← Book details Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 92

Sashe 71

Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shi ko bai wani daɗe ba ya fito daga wankan, sai da ya tabbatar da Balkisu ba ta ɗakin sannan ya saki jikinsa da ga shi sai towel ɗaure a kugunsa ya fito ba ya ɓata lokaci wajen shiryawa yanzu ma cikin lokaci ya shirya ya saka farar shadda gezner ɗinkin zamani riga da wando, rigar yau har ta fi sauka masa saboda yau jumma'a za su je masallaci tare da su Baffa, wani nishaɗi yake ji tun safe na tunowa da rayuwar baya amma labarin da Balkisu ta bashi ya ɗan hanashi sukuni.
Taje kansa ya yi da gemunsa da yake tunanin yau zai je gyaran fuska a rage masa gashin fuska. Turare ya fesa kaɗan saboda shi ba ya son kamshin turare ya yi masa karfi da yawa yanzu kan shi zai fara ciwo, ko Balkisu ta cika turare har kansa yake hawa in kuma ya shaƙa da yawa haka zai yini da ciwon kai, bai taɓa ce mata ta daina sawa ba, saboda shi a tunanin shi saboda abin da ba ya so shi kaɗai ba zai tauye mata haƙkinta tunda ita tana so ba.

Shi ya sa ko ba ya son abu ba ya faɗa, gani yake yi kamar son kai ne. In kuma yana son abu shima ba ya faɗa gani yake yi don shi kaɗai yana son abu kaza kamar ya shiga haƙƙi ne ya ce kowa sai ya so abinda yake so ko ya zama irin sa ba.
Sai ita Bilkisun ce da kanta ta gano ba ya son mu'amala da turaruka tunda in ya yi birthday tana siya masa a matsayin gift zai karɓa amma sai shekara ta sake zagayowa bai taɓa amfani da shi ba, uban turarukan dake ɗakin shi kamar za a buɗe shago amma baya amfani da su tun daga lokacin ta fahimci bai cika son ƙamshi ba, ita kuma gata tana son ƙamshi tana mu'amala da turare sosai in ka yi mata kyautar turare ba ta mantawa.

Ba ta daina amfani da shi ba amma in suna tare sai ta yi amfani da mai sauƙin ƙamshi, ita fa koda yaushe jikinta a cikin ƙamshi yake duk bayan wata ɗaya tana zuwa a yi mata gyaran jiki na skin care. Shi ya sa fatar ta kamar ta turawa wajen taushi da santsi sannan ba aikin da take yi, daga zuwa asibiti ta duba patients shike nan ta dawo gida ta kwanta.
Sannan gaba da baya tana cikin jin daÉ—in rayuwa.

Kan kujeran da ya tashi ya koma ya zauna da wayarsa a hannu ƙiran samsumg ita ce wayar da yake amfani da ita na Family, shi in ba zai yi kira ko an kira shi ba sai ta yi kwanaki bai yi amfani da ita ba, a wajen aiki kuma suna da wayoyin aiki shi ya sa.

Yana so ya tambayi wani labarin abin abin da ya faru amma ba zai iya ba.
WhatsApp ya buɗe ya shiga, 24/7 datar shi tana buɗe ne tun a can ma wajen aiki suna da wifi a Lagos ma haka. Ta kwana a kunne saƙonni su yi ta shigowa amma sai a fi wata bai duba ba. Tun ballatana in yana wajen aiki bai cika duba wayar ba.
Wasu saƙonnin ma sun fi wata biyu bai duba ba.
Ya ga saƙon Mahma tana tambayan lafiyan shi?
Giransa guda É—aya ya sosa da hannu É—aya yana jin nauyi , bai kyauta ba ya kamata ya kira Mahma.

Har da saƙon Maimartaba yana faɗin sun ji shuru kwana biyu ba a samun wayarsa Fulani ta damu.
Bai amsa ma wannan ba tunda lokacin da ya koma Lagos ya yi magana da su gabaÉ—aya.
Ƙasa ƙasa ya yi ta yi, can ne ya gano group ɗin Ammah da Baffa ya dai san an buɗe amma bai taɓa bibiya ba sai yau ya shiga ya ɗan duba saƙonni.

Ya ga Date É—in da Hamma Jibo ya sanar da labarin da Balkisu take faÉ—a masa an kwarari wata biyu cikin na uku ma.
Sake sosa giran shi ya yi, haka ne ƙololuwar nuna damuwarsa, tunani yake yi ko shi ya sa daga Baffa har Ammah duk suka rame masa a ido, bai yi magana ba ne amma a zuciyarsa sai da ya ce duk sun rame amma sai ya danganta haka da ɗan daɗewar da ya yi bai gan su ba.

Fita ya yi daga group É—in, ya je ya nemo KB da sunan shi ke a matsayin Friend a wayar LamiÉ—on.
Sai ya ga ma ya yi masa mgana.

"Amini mutanen Jimeta."

Haka ya rubuta masa dubawa ya yi sai ya ga yana online.

Rubutu ya fara yi na wani lokaci kamar zai rubuta wani abu ashe kalma É—aya ne ya rubuta.

"Amini."
Ya É—an ja fasali kamar yana ganin sa.

"Me ya faru..?

Ya sake rubutawa ya tura masa sai kuma ya dakata kawai yana kallon wayar.

"Naam Amini ya gajiya! Ya baƙun ta?

"Me ne ya faru kuma!?
A ina?

Duk wayar na hannunsa saƙonnin suna ture juna suka shigo
Sai ya fara rubutu sai ya goge ya yi ya kai sau uku sannan ya samu ya rubuta.

"Ummu Salama."

"Me ya samu Ummun?
Hamma Kabiru ya turo masa cikin mamaki.
Haushin chart ɗin Lamiɗo yake ji magana ba magana ba ya rabata ya ɓata maka lokaci.

Kawai sai ya kira shi Video call kamar ba zai É—auka ba sai dai ya É—aga kiran.
Hamma Kabiru ya bayyana a cikin lap na asibitinsu yana sanye da suit da farar rigar lapcot É—in sa. A jikin lapcop din an rubuta sunan shi..
Kabiru Hadi Baba.

"Amini wai me ya faru da Ummun ne?

Ya faÉ—a yana kallonsa, shuru ya yi masa yana kallonsa sanin halin shi ya sa ya ce" Wai ko maganar abin da ya faru da sakinta da É—an iskan yaron nan ya yi?
Sai da ya É—an lumshe idanuwansa sannan ya É—an gyaÉ—a masa.
"Kai ai an kwana biyu Amini, lokacin kana can wajen aiki shi ya sa ban faÉ—a maka."
Nan shima ya shiga sanar da shi duk abin da ya faru

"Amini na so Baffa ya cire hannunsa mu kai yaron nan kotu amma kasan dai halin Baffa, Ammah ma ta goya masa baya. Ya sako yarinya ga shi ya barta da wahalan ciki tunda ya sake ta an ce ba ta kara lafiya ba, kullum kuka da rashin cin abinci, ita a damuwa su Baffa ma cikin damuwa. Amini da a ce su Baffa sun matsa ma Ummu Salma ta cigaba da karatunta da yanzu duk wannan abubuwan da suka faru wallahi ba su faru ba."

Ya karishe faÉ—a yana jin haushi in ya tuna cin mutumcin da Habib ya yi musu.
Shuru kawai LamiÉ—o ya yi yana jinsa ba tare da ya yi magana ba.

"Wai yaron nan ne zai ce shi ba son Ummu yake yi ba auren sha'awa ya yi da ita yanzu kuma tunda ya gama moranta bari ya yada ƙwallon mangwaro ya huta da ƙuda"
Lamiɗo ya sake sosa giran shi na dama wannan karon kansa ya duƙar ƙasa bai kuma yi magana ba

"Ya ce ba ya son cikin jikinta tunda ya ce ta zubar ba ta zubar ba. Baffa kuma ya ce ta haifa su suna so kuma za su riƙe, ka ji halin da ake ciki ni tun zuwan da na yi ma ban koma ba, ga tausayi in ka ganta amma haushinta zai sa in kana kusa da ita ka yi mata dukan tsiya"
LamiÉ—o ya É—ago yana kallon shi.
"Me ya sa?
Ya tambaya a hankali kamar ba ya son magana.

"To Abdulrrahaman na faÉ—a mini har yanzu tana son wannan shegen bayan ya gama tozarta ta, saki uku fa ya yi mata Amini bayan ya haÉ—o ta maganganun cin mutumci, shi ne har yanzu take so? Wallahi da ina garin nan sai na taka wuyanta tunda ita shashasha ce."

Sai da LamiÉ—o ya motsa bakinsa ya É—an murmusa.
Amma dai bai yi magana ba shi kuma Hamma Kabiru ya shiga faÉ—a ta in da yake shiga ba ta nan yake fita ba, shi dai kawai su Baffa yake ba ma laifi da ba su yi ma Ummu aure ba da duk haka bai faru ba ya manta da zanen kaddaran bawa ba ka iya guje masa.

Gajiya LamiÉ—o ya yi ya motsa bakinsa ya katse Hamma Kabiru sanin halin shi in ya fara kawo hujjojinsa sai fa kowa ya fahimce sa.
"Ammah ta damu ko?
Shi ya sa ta rame ita da Baffa."
Ya tambaya É—aya bayan É—aya.
"Ai damuwa ta zama dole Amini, gwara ma Baffa ana iya gane damuwarsa Ammah ce sai dai ta kunshe ita kaÉ—ai."

Shuru ya yi, Ammah tana cikin damuwa duk ta rame baiwar Allah. Ko saboda Ammah da yana nan aka yi haka sai ya saka an yi ma yaron nan ladabi tun da ya saka Ammah damuwa ita da Baffa.
Lamido gajiya ya yi da tsarin Kabiru ya kashe wayarsa ya ce zai je gida za su je masallacin jumma'a da su Baffa, amma ya ce in ya dawo gida za su yi magana.

Hula ya baƙa saka da wani rufaffen takalmi mai rufewa.
Har ɗaki ya bi Balkisu sai ya isketa ta yi barci har bargon ya ɗan gyara mata sannan ya fita. A falo ya iske su Sultan suka naɗe shi suna kiran sunan shi, kaya ya ce Anitha ta sauya musu tare da su zai fita ba daɗewa aka shirya su Sultan ma kamar ubansa farar shadda ya saka har da hula Beena kuma wata riga ce yar kanti a jikinta pick colour ga takalminta na mata cover mai kalan pick, gashin kanta an kama mata da kananun ribbors masu kala-kala.
Chapter 71 · 0% Book details