← Book details Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 92

Sashe 50

Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ummin ikki ta faɗa tana faman goge ƙwallah.
Baffa ya sauke numfashi kafin ya amsa mata.
"Lafiya lau. Ya za a yi da sanin Allah komai zai wuce in sha Allahu."
Baffa ya faÉ—a cikin karfin hali kafin ya sake kallonta yana faÉ—in" Sannu da kokari mun gode sosai Allah ya bar zumunci."

"Amin yiwa kai ne Baffa. Allah ya saka ma wannan yarinyar."

Kowa ya yi shuru bai ce komai ba, sai da Baffa ya sake jan numfashi kafin ya ce" Ba komai. Komai zai wuce."
"In sha Allahu."
Hamma Abdullahi ya faÉ—a cikin damuwa.

Ammah dake zaune tun É—azu ba ta ce komai ba ta É—ago tana kallon Baffa kafin ta ce" Baffa ko za ka kira waliyin Habibun. Watakila su shiga ciki su iya gyara al'amarin."
Hamma Abdullahi na shirin magana Ummin ikki ta yi saurin cewa" Tab wani gyara kuma Aminiya?
Ammah ta kalleta cikin mamaki ba ita ba har Baffa ma.

"Saki uku fa ya yi mata."

"Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un."

Baffa ya yi saurin faÉ—a cikin fitan hayyaci, Ammah kuma sai ta kasa magana amma bakin ta na motsi.

"Wallahi tozarcin da yaron nan ya yi mana kenan. Takardan sakin ma tana hannun Baba."

Ummin ikki ta gama faɗa tana nuna Hamma Abdullahi shi ko bai yi magana ba ya zaro takardan sakin cikin aljihun wandon sa ya mika ma Baffa, hannunsa na rawa ya karɓa haka fa ya karɓi na Fatima shekaru talatin baya yau ma gashi zai sake karɓan na Ummu Salma, Allah kana gani.

Nan take Baffa ya warware takardan ya fara karantawa a bayyana ne, kafin ya gama ya jiƙe da zufa kafafuwansa sun gaza ɗaukansa sai da ya yi ɗan baya ya samu damar jingina da bangon ɗakin Ammah.
Ummi ikki sai ta hau kuka tana jero ma Habib addu'an Allah ya sa, Ammah ko wani nauyi ta ji daga ƙasan zuciyan ta. Ganin ta ya yi duhu sai kawai ta dafe kanta ta kasa mgana.

"Lalle wannan yaron ba shi da mutumci."

Ummin ikki ta faɗa cikin cizon yatsa, Ummu na zaune a yadda take amma abin da Baffa ya karanta ya yi mata fami a gyambon ta wataƙila da Baffa ya san ba ta san abin dake cikin takardan ba da bai karanta kowa ya ji ba, ita ba kanta take ji ba su Baffa ya za su ji? Ita ta riga ta gama Haddace kalaman Habib na baya son ta sannan ta daɗe da fahimtar manufar auran ta zuwa gare shi, su ne suka rage su sani duk kuma yadda ta kai ga yi ma maganar rufa rufa Habib ya fallasa komai.

Baffa ya yi shuru kawai da takarda a hannunsa ya kasa magana. Zuciyarsa na wani tafarfasa in da a ce zai iya wallahi da sai ya yi shari'a da Habibu amma kuma ba zai kai shi kara a kotun duniya ba sai dai ya kai shi a kara a kotun Allah. Ya gama cutar su ya cuce Ummu Salma ya gama da rayuwarta ko da sun yi ƙaran shi a gaban hukuma wani ɓata lokaci ne, sannan tonuwar asirin auran Ummu ne ga duniya amma a ƙotun Allah ne kaɗai zai karɓi sakamakon abin da ya aikata.

"Baffa bai kamata a bar yaron nan ya tafi haka ba gaskiya."

Hamma Abdullahi ya faÉ—a cikin jin haushi.

"In ya saki Ummu ba mu yi jayayya ba, amma maganar ya bar mata ciki ba shi da alaqa da shi bai ta so ba, tunda har shi ya yi cikin nan bai isa ya ce babu ruwan shi ba in ya yi taurin kai ai akwai hukuma sai mu yi ƙaran shi "

Ya faÉ—a yana kallon Baffa da ya yi shuru ya kasa mgana.

"Gaskiya magana, ita in mun ƙarbeta tamu ce amma ai cikin na shi ne bai isa ya ce babu ruwan shi ba"
Ummin ikki ta faÉ—a Baffa dai ya yi shuru bai yi magana ba sai kawai ya zura hannu a cikin aljihun wandon sa ya zaro wayarsa.

"Wa za ka kira Baffa?

Hamma Abdullahi ya tambaya sai kawai Baffa ya ɗaga masa hannu ba tare da ya yi magana ba. Lambar Alhaji Sheriff ya nemo lokaci ɗaya ya kira shi ya kara a kunne tana ta ringing bai ɗaga kiran ba sai da ta kusa katsewa sannan ya ɗaga wayar daga can bangaren da sallama, Baffa ya amsa cikin dattakon sa ran shi a ɓace yake shi ya sa bai tsaya ma wata doguwar gaisuwa ba.

"Alhaji kana da labarin É—an ku Habibu ya saki Ummu Salma saki uku?

Daga can bangaren Alhaji Sheriff dake zaune a ɗakin da mahaifin Habib ke jinya a cikin gidan su ya miƙe a razane cikin firgici ya ce" Innalillahi yaushe? Wallahi tallahi Alhaji ban sani ba."
Ya faɗa cikin tashin hankali to da man ai ba zai sanar da kowa in zai aikata abu mara kyau ba a yanayin maganar Alhaji Sheriff za ka fahimci bai sani ba sannan maganar kuma ta dake shi matuƙa.

"To ya sake ta saki uku gata nan ma na saka an je an taho da ita."

"Hasbunallahi wa'imal wakel. Alhaji wallahi bamu sani ba. Ba mu da labarin wannan hukuncin da Habibu ya yanke"

Alhaji Sheriff ya sake faÉ—a cikin É—imuwa da tashin hankali tare da nadamar yadda ya shiga lamarin Habibu, da yau bai shiga ba tuni bai ji kunyar da ya ji yau ba.

"Ba komai Alhaji kar ka damu na san da man ba ka sani ba, da man dalilin da ya sa na kira ka wani saƙo zan ba ka zuwa ga Habibu sannan na kafa shaidata akan maganata da kai "

Alhaji Sheriff ya ma kasa magana Gwaggo ma ta dawo É—akin da man ta É—an fita ne, jin wayar da Alhajin yake yi yana rantsuwan bai sani ba sannan yana ambaton sunan Habibu ya sa ta tsaya ta kasa fita cikin zullumin abin da kuma ya sake faruwa.

"A cikin takardan sakin ya rubuta cewa da man ba son Ummu Salma yake yi ba, jikinta ne ya sa ya aurete kuma yanzu tunda ya gama moran abin da ya aura domin shi, shiyasa ya sake ta."
Baffa ya faɗa yana jin ƙuna a ƙasan zuciyarsa.

"Lailahaillallah."

Alhaji Sheriff ya faÉ—a cikin tsorata da lamarin Habibu.

"Sannan kuma ya ce cikin dake jikinta ba ya so, shi ya sa ya ce ta zubar amma ta yi taurin kai. To saboda haka ya bar mata cikin kar wata rana a danganta shi da cikin har abada"

"Wannan ne kuma bai isa ba ƙarya yake yi. Tunda har ya amince da cikin na shi ne to ko ya mutu ne sai an danganta shi da wannan cikin."

Alhaji Sheriff ya faÉ—a cikin fushi mai tsanani saboda ya fahimci Habibu ya raina musu wayau yana wasa da hankalin su.

"Ai ba a dole Alhaji tun da har ya ce ba ya so to ba wanda zai masa dole akan haka. Tunda har da kansa ya yi ikirarin cewa har abada kar mu danganta shi da cikin jikin Ummu, to nima Alhaji Hadi Baaba a matsayina na mahaifin Ummu Salma na yi alƙawarin ko bayan raina kar Habibu ya kusanto ni ko ya kusanto Ummu Salma ko abin da za ta haifa nan gaba kamar yadda ya haramta ma kansa dangantakar shi da cikin jikinta nima na haramta masa ya danganta kan shi da Ummu Salma ballanta cikin dake jikinta, ni da man uba na ke ga Ummu Salma har abada sannan zan sake zama uban abin da za ta haifa. Har abada bana son na sake ganin fuskar Habibu."

Baffa ya gama faɗa yana jin zuciyarsa na tsalle saboda ɓacin rai da baƙin ciki.

Alhaji Sheriff daga can bangaren ya ruɗe yana ƙoƙarin magana amma tuni Baffa ya katse wayarsa ya bar shi tsaye cikin  mutuwar jiki da nadama mai yawa.

"Alhaji me ya faru ne?

Gwaggo ta tambaya cikin tashin hankali.

"Habibu ne ya saki matarsa saki uku."

Ya ba ta amsa kai tsaye ai sai ta saka salati tana É—auka tana direwa.
"Wai ko Habibu ya fara shaye-Shaye ne?
"Babu abin da yake sha, kawai yaron ba shi da mutumci ne."
Ya faÉ—a yana ta neman lambar Habibu amma sai dai ta yi ta É—if É—if ba ta shiga.
Mahaifin Habibu na kwance yana jin duk abin da ke faruwa ba mgana amma hawaye sun taru a idanuwansa har suna kwaranya ta gefe da gefen idanuwansa.

"Uhm wallahi na yi nadamar shiga maganar auren Habibu. Ba ki ji kunyar da na ji ba, yau na ji kunyar Uba, nima fa uba ne ya zan ji in aka yi ma Æ´ata abin da Habib ya yi ma ta su Æ´ar?

Ya faÉ—a cikin bayyana takaicinsa lokaci É—aya yana saka wayarsa cikin aljihun rigansa.

"Bai kyauta ba, sam ba daÉ—i kai innalillahi ga shi saki uku ne ballanta a gyara lamarin."

"Ai ko saki É—aya ne ni da kaina zan ba ma mahaifinta shawaran kar ya mai da ma Habibu ita. Ballanta ya cika gudirinsa tunda da man ya ce ba sonta yake yi ba jikinta ya aura kuma ya gama mora shi ya sa ya sake ta."

"Eyye."

Gwaggo ta faÉ—a tana zare ido cikin mamakin Habibu.

"Haka mahaifinta ya ce ya rubuta a cikin takardan sakin. Sannan ya ƙara da cewa ba ya son cikin jikinta. Su kuma sun ce tunda ba ya so to su sun karɓa amma ya sani har abada ba shi da hurumin sake danganta kan shi da abin da ke cikin yarinyar."

"Ba za a yi haka ba Alhaji."

Gwaggo ta faÉ—a har ta fara hawaye.

"An ma yi. Domin hukuncin ya yi mini daidai ko ni ne a matsayin su wallahi tallahi abin da zan yi kenan."

"Alhaji k.."

"Ba sai kin roke ni ba, ai magana ta kare Aina'u Habibu ya fara komai kuma ya ƙarƙare komai. Saƙon da mahaifinta ya bani ne na sanar miki, in ya zo gidan ki isar masa."

Yana gama faɗin haka ya saɓa babbar rigansa zai fice daga ɗakin.

"Alhaji  ka tsaya ka ji don Allah.'
Chapter 50 · 0% Book details