta kawai ta yi tana tafiya a falo ta iske Habib zaune a saman kansa ta tsaya tana kallon shi cikin mamaki, so take yi ta ga shin Habib ɗin ta ne ko sauya mata shi aka yi amma ba ta gano wani abu da zai saka Habib ɗin ta ya sha bambam da wannan dake zaune a gabanta ba.
Tashi ya yi zai bar mata falon da sauri ta sha gaban shi tana faÉ—in" Noori an ya kasan me kake faÉ—a kuwa?
Ta faɗa muryanta na rawa kaɗan ya rage ta fashe da kuka
"Kwana uku na ba ki , ki yanke ma rayuwarki hukunci. Kwana uku kacal."