Sashe 32
Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Baffa Umaru ya faɗa yana kallon ta ganin yadda ta ɗan rame, yana shigowa Jimeta
Harkokinsa sosai kuma yana zuwa gidan É—an'uwan na shi, kuma duk abin da ya danganci yaran Baffa na ba shi girman shi yana saka shi a ciki.
Kan Ummu na ƙasa ta amsa ta kasa mgana, Ammah ta kalle ta ta gefen ido kafin ta ce" Ke kaɗai kika zo? Ina shi Habibun?
"Yana waje."
"Bai shigo ba kuma?
In ji Ammah sai ta gyaÉ—a kanta kafin ta ce" Zai shigo daga baya."
Ammah ba ta sake magana ba ta miƙe ta kwashi farantin kwanukan da su Baffa suka yi amfani da shi ta fita zuwa kitchen.
Baffa Umaru ya sake tambayan Ummu Salma abin da ke faruwa ta sake warware mishi kamar yadda ta warware ma Baffa a farkon maganar.
"Wannan ai ba mgana ba ne, shi ma bai taki gaskiya ba."
Ya faɗa cikin ɓacin rai Baffa na gefe ya kaɗa kai kafin ya ce" Kuma tunda har an samu cikin maganar a zubar da shi ai bai ma taso ba."
"Sosai, bari Baban na shi ya ƙariso a zauna zan faɗa masa ba mu yadda da wannan tsarin ba."
Ita dai kanta na ƙasa ba ta yi magana ba ganin sun faɗa wata hiran ya sa Baffa ya ce ta je wajen Ammah kafin waliyin Habib ya iso, sai ta tashi a sanyaye ta koma ɗakin Ammah ta isketa tana shara, ta yi saurin ijiye jaka za ta karɓa da sauri Amma ta ce" Ke bar shi, ba ki jin daɗi je ki kwanta ki huta"
Fir Ammah ta ƙi sakar mata sharan dole ta haƙura ta koma ta zauna a saman kujera ta yi tagumi.
"Kin ci wani abu kafin ki fito?
Sai ta girgiza ma Ammah kai amma ba ta yi magana ba.
"Akwai kunun gyaÉ—a da kosai za ki ci?
Da sauri ta ce" Zan sha Ammah."
Saboda tana son Æ™osai ta daÉ—e ma ba ta ci ba kunun É yaÉ—an ma tana son shi har Æ™amshin É yaÉ—an take ji yanzu a hancin ta.
Ammah da kanta ta ajiye sharan da take yi ta je Kitchen ta zubo ma Ummu kunun sannan ta zuɓo mata ƙosan a wani faranti, ta kawo mata har ɗaki aiko ta zauna ta shan kunun tana cin ƙosan har wani lumshe idanuwanta take yi saboda da daɗi addu'a take yi a cikin zuciyarta Allah ya sa kar ta yi amai, Ammah na ta kallonta ta gefen ido. Tana sake tausaya ma rayuwar Ummu ta sake ramewa bisa ranar da ta zo har a cikin zuciyarta ta ke jin tausayin Autar nata kuma tun da ta ji wannan lamarin ba ta sake barci  tun daga dare har safe ba, addua'a take yi ba dare ba rana, tana roƙon Ubangiji da kar ya kaddara ma Ummu zawarci da kaddaran aure, domin kaddaran tana da nauyi Ummu Salma ta yi ƙanƙanta da fuskanta hakan.
Allah ya taimaki Ummu har ta gama shan kunun ta da ƙosai ba ta ji amai ba Ammah kuma ta gama sharan ta ta shiga wanka kafin ta fito har Alhaji Sheriff ya iso ashe shi Habib ya jira daga waje su Baffa suka fito sai suka shigo da su, ba daɗewa sai ga Hamma Abdullahi, Ummu ba ta ji wani fargaban zuwan shi ba tunda shi ɗan ba ruwan mu ne ɗakin Ammah ya leƙo duk da sun daɗe ba su haɗu ba, ko a fuska bai yi mamakin ganin ba, ballatana ya fahimci tana cikin wani hali.
"Ina kwana Hamma"
Ummu ta faÉ—a tana gyara zamanta kallonta ya yi kafin ya ce" Aa Ummu ke ce?
Sai ta gyaÉ—a mata kai.
Gaisawa suka yi sannan ya tambayi Amma sai ta ce tana wanka ficewa ya yi duk da ya yi mamakin ganin Ummu da mijinta tare da ƙanin mahaifinsa ya san da matsala amma bai tsaya tambayan matsalan ba, mgana ya zo su yi da Baffa amma ganin sa da ɓaki ya sa kawai ya bar gidan, ƙarin mamakin shi ganin har da Baffa Umaru ya ta so daga Mubi lamarin ya girmama a cikin zuciyarsa dai ya yi fatan koma mene ne Allah ya daidaita.
Kafin Amma ta fito wanka Baffa da kansa ya leƙo falon Ammah ya kira Ummu, hijabin ta sanya sannan ta bi bayan Baffa zuwa cikin ɗakin sa. Kan ta a ƙasa ta shiga cikin ɗakin a gefen su Baffa daga hannun dama ta zauna a saman cafet sannan ta ɗan ɗago kanta tana gaishe da Alhaji Sheriff wanda ke zaune shima a ƙasan cafet gefen shi kuma Habib ne ƙansa na ƙasa kamar na gari.
"Lafiya lau, kina lafiya dai ko?
Alhaji Sheriff ya faÉ—a bayan Ummu ta gaishe shi.
Kanta na ƙasa ta amsa da lafiya lau.
Bayan buÉ—e taro da addu'a, da Baffa Umaru ya yi sai ya maimaita abin da Baffa ya kira shi ya sanar da shi kan matsalan da ke faruwa tsakanin Ummu da Habib.
"Tabbas haka ka kira ni ka faÉ—a mini nima, nima na kira shi na yi masa mgana. Saboda ma a samu daidaito shi ya sa na ce gwara mu haÉ—a su gabaÉ—aya."
Alhaji Sheriff ya faɗa Baffa Umaru ya amsa da haka ne Baffa dai na gefe bai saka baki ba, Habib kuma kansa na ƙasa bai ɗago ba sai yanzu ya fahimci Ummu ta ɓoye ma iyayenta wasu abubuwan. Sai da ya murmusa lalle ta yi kuskure wataƙila da ta sanar da su duka abin da ke faruwa da sun sauƙaƙa mata wasu abubuwan da suke jiran ta anan gaba.
"Yanzu maganar zubar da ciki ba ta, na yi masa faɗa sosai kuma ya yi mini alƙawarin in sha Allahu hakan ba zai sake faruwa ba"
Alhaji Sheriff ya sake faɗa cikin taushin murya, Ummu ya sake kallo kafin ya cigaba da cewa" Ki yi haƙuri kin ji ko?
Sai ta gyaÉ—a kanta hawaye na kece mata ta saka gefen hijabin ta share da sauri.
"To Alhamdulillah mun ji daÉ—in da aka samu masalaha cikin lokaci. Kai Habibu abin da ka yi ba ka yi daidai ba tunda har cikin nan ya shiga ba ku É—au wani mataki daga farko ba, to sai dai ka yi hakuri Ummu Salama ta haihu, daga baya in kuka zauna kuka samu fahimtan juna za ku iya bari sai a lokacin da kuka sake shiryawa ku sake haihuwa wannan tsarin ku ne, ba ruwan mu a ciki amma mganar a zubar da ciki bai yi daidai ba kuskure ne mu kuma a matsayin mu na iyayen ku ba za mu bari ku kauce ma hanya ba shi ya sa muka shiga ciki domin mu samar muku da masalaha kuma Alhamdulillah kwalliya ta biya kuÉ—in sabulu."
Habib ya yi shuru yana sauraran Baffa Umaru har ya gama jawabinsa.
Baffa da ba zai yi mgana ba Baffa Umaru ya ce ya É—an tofa wani abu mana.
"Ni ba ni da wani abin da zan ce duk abin da zan faÉ—a kun gama faÉ—a sai dai ba zan fasa tunsar da su abubuwa guda uku zuwa huÉ—u ba."
Habib ya kalla sannan ya kira sunan shi.
"Habibu."
Sai da ya É—ago kansa sannan ya amsa da Naam Ummu ma ya juya ya kira sunan ta.
"Auta."
"Naam Baffa."
"Ku sani aure ibada ne, kuma shi da man ibada sai an ɗaure za a samu riba, dukkan ku saboda kun aminta da juna kuke zaune a inuwa ɗaya na aure. To ina so ku sani sai kun yi hakuri kun girmama junan ku , sannan za ku samu fahimtar juna. Ku sani ibadar da kuke yi sakamakon ku na wajen ubangijin ku, saboda haka in kuka yi wani abu saɓanin umarninsa ma duk yana sama yana kallon ku. Daga karshe ina mai sanar da ku da cewa ku ji tsoron Allah. Ku zaauna lafiya ku girmama zamantakewarku Allah ya yi muku albarka ya sake kaɗe fitina a tsakanin ku."
GabaÉ—aya su Baffa suka amsa da Amin, Ummu ma ta amsa a cikin zuciyarta Habib ne bai amsa ba domin kalaman Baffa sun shiga ne sun kuma fita, domin gani yake yi kamar ba su da amfani a wajen shi, bai so ya yi magana ba sai da Alhaji Sheriff ya É—an zungure shi sannan ya É—an yi gyaran murya yana faÉ—in.
"Ku yi haƙuri Baffa in sha Allahu hakan ba zai sake faruwa ba."
Habib ya fada yana ɗan cije baki, Baffa ya ɗan jinjina kai kafin ya ce" Na ji daɗin haka. Ubangiji ya zaunar da ku lafiya."
Zaman bai wani ɗau lokaci ba tunda an samu matsaya, Baffa ya ce Ummu ta tashi ta bi mijinta ta koma gidan ta, tun da dalilin da ya kawo su an samu masalaha, Ammah ba ta fito ba kuma Habib bai neme ya shiga ya gaishe ta ba suma su Baffa ba su buƙaci haka ba, Ummu kaɗai ta shiga ta yi ma Ammah sallama.
"Ki kula da kanki kin ji ko?
Sai ta gyaÉ—a ma Amma kai kafin ta ce" In sha Allahu Ammah"
Daga nan suka yi sallama har ƙofar gida su Baffa suka raka su, Alhaji Sheriff ya shiga motarsa shi ya fara tafiya sannan su daga baya, har sun shiga mota Baffa ya ƙwanƙwasa ma Habib gilashin mota ta bangaren sa, bayan ya zuge gilashin Baffa ya kalle shi lokaci ɗaya yana kallon Ummu kafin ya kira sunan shi.
"Habibu"
Ya amsa ƙansa na ƙasa amma a cikin zuciyarsa faɗi ya ke yi an fa dame ni
"Kai ne da kanka ka zo ka ce kana son Auta na kuma ba ka ita cikin yaƙinin cewa za ka iya riƙe mini ita amana. Ko ba haka ba?
"Haka ne"
"To ina so ka sani amanarta da na baka tun ranar da ta tashi a ƙarƙashin ikona na ke so ka sake tunawa. Habibu kar ka saka na ji na sare bisa yaƙinina akan ka, don Allah ka riƙe mini Ummu bisa amana da gaskiya."