Sashe 37
Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Haka ko aka yi yan biyun ya É—auka a mashin, da Isma'il a gaba domin shima rigima ya saka sai ya je, ga shi karami É—an shekara 4 amma ya iya rigima Ammah ta yi ta tsaki tana faÉ—in iyayensu sun sangarta su.
Saudat aka bari da Ammi za su taho tare da Nauwara da ta ce in ta ga Hamma Jibo ya daÉ—e za su hau kekepep ne su tafi.
**
Gidan Akhaji Sherif bai da wuyar ganewa suna shiga anguwar tambaya ɗaya suka yi aka kawo su tunda sananne a anguwa sakamakon fitattacen ɗan kasuwa ne, suna zuwa ƙofar gidan Baffa ya kira shi ya ce sun ƙariso da man shi yake jira ba daɗewa sai ga shi ya fito ya tarbi Baffa.
Hamma Jibo ma ya gaishe shi ya amsa cikin sakewa yana kallon shi
"Jibril jibo kenan babban yaro na ne, yana aiki Abuja."
Nan da nan Alhaji Sheriff ya washe baki suka yi musabaha da Hamma lokaci É—aya yana cewa' Ai na ga kama "
Da ya yi ma Baffa ta yin shiga cikin gida cewa ya yi ba zai shiga ba sai da ya yi masa magiya sannan ya amince suka shiga falon gidan Alhaji Sherif an kawo musu ruwa Baffa ne kaÉ—ai ya sha ban da Hamma Jibo.
"Alhaji ina fatan lafiya ko? Duk da dai lafiya ba za ta saka ka taso da kan ka zuwa wajena ba."
"Wannan gaskiya ne."
Baffa ya faÉ—a kafin ya gyara zama yana faÉ—in" Alhaji a matsayin ka na waliyin Habibu kai muka sani a matsayin wakilinshi shi ya sa da lamarin zubar da ciki ya taso muka neme ka, domin ka tsawatar masa."
"Gaskiya ne wannan."
Alhaji Sheriff ya fafa cikin gamsuwa da kalaman Baffa.
"To a wannan karon ma shi ya sa na sake neman ka."
"To. Me ya faru?
Ya tambaya cikin son ya ji kuma wani abu Habibu ya sake fitowa da shi.
"Ko maganar zubar da cikin ne bai barta ba har yanzu?
Alhaji Sheriff ya sake tambaya yana mai kallon Baffa.
"Ba shi ba ne, amma kuma ya fito da wani tsarin ne, ya fara yi mata horo da yunwa a takaice dai ya bar ta, tana ci da kanta jiya É—an'uwanta ga shi nan ya je gidanta ya dawo mini hankali tashe. Ya rantse mini har ga Allah bai ji daÉ—in ganin Auta a cikin yanayin da ya gan ta ba."
"Horon yunwa kuma? Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un.
Alhaji Sheriff ya faÉ—a cikin tashin hankali Baffa kuma ya cigaba da warware masa duka halin da ake ciki.
"Habibu bai sauya ba, duk abin da ya faɗa a gaban mu a gaban ka duk yaudara ce ya san tana da ciki kuma yana mata horon yunwa in yana tunanin wahala zai iya sanadin ciki ba ya tunanin halin da Ummu za ta shiga! Tsakani ga Allah Alhaji na kasa haƙuri da wannan rashin imanin horon yunwa ga mai juna biyu hatsari ne, bai rasa abin da zai ba ta ta ci ba, sai na fahimci kawai mugunta ne da son zuciya irin na ɗan adam "
Alhaji Sheriff ya ji zufa na keto mai saboda nauyi da kunya.
"Assha wannan lamarin bai yi daÉ—i ba Alhaji."
Ya faɗa cikin takaici da baƙin ciki.
"Wallahi bayan mun zauna da ku, ni da kaina na sake kiran shi na yi masa faÉ—a ya ce mini komai ya wuce, ko shekaranjiya mun haÉ—u a gidan su a gaban mahaifin shi na tambaye shi komai lafiya ya amsa mini da lafiya lau ashe ya yaudare mu ne ba mu sani ba"
Baffa ya jinjina kai kafin ya ce" Tabbas ya yaudare mu, bai saduda ba."
"Kai, amma Habibu ya ba ni mamaki,."
"Mu ma duk ya shayar da mu mamakin sa."
Baffa ya faÉ—a yana kallon Alhaji Sherif da Habibu ya gama kunyatawa a idanuwan su Baffa.
"Ka yi hakuri Alhaji bari na kira shi yanzu."
Da sauri Baffa ya ce" A'a ba sai ka kira shi yanzu ba. Ga dai saƙo na a gare shi in ya zo ka faɗa masa."
Shuru Baffa ya yi na É—an lokaci kafin ya cigaba da faÉ—in"
Ka sanar da shi in ya gaji da Ummu Salma ne to ya dawo mini da ita gida ni ban gaji da ita ba. Da ita da cikin jikinta duka suna da kyakyawan gurɓi a gidana."
Alhaji Sheriff ya ce" Aa ba za a yi haka ba Alhaji."
"Haka za a yi, sannan daga ƙarshe ka sanar da shi cewa lokacin da na aura masa Ummu Salma bai ganta cikin yunwa ba, saboda haka ba shi da hurumin yi mata horon yunwa a na shi gidan."
Baffa na gama faɗin haka ya miƙe yana gyara babban rigan shadda faran dake jikinsa.
"Jibo ta shi mu tafi."
Ya yi gaba Alhaji Sherif ya biyo bayan shi yana ta bashi haƙuri har waje.
"Don Allah Alhaji ka yi haƙuri. Wallahi ba da yawun mu Habibu ke yin wasu abubuwan ba tabbas ba san me ya sa ya koma haka ba."
"Ba komai, ba a dole in ba ya son ta babu matsala in ya dawo mini da ita."
Alhaji Sheriff ya yi ta ban haƙuri Baffa ya nuna masa ba komai amma in har Habib ya gaji to ya dawo da Ummu gida.
Sallama suka yi cikin girma kafin Baffa ya shiga mota Hamma Jibo ya tada motar suka bar layin.
Sai da suka hau titi sannan Hamma Jibo ya kalli Baffa da ya yi shuru yana faɗin" Baffa kana ganin Auta ba ta yi ƙanƙanta da zaawarci ba?
"In abin da Allah ya kaddaro mata kenan ai ba mu da yadda za mu yi Jibo amma tabbas yaron nan ya gaji da zama da Auta duk ya nuna alamun haka a bayyyane."
Hamma Jibo ya yi shuru bai yi magana ba sai dai yana ta furzar da iska daga bakin shi alamun lamarin ya dame shi.
"Kar ka damu, Fatima ta dawo hannuna a bazawara tana da shekaru sha bakwai ne, yau ina take? Tana can tana rayuwarta da mijinta da ya'yanta bai wuce ba, ya wuce Jibo sai dai mu tuna kawai. To itama Auta in hakan ta kasance da ita na san za ta ji ba daÉ—i amma in ta yi hakuri komai zai wuce ya zama wata rana sai labari."
Hamma Jibo ya jinjina kai yana mai gamsuwa da maganganun Baffa tabbas gaskiya ya faɗa duk kaddaran da ta same ka, in ka yi haƙuri wata rana za ka tuna har ka yi dariya.
Baffa ya yi ƙokari sosai ya san Baffa na da kara sosai amma akan ya'yan shi ko yan'uwan shi ba shi da wannan karan zai yi kawaici na farko na biyu ana uku kuma zai shiga gaba, sau tari in Baffa ya yi wani abun kamar ba jinin fulani a jikin shi, yana da kunya amma bai cika bari kunya na cutar da shi ba, Ammah ce mai kara da kunya kan ƴa'ƴan ta komai na su kuma da man Ummin ikki ne ke shigewa gaba. Ita in an ganta a gaba-gaba Lamiɗo ne da duk abin da ya shafe shi, in ko ba shi ba, ba ruwanta da sha'anin kowa ballatana ma ta shiga.
Da suka koma gida Amma ta faÉ—a ma Baffa Abdullahi ya zo neman shi ba ya nan, nan da nan ya É—aga waya ya kira shi ya ce ya zo gida ya same shi ya dawo.
Hamma Jibo kuma Nauwara ya É—auka a mota tare da su Saudat zuwa gidan Ummin ikki daga can zai wuce da su gidan Abdullahi.
Ko da wasa Baffa bai sanar da Ammah abin da ke faruwa ba, duk da ya san ta da kawaici amma yana da tabbacin yadda ya iya shanye damuwarsa ita ba za ta iya shanyewa ba, za ta shiga damuwa sosai ko da ba za ta yi magana ba.
***
Alhaji Sheriff tun fitan su Baffa daga gidansa yake kiran lambar wayar Habib amma ba ya samun shi har dare kuma bai same shi ba sai ya kira Malam Usman, ƙani yake gare shi, kuma shi ke bi ma mahaifin Habibu a haihuwa nan ya warware mishi komai, shi da yake ba shi da hali sosai Alhaji Sheriff duk a cikin su ya fi su rufin asiri.
"Assha Habibu bai yi tunani ba ya ɓata wayon sa sam."
Malam Usman ya faɗa cikin mamakin Habibu har da shi a cikin maganar auran nan na Habibu iyayen matarsa masu mutumci da ƙima ne.
"Wallahi Usman Habibu ya gama zubar mana da mutumci, na yi ta kiran wayarsa ban samu ba in na same shi zan ce gobe goben nan mu haɗu gaban mahaifinsa da uwar riƙon sa, na maimaita masa saƙon uban matarsa a gabansa sannan na zare hannuna a sha'aninsa ya je can ya yi duk abin da ya ga dama tun da ba ya jin shawara."
"Aa ba za a yi haka ba Yaya Sheriff. In ka ce masa haka ai sai ya sake lalacewa. Gwara dai mu taru mu sake jan kunnen sa, in ka same shi a waya ka sanar da ni, sai mu haÉ—u gabaÉ—aya mu sake jan kunnen sa."
"Allah ya sa ya ji to. "
Alhaji Sheriff ya faÉ—a cikin takaici sun cigaba da tattaunawa duk da dai akan mganar kafin su rabu da juna akan sai Alhajin Sheriff É—in ya kira shi in ya samu Habib a waya.
A ranar dai bai same shi ba sai a washegari, sai dai ya sanar da shi ba ya Jimeta yana Abuja a wajen aiki an tura su wata Seminar, kuma ba za su dawo ba sai gobe lahadi da yamma, nan take Alhaji Sheriff ya ce masa in ya dawo a daran su haɗu a gidan su bayan isha'i ya kashe wayarsa ba tare da ya jira cewar Habib ɗin ba, ya bar shi cikin tunanin abin da ya faru, ya san abin da ya yi shi ya sa ya kawo tunanin maganar Ummu Salma ce.
"Kai wannan yarinyar kamar mayya wai sai na ce mata na sake ta ne za ta gane na gaji da ita ne?