Sashe 1
Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*FARGAR JAJI.*
*Wattpad:JamilaUmar315*
*Arewabooks:JamilaUmarJanafty*
*To Hajiya Hauwa'u Inuwa Aminu (Anty Hairi) with love and gratitude"*
*"Littafin FARGAR JAJI goro ne zuwa ga Hajiya Zainab Inuwa Isah AUNTYSIS(My Anty) with your support na fara wannan labarin kuma da support É—in ki na rufe shi. Thank you for always being there for me. It means the world"*
*Littafin FARGAR JAJI na musamman ne zuwa Yayana JAMILU UMAR wanda ya yi aure ranar 04 ga watan April tare da Amaryansa Mariya Iman. Ina fatan Allah ya ba ku zaman lafiya tare da zuru'a masu albarka Amin.*
*Tukwaicin Littafin FARGAR JAJI zuwa ga DR FADILA KABIR. Anty Fadila tana sona tana son cigaba na, yadda kike sona da kula da al'amurana Ubangiji ke ma ya so ki, ya tsare gaban ki da bayan ki ya albarkaci rayuwar su Maheer Amin*
*Yabon Littafin FARGAR JAJI zuwa Aminiyata AISHA ALTO, na yaba miki Tawan Ubangiji ya yaba miki Allah ya dauwamawar da farinciki a rayuwar auren ki, Allah ya raya mana Noor da Yumna Amin*
*Fatan alheri ga Ƙannena masu kula da ni tare da rubutuna. *AISHA UMAR*,
*MARIYA UMAR(Hajiya)*
*Allah ya taimake ku, ya ba ku sa'a akan karatun ku Amin.*
*Jinjinar littafin Fargar Jaji zuwa Surayya Dee. Kawata mutuniyar kirki mai zuciyar zinare, kina da karamci da dattako Janafty ta gode miki Ubangiji ya ba ki zuru'a masu albarka Allah ya jiƙan magabata Amin*
*Gaisuwar littafin Fargar jaji zuwa ga iyayen É—akina*
*Khadija Salisu Yusuf*
*Haj Habiba Abubakar Imam (Yayata)*
*Haj Niima Bala Rabi'u (Anty Niima)*
*Haj Halima ÆŠalha Shehu (Umma)*
*Haj Hadiza Mahe Muhammad*
*Haj Sadiya Abu.*
*Haj Samira Baffa*
*Haj Zainab Abdulwahab*
*Haj Aisha Ahmad Iya*
*Haj Lubabatu Musa(Mama)*
*Barrister Salamatu Doma(Mommy)*
*Haj Halima Wada Kura*
*Godiya ga ƙawayena*
*Halima Yusuf Gwarzo( Besty)*
*Maryam Jumare*
*Nana Halima(Masoyiya)*
*Jamila Umar(Namesake)*
*Aisha Umar Ibrahim(Tawan)*
*Hafsat Mustapha(Sahiba)*
*Sumayya Bashir Kugu*
*"Na gode sosai Allah ya saka muku da alheri ya Allah ya bar zumunci.*
*Gaisuwar sada zumunci ga Aminaina*
*Maryam Aminu Musa(Kitty)*
*Ummulkhairi Sani Panisau(Khairi)*
*Muhammad Sani Lawal(Sayyid Amanar Janafty)*
*Sadeeq Rufa'i ÆŠanguguwa(Sadi namu)*
*Iyalan Fam ina son ku, Ubangiji ya so ku, Allah ya ƙara haɗa kawunanmu tare da danƙon zumunci na har abada Amin.*
*Fatan alheri zuwa ga Maryam Saminu Sulaiman(Anty Maryam). Wannan gaisuwar ta musamman ce daga Janafty tare da Surayya Dee. Mun gaishe da shugabar masu sharhi Allah ya yi ma rayuwa albarka Amin*
*Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai, Bismillah.*
https://chat.whatsapp.com/IF0uPZWtcCOIczsjhdCbIZ?mode=gi_t
https://www.arewapen.com/u/jamilaumarjanafty
*01*
*SHIMFIÆŠA*
*NIGERIA.*
*ADAMAWA:YOLA.*
Jahar Adamawa(Fula: Leydi Adamawa) jaha ce da ke shiyyar Arewa maso gabashin na shiyyar Nageria. Jihar Adamawa na daga cikin Jahohin mafi girma a Nageria, kuma ta mamaye kusan faɗin 36,917sqkm. Jahar ta haɗa iyaka da Barno daga arewa maso yamma. Gombe jaha daga yamma taraba daga kudu, maso yamma a yayin da ta haɗa iyaka da ƙasar kamaru daga gabas. Jahar ta samo asalin sunanta ne daga tarihinta daga Masarautar Adamawa, tare da tsohon babban birnin Masarautar watau YOLA wanda take a matsayin babban birnin Jahar Adamawa a yau.
Jahar ta kasance daga cikin mafi rabe-rabe tare da harsuna na asalin garin dabam-dabam fiye da guda 100. An kafa Jahar a shekaran 1991 a sa'anin da a ka raba tsohuwar Jahar gongola don samar da Jahar Adamawa da Taraba.
A cikin jihohi guda 36 na Nigeria. Jihar Adamawa ta fi kowacce girma ta fuskar faɗin ƙasa, amma ita ce ta 13 a jerin jihohi masu ƙarancin yawan jama'a tare da kimanin mutum milayan 4.25 dangane da ƙiyasin shekaran 2016. Dangane da yanayin kasa kuma jihar ta ƙunshi tsuddai da tsaunuka(kamar su Atlantika, mandara da kuma shebshi) da kuma tsaunin Adamawa pleateu tare da kogi zagaye da tsaunika.
Yanayin damshin zafi/Sanyi na Jihar Adamawa yana farawa ne, a watan nuwamba, garin na da zafi sosai musamman a lokacin zafi, sannan lokacin sanyi na farawa ne daga watan december zuwa watan fabarairu na kowacce shekara.
****
*YOLA:JIMETA*
*AREA:Jalingo street.*
*7:20PM*
JImeta birni ne, a garin Yola ta jihar Adamawa Nigeria. Yawan mutane garin ya kai 73,080 a shekaran 1991. Tsayin Jimeta yana da mita 135, kuma yana gefen kogin Benue.
Ta duba agogon wayarta sau shurun masaƙi ba tare da ta gaji ba, zaune take a saman kujera mai zaman mutum biyu da suka yi ma falonta ƙwanya. Ta yi kwanciyar rigingine tana kallon rufin POP ɗin da ke falon. Ƙaramar fankar dake saman ɗakin ke gudu idanuwanta na wajen kamar tana ƙirga adadin juyawar da fankar take yi a zahiri. A baɗini kuma hankalinta ba ya wajen zuciyarta da hankalinta sun tafi tunanin me ya hana Habib dawowa gida a lokacin da ya saba dawowa?
Ajiyar zuciya ta sauke lokaci ɗaya tana sake nisawa, sannan ta tashi daga kishigiɗan da ta yi ta samu nasaran zama sosai a zaman kujeran, wayar da ke gefenta ta miƙa dogon hannunta fari tas mai ɗauke da ƙunshi ja ta jawo wayar ta latsa gefe haske ya bayyana Idanuwanta na kan lokaci dai dai agogon wayarta na ƙara minti ɗaya daga cikin mintinan da ya ke ƙirgawa.
7:30Pm, iskar bakinta ta fesar kafin ta miƙe a kasalance, kasalan da ta fara jin tana muƙurƙusan jikinta a kwana biyu nan, bakin window ɗin dake falon ta isa ta yaye labulan tana mai kai duban ta zuwa haraban gidan da ba ka ji motsin komai sai ƙaran wucewar iska, sai kukan tsuntsaye, akwai haske tarwar a haraban gidan saboda akwai wutar nepa ta kai duban ta zuwa ga flat ɗin da gefen su, shima dai shuru amma akwai haske daga cikin gidan alamun masu gida suna ciki suna gudanar da rayuwar su kamar kullum, idanuwanta ya hango mata motar mai gidan a fake a bakin compoud, sai ita kaɗai ne mijinta bai dawo gida ba?
Gidan su gidan haya ne, sun kai kimanin su shidda a ciki. A jere flat ɗin suke amma suna sharing filin compound ɗaya, sai ka yi sati biyu ba ka haɗu da wani na kusa da kai ba wasu ma ana yin wata, wani lokacin ma in dai ba fita za ka yi ba, wataƙila wata ma ta fito za ta fita sai ku haɗe ku gaisa amma ba mai shiga bangaren kowa musamman da yake akwai ma'aikata da masu fita makaranta a gidan.
Ta yi wani luu da idanuwanta lokacin da iska ya taso sai ta kai kallon ta ga sararin samaniya, ashe haɗari ne ya haɗu sosai sannan ya ta so lokaci ɗaya da iska, suna cikin tsakiyar damuna ne, ana yawan samun ruwa musamman ma da daddare. Sanyi ne ta ji ya fara shigar ta har tsikar jikinta na tashi, saboda ƙaramar riga ce a jikinta. Sai ta yi saurin rufe window ɗin ta zuge labule ta ƙamƙame jikinta da gudu-gudu sauri-sauri ta koma kan kujeran da ta tashi ta zauna, wayarta ta sake jawowa a karo na uku ta sake kiran lambar Habib da ta yi ma Saving da NOORI, kamar sauran kiran wannan ma har ya katse bai ɗaga ba sannan bai biyo baya ba, ta fara jin ba daɗi saboda ba haka ya saba ba, duk in da ya ke yana dawowa gida kafin sallar isha'i, in kuma zai kai bayan isha'i a waje sai ya kira ta ya shaida mata. Amma yau ya makara kuma tana ta kiran shi bai ɗauka ba sai ta fara tunanin wataƙila ba lafiya ba ko wani abu ne mara daɗi ya same shi?
"Aa ba abin da zai faru da Noori na"
Ta faɗa a fili tana mai furzar iska daga bakinta, ƙokarin karfafa ma kanta gwiwa take yi na cewa ba abin da ya same shi, saboda ita ba ta iya shiga damuwa ba yanzu nan sai ta rasa hankalinta. Ta fi karfafa ma kanta gwiwa da cewa wata ƙila ya biya ta gidan su ne, wata ƙila can ya tsaya shi ya sa ya ɓata lokaci bai dawo ba, sannan watakila wayarsa na silent ko bata tare da shi, shi ya sa bai ji kiran ta ba.
"In sha Allahu yana lafiya. Ki natsu Ummu-Salma."
Ta faɗa a fili tana sake karfafa kanta, ajiyar zuciya ta riƙa saukewa a jere har sai da ta samu natsuwa sannan ta iya sauke numfashi a hankali. Jikinta ta bi da kallo a duk dare a irin wannan lokacin haka take yin ado domin tarban mijinta Habib, yau ma ɗin ba ta sauya zani ba ta yi adon ta cikin riga da wando, rigar ba ta ko rufe mata cibi ba, kuma sagalan hannayenta na vest ne shi ya sa take jin sanyi na shiga jikinta, sannan wandon jikinta iyakarsa ƙwarinta sannan ya ɗameta sosai ya bayyana suran jikinta. Kanta ba ɗankwali gashinta ta saka band ta ɗaure ta saki jelan daga tsakiya, fuskarta ba kwalliya ta yi sosai ba amma ta saka jan baki mai ƙyalli yana ɗaukan ido, daga ita har falon suna tashin ƙamshi mai sanyaya zuciyar ma'abocin son ƙamshi.
Ummu-Salma Hadi BaBa farar mace doguwa, Bafullatan hausa-fulani daga tsatson fulanin Mubi, haihuwan Jimeta, ba sai an faɗa maka ba kana ganin ta za ka shai da ita ɗin jinin fulani ce daga yanayin ta da komai na ta, sannan da yanayin mganarta da ba ta da hausa sosai, kyakyawa ce ajin farko ga fari ga hanci ga zati da zubi, komai na cikar ƙimar mace ubangiji ya riga ya bata. A ƙiyasin shekarunta ba za ta gaza shekaru 24 a duniya ba.
Lokaci bayan lokaci tana cigaba da duba agogon wayarta, har takwas ta kusa saura mintina goma, ga shi har an fara yayyafi. Ganin haka ya sa ta miƙe ta buɗe ƙofar tiolet ɗin dake tsakanin bedrooms ɗin ta guda biyu ta ɗauro alwala, bedroom ɗinta ta shiga mai ɗauke da makeken gado da wardrope, hijabin sallan ta na saman gado da ta yi sallar mangariba shi ta zura bayan ta shimfiɗa sallaya ta da salla, bayan ta idar tana zaune tana ƙirga yatsunta lokaci ɗaya ta ƙura ma waje ɗaya ido tana tunani.
"Wai ina Noori ya tsaya ne?